NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan ya yi parking ta buɗe murfin Motar ta fito, shi ma ya biyo bayan ta ya fito. Ya zagayo inda take tsaye a jikin Motar ya kama hannunta yana kallon ta ya ce “Princess what happened?” Ta girgiza masa kai tana ƙoƙarin k’wace hannunta. Ya sakar mata hannun tare da matsowa daf da ya marairaice ya ce “I’m sorry Dear.” Ta sauke numfashi ganin kamar zai rungume ta, ta ce “Babu komai fa Uncle.” Ya ce “Sure?” Ta gyaɗa masa tana murmushi. Ya sauke ajiyar zuciya tare da kama hannunta suka nufi cikin gidan, ta yi ƙoƙarin k’wace hannun nata amma ya ƙi sakar mata. Mai aikin Mamy ce ta zo ta buɗe musu ƙofa bayan ya danna beil. Neehal ta samu ta k’wace hannunta ta bi bayan sa suka shiga cikin falon da sallama. Ahmad ya nuna mata kujera ya ce ta zauna, ta zauna, amma a ƙasa kan carpet. Ba jimawa Mamy ta fito daga ɗakinta mai aikinta da ta kira ta na biye da ita a baya. Da fara’a haɗe da murna Mamy ta ce “Sannu da zuwa yarinyar kirki, d’iyata ashe zan ƙara ganin ki?” Neehal ta yi murmushi cike da kunya ta gaishe da Mamy. Mamy ta amsa mata tare da rungume ta a jikinta cikin kulawa, tana tambayar ta su Mama. Neehal ta ce “Tanan nan lafiya, ta ce a gaishe ki.” Mamy ta ce “Ina amsawa.” Ahmad ya miƙe yana duban Mamy ya ce “Bari in je in dawo tunda yau bata ni kike ba.” Mamy ta ce “Sai ka dawo, ina ta murnar ganin Ƴata ina zan tuna da kai.” Ahmad ya ce “Shikenan ai.” Sannan ya kalli Neehal ya kashe mata ido ya ce “Sai na dawo Princess.” Bata iya ce masa komai ba saboda kunya har ya fice. Mai aikin Mamy ta kawowa Neehal abinci da drinks da su snacks. Mamy kam sai nan_nan take da Neehal. Da ƙyar ta tilasta mata ta tsakuri abinci cikin jin kunya. Mamy kam sai janta take da hira. Da lokacin Sallar la’asar ya yi ta kai ta bedroom ɗinta ta yi Sallah. Bayan ta idar ba jimawa Ahmad ya dawo gidan, ta fito suka tafi. Mamy ta bata leda mai ɗauke da turaruka da kayan shafe_shafe, shi ma dak’yar ta karɓa dan Ahmad ne ma ya karɓar mata. Kafin biyar sun ƙarasa gida, ta fito ta bar shi a Mota dan karɓo masa sak’on da Mama ta ce zata ba shi. Sai da ɗauko tsarabar data yiwa su Afrah sannan ta biya ɗakin Mama dan karɓar sak’on Ummi. Mama ta bata wata leda wadda bata san mene a ciki ba ta kay masa, ta buɗe bayan Motar ta ajiye sannan ta shiga cikin motar kamar yadda ya ce mata, tana shiga ya kulle motar sannan ya tasa ta a gaba da kallo, ganin lokaci yana tafiya ta ce “Uncle kar fa time ya ƙure baka tafi ba, kuma ka ce sai ka koma gidan Mamy kafin ka wuce airport.” Ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce “Ban gaji da kallon ki ba ko kaɗan Princess, kamar na d’aga tafiyar haka nake ji.” Ta juya masa ido ta ce “Ni dai nafi son ka tafi yau, saboda na san yanzu twins ɗina suna can suna damuwar rashin ganin ka two days.” Ya ɓata fuska ya ce “Kin fi son yaranki akaina kenan?” Tana dariyar tsokana ta ce “Eh mana.” Ya marairaice fuska kamar wani maraya ya tallafi fuskarsa da hannayensa biyu ya tsura mata ido. Ta ce “Me nene?” Ya nuna mata kanta da hannunsa, a shagwab’e ta ce “I’m sorry My Uncle.” Ya lumshe ido ya buɗe bai ce komai ba, seriously kamar ya fasa tafiyar saboda ita haka yake ji. Amma ya san hakan ba zai yiyu ba, saboda aikinsa da kuma yaransa da su Ummi. Ya duba agogon hannunsa sannan ya dube ta ya ce “Zan wuce Princess.” A sanyaye ta ce “Sai yaushe?” Dan itama ta fara jin ba daɗi saboda tafiyar da zai yi. Ya ce “Next week idan na samu chance, idan kuma ban zo ba sai upper week.” Ta ce “Amma zaka taho mun da Yarana in gan su ko?” Ya ɗan matso kusa da ita ya ce “Idan ma cewa kikai in dawo miki da su gurin ki gaba-ɗaya da zama zan iya Princess.” Ta kalle shi da sauri cikin mamakinsa, ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, ya ƙara da faɗin “In dai a kan farincikin ki ne Princess babu abun da ba zan iya ba.” Cikin murna ta ce “To ka dawo mun da su Please ka ji Uncle?” Ta yi maganar da iya gaskiyar ta har cikin ranta. Ya yi murmushi ya ce “An gama Princess, next zuwan da zan yi Insha Allahu zan taho miki da su da kayan su gami da komai na su.” Cikin jin daɗi ta ce “Thank you so much Uncle.” Ya ja dogon hancinta ya ce “You deserve everything from me my Baby.” Ta yi murmushi ba ta ce komai ba, ya kama hannunta tare yi mata pick a kuncinta, so romantic voice ya ce “Bye Princess I will miss you.” Ta lumshe idonta murya ƙasa_ƙasa ta ce “Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya.” Ya amsa da Ameen tare da sakar mata hannunta. Ta buɗe murfin Motar a hankali ta fito cikin sanyi jiki, bayan ta rufe ta d’aga masa hannu. Yana murmushi ya ce “I love You!” Ta juya da sauri ta nufi part ɗin Mama cikin matsananciyar kunyar sa, zuciyarta cike fal da murnar ya ce zai dawo mata da twins ɗinta su cigaba da zama a gurin ta……..✍️

A yi haquri da wannan hilis

By
Zeey Kumurya

[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣6️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………Mama tana kitchen tana girkin dare, Neehal ta shiga kitchen ɗin ta rungume Mama tana murmushin farinciki. Mama ta ce “Lafiyarki kuwa zaki zo ki ɗane mun jiki, ina cikin aiki?” Neehal ta bar jikinta cikin murna ta ce “Mama Uncle Ahmad ya ce zai dawo mun da su Afrah.” Mama tabar abun da take ta juyo ta fuskance ta, ta ce “Kamar ya fa?” Ta ce “Mama zai dawo mun da su, su cigaba da zama a gidan nan.” Mama ta ce “Uhm, na san Ahmad zai yi haka ne saboda da ke, ni kuma ba zan taɓa yarda da hakan ba, saboda Ahmad da Family ɗinsu sun fi mu buƙatar twins a kusa da su, especially ahalin mahaifiyarsu data rasu, tunda su suke kallo su ji daɗi a madadin mahaifiyarsu.” Neehal ta shagwab’e fuska ta ce “Mama wlh na yi kewar twins over, kawai ina daurewa ne saboda karki mun faɗa ki ce ina damuwa.” Mama ta ce “Nima ai na yi kewar su, sometimes ina zaune sai inga kamar za su zo su haye mun jikina kamar yadda suka saba, amma ya za mu yi dole mu haqura mu barwa danginsu su.” Neehal kamar zata yi kuka ta ce “To ai za suna zuwa gurin Family ɗin nasu akai_akai.” Mama ta ce “Sai kuma ki yi, amma ba dani za ai wannan son zuciyar ba.” Ta juya ta cigaba da aikin ta. Neehal ta matso jikin Mama kamar zata yi kuka ta ce “Ki yi haquri Mama idan ranki ya ɓaci, zan je masa ya fasa dawo su ɗin kawai.” Mama ta sassauta murya ta ce “Shikenan kar ki mun kuka, je ki ki huta idan na gama girki za mu yi magana.” Neehal ta ce “Bari in taya ki aikin.” Mama bata hana ta ba suka ci-gaba da aikin tare Mama na ƙara yi mata Ƴar nasiha akan rayuwa. Bayan Sallar isha’i suka yi waya da Sadik ya sanar mata sun isa ibadan lafiya. Ba su yi wata doguwar waya ba saboda Sadik ɗin yana tattare da gajiya yana son ya kwanta ya huta. Bayan sun gama wayar ta nufi part ɗin Daddy, two days ba ta je sun yi hira ba, da safe idan ta je gaisawa kawai suke saboda yana sauri zai fita. Sai da goma ta wuce Mama ta koro ta, ta ce hirar ta isa haka dare ya yi kuma. Bayan ta dawo ɗaki kamar zata kira Ahmad ta ji yaa ya sauka sai kuma ta fasa, ta kunna data kawai ta shiga media. Haka kawai ta ji Ameen ya faɗo mata a rai da yanayin data gan shi jiya na ɓacin rai, har tay bacci bai daina faɗo mata a rai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button