NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ta shiga har gidan Binta ta gaishe ta, Binta ta karɓe ta hannu bibbiyu duk da bata gane ta ba da farko, sai da Neehal ɗin ta mata bayanin kanta sannan ta gane ta. Cikin mamaki ta ce “Neehal ke ce? Kin canza gaba-d’aya ai shi yasa ban gane ki ba.” Neehal ta yi murmushi ta tambayi yaranta, tace mata duk suna nan k’alau. Binta ta gyara zama ta ce “Kin ga yanda Ubangiji ya yi da Fauziyya ko? Ko shakka babu alhakin ki ne ya fara bibiyarta, dan kaɗan ma ta fara gani. Umar ya ƙaro Aure da macen kirki Ƴar gidan manyan mutane da tarbiyya da ya gane Fauziyya ba matar k’warai ba ce. Gaba-d’aya ta canza shi ta mayar da shi mutumin k’warai, Fauziyya tay ta haukanta na kishi ta gama dan Umar ya watsar da ita a kwandon shara. Daga baya kuma da taga ba sarki sai Allah sai ta risina, tunda bata da inda ya fi nan ɗin, dan iyayenta ba ƙarfi gare su ba suma ta kansu suke, ita ce ma take taimakon su. Yarinyarta kuma Iman! kullum sai uban ya mata dukan tsiya akan yawon banzan da take, amma kamar ma ƙara tura ta yake, har ya gaji ya daina dukan nata ya koma yi mata addu’a. Da taimakon Hauwa (Amaryar Uncle Umar) an samu yarinyar ta ɗan rage yawon har tana zuwa makaranta yanzu. Amma Fauziyya kullum cikin yawo take da ita a unguwa tana faɗin Ita ta yiwa Ƴarta asiri ta lalace.” Neehal ta jinjina kai kawai zuciyarta babu daɗi akan rayuwar da Iman da jefa kanta a ciki. Gashi ita ba ci ta rasa ba balle ta ce wahalar rayuwa ce, Uncle Umar babu abun da baya yiwa iyalinsa na buk’atun rayuwa. Ta ɗan daɗe a gidan Binta kafin ta mata sallama ta fito bayan ta bata kuɗaɗen dake cikin jakarta duk da da ƙyar Bintan ta karɓa. Wajen ƙarfe uku ta ce zata tafi, amma Aunty Hauwa ta ce baza ta tafi ba sai ta jira Uncle Umar ya dawo sun gaisa. Haka ta zauna ba dan ranta ya so ba, dan bata san irin tarb’ar da zai yi mata ba. Can yamma kuwa sai gashi ya dawo, Aunty Hauwa ta sanar masa da zuwan Neehal. Abun mamaki sai Neehal ta ga yana murna da zuwan nata, tare yi mata magana cikin salama da kulawa. Ya zauna a falon Aunty Hauwa yana ta jan ta da hira, ya tambaye ta matakin karatun ta a yanzu da kuma sauran wasu abubuwan na rayuwa. Daga ƙarshe kuma ya mata maganar dukiyarta dake hannunsa, ita da yake ma babu abun da ta nema ta rasa a rayuwa tama manta tana da wata dukiya a gurinsa. Sai kusan Magriba ta baro gidan, sunyi_sunyi ta tsaya a yi Magriba kafin ta tafi amma ta ƙi, ta sanar musu Mama zata mata faɗa idan ta yi dare. Sai ga su Uncle Umar da Aunty Fauziyya rakiya har bakin Motar ana ta dashare mata baki.

Sai bayan Magriba ta ƙarasa gida, zuciyarta cike da zumud’in ta je ta bawa Mama labarin canzawar da Uncle Umar yay mata. A falon ƙasa ta tarar da Mama da Ameen har da Hafsah a zaune sune hira. Ta ƙaraso cikin falon da sallama. Suka amsa mata, Hafsat ta bi ta da kallo cikin tsananin tsanar ta, Ameen kuwa bai ko d’ago ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake ta aikin latsawa. Mama ta ce “Sai yanzu.” Ta ce “Eh Mama, sai da na jira Uncle ɗin ya dawo muka gaisa.” Mama ta ce “Kin kyauta kuwa, suna nan k’alau dai?” Ta ce “Lafiya k’alau suna gaishe ki.” Ta mai da dubanta ga Ameen ta ce “Yaya Ina yini.” Ciki_ciki ya amsa da faɗin “Lafiya.” Ta mayar da duban ta ga Hafsat itama ta gaishe ta. Hafsah ta amsa da fara’ar munafurci akan fuskarta, har da tambayarta ya aiki. Ko zama bata yi ba ta wuce upstairs dan yin sallar dake kanta. Ameen ya bi ta da kallo ta ƙasan ido. Bayan 10 minutes ya miƙe ba tare da ya kalli inda Mama da Hafsah suke ba, ya bi bayan ta upstairs ɗin………✍️

A yi haquri da typing error, ban yi edit ba ne.

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣7️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………Idar da Sallar ta kenan ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo. Ta juyo da sauri dai_dai lokacin da ya yi Sallama a can ƙasan mak’oshinsa. Ta amsa masa cikin nazartar yanayin sa. A hankali ta ce “Yaya!” Ya amsa mata da ido ba tare ya yi magana ba. A hankali kuma ya fara takowa ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta tare da zuba mata narkakkun idanunsa da suke a lumshe. Ta yi ƙasa da kanta gabanta na fad’uwa saboda fargaba, a tunaninta wani laifin ta yi ya zo ya yi mata masifa kamar yadda ya saba. Ji ta yi Gaba-d’aya ta takura da kallon da yake bin ta da shi, sai cukuikuye hannuwanta take a cikin hijabin dake jikinta. Ta d’ago kanta ma ta dube shi ta kasa, ga k’amshinsa kamar ƙara buɗe mata kofofin hancinta a kai saboda yanda take jin sa. “From where are you?” Ta ji muryarsa a ɗan zafafe yana tambayar ta. Ba tare data yi wani k’wakwk’waran motsi ba ta ce “Gidan Uncle Umar.” Ya yi shiru na wasu sakanni kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce “Mene haɗin ki da wannan guy ɗin?” Ta d’ago ta kalli fuskarsa cikin rashin fahimta ta ce “Wanne guy ɗin Yaya?” Ya ɗan taune lip ɗinsa ya ce “Baban twins kika ce ko wanene ma oho? Ya yi maganar irin i don’t care ɗin nan. Ta ɗan yi murmushi ta ce “Oh Yaya wai Uncle Ahmad kake nufi?” Ya kalle ta kallon mamakin Uncle data kira Ahmad da shi. Ya ce “Eh shi.” Ta girgiza kai tana kifkifta idanuwa ta ce “No.. nothing.” Ya wurga mata wani kallo ya ce “Tarbiyyar da Mama ta yi miki kenan ki dinga tsayawa wani k’ato yana riƙe miki hannu ko?” Ya ƙarashe maganar a ɗan tsawace. Ta tsorata sosai dan bata taɓa tunanin ya ga lokacin da Ahmad ya riƙe mata hannu ba. Ya sassauta murya ya ce “Why Miemerh? Idan da Mama ta fito a time ɗin fa Me zaki ce mata?” Jikinta ne ya yi sanyi ta rasa me zata ce, tabbas da ace tsautsayi ya sakko da Mama ta ga sanda Ahmad ya riƙe mata hannu da kashinta ya bushe a gurin Maman, tunda ta sha nusar da ita akan illar hakan ga ƴa mace. Sai ta ji haushin kanta dana Ahmad ɗin ya cika mata zuciya. Zata yi magana kenan suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Mama ce ta shigo, ta dubi Ameen ta ce “Me kake yi anan?” Ya miƙe ba tare da ya yi magana ya nufi ƙofa, Mama ta matsa masa ya fice tana bin sa da kallon tuhuma. Ta mayar da duban ta ga Neehal bayan ya fice ta ce “What happened?” Cikin rashin gaskiya ta ce “Nothing.” Mama ta tab’e baki ta ce “Ku kuka sani.” Sannan ta juya ta fice. Neehal ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idonta, haka kawai ta ji wata irin kunyar Ameen ta rufe ta, yanzu bata san irin kallon da yake mata ba a cikin ransa na ganin Ahmad ya riƙe mata hannu. Ta yiwa kanta alƙawari ba zata ƙara bari haka ta faru ba. Tunda dama hakan bai taɓa faruwa a gare ta da wani ɗa namiji ba sai Ahmad ɗin, shi ma dan tana masa kallon kamar jininta ne, kuma ta san ba da wata mummunar manufa yake riƙe mata hannun ba.

Hafsah ta cika ta yi fam kamar zata yi bunduga saboda baƙin cikin bin bayan Neehal da Ameen ya yi, a haka ya sakko ya same ta. Ta yi saurin ɓoye ɓacin ranta ta k’ak’alo murmushi ta ce “Baby har ka sakko.” Ya zauna a kusa da ita cikin kulawa ya ce “Eh, bari na je na yi sallah, idan na dawo sai mu wuce gida ko? Ta ce “Ai na ɗauka a nan zamu kwana.” Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Ta yi murmushi cikin ranta tana jin wata irin k’aunarsa na ƙara cika mata zuciya. Ita kanta ta san ta yi dace da mijin kere sa’a, dabi’un Ameen suna bala’in burge ta, more especially muskilancinsa yana bala’in tafiya da imaninta. Yana ɗaya daga cikin abun da ya ja hankalinta a kansa, gashi ya iya kula da mace, ta tabbatar za a bashi lamba ɗaya a wannan fannin, ta san sai a tara maza ɗari kafin a samu wanda iya tarairayar mace da nuna mata tsantsar k’auna kamar Ameen ɗinta. Ya miƙe ya fice daga falon, ta bi shi da kallo. Komai nasa kyau yake mata, tafiyarsa ma kaɗai abun burgewa ce. Tana son Ameen over shi yasa bata son ɓacin ransa ko kaɗan, duk abun da ta san zai ɓata masa rai ko yaya ne gudun shi take. Shi yasa take danne duk abun da take ji a ranta a duk lokacin data gan su tare da Neehal, dan ta san bata isa ta nuna masa ɓacin ranta ba akan haka. Ta tsani Neehal over, tsanar da ita kanta bata san adadinta ba, tun lokacin data samu labarin ba su Mama ne suka haife ta ba ta ji yarinyar gaba-d’aya ta fice mata a rai.. Maganar Mama data dawo falon ne ya katse mata tunanin da take. Mama ta ce “Au Ameen ɗin fita ya yi?” Hafsah ta ce “Eh ya je masallaci.” Mama ta ce “To mu je sama kema ki yi Sallar, na ji an fara kira.” Hafsah ta miƙe ta bi bayan Mama. Bayan ta idar da Sallah Mama ta kawo mata abinci, tana cikin ci Ameen ya dawo gidan. Neehal kuwa tana ɗakinta ta ƙi fitowa, har sai da ta tabbatar sun bar gidan sannan ta fito falo. Anan ta tarar da Mama, ta zauna a kusa da ita ta shiga bata labarin zuwan ta gidan Uncle Umar. Cikin farin ciki Mama ta ce “Masha Allah, na ji daɗin wannan labarin, dama kullum fata na da addu’a ta Allah ya waiwayo da hankalin danginki gare ki, ku dinga zumunci kamar kowan ne ahali.” Neehal ta ce “Nima Mama na ji daɗi sosai, ba ki ga yanda Uncle Umar yake mun magana ba, cikin kulawa kamar ma kunya ta yake ji akan abubuwan da yay mun a baya.” Mama ta ce “Haka muke so dama, Allah ya ƙara shirya mu ya nuna mana gaskiya da sani akan abubuwan da muke aikatawa ba dai_dai ba.” Neehal ta ce “Ameen.” Mama ta ce “Ki je ki ci abinci, bari na je part ɗin Daddy.” Neehal ta ce “Toh.” Tare da miƙewa, ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta ta kira Uncle Usman ta sanar masa sauyawar da Uncle Umar yay mata. Daren yau ba su yi waya da Ahmad ba, tana ganin yana kiran ta ƙi pick. Washegari da safe ma tana ganin kiran sa lokacin tana gurin aiki shima ta ƙi ɗauka. Bayan Magriba Sadik ya zo gidan kamar yadda ya saba zuwa, sun jima suna hira a gurin da suka saba zama. Har yake mata zancen shi kam zai turo iyayensa a yi maganar aurensu ya matsu ya ganta a cikin gidansa a matsayin matarsa ta sunna. Cikin jin kunya ta ce masa babu matsala zata yiwa Mama maganar idan ta koma ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button