NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan Sallar isha’i Mama tana falon sama tana kallo wayarta dake hannun kujerar da take kai a zaune ta fara ringing. Ta ɗauko ta duba tare da d’agawa ganin Aunty A’isha ce ke kiran. Ba tare da gaisuwa ba Aunty A’isha ta ce “Adda Fateemah! Yanzu Mai_gidan su Abban Neehal ya kira ni ya sanar mun cewar an samu nasarar kama mutanen da suka kashe Abban Neehal ɗin da Ummanta……..✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣8️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

Ku yi haquri da rashin ganin update akan lokaci, kun san an ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi.

……….Cikin hanzari mai nuni da tsantsar mamaki Mama ta tari numfashin Aunty A’isha da faɗin. “Da gaske A’isha?” Aunty A’isha ta ce “Dagaske mana Adda, shi Alhaji Alin ne tun bayan rasuwar su Abban Neehal ba jimawa ya kamu da rashin lafiya, aka fitar da shi Saudiyya ake masa magani. Ashe duk wannan shekarun da suka wuce abun yana ransa, sai a ƴan watannin da suka wuce ya samu lafiya ya dawo Nigeria. Shine yana dawowa yasa aka duk’ufa da binkicen waɗanda suka yi kisan a lokacin da ya samu labarin har yanzu ba’a gano su ba. Yanzun nan shi ya kira ni da kansa muna gama waya da shi na kira ki, ya sanar mun cewa tunda ya dawo ƙasar nan yake neman mu, amma bai samu labarin inda muke ba, sai daga baya tunanin ya je gadon ƙaya inda muka zauna ya zo masa, to a wurin wata mak’ociyarmu aka samo masa Number ta.” Mama ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin “Alhamdulillah, Allah mun gode maka, yanzu ya ake ciki game da waɗanda suka yi kisan? Ya sanar miki ko su waye suka yi?” Aunty A’isha ta ce “A’a bai sanar mun ba, ya dai ce mun suna hannun Police a halin yanzu, ranar Monday za’a shiga kotu a yanke musu hukunci tunda sun amsa laifunsu, sauran bayani kuma ya ce sai mun haɗu.” Mama ta ce “Ki ji wani ikon Allah A’isha, shekara fiye da goma sai yanzu Allah ya toni asirinsu, Allah ya ƙara tona asirin duk wasu masu laifi a cikin duniyar nan.” Aunty A’isha ta ce “Ameen ya Allah, wallahi adda ba ki ji yanda na ji daɗi ba, Alhaji Ali ya cika ubangida na gari da ya tsaya tsayin daka ganin jininsu Abban Neehal bai tafi a banza ba.” Mama ta ce “Allah ya saka masa da Alkhairi ya biya shi da gidan Aljannah.” Aunty A’isha ta ce”Amin ya Allah, ya ce akai masa Neehal yana son ya gan ta.” Mama ta ce “Aiko bai faɗa ba dole mu je har gida mu yi masa godiyar wannan jajircewar da ya yi, gobe gobe ma Insha Allahu za mu je, a wacce unguwa yake da zama?” Aunty A’isha ta ce “A rijiyar zaki, ya turo mun da address ɗin gidansa ta message.” Mama ta ce “To Insha Allahu da safe za mu je, bari in je in sanar da Daddy wannan abun al’ajabi da farincikin.” Aunty A’isha ta ce “Tom shikenan da safen zan biyo ta nan sai mu wuce, nima bari in je in sanar da Abban Maryam, in kira Sadiya itama in sanar mata.” Mama ta ce “Allah ya kai mu goben, sai mun yi waya.” Daga haka suka yi sallama.

Mama ta dafe kanta tana sauke numfashi, zuciyarta cike da d’oki da zumud’in jin asalin zancen, domin ta san wa ya kashe su Abba ko kuma wa ya turo a kashe su, da kuma son sanin ko mutum ɗaya ne ya yi kisan su Abba da su Anwar? A ɓangaren Aunty A’isha itama tunanin da take yi kenan. miƙewa Mama ta yi ta nufi part ɗin Daddy cikin sauri dan ta sanar masa halin da ake ciki.

Cike da mamaki da kaɗuwa Daddy yake duban Mama bayan ta gama sanar masa da abun da yake faruwa. Zuwa can ya nisa ya ce “Allah buwayi gagara misali, dama an ce duk wanda yay kisan kai da wuya ya mutu Ubangiji bai toni asirinsa ba, saboda haqqin rai ba ya taɓa barin mutum ya zauna lafiya a duniya.” Mama ta ce “Wannan haka yake, Allah ka raba mu da mummunar ƙaddarar da zata kai mu ga dana sani, su kuma azzaluman mutane irin waɗannan Allah ka cigaba da tona musu asiri!” Daddy ya ce “Amin Amin Doctor.” Mama ta cigaba da magana. “Mutum bai ji ba bai gani ba kawai saboda rashin imani a zo har cikin gidansa a kashe shi saboda neman duniyar da kowa sai ya bar ta, mutane ba sa tuna Allah a ransu, ba sa tunanin inda suka kashe mutum ya je suma komai daren dad’ewa za su je.” Cikin jimantawa Daddy ya ce “Ai ke dai ki bar mutum kawai Doctor, amma in dai duniya ce gata nan ta ishi kowa, kuma Duk abin da mutum ya shuka dai shi zai girba , walau na sharri ko na Alkhairi.” Sun zanta akan al’amarin sosai sannan Mama ta miƙe dan zuwa ta sanar da Neehal itama.

Tana kwance ruf da ciki akan gadonta, system ɗinta na gabanta tana latsa ta cikin kwarewa, idanunta sanye da siririn glass mai ɗan duhu, wanda bata fiya amfani da shi ba, sai irin wannan lokacin idan zata yi using system. Mama ta shigo ɗakin tare da zama a bakin gadon bayan ta yi sallama. Neehal ta amsa mata tare da tashi zaune ta cire glass ɗin fuskarta ta ajiye a gefen ta. Mama ta ce “Aikin ne har yanzu baki gama ba.” Ta ce “Na kusa ƙarasawa saura kaɗan, zuwan Uncle Ahmad ne ma ya tsayar da ni.” Jinjina kai Mama ta yi tare da juyowa ta fuskance ta sosai ta ce “D’azu Auntinki ta kira ni take sanar mun an kama waɗanda suka kashe su Ummanki.” Neehal ta waro Ido waje cikin kaɗuwa ta ce “Su waye Mama?” Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Aunty A’isha ta sanar mata. Kuka ta saka cikin kukan take faɗin “Mama me su Umma suka musu da suka kashe su? Su waye waɗannan mutanen da suka raba ni da mahaifana rabuwa ta har abada a rana ɗaya? Me nay musu suka zaɓi mayar da ni marainiya?” Kuka take sosai mai ban tausayi, mutuwar su Umma ta dawo mata sabuwa fil a cikin ranta, duk da a lokacin da suka rasu tana ƙarama amma har yanzu gawar iyayenta kwance cikin jini bata daina hango ta acikin idanunta ba, kuma har ta koma ga mahaliccinta ba zata taɓa mantawa ba. Mama ta rungume ta a jikinta cikin tsananin tausayinta, tare da rarrashinta da kalamai masu taushi har ta samu ta bar kukan. Mama ta d’ago ta tana share mata hawaye ta ce “Komai rubutacce ne daga Allah, Ubangiji ya riga ya tsara rana ɗaya Umma da Abba za su rasu kuma a lokaci ɗaya, ko da waɗan can Mutanen ba su kashe su ba idan kwanan su ya ƙare dole su bar duniya. Dan haka addu’ar mu kawai suke buƙata a halin yanzu, ita ce kawai soyayyar da za mu nuna musu. Mutuwa dole ce Neehal, mu ma nan zaman jiranta muke, fatanmu Allah yasa ta zo mana cikin sauqi.” Cikin matuƙar sanyin jiki Neehal ta ce “Haka ne Mama, Allah ya ji k’an Umma da Abba da ma dukkan musulmin da suka riga mu gidan gaskiya, mu kuma Allah yasa mu cika da imani.” Mama ta ce “Ameen dan darajar Annabi.” Lumshe idonta ta yi bata kuma cewa komai ba, cikin zuciyarta kuwa ji take dama a bata dama ta kashe azzaluman mutanen da suka kashe mata iyaye da hannunta, saboda wata muguwar tsanar su data cika mata zuciya. A hankali ta yi baya ta kwanta akan gadon saboda sarawar da ta ji kanta ya yi mata lokaci ɗaya. Mama ta janyo system ɗin da take amfani da ita ta yi saved na aikin da take sannan ta kashe ta, ta ɗora ta akan bedside locker. Shafa fuskar Neehal ta yi cikin raunin zuciya da tausayinta, cikin kulawa ta ce “Ki yi addu’a idan kina jin zuciyarki babu daɗi ba wai ki yi kuka ba, idan kin kasa barci kar ki kwanta ki yi ta tunane_tunane, ki tashi ki kaiwa Allah Kukanki.” Ta gyaɗa mata kai ba tare data buɗe idonta ba. Mama ta kashe mata light ɗin ɗakin sannan ta fice zuciyarta babu daɗi. Iyayenka ko da ace baka san su ba kana jariri suka rasu idan ka girma aka baka labarinsu dole ka ji feeling a kansu da son kasance tare da su, balle ita da tana da ɗan wayonta suka rasu, dole abun ya dinga taɓa mata zuciya. Kuma da a ce mutuwa suka yi kamar kowa ba kashe su a kay ba, abun ba zai dinga damun ta over ba. Amma yanzu gani zata dinga yi kamar da ba’a kashe su ba da suna raye har yanzu….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button