NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Washegari kafin ƙarfe goma sha ɗaya na safe sun gama shiryawa dan zuwa gidan Alhaji Ali, Neehal dai kamar mai cuta komai a sanyaye take yin sa. Daren jiya kam ko wayar love ɗin data saba bata iya yi ba, da ta tashi da safen nan ma ko bi takan wayar bata yi ba. Sai da Mama ta ce mata ta kira gurin aikinsu ta sanar musu ba zata samu damar zuwa yau ba sannan ta ɗauki wayar. A time ɗin ne ta ga missed call ɗin Sadik, Ahmad har ma da Ameen wanda kiran nasa ya bata mamaki. Ahmad kam har da text yay mata ya sanar mata ya wuce Abuja, dama tun jiya ya faɗa mata da sammako zai yi ya koma. Bata bi kiran ko ɗaya daga cikinsu ba saboda tana cikin mood ɗin da ko doguwar magana bata son yi.

A lokacin itama Aunty A’isha ta ƙaraso gidan, bayan sun gaggaisa suka rankaya suka tafi a Motar Mama wanda direban Maman ne zai kai su. Suna tafe suna ƙara jimanta al’amarin a tsakanin su. Neehal dai ta yi shiru kawai tana sauran su. Aunty A’isha ta dube ta, ta ce “Daughter baki da lafiya ne?” Mama ce ta bata amsa da faɗin “Tun jiya dana faɗa mata zancen nan shine duk ta koma haka.” Aunty A’isha da itama dauriya kawai take dan mutuwar tsohon Mijin nata da abokiyar zamanta ta dawo mata sabuwa a ranta. Ta kwantar da kan Neehal a ƙafaɗarta bata ce komai ba. Mama ta ce “Na kira Hajiya na faɗa mata, ta ce zata zo kafin Monday a yi zaman kotu da ita.” Aunty A’isha ta ce “Allah ya kai mu, ya kuma sa a ƙarƙare shari’ar a ranar, kin san shari’ar ƙasar nan tsaf zasu iya cewa sun d’age shari’ar.” Mama ta ce “Ai tunda waɗanda suka yi laifi sun amsa babu buƙatar wani jan magana na daban, hukunci kawai za’a yanke musu dai_dai da abun da suka aikata.” Aunty A’isha ta ce “Haka muke fata dama.” Bayan sun ƙarasa gidan Alh Ali Aunty A’isha ta kira shi ta sanar masa, ɗaya daga cikin ma’aikatan gidansa ya aiko ya shigar da su. A wani babban falo aka sauke su, dattijuwar matarsa ta karɓe su hannu bibbiyu dan ta san da zuwan nasu. Alh.Ali ya yi mata bayanin komai. Kuma ta shaida fuskar Aunty A’isha dan kafin Abba ya rasu suna ɗan zuwa tsohon gidansu idan abu ya samu. Tana ganin Neehal ta ce “Wannan yarinya kamar an tsaga kara ita da mahaifiyarta.” Da kanta ta musu jagora har falon Alhaji Ali. Yana zaune shi kaɗai a falon yana kallon labarai suka yi sallama, ya amsa musu cikin sakin fuska. Suka ƙarasa suka zauna matar tasa ta ce “Ga iyalan Alh.Muhammad sun ƙaraso.” ya yi murmushi yana duban Neehal ya ce “Masha Allah, wannan ce Amaryar tawa?” Suka yi murmushi dukan su, Neehal ta ƙarasa ta tsugunna a gabansa ta gaishe shi. Ya amsa mata cikin fara’a da kulawa, su Mama ma suka gaishe shi, ya amsa musu. Aunty A’isha ta ce “Ya jiki kuma Alhaji? Ashe cuta ka sha Wlh ba mu da labari.” Ya nuna ƙafarsa ya ce “Ciwon Ƙafa ne ya sako ni a gaba, na fi shekara biyar a zaune bata takuwa, kuma tunda muka je Saudiyya ake ta maganin, sai yanzu Ubangiji ya kawo sauqi.” Mama ta ce “Subhallahi, Lallai kasha jinya Alhaji, Allah Ubangiji ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne.” Suka amsa da “Ameen.” Ya dubi Aunty A’isha ya ce “Ya ƙarin haquri rashin su Alhaji Muhammad, tun bayan rasuwar su ba mu ƙara haɗuwa ba, na samu labarin ma kin yi aure.” Aunty A’isha “Haquri Alhamdulillah, ai tun bayan dana gama takaba na yi aure.” Ya ce “Masha Allah, Allah ya raya zuri’a ya ƙara haqurin zama da juna. Su kuma Alh. Muhammad Ubangiji Allah ya ji k’ansu ya gafarta musu.” Suka amsa da Ameen gaba_ɗaya. Daga nan suka shiga tattaunawa akan abun da ya kawo su. Inda Alhaji Ali ya sanar musu da cewa. “Bayan ya dawo daga Saudiyya ne ya bibiyi al’amarin, inda aka tabbatar masa har yanzu ba a gano wand’anda suka yi kisan ba, hankalinsa ya tashi ya dinga faɗa akan rashin tsaurarara bincike na ƙasar nan da ba’ayi, sannan ya saka lauyoyi da jami’an tsaro su binkito masa. To ana cikin haka ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kisan su Abba ya fito daga gidan yari bayan shekaru takwas daya shafe a gidan yarin, bisa laifin fashi da makami da aka kama shi da shi, dama irin ƴan daban nanne da masu kuɗi da ƴan siyasa suke amfani da su dan cimma wata buƙata ta su, daga zarar buƙatar tasu ta biya kuma da su da banza duk ɗaya ne a gurinsu. Bayan ya fito ya nemi wanda sukay kisan su Abban tare wanda shine yakasance kamar babbansu a jan ragamar aikin, ya buk’aci daya ba shi cikon kuɗin aikinsa, shi kuma wancan ɗin sai ya hana shi ya ce ya cinye. To saboda baƙin cikin cinye masa kuɗin da aka yi shine ya ɗauki alwashin sai ya tona musu asiri in ya so kowa ya rasa duk a kama su. Da kansa ya kai kansa Police station ya faɗi laifinsa, aka kuwa yi ram da shi nan take, sannan ya faɗi inda sauran biyun suke su ma aka je aka kamo su. Da farko su sun musa, amma da suka ji duka sai suka fadi gaskiya, suka ce tabbas su sukai kisan amma su ma wani mutum ne ya ba su kwangilar yin kisan. Yanzu haka suna Bamfai a tsare, Ranar Monday Insha Allahu za’a yi shari’ar a babbar kotun jiha, dan yanke musu hukunci dai_dai da abun da suka aikata. Sai dai har yanzu sun ƙi faɗar wanda ya saka su aikin, dan su yaran biyun dama ba su san shi ba, babban nasu ne ya san shi. Amma ana saka rai Insha Allah za su faɗi koma waye a zaman kotu, lauyoyinmu suna ta faɗi tashi akan haka. Na samu duk wannan bayanan ne ta bakin amintaccen lauyana wanda shi ne lauyan da zai tsaya a gaban kotu a matsayin lauyan iyalan Alhaji Muhammad Gabasawa dan ganin kotu ta bi musu hak’k’in su.” Sai bayan Azhar su Neehal suka baro gidan nasa zuciyoyinsu cike da al’ajabi.

Ranar Asabar sai ga Hajiya ta zo Kano kamar yadda ta faɗa. Kwanakin nan da zazzaɓi mai zafi Neehal ta yi su, dan ko falo bata iya takowa ba tana kwance, ko toilet zata sai Mama ta taimaka mata. Ranar Monday ranar shiga kotu ta tashi jikin nata da ɗan dama, har ta yi wanka da kanta ta shirya. Daa Mama ta ce ta zauna a gida ba sai ta je court ɗin ba, amma ta ce zata iya zuwa ai ta ji k’warin jikin nata. Ƙarfe tara da ƴan’mintuna suka bar gidan gaba-ɗayansu har su Dije da Daddy zuwa court, dan ƙarfe goma za’a saurari ƙarar. Duk wannan abun da yake faruwa Ahmad da Sadik ba su sani ba dan Neehal bata sanar da su ba, tunda ko waya bata yi da ɗayan su ba saboda rashin lafiyar da take. Idan sun kira ta Mama ce take d’agawa. Sadik ya zo har sau biyu ya duba ta, Ahmad ma ya zo sau ɗaya ranar Sunday. Mama ta ce masa, dama bai wahalar da kansa ya zo ba tunda yana da nisa kuma dududu kwanansa uku da barin garin. Ameen kuwa tun ranar Friday da ya dawo garin every morning and night sai ya zo ya duba ta….

Ƙarfe goma dai_dai court ta cika ta tunbatsa da mutanen Daddy da suka samu labari da mutanen Alhaji Ali gami da wasu daga cikin abokan Abba, sai ƴan jarida da sauran mutane, har da su Uncle Umar da iyalansa da Kawu Musa. Uncle Usman ne bai samu damar zuwa ba. Shigowar Alk’ali yasa kotun yin tsit daga hayaniyar dake tashi a cikin ta, hakan kuma ya yi dai_dai da shigowar jami’an tsaro da waɗanda ake ƙara akan laifin kisan su Umma……..✍️

Page ɗin yau bana soyayya ba ne, bare a cika mana kunne da team ɗin anace dana k’anin kurma.????‍♀️????

By
zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣9️⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button