NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………..Bayan Alk’ali ya zauna a mazauninsa aka miƙo masa wani ɗan abun rubuta da pen. Bayan 2 minutes wani mutum ya miƙe ya ɗan rankwafawa ya yi gaisuwa ga Alk’ali sannan ya fara karanto takardar dake hannunsa kamar haka “Zamu saurari shari’a ta gaba akan gisan gillan da wasu mutane suka aikata wa marigayi Alhaji Muhammad Gabasawa tare da mai ɗakinsa, shekara goma sha ɗaya da watanni da suka wuce.” Sannan ya koma ya zauna. Neehal ta lumshe idonta bayan ta gama ƙarewa wadanda suka yi kisan kallo, zuciyarta na mata k’una. Barrister Murtala Gaya (Lauyan Alhaji Ali) ya miƙe ya kai gaisuwa ga Alk’ali sannan ya fara magana. “Sunana Barrister Murtala Gaya, Ni ne lauyan masu ƙara, ina roƙon wannan kotu mai adalci da ta yankewa waɗan nan azzaluman mutanen da suka yiwa Alhaji Muhammad Gabasawa da mai ɗakinsa gisan gilla hukunci dai_dai da abun da suka aikata.” Ya rank’wafawa ya ce “Na gode ya mai girma mai shari’a.” Alk’ali ya ɗan yi rubuce_rubuce sannan ya d’ago ya dubi mutane ya ce “Ko akwai lauyan da yake kare masu ƙara?” Wani Barrister ne ya miƙe cikin girmamawa ya ce “Eh akwai ya mai girma mai shari’a. Sunana Barrister Garba Dan_ladi, nine lauyan dake kare waɗanda ake ƙara.” Sannan shi ma ya ɗan rank’wafawa ya ce “Na gode ya mai girma mai shari’a.” Sannan ya koma ya zauna. Barrister Murtala Gaya ya miƙe a karo na biyu yana duban Alk’ali ya ce “Ya mai girma mai shari’a ina son zan yi magana da waɗanda ake ƙara.” Alk’ali ya ce “Kotu ta baka dama.” Ya rank’wafawa ya ce “Na gode ya mai girma mai shari’a.” Sannan ya yi fito daga gurin da yake ya ƙarasa inda masu laifin suke ya ɗan kare musu kallo na wasu sakanni sannan ya ce. “Kotu tana son sanin sunayenku da kuma yanda kuka gudanar da kisan kai ga Alhaji Muhammad Gabasawa da iyalinsa, tare kuma da son sanin wanda ya turo ku aikata hakan.” Da sauri Barrister Garba ɗan ladi ya miƙe ya ce “Ina da ja ya mai shari’a, bai kamata Barrister Murtala ya dinga tambayar waɗanda ake ƙara wanda ya turo su aikata laifin da sukay ba, saboda ba don haka ake zaman wannan kotun ba.” (Da alama dai wanda ya turo a kashe su Abba shine ya ɗauki Barrister Garba.) Barrister Murtala ya tari numfashinsa da faɗin “Dole ne in musu wannan tambayar ya mai girma mai shari’a, saboda waɗanda ake ƙara sun sanar da jami’an tsaro cewar turo su akay, amma sun ƙi faɗar ko waya ne, da alama an musu babban gargadi’ ko barazana mai tsoratarwa. Mu kuma muna so mu sani saboda shi ma a nemo shi a duk inda yake a hukunta shi.” Alk’ali ya dubi Barrister Garba ya ce “K’orafi bai karbu ba Barrister Garba.” Ya mayar da dubansa ga Barrister Murtala ya ce “Barrister Murtala cigaba da tambayarka kotu na sauraren ka.” Ya yi murmushi ya ce “Na gode ya mai girma mai shari’a.” Sannan ya ƙara maimaita tambayar da ya yi wa waɗanda ake ƙara. Ɗaya daga cikinsu ya ce “Sunana Hakim ilyasu.” Sai babban nasu shi ma ya ce “Sunana Bilyaminu saminu.” Na ƙarshen kuma ya ce “Sunana Zakari Mu’azu.” Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce “Kotu tana sauraren ku, Malam Zakari da Bilyaminu da Hakim.” Wanda ya fara faɗar sunansa wato Hakim ya ce “Watarana muna zaune da yamma ni da abokina Zakari……ya nuna Bilyaminu sannan ya cigaba da magana. Bilyaminu ya zo ya same mu a kan yana so zamu yi wani aiki tare da shi, ya tabbatar mana da za mu samu kuɗi mai tarin yawa a wannan aikin, cikin zumud’i muka ce masa za mu yi ko wanne irin aiki ne. Da farko da ya sanar mana aikin kisan kai ne mun tsorata, muka ce gaskiya baza mu iya ba, domin ba mu taɓa aikata hakan ba, iyakacinmu k’wace da haurawa gidan mutane, ko kuma raka irin su Bilyaminu fashi da makami. Amma Bilyaminu ya nuna mana ruwan kuɗi ya ce, mutumin da zamu yiwa aiki hamshaqin mai kuɗi ne, zai ninka mana kuɗin da muka gani a gurin Bilyaminu sau goma. Nan fa muka ruɗe mun ji zamu kuɗi, muka je mun amince amma fa muna tsoron kar a samu matsala. Bilyaminu ya ce babu matsalar da za’a samu, koma da an samu wanda ya samu aikin zai tsaya mana dan Babba ne a ƙasar nan, dan haka mu kwantar da hankulanmu babu abun da zai faru. Da jin wannan batu sai muka amince.” Hakim ya ɗan numfasa, Barrister Murtala ya ce “Dama already kum san shi Bilyaminun ne kuna da alaƙa dashi?” Hakim ya ce “Ehh, babba ne shi a daba kuma kamar oga yake a gurin mu.” Barrister Murtala ya jinjina kai ya ce “Cigaba kotu na saurarenka ka sanar mata yanda kuka gudanar da kisan.” Hakim ya cigaba da magana. “Tun a ranar Bilyaminu ya fara ba mu kuɗaɗe masu kauri, ya ce sauran kuma sai aiki ya kammala zai ba mu. Muka amince cike da k’warin gwiwa da murnar za mu samu kuɗaɗe. Bayan kwana biyu da daddare Bilyaminu ya zo ya ɗauke mu a wata Mota shida wasu mutane guda biyu, gaba-ɗayansu fuskokinsu a rufe da baƙin k’yalle. Wani ɗan gida ya kai mu ya ba mu wasu kaya bak’ak’e muka saka a jikinmu tare da baƙin k’yallen muma muka ɗaure fuskokinmu. Sannan ya bamu bindigu muka zira a aljihun wandunanmu. Bayan dare ya tsala muka fita a wannan Motar zuwa gidan mutumin da muka kashe, ta bayan gidan Bilyaminu ya yi parking motar muka fito ya buɗe ƙofar dake bayan gidan muka shige, shi ya yi mana jagora har cikin ɗakin baccinsu. Dama Bilyaminu ya sanar mana za su yi magana da mutanen, idan sun amince da buƙatarsa wadda ba mu san ta mene ba kar mu yi musu komai, idan kuma mun ji sun yi gardama mu sakar musu harbi. Bayan ya gama rad’a musu maganar da zai faɗa musu muka ji mai gidan cikin ƙaraji yana cewa ba zai taɓa amincewa da buƙatar su ba, da ido Bilyaminu yay mana inkiya. Babu jira ni da Zakari muka sakar musu bullet bibbiyu a ƙirjinsu, Bilyaminu ya ƙara musu ɗai_ɗai. Sauran mutum biyun da su zo ɗaukar mu tare da Bilyaminu waɗanda ba mu san su ba, su ba su yi harbin ba. Suna dai tsaye riƙe da bindigu a hannunsu. Mu ukun nan mu kai kisan.” Ya yi shiru yana jan numfashi. Neehal ta runtse idanta hawaye mai zafi na zuba daga cikinsu. Aunty A’isha ma runtse idanunta tay tana tuno sanda ta ji ƙarar harbin a cikin kunnenta. Hajiya kuwa tsinuwar Allah take ja musu a cikin zuciyarta. Barrister Murtala ya jinjina kai cikin k’warewar aiki ya dubi Zakari ya ce “Ka ji duk abun da ɗan’uwanka ya faɗa, gaskiya ne?” Zakari ya ce “Eh haka ne.” Barrister Murtala ya mayar da dubansa ga Bilyaminu wanda ko cikin duhu mutum yay gamo da shi zai tabbatar da rikak’k’en ɗan ta’adda ne. Saboda zubinsa da yanke yake muzurai da ido da kuma tabo_tabon yanka dake jikinsa. Ya ce “Malam Bilyaminu ka ji duk abun da Hakim ya faɗa haka ne?” Cikin shakak’k’iyar murya ya ce “Eh Haka ne.” Barrister ya jinjina kai ya ce “Kotu tana san sanin wanda ya turo ku ku kay wannan ɗanyen aikin da kuma sanin ina sauran mutum biyun da ku kay aikin tare?” Bilyaminu ya ce “Sauran mutum biyun da mukay aiki tare ɗaya ya shek’a barzahu a cikinsu, ɗayan kuma yana kurkuku a halin yanzu sakamakon wani kisan da yay aka kama su, an yanke masa hukuncin d’aurin rai da rai. Batun wanda ya samu wannan aikin kuma wani babban mutum ne kuma sananne a ƙasar nan. Shi ya bani address ɗin gidan da za mu yi kisan, har yanda tsarin gidan yake da hanyoyin da zamu bi har zuwa ɗakin baccinsu, kuma shi ya ba ni mukullin da na yi amfani da shi na buɗe ƙofar gidan ta baya. Ban san dalilin da yasa ya ce mu je mu kashe mutumin da matarsa ba, ya dai faɗa mun kawai idan na je na nuna musu hotonsa, na ce masa za su amince da buƙatar da yake da ita a kan ƴarsu ko a’a? Idan sun je za su amince kar mu yi musu komai, idan kuma sun ƙi amince mu kai su k’iyama, dan za su iya tona masa asiri. A halin yanzu mutumin ba ya numfashi a doron ƙasa ya mutu shi ma. Kuma na riga na yi masa alƙawari bisa wani sharad’i namu na sirri ba zan taɓa faɗar sunansa ba a cikin wannan aikin ko me za’a mun kuwa.” Barrister Murtala ya jinjina kai cikin gamsuwa ya ce “Ko zaka iya faɗawa kotu alaƙar dake tsananinka da mutumin da ya saka ku aikin.” Ya ce “Eh, alaƙa ce kawai irin ta mai kuɗi da ƴan hark’alla irin mu, idan suna buƙatar aiki irin wannan su saka mu su biya mu da ƴan silalla.” Barrister Murtala ya juyo ya kalli Alk’ali ya ce “Ya mai girma mai shari’a, ina son wannan kotu ta bani dama in gayyato wani bawan Allah wanda yake da masaniyar komai akan wanda yasa su Bilyaminu kashe su Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa. Tunda shi Bilyaminu ya ƙi faɗa” Alk’ali ya ɗan yi rubuce-rubuce ya d’ago ya ce “Kotu ta baka dama Barrister Murtala.” Ya rank’wafawa ya ce “Na gode ya mai girma mai shari’a.” Sannan ya ce “Ina son gayyato Hashim Isma’il na_kowa .” Alk’ali ya dubi mutane ya ce “Kotu na san ganin Hashim Isma’il na_kowa a gabanta.” Alhaji Ali ya maimaita sunan a cikin zuciyarsa “Hashim Isma’il na_kowa?” Mamaki bai gama kashe shi ba sai da wani magidancin mutum da aƙalla zai yi shekaru arba’in a duniya ya fito gaban kotu, domin kuwa ɗan amininsa ne Alhaji Isma’il na_kowa, tsohon sanatan Kano ta tsakiya, kuma mutumin da yake matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Aunty A’isha ma mamakin ne ya kusa kashewa domin ta san mutumin a gurin Abban Neehal, mutuminsa ne sosai. Ba iya Aunty A’isha da Alhaji Ali kawai ambatar sunan Isma’il na kowa ya bawa mamaki ba, mafi yawan mutanen gurin sun cika da mamakin ganin ɗan senator Na_kowa a matsayin wanda zai ba da shaida. Wata mata kuwa har zabura ta yi ta miƙe, na kusa da ita su kay saurin mayar da ita ta koma ta zauna. Barrister Garba ɗan_ladi ma ya firgita ba kaɗan ba, dan har gumi ya fara gogewa, sai dai babu bakin magana tunda ba shi da abun cewa da kotu zata saurara. Bilyaminu ma ido k’walalo waje alamun razana yana kallon Hashim. Cikin nutsuwa Hashim ya faɗi sunansa kamar yadda Barrister Murtala ya ce masa. Sannan ya buk’aci da ya ba da shaida kamar yadda ya fito da nufin hakan. Ya gyara tsayuwa ya ce “Mahaifina Senator Na_kowa shine wanda ya saka su Bilyaminu yin wannan kisan.” Kafin ya gama rufe bakinsa kotu ta barke da hayaniya gami da sallallamun jama’a. Alk’ali ya buga gudu ma tare da faɗin “Order.” Nan dan kotun ta ƙara yin tsit kamar ba mutane a ciki. Alk’ali ya dubi Hashim ya ce “Cigaba da baya nanka kotu na sauraren ka.” Ya cigaba da magana. “Watarana tun ina saurayi kafin na yi aure na je part ɗin mahaifina dan amsa kiran da yay mun. Ina shiga falonsa na ji yana waya a balcony inda yake cewa. “Kar ka damu mutumina, ko Alhaji Muhammad Gabasawa ya yarda ko kar ya yarda sai na biya buƙata ta da ƴarsa tunda zuciyata ta ƙwadaitu da ita, kasan bana had’iyar yawu a banza. Ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya kece da dariya ya ce, Kar ji komai na waje na kamar kaima ka huta da wannan yarinyar nan ne, kasan dama muna neman yarinya ta cikon goma kamar yadda boka ya ce mana akan aikin mu, to ina tabbatar maka da ita za’a za mu cike, zan biwa Gabasawa ta tallama ya bani ƴarsa in cika shi da ƴaƴan banki, idan kuma ya yi taurin kai kawar da shi a doran ƙasa ba wahala zai mun. Ya ƙara yin shiru na wasu sakanni sannan cikin dariya ya ce, Ah, to dan yana mutumina ai bai kai ya biyan buƙata ta ba a gurina. Ni fa dama dan na yi mu’amalar jin daɗi da shi na shiga cikin rayuwarsa, to kuma na fuskanci ba zai taɓa amincewa da buƙata ta ba, wai shi mai tsoron Allah, dan haka kawai zan huta ƴarsa ma ya wadatar. Wani irin juyawa na ji kaina yana mun, na yi baya da sauri na fice daga falon cikin tsananin tashin hankalin jin abun da mahaifina yake aikawa. Da ƙyar na iya ƙarasawa part ɗina na zube a kan kujera. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al’amuransa ba tare da ya sani ba. Anan na gane mahaifina cikakken ɗan luwaɗi ne sannan kuma k’wararre a rapping ƙananan yara mata, duk a saboda neman duniya da mulki. Lokacin dana samu labarin rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da matarsa ko tantama ban yi ba na san aikin mahaifina ne, amma ban sanar da kowa ba saboda yanda idonsa ya rufe a neman duniya nima zai iya sawa a kashe ni matuƙar na faɗa. Sai dai cikin ikon Allah bayan rasuwar Alhaji Muhammad Gabasawa da wasu kwanaki shima Dad Allah ya saukar masa da ciwo wanda aka rasa gane kansa da gindinsa. Ciwo kullum ƙara tsanani yake ana magani amma kamar ba’ayi. Ya shafe fiye da shekara biyu yana jinya kafin ya mutu, mutuwar da bana fatan duk wani wanda na sani a duniya ya yi irin ta. Domin kuwa babu alamar dacewa a tafiyar.” Sai kuma ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. “Ganin ya rasu sai na bar abun a raina ban sanar da kowa ba, sai a cikin satin nan muka haɗu da Barrister Murtala ta sanadin wani abokina wanda shi ma Barrister ne, a nan ya ji yana bashi labarin case ɗin dake gabansa. Gabana ya faɗi amma ban sanar da shi komai ba a lokacin har muka rabu, sai daga baya dana koma gida na kasa zaune na kasa tsaye, na rasa abun da yake mun daɗi. A jiya ne na yanke shawarar na nemi Barrister Murtala na faɗa masa gaskiyar cewa mahaifina ne ya saka a yi wannan kisan, ko iyalan mamacin za su yafe masa dan ya samu sassauci daga azabtar Ubangiji. Da taimakon abokina kuma abokin Barrister Murtala na gano inda Barrister Murtala yake da zama na je na ba shi wannan labarin, shine ya buk’aci dana zo kotu yau na faɗa a gaban Alk’ali.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button