NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Kotun ta yi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen ciki, ba ƙaramin tashin hankali Alhaji Ali ya shiga ba da jin wannan labarin, tabbas da wanine ya faɗa masa wannan maganar ba ɗan cikin Senator na_kowa ba, ba zai taɓa yarda ba. Saboda yanda yake mutum na k’warai a idon al’umma, da kuma yanda yake nuna yana matuƙar son Alhaji Muhammad Gabasawa. Lallai ka ji tsoron ɗan Adam ka kalle shi kawai, domin ba kowa ka san abun da ke cikin zuciyarsa ba. Neehal kuwa toshe bakinta ta yi saboda kukan da ya taho mata, kifa kanta ta yi hawaye na zuba a kan kuncinta kamar an buɗe famfo. ‘Dan kare mutuncinta da ganin bata tozarta ta wulaqanta ba, aka kashe Ummanta da Abbanta? Tabbas babu wanda ya kay iyayenka k’aunarka a duk duniya, har abada ba zata yafewa Senator na_kowa ba da su Bilyaminu, ko da kuwa zata ga ana babbaka naman jikinsu a gabanta. Aunty A’isha ma kuka take yi, Mama kam ta daure zuciyarta sai jujjuya kai take tana da Allah wadai da wannan halin rashin imanin da zallar zalunci. Hajiya kuwa sai matsar hawaye ake tana ƴan maganganunta ƙasa_ƙasa. Sauran mutane wanda suka san yanda Abban Neehal suke mutunci da Senator na_kowa abun ya girgiza zuk’atansu. Barrister Murtala ya dubi Hashim ya ce “Kotu tana godiya bisa ga shaidar da ka bayar, zaka iya komawa ka zauna.” Sannan ya dubi Bilyaminu dake ta aikin zazzare ido ya ce “Ka ji abun da Hashim ya faɗa, gaskiya ne Senator Na_kowa ne yasa ku wannan aikin?” Bilyaminu ya ce “Eh shine.” Barrister Murtala ya yi murmushi ya mayar da dubansa ga Alk’ali ya ɗan rank’wafawa ya ce “Ya mai girma mai shari’a, ina roƙon wannan kotu mai adalci data yankewa waɗanda ake ƙara hukunci dai_dai da abun da suka aikata, bisa ga shaidun da aka gabatar da kuma amsa laifunsu da sukai da bakinsu. Na gode ya mai girma mai shari’a.” Sannan ya juya ya koma inda yake a zaune d’azu ya zauna. Alk’ali ya ja gwauron numfashi dan shi kan shi abun ya daki zuciyarsa ba kaɗan ba sannan ya d’ago daga rubuce-rubucen da yake ya ce. “Bisa tarin hujjoji da bayanai da wannan kotu mai adalci ta tattara ta yankewa Bilyaminu,Zakari da Hakim, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an ba su horo mai tsanani a gidan kaso. Sannan kuma kotu ta yabawa Hashim Isma’il na_kowa k’warai bisa yanda ya bayar da shaida ga abun da mahaifinsa ya aikata. Shi kuma Senator Na_kowa da wand’anda suka yi kisan tare da su Bilyaminu tunda sun riga mu gidan gaskiya hukuncinsu yana gurin mahaliccin su.” Alk’ali ya buga guduma gum!gum! Har sau uku. Sannan mutane aka haɗa baki gurin faɗin “Koto! Su Bilyaminu kuwa ido ne ya raina fata ganin yanda gandirobobi (Ma’aikatan gidan yari) suka ƙaraso inda suke suka fara daurawa musu ankwa a hannuwansa, a gefe guda kuma ga turmutsitsin ƴan jarida kowa na son ɗaukar rahoto. Barrister Murtala kuwa sai gaisawa mutane suke zuwa suna yi da shi, shi kuma yana murmushin samun nasara.

Hajiya ce ta fara miƙewa a cikin su Mama tana faɗin. “Wannan la’anannen Senator ɗin Ubangiji ya ƙara masa azabar k’abari, mutane sai son zuciyar tsiya da rashin imani, wannan irin zalunci haka har ina?” Sai kuma ta kalli Neehal da har yanzu bata d’ago kanta ba ta ce “Wannan yarinya Allah ya bi miki haqqinki na marainiyar ƙarfi da ya ji da aka mayar da ke baki ji ba, baki gani ba.” Aunty Sadiya ta taso daga inda take zaune ta dawo gurinsu tana murmushin takaici ta ce “Masha Allahu, an gano waɗanda suka kashe su Abban Neehal an hukunta su, saura kuma wanda yake kashe su Anwar shi ma.” Kafin wani a cikin su ya yi magana Alhaji Ali da Daddy da sauran abokan Abba sun ƙaraso gurin, ƴan jarida na bin su yuu a baya dan son jin tofa albarkacin bakinsu a game da wannan al’amari a matsayin su na iyalan waɗanda aka kashe. Alhaji Ali ya dubi Aunty A’isha ya ce “A’isha! kin ji abun da bamu taɓa tsammani ni ba ko? Lallai ka ji tsoron duniya da mutanen cikinta, saboda ko mafarki na yi aka ce mun Na_kowa zai yiwa Gabasawa haka zan farka in yi tunanin ko addu’ar bacci ce ban yi ba, shaid’an ya kawo mun ziyara.” Aunty A’isha ta girgiza kai ta ce “Yanda Abban Neehal yake yawan zancen mutumin nan da k’aunarsa da faɗar kirkinsa da mutuncinsa ashe shi zai yi sanadin barin sa duniya.” Aunty Sadiya ta ce “Mutane sai addu’a kawai, amma wanda baka taɓa zaton zai iya cutar da kai ba, sai a wayi gari ya maka abun da ko mak’iyin ka na fili ba zai maka ba.” Nan dai suka ci-gaba da tattauna al’amarin, su Uncle Umar ma sun ƙaraso ana jimanta abun da su, dan ya san Senator Na_kowa mutumin Abba ne sosai. Mama kuwa magana ma ta kasa yi, sai bin su da ido kawai take.

A hankali Ameen yake takowa cikin takunsa mai ɗaukar hankali zuwa inda Neehal take, wadda bata ma san ya zo court ɗin ba tunda ba tare suka zo ba. Hannunsa yasa ya d’ago fuskarta bayan ya ƙarasa daf da ita, tun kafin ta kalli fuskarsa ta san shine saboda k’amshinsa da baya buya da ya ziyarci hancinta. A hankali ta d’ago ta dubi fuskarsa idanunta taf da ruwan hawaye, sai kuma ta miƙe da sauri ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Yasa hannunsa ɗaya ya zagaye bayanta yay mata kyakkyawar runguma ba tare da ya ce komai ba, sai lip ɗinsa da yake taunewa alamun abun ya taɓa masa zuciya sosai shi ma. Tsahon mintuna biyu tana jikinsa sannan ya d’ago ta a hankali ya rabata da jikinsa. Bai ce komai ba ya saka tafin hannunsa ya shiga share mata hawayen. Ta sauke ajiyar zuciya tare da yin ƙasa da kanta, ya kalli gefensa inda su Mama suke har yanzu gurin a cike yake da mutane. A hankali ya kama hannunta, bata musa ba ta bi shi suka fice daga cikin court ɗin. Da kansa ya buɗe mata Motarsa ta shiga ta zauna, sai aikin sassauke numfashi take. Ya zagaya ya shiga driver seat ya zauna shi ma. Yana ƙoƙarin kunna Motar wayarsa ta fara ringing, ya ɗauko ta daga aljihun gaban rigarsa, ganin Mama ke kiransa ya yi picked. Mama ta tambaye shi yana tare da Neehal ne. A takaice ya ce mata “Eh.” Ya mayar da wayar aljihu tare da kallon Neehal wadda ta dunk’ule kanta a waje ɗaya saboda zazzaɓin jikinta dake son dawo mata sabo. Hannunsa ya kai ya taɓa goshinta ya ji da zafi, jikinta kuwa sai rawar ɗari yake. A hankali ya janyo ta ya kwantar da kanta a kan ƙafaɗarsa cikin tsananin tausayinta. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da lumshe idanunta, hannunta ɗaya ta saka ta zagaye bayansa da shi. Ya ɗan lumshe ido ya buɗe sannan ya kunna Motar ya yi reverse suka bar harabar court ɗin. A haka suka ƙarasa gida tana jikinsa har bacci ya fara ɗauke ta. Bayan ya yi parking ya d’aga kanta a hankali daga kan ƙafaɗarsa ya ɗan tsurawa beauty face ɗinta ido, gigirarta ya shafa da finger ɗinsa a hankali gami da ɗan bakinta da ya ɗan turo gaba saboda baccin da take. Hakan yasa ta buɗe idonta dake cike da bacci, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Yatsina fuska ta yi saboda kanta da ta ji yana sara mata, cikin muryar wanda ya ci kuka ya k’oshi ta ce “Yaya kaina ciwo.” Ya shafi kuncinta ya ce “Sorry dear, mu je ciki ki sha magani.” Ta gyaɗa masa kai tare da barin jikinsa cikin harfin hali, dan sosai take jikin nata babu daɗi. Ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagayo ya buɗe mata itama ta fito. Hannunta ya kama suka nufi part ɗin Mama. Ya yi amfani da key ɗin hannunsa na part ɗin ya buɗe musu ƙofa suka shiga. Ta saki hannunsa da nufin ta kwanta anan falo kan kujera, fahimtar hakan yasa ya ƙara kama hannun nata ya ce “Mu je daki sai ki kwanta.” Bata musa ba, amma bata ce komai ba. Har bedroom ɗinta ya raka ta ta kwanta akan gado. Yana ƙoƙarin fita ta ce “Yaya zan yi fitsari.” Bai ce komai ba ya dawo ya taimaka mata ta tashi ya rakata har bakin toilet, ta shiga ta yi ta fito, ya ƙara kama hannunta zuwa bakin gado sannan ta hau ta kwanta tare da jan bargo ta lullub’e jikinta da shi. Fita ya yi daga ɗakin, ba jima sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da drug da ruwa. Ya zauna a bakin gadon cikin kulawa ya ce “Tashi ki sha magani.” Ta tashi zaune da ƙyar tana yamutsa fuska, ya bare mata maganin ya bata ta sha ta kora da ruwa. A hankali ya ce “Allah ya sauwaqe.” Ta kalle shi idanunta cike da hawaye ta ce “Ameen, Thank you.” Ta koma ta kwanta. Ya matso kusa da ita ya shafi gefen fuskarta cikin wata irin murya ya ce “Don’t cry, bana son inga kina kuka, bana jin daɗi.” Ta tsura masa ido kamar me mamakin abun da ya faɗa, shima kallon nata yake yi. Ta kama hannunsa a hankali ta ce “Insha Allah Yaya na daina kukan tunda baka so.” Ya yi mata ɗan murmushi ya ce “Sleep well.” Itama murmushin ta masa ta mayar da idanunta ta lumshe. Ya zare hannunsa a hankali daga cikin nata, ya gyara mata hijabin jikinta da ya ɗan shak’e mata wuya, sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button