NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Duk mai son shiga group ɗin NEEHAL FAN’S ta mun magana ta Number na 09066710753, amma in kin tabbatar za ki na comments and share.

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

0️⃣4️⃣

………….Mama bayan ta gama haɗa break fast din ta ɗibi na Dad ta haɗa masa a cikin tire, tana ƙoƙarin fita Dije mai aiki ta shigo kitchen d’in, ta risina ta ce “Ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya” Mama ta ce “Lafiya kalau Dije, yawwa dama na gama sai ki haɗa wanke_wanke ki yi ki gyara kitchen d’in” cikin girmamawa Dije ta ce “Toh Hajiya” Mama ta fita daga kitchen d’in, Zulai mai aiki ta na mopping a falon, ganin Mama ya sa ta ajiye mopper ɗin hannunta ta taho da sauri ta na faɗin “Sannu da fitowa Hajiya” Mama ta ce “Yawwa mun tashi Lafiya” Zulai ta ce “Lafiya ƙalau Hajiya” tana ƙoƙarin karɓar kayan hannun Mama, Mama ta ce “Ki barshi ki je ki ci gaba da aikin ki kawai, idan kun gama sai ku ɗibi abinci a kitchen ku karya” Zulai ta ce “Toh Hajiya” ta koma ta cigaba da aikinta, Mama kuma ta nufi part din Dad.

Dad ya na bedroom d’insa, Mama ta ajiye masa break fast d’insa a kan dinning sannan ta nufi bedroom d’innasa, da sallama ta shiga ya na zaune akan gadonsa ya na operating system, d’agowa ya yi ya na duban Mama tare da amsa mata sallamar da ta yi, Mama ta zauna a gefensa ta na faɗin “Your break is ready” Dad ya yi murmushi ya ce “Godiya nake matar Aljannah” Mama ta yi murmushi ta tashi ta ɗauke system ɗin gabansa ta ajiye a kan bedside locker ta ce “Mu je ka yi break idan ka gama sai ka cigaba da aikin” Dad ya yi murmushi ya mik’e ya bi bayan Mama suka fita zuwa falonsa, Mama ta koma ta ɗauko tea plaks ta dawo ta yi sarving ɗin su suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bayan sun gama Mama ta yi hamdala ta na goge bakinta da tissue ta ce “Wai Ni kuwa Dad ya ku ka yi da Son jiya?” Dad ya ce “Na masa magana a kan ya kamata zuwa yanzu a ce ya na da iyali shima ya ce Insha Allah bayan bikin daughter zai fitar da mata shima” Mama ta sauke numfashi ta ce “Amma Dad me ka fuskanta ya na damun Ameen, tun jiya da yawo gabad’aya hankalina ya kasa kwanciya da yanayin da na gan shi” Dad ya ce “Nima a nawa ɓangaren hakane Doctor, abun da ya ƙara tayar mun da hankali da Muhammad ramar da ya yi da kuma yanda ka na kallonshi za ka hango zallar damuwa a tattare da shi, kuma duk abin da yake damun Muhammad ba ƙaramin abu ba ne, dan kin san Muhammad tun ya na ɗan ƙaramin shi, yaro ne mai juriya, haƙuri, kawaici gami da tawakkali, zai yi wuya ka gane ya na cikin damuwa ko ka fuskanta, idan har ba shi ya furta maka ba, wannan dalilin ya sa nasan lallai abin da yake damunsa ba ƙaramin abu ba ne” Mama ta sauke wani gwauran numfashi tare da dafe kanta ba ta ce komai ba, Dad ya kama hannunta cikin lallami ya fara mata magana da faɗin “Kinga Doctor ki kwantar da hankalinki, Insha Allahu ba wata matsala ba ce, ba na son in ga kina damuwarnan, kamar yadda ya ce mu dinga masa addu’a ki dinga masa, Insha Allahu koma meke damunsa Allah zai yaye masa” Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Allah ya sa” Dad ya saki hannunta tare da mik’ewa ya na faɗin “Yawwa ko kefa, ba na son na ga ki na yawan damuwarnan ko kaɗan, dama naga kwana biyu kin ɗan fa ɗa” Mama ta mik’e itama ta na faɗin “To ba dole ba Dad ka ga ina rama, autatah za ta tafi, ai ahakanma ina ƙoƙarin b’oye damuwata dan kar ta damu itama” Dad da ya fara tafiya ya ce “To ya za’ai sai haƙuri, Ni kaina na fara kewar daughter tun yanzu”

Bayan Mama ta gama gyara part d’in Dad ta haɗa masa ruwan wanka ya yi, ta dawo part d’inta ta baro shi ya na aiki tun da Yau Sunday ba fita zai yi ba. Ɗakin Hajiya ta shiga ta tarar da ita ta na haɗa kaya, Mama ta zauna a gefen gado ta ce “Hajiya ashe kin tashi, har General ya na cewa zai zo ya gaishe ki, na ce ya bari sai anjima dan nasan da k’yar in kin tashi” Hajiya ta ce “Na tashi mana, ko zan zauna ina ta barci har wannan lokacin kamar wata marar aikin yi” Mama ta ce “ai na san ki ne Hajiya da son bacci” Hajiya ta ce “To yau ban yi ba, tun ɗazu na tashi nake haɗa kayana ba sai goben ta yi Mahmud ɗin ya zo ba in yi ta kame_kamen ban gama shiri ba” Mama ta ce “Ai da kin barshi Hajiya na haɗa miki ko kuma na turo su Dije su haɗa miki, tun da ko karyawa ba ki yi ba” Hajiya ta kama hab’a ta ce “Rufa mini asiri, masu aiki da haɗa mun kaya, lalacewar tawa bata kai haka ba, kema na hutashsheki tun da ba wani abu na aiki nake a gidan ba, dan haɗa kaya dai ba zai mun wahala ba” Mama ta ce “Shikenan bari na kawo miki abincinki” Mama ba ta jira amsar Hajiya ba, ta mik’e ta fice.

Ƙarfe 11 Ameen ya shigo falon Mama, su na zaune ita da Hajiya suna kallo, Mama ta bishi da kallo har ya zauna a gefenta, cikin muryarsa kamar baya son magana ya ce “Morning Mum, dafatan kin tashi lafiya” Mama ta ce “Lafiya k’alau and you?” Ya ce “Fyn” Mama ta ce “Masha Allah, yau za ka wuce Lagos ɗin ko sai gobe?” A hankali ya ce “Tomorrow in the morning” Mama ta ce “Allah ya kai mu” Hajiya dake saurarensu ta keɓe fuska ta ce “In Mutum bai kula ni ba, sai me? Daga yau ma ba ƙara gani na za ka yi a gidanku ba, sai wani lokacin kuma” ɗan Murmushi Ameen ya yi bai ce komai ba, sai ma mik’ewa da ya yi ya nufi part d’in Dad, Hajiya ta bishi da harara” Mama ba ta ce komai ba, sanin da ta yi ba’a shiga tsakanin Hajiya da Ameen, dan Hajiya ko wata ta yi ba ta zo gidan ba, da kanshi ya ke zuwa har Gombe ya ɗaukota.

Kafin la’asar Neehal ta dawo gida, tare suka taho gidan yau da Haneefah, a falo suka tarar da su Mama da kannenta guda biyu mata masu kama da ita, sun zo yiwa Hajiya sallama, Aunty A’isha da Aunty Sadiya, Neehal ta tafi da sauri ta rungume Aunty Sadiya dan tafi kusa da kofa, Haneefah kuma ta rungume Aunty A’isha, Neehal ta ce “Aunty Sadiyata welcome” Aunty Sadiya na murmushi ta ce “Yawwa my daughter, ya aiki?” Neehal ta ɓata fuska cike da shagwab’a ta ce “Alhamdulillah, sai gajiya” Aunty Sadiya ta ce “Sorry dear, za ta tafi itama” sakin Aunty Safiya ta yi ta koma ta yi hugging Aunty A’isha tare da gaisheta” Aunty A’isha na murmushi ta ce “Lafiya k’alau, Neehal yanzu an gujeni ko, yaushe rabonku da gidana” Neehal ta ce “Kai Aunty ko wata fa ban yi da zuwa ba” Aunty Aisha’ ta ce “To ai da ko sati ba kya yi ba ki zo ba, ko Anwar d’inne ya hana ki fita?” Haneefah tay karaf ta ce “Baruwan Angonmu, Mama ce ke hanamu fita” Mama ta harare ta ta ce “Ta yaya zan bar ku ku fita ba’amun aiki ba, duk randa fa ba su je aiki ba ko school, wuni suke a d’aki su na shiririta, sai na je na fatattako suke saukowa su yi abun da ya dace, can gidan Barrister ma ta ce in sun je haka suke, kamar wasu yara” Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, ta zauna kusa da Hajiya, wadda ta ƙurawa TV ido ta na kallo. Aunty A’isha ta yi murmushi kawai, Haneefah ta dubi Aunty Sadiya ta ce “Aunty Sadiya dama ina shirin kiranki, wasu freinds ɗinmu sun turo mun kuɗin ankon Neehal bari na miki transfer yanzu” Aunty Sadiya ta ce “Toh, na atamfa ne ko na less?” Haneefah ta ce “Duka” Neehal ta lumshe idonta gabanta na faɗuwa, tunawa da ta yi nan da 2 months fa inda rai da lafiya an yi aurenta, shikenan za ta bar Mamanta da Yayanta da Dad ɗinta mutane mafi soyuwa a gareta, ƙoƙarin mai da kwallar da ta ciko idanta ta yi ta mik’e ta wuce sama. Da yamma bayan su Neehal sun ci abinci sun yi wanka suka tafi gidansu Haneefah, Mommy ta na zaune a falo suka shigo gabad’aya suka yi kanta suka ruk’unk’ume ta, Mommy ta ce “Uhm, Allah ya kawo ku, Kwana biyu bakina shiru amma yau za ku zo ku samun ciwon kai” Neehal ta ɓata fuska ta ce “Kai Mommy ko irin yar tarb’ar nan ma babu” Mommy ta ce “Ban san ta ba, ba kuma zan yi ba, a ɗaga mun jiki Ni, ba daɗi nake ji ba” Haneefah ta tashi daga jikin Mama tana faɗin “Shiyasa wlh gwara gidan Mama sau dubu da nan” ta ƙarashe zancen ta na shigewa kitchen. Mommy ta ce “Ni da za ki tattara kayanki, ki koma gidan Maman da kin taimaka mun” Neehal ta yi dariya ta ce “Ai ba za ki iya kwana 2 ba ki ga Besty ba, abun da ko kwana ɗaya ta yi kinta kiranta a waya kina ta dawo” Mama ta ce ”Ai dan ba Ni da mai mun aiki ne, amma ba wai kewarta nake ba” Haneefah ta dawo falon ta na duban Mama ta ce “Mama cake za mu yi wa ya Anwar, na gidan Mama kwananne ne, kuma na duba kitchen kamar ba ki da butter” Mama ta ce “Babu kam, amma bari na ba wa idi ya karb’o, tun da ɗana za’aiwa” Neehal ta ce “Au da mu za mu ci, ba za ki bayar a siyo ba?” Mommy ta ce “Sai dai ku siyo da kanku ko kuma ku haƙura da cin” Haneefah ta ce “Mommy nan da wasu watanni fa kin dena ganinmu a kai a kai, ki dinga lallaɓamu fa” Mommy ba ta kula ta ba ta shige ɗakinta dan ɗakko kuɗi. Neehal ta dubi Haneefah da damuwa a fuskarta ta ce “Besty Yau gabad’aya ban ga Yayana ba, ba na jin daɗi” Haneefah ta ce “Why?” Neehal ta ce “Da safe da zan fita, na san ya na bacci, da muka dawo kuma ban ga car ɗinshi ba, na tambayi Mama shi, ta ce sun fita tare da Dad” Haneefah ta ce “ki kirashi mana” Neehal ta ce “Good idea” ta ƙarashe zancen tare da zaro wayarta daga cikin small handbag ɗinta mai kyau, kiran duka numbobin sa ta yi amma bai ɗauka ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button