NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Daf da Magriba Sadik ya shigo gidansu a gajiye, a falon Maamah ya tarar da Hajiyarsu da Batul, Maamah kuma tana bedroom ɗin Abba tana gyara saboda ta karɓi girki da yammar nan. Ya zauna a kusa da Hajiya cikin mamakin ganin ta ya ce “Ƴar tsohuwar nan ke ce a gidan namu? Zuwa babu sanarwa, ai da kin faɗa dana taho miki da tsarabar goruba.” Ta rank’washi kansa ta ce “Giginya zaka siyo mun ba goruba ba, ɗan nema kawai.” Ya yi murmushi tare da miƙewa yana faɗin “Kin yiwa kanki tunda ba kya so, bari na shiga ciki na fito.” Ta ce “To a fito lafiya.” Batul ta ce “Sannu da zuwa Yaya.” Ya ce “Yawwa, ina Maamah?” Ta ce “Tana ɗakin Abba.” Bayan ya dawo daga masallaci Maamah ta kawo masa abinci yana ci suna hira da Hajiya har ta sako masa zancen Neehal inda ta ce “Abubakar ashe ka fara yunƙurin yi mini kishiya ban sani ba?” Ya yi murmushi ya ce “Har kin samu labari kenan?” Ta ce “Shine ma abun da ya kawo ni gidan nan yau?” Ya ce “Kamar ya Hajiya, ko duk kishin ne?” Ta sanar masa yanda suka yi da su Abba da Kawu a tak’aice.” Sadik ya ajiye cokalin hannunsa fuskarsa na nuni da damuwa ya ce “Hajiya wannan zancen fa ba gaskiya ba ne, shati faɗin mutane ne kawai.” Hajiya ta ce “Koma mene ne dai mahaifinka ya ce zai bincika, in ma gaskiya ne in ma ƙarya ne duk zai gano, amma kafin nan ka fara tuntubar ita yarinyar da zancen, idan har tana sonka da gaskiya saboda Allah kuma ba su da wata manufa akan kisan ake yi zata faɗa maka gaskiya da bakinta.” Sadik ya marairaice ya ce “Insha Allahu Hajiya zan tambaye ta, Amma dan Allah Hajiya ko me zai faru karki bari su Abba su hana ni Aurenta, ina sonta sosai wallahi.” Maamah dake sauraren hirar tasu cike da tausayin ɗan nata ta ce “Sadik, ka yi addu’a kawai, idan Alkhairi ce a gare ka Allah ya baka ita, idan kuma ba Alkhairi ba ce Allah ya baka wadda ta fita, sautari wani abun da muke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, rashin sa a tare mu ya fi zama Alkhairi.” Ya kalli mahaifiyar tasa ya ce “Shikenan Maamah, Insha Allahu zan cigaba da addu’a akan wacce nake yi.” Hajiya ta ce “Shi ya fi dai, muma zamu taya ka da addu’ar, abun da mahaifiyarka ta faɗa gaskiya ne.” Ya yi shiru cikin damuwa, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya rabuwa da Neehal ba, kuma Insha Allahu itace matarsa.”
Bayan su Neehal sun idar da Sallah ba jimawa Ameen ya zo gidan. Su Afrah suka tafi da gudu gurinsa suna faɗin “Oyoyo Uncle.” Ya d’aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi. Sannan ya kamo hannunsu zuwa bakin gado ya zauna ya gaishe da Mama. A hankali Neehal ta dube shi ta ce “Ina yini Yaya.” Ya kalle ta ya ce “Lafiya k’alau.” Ta ce “Ya jikin Aunty Hafsah?” Ya ce “Da sauqi, ya naki jikin?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya mayar da duban sa ga su Afrah ya ce “Yaushe kuka zo?” Afrah ta ce “D’azu Daddy ya kawo mu.” Ya shafi kuncinsu bai ce komai ba. Mama ta ce masa “Ya aikin naku? Ya ce “Alhamdulillah, Hajiya ta wuce kenan?” Mama ta ce “Eh, tun safe ba ku yi waya ba ne?” Ya ce “Na ga missed call ɗinta tun safe, na kira ta kuma d’azu bata ɗauka ba.” Mama ta ce “May be time ɗin suna hanya, amma mun yi waya kafin Magriba ta ce sun ƙarasa.” Ya ce “Okay.” Mama ta dubi Neehal ta ce “Zubo masa abinci, na san da ƙyar in ka ci tunda Hafsah bata da lafiya, suma su Afrah ki zubo musu.” Ta ce “Toh.” Tare da miƙewa ta fice. Ya ce “Allah yasa ina cin abin da kuka dafa.” Mama ta ce “Koma mene haka zaka ci, har yanzu baka daina zaɓe zaɓen abinci ba ko Ameen? To tuwo na yi, itama Neehal yanzu ta gama cewa baza ta ci ba, na ce mata ta kwana da yunwa kuwa dan babu mai sake mun wani sabon girki yanzu, tunda ku tsurfar ku ta muku yawa.” Ya yi ɗan murmushi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Kitchen ɗin ya shiga inda ya tarar Neehal tana ƙoƙarin zuba miya. Ya ce “Kar ki zuba.” Ta juyo ta dube shi ta ce “Ka fasa ci?” Ya gyaɗa mata kai. Ta ce “Na manta ashe fa baka cin tuwo, in dafa maka wani abun to?” Ya ce “Like what?” Ta ce “Akwai miya, sai ka faɗi abun da kake so in dafa maka.” Ya ce “Okay, dafa mun ko mene ma.” Ta ce “Toh.” Ya juya ya fice. Ta dauko tukunya ta ɗauraye sannan ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora. Ta buɗe frizer ta ɗauko kayan salad ta zauna ta fara yankawa kafin ruwan ya tafasa. Mama ce ta shigo kitchen ɗin ta dubi tukunyar data ɗora ta sannan ta dube ta, ta ce. “Me kike yi haka?” Ta ce “Yaya zan dafawa abinci, kin san ba ya cin tuwo.” Mama ta ce “Oh, yanzu kin warke kenan zaki iya girki?” Ta ce “To Mama naga bai ci abinci ba, kar ya zauna da yunwa, kuma ba wani girki mai wahala zan yi ba.” Mama ba ta ce komai ba ta juya ta fice. Mintuna kaɗan ruwan ya tafasa, ta ɗauko macaroni ta zuba fiye da rabin leda. Bayan ta gama ta juya a plate ta kai masa falo ta ajiye a gaban sa. Ya dube ta ya ce “Thank you.” Sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kan carpet, ya dubi abincin ya ce “Take another spoon.” Ta koma ta ɗauko ta kawo masa, bai karɓa ya ce “Zauna mu ci.” Ta ce “Yaya na k’oshi.” Yay mata wani kallo, ba shiri ta zauna suka fara ci tare. A takure take sosai saboda ba su taɓa cin abinci tare ba, kanta a ƙasa take cin abincin ta kasa d’agowa ta kalle shi. Shi kuwa kallon ta ya ma fi cin abincin nasa yawa. Ba su fi rabin abincin ba ta ce ta ƙoshi, ya ce bata isa ba sai sun cinye duka. Dama Mama ta gama masa mitar tunda yasa a yi masa girki, to kar ya bar mata sauran abinci ko d’igo ya cinye duka. Haka ta haqura suka ƙarasa ci. Bayan sun gama ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen, su Afrah ta zubawa ragowar abincin a plate ɗin, kafin ta fito har ya fice daga falon. Ta wuce sama ta kai musu abincin, ta tarar su Cake ma suke ci da yoghurt. Ta ajiye abincin ta ce in sun gama sa ci, sannan ta fita zuwa ɗakinta. Tana ɗaukar wayarta ta tarar da missed call ɗin Sadik har huɗu, da chaji ma zata saka wayar, amma dai ta kira shi duk da ta ji an fara kiran isha’i, ya d’aga ya ce mata idan ya dawo daga masallaci zai kira ta.
Bayan an yi Sallar ya kira ta, ta daga suka gaisa ya tambaye ta jikinta ta sanar masa ta ji sauƙi. Cikin damuwa ya ce “Wifey wai me yake faruwa ne?, kwana biyu naga gaba-ɗaya kin canza mun, kafin ki yi rashin lafiyar nan idan na kira ki sometimes da daddare sai in ji call waiting, ina tsoron kar wani ya mun ƙafa fa.” Ta yi shiru dan ita kanta ta san tunda Ahmad ya shigo cikin rayuwarta ta canzawa Sadik, dan ma yana da haquri da wani ne da tuni sun yi faɗa, ko kuma inda ita ce yake mata haka bata san ya za tay ba. Cikin sanyin murya ta ce “Ka yi haquri Husby, ni kaina na san ban kyauta maka ba, amma babu abun da ya faru, kuma babu wanda yay maka wata ƙafa balle hannu, har yanzu kai kaɗai ne a zuciyar Neehal.” Cikin jin daɗi ya ce “Dagaske Wifey?” Ta ce “Gasken gaske ma, Ya Sadik ina da kai me zan yi da wani ɗa_namiji kuma?” Ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Har na ji daɗi a raina, dan bana son abun da zai raba ni da ke.” Ta ce “Insha Allahu Husby zamu rayu tare har ƙarshen rayuwarmu.” Ya ce “Amin Amin Wifey.” Suka Cigaba da hirar su ta masoya Sadik ya sanar mata Insha Allahu gobe zai zo, akwai maganar da yake son su yi. Ta ce Allah ya kai mu lafiya sai ya zo ɗin. Bayan sun gama wayar ta yi tagumi ta fara tunani, tabbas ta san zuciyarta Sadik take so, so mai tsanani ma kuwa, amma abun da ta rasa ganewa matsayin Ahmad a gurin ta, da farko tana masa kallon like ɗan’uwanta na jini, amma a kwanakin nan lissafin yana ƙoƙarin sauyawa a cikin zuciyarta game da shi. Ga kuma tausayinsa mai tsanani da take ji, saboda koda bai faɗa ba tana hango sonta mai tsanani a cikin kwayar idonsa, ga kuma yaransa da Allah ya ɗora mata kaunarsu, bata jin zata iya jurar Ahmad ya auri wata matar ta riƙe masa su Afrah, ta san kuma koda bata aure shi ba in ta ce masa ya bar mata su zai bata, amma ta san Mama baza taɓa yarda da hakan ba. Last abu kuma da yake damunta shine, ko zata yi auren at this time ko baza ta yi ba sai Allah, za’a barta da wanda zata aura ɗin ne ko za’a kashe mata shi kamar su Anwar?…. Shigowar su Afrah ya katse mata tunanin da take. Suka haye jikinta suka ce ta kira musu su Ummi, ta kira Zahra bayan ta ɗauka sun gaisa ta ba su wayar, suka yi mata surutun su sannan ta kaiwa Ummi wayar itama suka yi magana, har Dad ɗin su Ahmad yau sun gaisa da Neehal. Ta gaishe su cikin girmamawa su kuma su kay ta saka mata albarka. Bayan sun gama wayar ta ja su toilet tay musu wanka, tana shirya su suka dame ta akan ta kira musu Daddy’nsu. Ta kira shi kuma bai d’aga ba. Bayan ta shirya su, ta kama hannunsu suka nufi part ɗin Daddy dan su gaishe shi. Sai da goma ta wuce ta dawo part ɗin Mama ɗauke da Amrah a hannunta, Mama kuma ta biyo ta da Afrah dan har sun yi bacci. Bayan ta yi wanka ta sha magungunanta ta kwanta, lokacin sha ɗaya saura ƴan mintuna, ta ɗauko wayarta ta tarar da missed calls ɗin Ahmad, ta bi bayan kiran nasa, sai da ta kusan katsewa ya ɗaga cikin muryar bacci suka ɗan yi magana kaɗan, ya sanar mata fita suka yi da Mamy bayan ya koma gida, shi yasa bai kira ta ba, sai bayan sun dawo ya ga missed call ɗinta. Suna gama wayar itama bacci ya ɗauke ta.