NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ƙarfe biyar da ƴan mintuna Mama ta dawo, ɗakin Neehal ta leqa ta tarar da ita zaune a kan gado tana latsa waya. Ta d’ago ta dubi Maman ta ce “Sannu da zuwa.” Mama ta ce “Yawwa ya jikin?” A hankali ta ce “Da sauqi.” Mama ta ce “Ashe su Afrah sun zo, har yanzu ba su dawo ba ne?” Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta juya ta fice ganin kamar bata son magana, ita kuwa ranta ne a ɓace har lokacin, sai taune lip ɗinta take. Kafin Magriba Ahmad ya dawo da su Afrah, da gudu suka je suka rungume Mama dake zaune a falon ƙasa. Mama ta shafa kanwunansu tana murmushi ta ce “Welcome yarana.” Ahmad ya zauna a kan carpet ya gaishe da Mama cikin girmamawa. Ta amsa masa tare da tambayarsa yanda ya baro Mamy da su Ummi. Su Amrah suka bar jikin Mama suka nufi upstairs dan sun san Auntin nasu tana can. Tana nan yanda Mama ta bar ta suka shigo ɗakin suna kiran sunanta. Ta d’ago ta kalle su bata ce komai ba, suka hawo kan gadon da murnar su, Afrah ta ce “Aunty mun dawo, Mamy ta ce mu gaishe ki.” Ta yi ɗan murmushi ta ce “Sannun ku da dawowa, to ina amsawa.” Amrah ta ce “Daddy yana ƙasa shi da Mama.” Ta yi shiru bata ce komai ba, yaran suka cigaba da yi mata hira. Kiran Ahmad ne ya shigo wayarta, ta ɓata rai kamar yana gabanta ta ƙi d’agawa, haka kawai ta ji tana jin haushin shi ba tare da ta san dalili ba. Bayan kiran ya katse wani ya ƙara shigowa, still ƙin ɗagawa ta yi. After three minutes Mama ta turo ƙofar ɗakin ta ce mata ta je Ahmad yana jiran ta. Fuska a cukule ta ɗauki wayarsa dake kan bedside locker ta fice daga ɗakin, su Afrah suka mara mata baya……..✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
5️⃣3️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#
………..Cikin sauri ta zare jikinta daga na Ahmad, shima bai yi musu ba ya sake ta tare da faɗin “Ki yi a hankali Princess.” Ganin yanda ta zare jikin nata cikin gaggawa ta koma ta kwanta a kan gadon, wani irin fad’uwa gabanta yake kamar zata yi fitsarin sa gami da matsanancin tsoron da ya cika mata zuciya saboda ganin Ameen, ta runtse idanta tare da jan bargo ta lullub’e jikinta. Cikin matuƙar shock Ameen yake kallon su, tun daga turo ƙofar da ya yi ya kasa ko da d’aga ƙafarsa ne, shi mutum ne da ba kasafai ake gane halin da zuciyarsa take cike ba, amma a yanzu kallo ɗaya zakai masa ka san ran Maza ya kai matuƙar ɓaci. Afrah ta waro Ido ta ce “Uncle are you a soldier? Dama Aunty Zahran mu zata gan ka, she like soldiers over.” Amrah ta ce “Uncle show me your gun, I want to see it.” Ahmad ya ɗauke idonsa daga kan Neehal ya dube su ya ce “Ba ku gaishe shi ba sai surutu ko?” Yaran suka rufe baki a tare suna murmushi. Ameen bai bi ta kan zancen yaran ba ya tako zuwa inda Neehal take, Idanunsa akan Ahmad yana masa wani kallo ta gefen ido. Ahmad ya miƙe tsaye, Allah ya taimaka Neehal bata ɓata shi ba kamar yadda ta yi zato. Hannu ya miƙawa Ameen yana murmushi ya ce “Barka da zuwa Babban Yaya.” Ba tare da Ameen ya kalle shi ba ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha amma bai ce komai ba. Ahmad ya lura da yanayin da Ameen ɗin yake ciki, sai ya danganta hakan da halin sojoji ne kodayaushe fuska a cukule, ko kuma wani ne ya ɓata masa rai, amma ko kaɗan rashin maganar bai dame shi ba. Neehal wadda tun sanda Ahmad ya yiwa Ameen magana ta buɗe idonta ta kalle shi hawaye na zuba daga cikin idanunta, ganin ya zauna a kusa da kanta ta runtse ido da sauri cikin saddaqarwar zata ji duka a jikinta saboda ganin yanayinsa, ta san Ameen ta san waye shi, ta kuma san ɓacin ransa babu kyau. Saboda tsabar fargaba da tsoron da zuciyarta ke ciki da wani irin gudu ta ji jinin yana fita daga jikinta, ga gefen mararta da ya k’ulle. Zuba mata ido kawai ya yi bai ce komai ba, wanda hakan yasa ta kuma runtse idonta da sauri tare da jan bargo ta rufe har fuskarta. Ahmad daga tsayen da yake ya ce “Princess bari na je na kawo miki magani ki sha, Allah ya baki lafiya.” Bai jira amsar ta ba ya nufi ƙofa, Ameen ya bi shi da kallo har ya fice, yaransa suka mara masa baya cikin gudu wai sai sun bi shi. Ya dauke idonsa daga bakin ƙofar yana ɗan furzar da numfashi, akan syringe ɗin allura dake ƙasan gadon idanunsa suka sauka, ya ɗauke kansa ya mayar kan Neehal wadda ƙirjinta ban da bugawa babu abun da yake. Ya ɗan lumshe idonsa ya buɗe sannan ya janye bargon daga kanta tare da ɗora hannunsa ɗaya akan goshinta. Ta buɗe ido cikin tsoro wanda hakan yay dai-dai da zubar wasu sabbin hawayen, cikin muryar marasa lafiya ta ce “Yaya!” Cikin muryar da bata taɓa zaton zai mata magana ba nan kusa ba ma yanzu ba ta ji ya ce “Na’am.” A matuƙar sanyaye. Ta kama ɗayan hannunsa tare da fashewa da kuka ta ce “I’m sorry.” Ya taune lip ɗinsa sannan ya ce “For what?” Ta yi shiru sai kukan ta cigaba da yi tana ƙara k’ank’ame hannunsa cikin nata. Ya shafa kuncinta da ya jik’e da hawaye ya ce “Stop crying Miemerh, kin ga baki da lafiya, kuma You promised to me kin daina.” Cikin matuƙar mamakin yanda yake mata magana cikin sanyin murya mai cike da tsantsar kulawa ta tashi zaune tana yamutsa fuska tare da goge hawayen fuskarta da bayan hannunta. Ta kwantar da kanta akan ƙafaɗarsa, tana sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da ƙara lafewa a jikinsa. A hankali ya ce “Ya jikin naki?” Ta ce “Ya yi sauqi, Uncle ya mun allura.” Ya ce “Na gani ai.” A zaton ta gatse yay mata sai ta ce “Dagaske fa Yaya.” Bai kuma magana sai hannunsa da ya ɗora akan cikinta ya ɗan danna cikin. Ta ce “Aushh! da zafi fa Yaya.” Ya ce “Ba haka Mama take miki ba?” Ta matso k’walla ta ce “Ai itama yana mun zafi idan tay mun.” Ta cire hannunsa daga kan cikin tare da ƙoƙarin saukowa daga kan gadon, jikinta lullub’e da bargo. Ya riƙe ta tare da faɗin “Where are you going?” Ta ce “Toilet.” Ya sake ta, ta sauko tana ƙara rufe jikinta da bargon, locker mudubi ta nufa tana jan ƙafa da ƙyar ta janyo ta ɗauki abu a leda, ba tare da juyo ba ta shige toilet. Ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo da idonsa kan gadon, abun da ya gani a zanin gadon dai-dai inda ta tashi ya ƙurawa ido. A hankali ya tashi ya cire zanin gadon gaba-ɗaya ya ajiye a ƙasa. Ta yi kusan 30 minutes a toilet ɗin sannan ta fito, har lokacin yana zaune a ɗakin idanunsa a lumshe. Tana yamutsa fuska ta ƙaraso, ganin zanin gadon a ƙasa ta ji wata irin kunya ta lullub’e ta domin ta gane ɓaci ya yi, bata kalli inda yake ba ta faɗa kan gadon ba tare data saka wani zanin gadon ba, kwanciya ta yi tare da juya masa baya. Sai a lokacin ya buɗe idonsa ya kalli bayanta. “Miemerh!” Ya kira sunanta, ta ce “Na’am.” Ya ce “Juyo.” Ba musu ta juyo, amma bata iya kallon fuskarsa ba. Cikin muryar da idan yay mata magana da ita take bala’in tsorata ta ji yana cewa. “Ina gurin aiki aka kira ni baki da lafiya kuma Mama bata nan, hankalina a tashe na baro abubuwan da nake na taho dan taimakon ki, amma ina zuwa na tarar dake a jikin wani.” Ya ɗan taune lip ɗinsa sannan ya miƙe ya zuba hannayensa duka a aljihu ya ce “I will punish you, kin san ba ay mun laifi in ƙyale.” Ta saka kuka zata yi magana ya ce “Shiiii.” Sannan ya ɗan sunkuyo da kansa kusa da fuskarta a hankali ya ce. “Just Sleep.” Ta had’iye kukan nata tare da lumshe ido. Ya shafi gashin gigirarta ya ce “I will go, idan ya dawo ma still ki kuma ɗane jikinsa.” A firgice ta ce “Wallahi Yaya allura yay mun, kuma su Aunty Dije suna nan yay mun ka tambaye su ka ji, dan Allah Yaya ka yi haquri kar ka faɗawa Mama.” Bai ce komai sai iska da ya shiga hura mata a fuska daga cikin bakinsa. Ta ja hanci tare da turo baki gaba tana cigaba da tsiyayar da hawaye, a hankali ta ji wani irin bacci na fizgarta, 80% na ciwon cikin d’azu ya tafi, yanzu kaɗan_kaɗan yake mata. Jin saukar numfashinta alamun ta tafi duniyar bacci, ya gyara mata kwanciyar kanta akan pillow sannan ya juya fice daga ɗakin. A falo ya tarar da su Dije, ya sanar musu ta yi bacci su kula da ita. Suka amsa masa cikin girmamawa tare da fatan Allah ya tsare hanya. Da Ahmad ya dawo ko saman bai kuma hawa ba, ya bawa su Dije magungunan da ya siyo mata bayan sun sanar masa ta yi bacci. Ya kuma ba su sallahun idan ta tashi su ce mata ya wuce Abuja. Ba dan wayar da ake ta zabga masa ba a gurin aiki da babu abun da zai sa ya koma Abuja a yau, ko dan rashin lafiyar Neehal. Dan ma ciwon nata na lokaci ɗaya ne, ya san nan da anjima zata wartsake Insha Allah. Amma sosai tausayinta ya cika masa zuciya, na ganin tana cikin mata masu shan wahala a lokacin al’adar su.