NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A falo Neehal ta zauna bayan ta fito, bata koma bedroom ba. Tana zaune a nan Ameen ya fito daga ɗakin. Ta kalli agogon dake falon ta ga goma na safe ta wuce, ta ce masa “Yaya me za’a girka for lunch?” Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta, ya ce. “Tun yanzu?” Ta ce “12 za ni gurin aiki ne, shi yasa.” Ya ce “Ki dafa ko me kike so.” Ta ce “Ka faɗa dai, kar in dafa abin da baka ci, ko kuma wanda Aunty Hafsah bata ci.” Ya ce “Ita ai bata iya cin abinci, for me kuma ko me kika dafa i will eat.” Ta ce “Ko tuwo ne?” Ya harare ta. Ta tashi tana dariya ta sauka ƙasa, ya bi ta da kallo. A falon ƙasa ta samu ƴan’mata guda biyu masu aikin gidan, ta shiga kitchen ba tare data musu magana ba. Kamar yadda ta tsokani Ameen tuwon ta ɗaura, duk da itama bata wani ci sosai amma kawai sai ta ji shi take son yi. Tuwon semo ta yi, miyar zogale tare da taimakon ƴan’mata nan, wanda bayan shigowar ta kitchen ba jimawa suka biyo ta wai za su taya ta aikin, ta ce musu to bismillah. Suna aikin suna mata hira, dan surutu ne da su ba kaɗan ba, farkon hirar kyawunta suka fara yabawa, har suna cewa sun kasa gano waya fi kyau tsakanin ita da Ameen. Yanda suke acting a hirar sai suke bata nishad’i, ta dinga murmushi, wani abun kuwa idan sukay dole sai ta dara, because they are so commedians. Sai ta ji daɗi a ranta ta samu masu ɗebe mata kewa a gidan, kuma ga su yara ne ba za su wuce 18 years ba. Ta tambaye su sunayensu suka sanar mata, Harira da Saude. Ba ta gama girkin ba sai kusan 12, saboda da ɗan yawa ta yi saboda ta san za’a iya yin baƙi ƴan zuwa dubiya, ta kwasawa Ameen nasa daban a cikin ƙaramar warmer, ta ce wa su Saude idan ya zo neman abincinsa gashi nan. Ta ɗibi kaɗan ta ci saboda saurin da take yi ta tafi gurin aiki dan ta yi late, bayan ta gama ci ta hau sama ta shirya cikin sauri ta fito ta shiga ɗakin Hafsah ta sanar mata zata tafi, kamar an mata dole ta ce ta je driver ya kai ta. Direban gidan ne ya kai ta gurin aiki kamar yadda Hafsan ta faɗa, ba ta ga Ameen ba kuma bata ga Motarsa a parking space ba, hakan ya tabbatar mata da baya gidan kenan.

Ƙarfe Shida na yamma ta tashi daga aiki, tun kafin ta fito daga office aka aiko an zo ɗaukarta. Bayan ta fito ta ga direban gidan Ameen ne, dama da ya kawo ta ya tambaye ta ƙarfe nawa zata ta tashi ta sanar masa. Bayan ta koma gidan ta shige ɗaki bata fito ba har akay Magriba, saboda baƙin da ta ga an yi. Tana zaune akan sallaya suna chat da Sadik aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta d’ago tana dubansa tare da amsa masa sallmar da ya yi. Ta ajiye wayar ta ce “Sannu da zuwa Yaya.” Bai amsa mata ba ya zauna a kusa da ita. Ta ɗan lumshe ido ta buɗe saboda k’amshinsa da ya cika mata hanci. Ta yi ƙasa da kanta saboda yanda ta ga yana kallon ta, lokuta da dama tana mamakin yanda yake yawan kallon ta, ta kan tambayi kanta ko kallon na mene ne? Ganin ba shi da niyyar magana ta ce “Mun yi waya da Mama ta ce, idan tana free za su zo anjima ita da Daddy.” Ya ce “Allah ya kai mu.” Sai kuma ya ɓata fuska ya ce “Dama zuwa kika yi dan kina bari na da yunwa?” Ta masa kallon mamaki ta ce “Yunwa kuma Yaya?” Ya ce “Eh.” Ta yi murmushi dan gano bakin zaren, ta ce. “Amma dai ka ci wani abun?” Ya girgiza mata kai, ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi ta ce, “Da ka ci tuwon Yaya ko kaɗan ne, ya yi daɗi fa, nima na ci, amma shine ka zauna da yunwa.” Ya ce “Ai baki so in ci ba dama.” Ta ce “To yanzu bari in tashi in dafa maka wani abun ka ci, me kake so in dafa maka Yayana?” Ya ce “No ki huta I knew you are tied.” Ta ce “Zan iya fa Yaya, ai na huta.” Ya ce “No ki bar shi, mu je dai ki raka ni unguwa.” Ta ce “Toh Yaya.”

Ya miƙe ya fita, ta tashi ta cire hijabin jikinta ta ninke, sannan ta ɗauko mayafin abayar dake jikinta ta yane kanta da shi, ta fesawa jikinta turare kaɗan sannan ta ɗauki wayoyinta ta bi bayan shi. A falo ta zauna jiran shi, ba jimawa ya fito daga ɗakinsa inda Hafsat take a yanzu. Da ido yay mata alamar ta tashi su tafi, ba tare ta ce komai ba ta miƙe ta bi shi a baya. A falo ta tarar da su Harira suna kallo, su kai musu a dawo lafiya. Restaurant suka je ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya biya ya siyo mata ice-cream da choculate da ya san tana matuƙar son su. A hanyar dawowa ta shagwab’e fuska ta ce “Yaya ka kai ni in ga Mama, sai mu dawo.” Ba tare da ya dube ta ba ya ce “Ba ta ce zasu zo ba?” Ta ce “Ai na san da ƙyar za su zo, dama haka ta ce sai ta samu time.” Bai kuma magana ba bai kuma kaita gidan ba, gidansa suka koma. Bayan an yi Sallar isha’i ta ci abinci sai ta sauko ƙasa gurin su Harira dan su yi hira. Saude ta ce “Mai kyau, d’azu na gan ki a talabijin.” Neehal ta yi murmushi ta ce “Ni kuma? ba ni ba ce gaskiya, sai dai mai kama da ni.” Saude ta ce “Alkur’an ke ce, da na je kaiwa Hajiya kifin data ce in sake d’umama mata ne na ga mai_gidan yana kallo, kuma har ɗan tsayawa na yi na ga kayan da kika fita da su ne a jikin wadda na gani.” Neehal ta yi ƴar dariya saboda yanda Sauden ta yi maganar ta ce “Ƴan biyu ce ni ai, to ɗayar kika gani ba ni ba.” Saude ta ce “Tab’ amma kuna kama sosai, har fa yanda kike yi da idonki haka take yi.” Neehal ta ce “Ya nake da idon?” Harira ta gyara zama ta ce “Ni zan gwada miki.” Sai ta wani lumshe ido ta buɗe tare da keɓe baki ita a dole iyayi take tana gwada yanda Neehal take magana. Neehal ta yi dariya sosai wadda ta ƙara fito da kyawun fuskarta, kumatunta suka lotsa kamar an cire naman gurin. Saude ta taɓa dai_dai gurin cikin santi ta ce “Ke kam ki godewa Allah, ya baki kyau, wannan abun yana ban sha’awa, tun ɗazu in kina magana shi kawai nake kallo.” Neehal ta ce “Allah ya baki miji mai irinsa, sai ki yi ta kallon sa.” Saude ta washe baki ta ce “Allah ya amsa bakin ki mai kyau.” Suna cikin hirar su mai daɗi dake sanya Neehal nishad’i Ameen ya shigo falon, sai ta ga su Harira cikin sauri sun tashi sun shige ɗakin da suke bayan sun masa sannu da zuwa. Neehal ta bi su da kallo, sannan ta mayar da idonta kan Ameen dake kallon ta hannunsa riƙe da leda, ta ɗan ɓata fuska ta ce “Sannu da zuwa.” Ya ce “Yawwa.” Tare da shiga kitchen ya ajiye ledar hannunsa, ya dawo falon ya ce wa Neehal. “Miemerh Please ki shiga kitchen ki soyawa Hafsah kajin can.” Neehal ta ɓata fuska amma bata ce komai ba ta tashi ta shiga kitchen ɗin dan babu musu a tsakanin ta da shi. Ya bi bayan ta zuwa kitchen ɗin, ta juyo ta kalle shi, ya nuna mata inda kajin suke. Ta ɗauko tana turo baki gaba ta juye su a abu, a yayyanke suke a wanke tass. Ta ƙara ɗauraye su, ta ɗauko tukunyar da zata cinye su ta ɗauraye ta juye su a ciki, sannan ta saka musu magi da spices da ɗan yaji ta kunna gas ta ɗora. Duk abun da take yana tsaye yana kallon ta, ya jingina da ƙofar kitchen ɗin. Bayan sun mata yanda take so ta sauke ta tsame su ta zuba a cikin colander, sannan ta tsiyayo mai a jarka ta zuba a kasko ta ɗora akan gas ɗin. Ta ƙara juyowa ta ga har lokacin yana kitchen ɗin, ta turo baki ta cigaba da abun da take. Har ta fara soyawa bai fita ba, ita kuma duk ta takura kamar ta ce masa ya fita. Sai da ya gaji dan kansa ya fita. Tana soya na ƙarshe ya dawo kitchen ɗin, naman ya yi irin ƙarar nan da yake yi a cikin mai, har man ya ɗan fallatso mata a hannu. Ta ɗan ja baya tare da yarfe hannun, ya matso kusa da ita da sauri ya kama hannun yana dubawa. Ta shagwab’e fuska kamar zata yi kuka. Murya ƙasa_ƙasa ya ce “Sorry dear, don’t cry.” Ta kalli fuskarsa tana turo baki gaba tare da gyaɗa masa kai, Idanunsa suna kan hannunta hakan yasa ta ƙurawa fuskarsa ido kamar mai neman wani muhimmin abu a fuskar, sai da ya d’ago sannan ta yi saurin lumshe idonta tare da sakin ajiyar zuciya a hankali. Ta matsa daga kusa da shi tare da zare hannunta daga nasa. Ya ce “Zaki iya ƙarasa suyar kuwa?” Ta d’aga masa kai alamar eh. Ya juya zai fita cikin siririyar murya ta ce “Yayah.!” Ya juyo ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. Ta yi shiru dan ta kasa faɗar abun da yake ranta, ba yabo ba fallasa ya ce “What happened?” Ta ce “Nothing.” Yay mata wani kallo sannan ya juya ya fice. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta na mata wari irin lugude, wani b’arin na zuciyar kuma mamakin Ameen take, yanda yake mata magana babu faɗa bare haɗe rai, ko dan ta zo gidansa ne? Jiki a sanyaye ta kwashe sauran naman da ya fara k’onewa. Sai da ta kimtsa kitchen ɗin sannan ta fice. Tana komawa ɗaki ta tarar da missed call ɗin Mama da Ahmad. Mama ta fara kira, tana ɗauka ta ce mata. “Shine ba ku zo ba Mama?” Mama ta ce “A gajiye Dad ya dawo ne shi yasa, sai gobe Insha Allah, ina kika shiga nay ta kiran ki?” Ta ce “Ina ƙasa, wayar kuma tana sama a ɗaki.” Mama ta ce “Ya jikin Hafsan?” Ta ce “Da sauƙi.” Mama ta ce “Babu matsalar komai dai?” Ta ce “Nothing Mama, ina Dad?” Mama ta ce “Ya kwanta bacci, saboda gajiyar dake damun sa, shi yasa ni kiran ki ɗazu ai, kuma baki d’aga ba, yanzu kuma ya yi bacci.” Neehal ta ce “Ki gaishe shi idan ya tashi, har na fara kewarku Mama.” Ta ƙarashe maganar cikin shagwab’a. Mama ta ce “Rigimarki da yawa take Daughter, yau ma fa kin gan mu.” Ta ɓata fuska ta ce “Ni dai dan Allah ku zo gobe in gan ku.” Mama ta ce “Allah ya kai mu goben lafiya, daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Ahmad ta kira, kamar mai jiran kiran ringing ɗaya ya katse ya kira ta. “Princesss.!” Ya kira ta cikin shauƙi after she picked, ta ce “Uhm, Uncle ina yini?” Ya ce “Ga shi nan, babu daɗi tunda yau throughout ban ji muryarki ba.” Ta ce “To yanzu ai ka ji ai, sai ka ji daɗin.” Ya yi murmushi mai sauti ya ce “Ni da jin daɗi Baby ai sai ranar da aka kawo mun ke gidana a matsayin mata, na san zan yi farincikin da ban taɓa yin irinsa ba a rayuwata Princess, na san a ranar i war haka masu kawo mun ke sun tafi, sai mu kaɗai a gidanmu, muna making love.” Ta rufe fuska kamar yana gabanta cikin jin kunya, ya ce “Princess ban san irin son da nake miki ba, kuma na san duk bayanin shi da zan miki baza ki gane ba, amma da zarar kin zama tawa, I know you will understand more.” Ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, Ahmad da Sadik suna ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, ga abun da yake ƙara bata haushi idan tana tare da kowannen su Heart ɗinta shi kaɗai take tuna mata, ta rasa gane wa take so da k’auna a cikin su, zuciyarta ta kasa tantance mata wanda ya kamata ta zab’a a matsayin abokin rayuwarta. ‘Na barwa Allah zaɓi, Allah ka zaɓan mafi Alkhairi.’ Ta faɗi haka a cikin ranta. Ahmad ya cigaba da yi mata hira mai daɗi cikin iya tsara kalamai masu kwantar da zuciya. Har bacci ya fara cin ƙarfin ta, saboda gajiyar dake tattare da ita. Jin hakan yasa yay mata sai da safe ya katse wayar, tashi ta yi dak’yar tana lumlumshe idanuwa ta rage kayan jikinta sannan ta kashe hasken ɗakin, ta kunna fitilar gado. Har ta kwanta ta ƙara tashi ta kunna light ɗin ɗakin sannan ta shiga toilet ta yi fitsarin da ya matse ta, bayan ta fito ta kulle ƙofar ɗakin tare da kashe light, sannan ta hau kan gadon ta ware bargon dake ninke a gefen gadon daga gurin bango ta lullub’e jikinta. Da ƙyar ta iya yin addu’ar kwanciya bacci, saboda baccin dake cin ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button