NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Cikin dare ta yi juyi, haka Allah ya halicce ta indai zata yi juyi a bacci sai ta ɗan farka, kamar an ce ta buɗe ido sai ta ga kamar an turo ƙofar ɗakin an shigo, ta ware idanunta dan tabbatarwa gabanta na dokawa a million. kamar a mafarki ta ga ana nufo gadon ta ɗan hasken bedside lamp. Ta ƙara waro idonta ganin dagaske fa ita ake tunkarowa har anzo bakin gadon, ta yunƙura ta tashi zaune cikin rawar jiki tare da ware baki da nufin ta ƙwala ƙara, amma sai ta ji ana fesa mata wani abu a fuska kamar shantos, ta fara jujjuya kai a ƙoƙarin ta na nemo iskar Ubangiji ta shak’a ba wannan abun mai wari da ake fesa mata ba. Cikin sakanni ƙalilan hankalinta ya gushe daga jikinta, daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba………✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
5️⃣6️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#
………..Alarm ɗin da ta saita wayarta da shi wanda yake tashin ta idan ta koma bacci bayan sallar asuba shi ya tashe ta ƙarfe 6:30 am. Ta ja gwauron numfashi sannan a hankali ta buɗe idonta da sukai mata nauyi, ɗakin data ke ta fara bi da kallo, a hankali ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata inda take da kuma abun da ya faru a farkawar da tay daren jiya. Ta yunƙura ta tashi zaune da sauri cikin matuƙar tsoro zuciyarta na mata wani irin bugu kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Ta kalli ƙofar ɗakin ta ga babu alamar an buɗe ta a rufe take ruf, ta dawo da idanta kan gadon da take ta kalli gefen ta, shima babu alamar an yi wani abu a gurin. Ta yaye bargon dake lullub’e a jikinta da sauri ta shiga duba jikinta, amma babu alamar ko hannu an ɗora a jikin nata. Ta miƙe cikin rawar jiki ta sauko daga kan gadon ta yi taku uku ta ji ta rass, babu alamar wani ciwo a jikinta. Dafe kanta ta yi da hannunta a fili ta ce “Ko mafarki na yi ne?” Ta ja numfashi mai ƙarfi hakan yasa ta ji warin abun da aka fesa mata jiya ta cikin mak’oshinta. Ta kai hannu ta shafa fuskarta sai ta ji wani abu mai maik’o a fuskar kamar ta shafa mai. Ta goga hannunta sosai a fuskar sannan ta kai hannun hancinta ta shinshina. Tsoron ta ne ya ƙaru jin warin abun da aka shak’a mata, hakan ya tabbatar mata da ba mafarki ta yi ba, da gaske wani ko wata ya shigo ɗakin nan jiya, kuma ga dukkan alamu cutar da ita ake son yi tunda gashi an fesa mata abun da ya gusar mata da hankali. ‘To waye? Kuma me yake nema a gurin ta?’ Tsoron ta ne ya ƙaru sosai kamar a yanzu ne aka shigo ɗakin, ta nufi ƙofa da sauri cikin kyarmar jiki ta buɗe ta fita falo da gudu a gigice. Ameen yana zaune akan carpet yana karatun Alqur’ani a hankali, ya ji an buɗe ƙofa da ƙarfi, ya juya da sauri idanunsa suka sauka a kanta. Ta ƙaraso inda yake da gudu ta faɗa jikinsa ta baya tare da fashewa da kuka. A ruɗe yake tambayar ta me ya faru ganin gaba-ɗayanta a firgice take. Ta kasa magana sai ƙofar ɗakin kawai take nuna masa. Ya matsar da Alkur’anin gaban sa gefe, ya dawo da ita gaban sa, tana ƙoƙarin ƙara ruk’unk’ume shi ya riƙe ta, cikin damuwa ya ce “Miemerh! Mai ya faru? Talk to me please.” Cikin sheshshek’a ta ce “Wani ne ya shigo ina bacci, ya fesa mun wani abu a fuskata, dan Allah Yaya ka mayar da ni gurin Mama kar ya ƙara dawowa.” Ta ƙarashe zancen tare da faɗawa ƙirjinsa ta k’ank’ame shi, ilahirin jikinta rawa yake. Fuskantar da ya yi a tsorace take sosai, sai ya saka hannunsa ya zagaye bayan ta da su, a hankali ya shiga karanto addu’a yana tofa mata, dan ya fi zaton mafarki ta yi wanda ya firgita ta. A hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya, rawar da jikinta yake ta ragu. Jin haka yasa ya d’ago ta daga jikinsa, ta buɗe idonta dake shatatar da hawaye ta ce “Ni dai ka kaini gurin Mama dan Allah Yaya.” Yana gyara mata gashin kanta da ya barbazo saman fuskarta ya ce “Relax Miemerh, babu komai fa, may be mafarki kika yi, dan babu wanda zai iya shigowa cikin gidan nan, saboda gaba-d’aya doors ɗin a rufe suke, ni da kaina na rurrufe su. Kuma babu ta yanda za’a iya haurowa a shigo, bare na ce ko haurowa akay.” Cikin kuka ta ce “Wallahi Yaya ba mafarki na yi ba gaske ne.” Ta bashi labarin duk abun da ya faru, cikin tashin hankali yake kallon fuskarta. Ta kai hannunsa kan fuskarta_ta, ta ce “Ka taɓa ka ji Yaya zaka ji wani abu kamar mai yana wani irin wari, kuma ni ban shafa komai ba kafin na kwanta.” Bai ce komai ba ya sake ta ya miƙe ya nufi ɗakin, ta miƙe itama da sauri ta bi bayan shi. Dudduba ɗakin ya yi gami da toilet amma bai ga kowa ba, bai kuma ga wata alamar an shigo ba, ya tsaya yana sauke numfashi, shi kansa hankalin shi ya tashi ba kaɗan ba, saboda tabbatarwar da ya yi an shigo ɗin ba ƙarya ta yi ba, ya gane hakan ne ta ƙofar bantlation ɗin ɗakin da ya tura ya ji ta a buɗe, kuma shi ya san a rufe suke barin ta, tunda suka zo gidan ma zai iya k’irga time ɗin da aka buɗe ta. Neehal kam duk inda ya ɗora ƙafarsa nan take ɗora ta_ta, hannunta riƙe da nasa tana faman tsiyayar hawaye. Ya kamo fuskarta yana kallon idonta cikin tashin hankali ya ce “Kuma baa ki gane kowa ne ya shigo ba?” Ta girgiza kai ta ce “Ban gane ba Yaya, ai time ɗin ɗakin babu haske sosai, kuma cikin bacci ne idona bai gama washewa ba, da ƙyar ma na iya tashi zaune.” Ya saki fuskarta ya ɗan lumshe idonsa a hankali tare ciza lip ɗinsa, tsawon wasu sakanni sannan ya buɗe idon ya ce “Kin yi Sallah?” Ta girgiza masa kai alamar a’a. Ya ce “Je ki yi.” Ta ce “Toh Yaya karka fita dan Allah, ka jira ni in fito tsoro nake ji.” Ya gyaɗa mata kai kawai sannan ya koma bakin gado ya zauna tare da tallafe kansa da hannayensa guda biyu ya faɗa duniyar tunani. Harta fito ta zira abayar data cire jiya ta zira hijabi ta tayar da Sallah bai yi ƙwaƙkwaran motsi ba. Sai bayan ta idar ya tashi ya fita ba tare ya ce komai ba, ta bi bayan shi da sauri dan gani take kamar tana kadaicewa za’a kuma zuwar mata. Dawnstairs ya sauka ya fice daga part ɗin gaba-ɗaya. Ganin su Harirah suna kaikawo a falon ƙasa sai ta zauna a nan dan jiran shi. Wata irin kalasa take ji a jikinta, ga wani bacci_bacci dake fizgar ta, da alama abun da aka shak’a mata har yanzu bai bar ta ba, amma tsoro da fargaba sun hana baccin ɗaukar ta. Ameen ya jima a wajen kafin ya dawo, dan sai wajen 8 ya dawo. Neehal ta takura masa da kukan ita dai ya mayar da ita gida gurin Mamanta, dole ba dan yaso ba ya mayar da itan, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba balle su yi sallama da Hafsah, dan ko saman ƙin komawa ta yi. Cikin mamaki ganin su a wannan lokacin Mama ta tarb’e su, bayan sun zauna Neehal ta mata bayanin abun da ya faru cikin kuka. Hankalin Mama fa ya tashi ba kaɗan ba, ta je ta taso Daddy ta faɗa masa abun da yake faru. Cikin damuwa ya ƙaraso part ɗin Mama ya ƙara tambayar Neehal ƙarin bayani, ta faɗa masa. Daddy ya ce, ta kwantar da hankalinta Insha Allahu koma waye Allah zai toni asirinsa. Ameen kuwa ya tabbatarwa Mama da Daddy cewar, akwai binciken da zai yi koma mene ne zai gano da yardar Allah. Mama kuwa sai da ta caje ƴarta ciki da waje ta ga babu abun da akai mata sannan hankalinta ya ɗan kwanta. A daren ranar Neehal ƙin kwanciya ta yi a ɗakinta ita kaɗai, saboda a tsorace take, sai a ɗakin Mama suka kwana tare da Maman. Washegari da safe Ameen ya kawo mata kayanta, tare da saƙon Hafsah na ta tafi babu ko sallama, dan Ameen bai sanar mata abun da ya faru ba.