NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

AFTER FOUR MONTHS
Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu na final year first semester, 8 weeks da suka wuce, and now suna shirye_shiryen fara first semester level Four exam. A ɓangaren soyayyarta da Ahmad da Sadik kuwa kowa yana nan yana zuba mata gwanintar sa, ita kuma ta dage da addu’ar neman zaɓin Allah. Every weekend sai Ahmad ya zo Kano ya gan ta, sai da randa aka samu wani akasi ne ba ya zuwa, jiki da jini sai Allah. wani Ikon Allah ba su taɓa haɗuwa da Sadik ba, sai dai sun haɗu da Ameen ba iyaka, dan shi kullum sai ya zo gidan da daddare. Har wata rana ya kasa haquri ya tambayi Mama, wai me Ahmad yake zuwa yi gidan ne, A tak’aice Mama ta ce masa zumuncin Allah yake zuwa. Kafin Neehal su koma school ta je Gombe ta kwanar musu biyu, haka ma ta je Abuja gidan Yayan Dad da gidansu su Hameedah, har gidan su Ahmad ta je. Ta ga karamci da k’auna a gurin ahalin Ahmad, twins suka dinga murna Aunty ta zo gidan su. A ɓangaren Sadik kuwa, bayan mahaifinsa ya gudanar da binciken da ya ce zai yi ya zo ya sanar musu cewar gaskiya ne abun da Umma take faɗa akan Neehal. Hajiyarsu da Kawu suka ce dole sai dai Sadik ya rabu da Neehal ya nemi wata yarinyar ya aura. Shi kuma ya ce ba zai iya ba, dan ba zai iya rayuwa babu ita ba, ya ƙi ci ya ƙi sha, ya tada hankalinsa, damuwar da ya sanya wa ransa gami da yunwa suka taru suka haifar masa da ciwo mai tsanani, wanda har ya kai shi ga kwanciya a gadon asibiti. Hankalin Maamah dana Abba ya tashi ba kaɗan ba, Maamah ta kira iyayenta ta sanar musu halin da ake ciki. Mahaifin Maamah da ya zo duba Sadik ya ji abun da yake faruwa yay ta faɗa, ya ce wannan ba hujja ba ce wadda za’a hana Sadik auren Neehal, da mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke, sai ya rabu da Neehal ɗin kuma idan kwanansa ya ƙare dole ya tafi, dan haka shi zai tsayawa Sadik ɗin a auransa da Neehal, tunda ita yake so. Wannan magana ta Abeey (mahaifin Maamah) ita ta sanyayawa Sadik rai gami da ƙwarara masa gwiwa, har ya fara kwantar da hankalinsa ya samu lafiya. Hajiya da Kawu kuwa suka ce babu saka hannunsu a wannan al’amarin, dan haka duk abun da ya faru da Sadik babu ruwan su. Abeey ya ce “Babu abun ma da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi.” Abbansa kuwa bin al’amarin kawai ya yi da addu’a, dan ita ce mafita. Sadik ya so tun lokacin a zo a yi maganar auran su da Neehal, amma Maamah ta dakatar da shi ta ce, ya bi komai a sannu, ya bari ya ƙarasa ginin gidansa and kuma akwai lefe, dan haka idan ya gama shiryawa sai aje a yi maganar auren, a saka lokaci ƙanƙani a yi a wuce gurin.
A month ɗin da ya wuce ne asirin Safeenah wadda tasa aka sace su Afrah ya tonu. Ta hanyar Gaye wanda jami’an tsaro suka samu nasarar kama su shi da yaransa akan dukan da suka yiwa Saudart. Bayan an kama sun ne ya yi bayanin dalilin dukan da sukay mata. Daga Zariya aka je har Abuja aka kamo Safeenah, wadda zuwa lokacin duk ta fige ta rame saboda zullumi da tsoro. Babu wanda bai yi mamakin jin Safeenah ce ta saka a sace su Afrah ba, kasancewar ta ƙanwar Mahaifiyarsu ta jini. Mamanta tay ta kuka tana Allah wadai da halin ta, duk da ba shiri suke da Ammi kishiyar ta ba, amma bata taɓa tsammanin ƴarta zata cutar da ahalinsu har haka ba. Ahmad ma ya sha mamaki ba kaɗan ba, duk da ya san Safeenah tana sonsa amma bai taɓa tunanin son zuciyarta har ya kai haka ba, dan shi a gurinsa wannan hauka ne da jahilci ba so ba, dan duk mutumin da yake k’aunarka to zai so ƴaƴanka. Safeenah ta yi nadama mara amfani ita da ƙawarta Saudat, dan har ita Alk’ali ya tisa prison bayan an gabatar da su a gaban kotu bisa laifin bayar da kwangilar kisan kai, duk da bata gama warkewa daga jinyar dukan da yaran Gaye sukay mata, sai dai an cigaba da ɗora ta akan magani a gidan kason.
Yau ta kama ranar Alhamis, misalin ƙarfe huɗu da mintuna na yamm Neehal ta dawo gida daga school. A falo ta ajiye handbag ɗinta da sauran tarkacen school, kitchen ta nufa saboda hango Mama da ta yi a ciki. “Mama sannu da aiki, am back.” Ta faɗi haka bayan ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce “Sannunki da zuwa, shine zaki shigo mun babu sallama.” Ta ƙarasa ta rungume Mama ta baya a shagwab’e ta ce “Na yi sallama fa ba ki ji ba ne. Mama duk na gaji yau ɗin nan.” Mama ta shafi kuncinta ta ce “Ki je ki yi wanka ki sakko ki abinci, idan kin huta akwai maganar da za mu yi.” Ta bar jikin Maman tare da faɗin “Tom Mamana, Yaya ya kawo miki saqo ki bani?” Mama ta ce “Ya kawo tun safe, ki duba kan mudubi zaki gani.” Ta ce “Me ya kawo mun?” Mama ta ce “Ban duba ba, ki je ki gani, zaki gan shi a cikin leda.” Ta juya cikin murna ta fice daga kitchen ɗin. Ɗakinta ta fara shiga ta yi wanka, bayan ta shirya ta je ɗakin Mama ta ɗauki ledar da Ameen ya kawo mata ta buɗe. Kwalin sabuwar waya ta gani kamfanin iPhone, ta shiga buɗe kwalin da sauri ta zaro sabuwar wayar ta shiga jujjuya ta a hannunta cikin tsananin murna, da sauri ta tashi ta sauka ƙasa ta shiga kwad’awa Mama kira. Mama ta fito falo da sauri jin kiran tana faɗin, “Ke lafiya kike mun wannan kiran?” Ta rungume Mama tana murmushin farinciki ta ce “Mama Yaya ya siyo mun sabuwar phone.” Mama ta yi murmushi tare da zare ta daga jikinta ta karɓi wayar tana kallo ta ce “Congratulation Dear, Ameen ya hutar da ni, na huta da mitar kullum Mama anyo sabuwar waya kaza ki siya mun ko ki sa Dad ya siya mun.” Neehal ta yi dariya ta ce “Mama tun sanda result ɗinmu na last semester ya fito na nuna masa, da ya gani shine ya ce na yi ƙoƙari sosai me nake son na siya mun? Na ce masa kome ne ma ina so. Ni har na manta mun yi haka da shi, ashe shi bai manta ba yana sane. Jiya da ya zo da daddare shine ya ce mun zai kawo mun sak’ona yau na alƙawarin da yay mun.” Mama ta ce “Ya kyauta sosai, sai kira shi ki yi masa godiya.” Ta ce “Toh Mama bari na saka wayar a chaji.” Mama ta bata wayar ta koma sama. Bayan ta saka chajin ta sauko ƙasa ta ɗebo abinci ta ci.
Tana gama cin abincin ta ɗauki wayarta ta kunna data, ko 5 minutes ba ta yi da ɗaukar wayar ba kiran Ahmad ya shigo. Ta yi murmushi sannan ta d’aga ta kara a kunnenta, muryar su Afrah ta ji a maimakon ta Ahmad, suna kiran sunanta cikin karaɗin su. “Aunty! Aunty!” Ta ce “Na’am, Yaran kirki dafatan kuna lafiya?” Amrah ta ce “Lafiya k’alau Aunty.” Ta ce “Ina Ummi da Aunty Zahra da Abba?” Suka ce “Suna gida.” Ta ce “To ku gaishe su.” Suka shiga yi mata hirar makarantarsu da bata labarin kayan wasan da Daddy ya siyo musu. Ta ce “Lallai ƴan gatan Daddy, ina Daddy’n yake?” Amrah ta ce “Gashi nan a kwance, bashi da lafiya.” Cikin damuwa ta ce “Bashi da lafiya kuma, me yake damunsa?” Ahmad dake kwance yana sauraren su ya tashi zaune tare yi musu alamar su kawo masa wayar. Amrah ta ce “Ya tashi Aunty, ya ce na bashi wayar.” Yarinyar ta miƙa masa wayar, ya karɓa ba tare da ya cire ta a speaker ba ya ce “Princesss.!” Cikin kasalalliyar murya. Ta ce “Na’am Uncle, meke damun ka?” Ya sauke numfashi ya ce “Babu komai.” Cikin shagwab’a ta ce “Please Uncle ka faɗa mun, hankalina gaba-d’aya ya tashi da aka ce mun baka da lafiya.” Ya ce “Ba ciwo nake ba Princess, kawai ina jin wani iri a cikin zuciyata kamar zan rasa ki.” Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Twins dake kallon sa suna sauraren su duk da ba fahimta suke ba, Afrah ta ce “Daddy Aunty ta yi shiru, ko ta kashe wayar ne?” Ya ce “A’a bata son magana da ni ne, Aunty ku kaɗai take so bata so na.” Yarinyar ta waro Ido ta ce “She like you Daddy.” Ya ce “No, ask her?” Yarinyar ta ɗauki wayar da sauri tare da ɓata fuska ta ce “Aunty wai bakya son Daddy’n mu?” Amrah ta tari numfashin ƴar’uwarta da sauri da faɗin “Daddy yana da kirki fa Aunty.” Neehal ta sauke numfashi tare yin murmushi domin ta gane wayo Ahmad ya shirya mata. A hankali ta ce “Ina son Daddy sosai Yarana, wasa yake muku.” Ahmad ya lumshe idonsa tare yin wani sassanyan murmushi, duk da ba direct shi ta faɗa wa tana son shi ba amma kalmar ta doki zuciyarsa. Afrah ta kama hannunsa ta ce “Daddy Aunty ta ce tana sonka.” Ya girgiza kai ya ce “Ai bata faɗa mun ba, ku ta faɗa wa.” Cikin shagwab’a Amrah ta ce “Aunty please ki cewa Daddy kina son shi, tunda kina son mu ai kina son Daddy’n mu ko?” Ta ce “Eh mana, bawa Daddy wayar za mu yi magana da shi.” Ya karɓa ya cire ta a speaker sannan ya kara a kunnensa ya ce “Uhm? ina jin ki.” Ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, ta ce. “Uncle meke damun ka?” Ya ce “Babu komai sai son ki Princess.” Ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Ya yi ƙasa da murya ya ce “Princess please say you love me, baki taɓa faɗa mun ba fa.” Ta ce “Gashi nan kai ka faɗa, kuma already You know I…..” Sai kuma ta yi shiru. Cikin zak’uwa ya ce “Please Princess say it, ko zan ji daɗi a raina.” Ta lumshe ido cikin shauƙi tare da yin ƙasa da murya sosai ta ce “I Love You Doctor Ahmad!” Sai kuma ta yi saurin zare wayar daga kunnen ta, ta yi hanging up. Sai jin ɗil ya yi alamun ta kashe wayar. Ya yi murmushi cikin tsananin farinciki ya ajiye wayar a gefen sa, sai ya tuno lokacin da tana ƙarama da ya ce mata I love You, ta ce “Love You too Uncle.” Ya janyo ƴaƴansa da suka fara wasan su da sabbin teddy’s ɗin da ya siyo musu ya rungume su a jininsa ya ce “Aunty ta kusa dawowa nan gidan mu zauna tare da ita.” Yaran suka waro suka ce “Daddy When?” Ya ce “Soon Insha Allah.” Sai suka bar jikinsa suka fara murnar Aunty zata dawo gidansu.” Ahmad ya bi su da kallo yana tunanin farincikin da kids ɗinsa za su yi idan ya auri Neehal, da shi da his kids suna buƙatar ta a cikin rayuwar su, yaran suna sonta sosai dan har mamakin hakan yake, dan yanzu komai za su yi sai sun ambaci sunan Aunty, in unguwa suka ce suna dawowa za su je akira musu Aunty su bata labari, idan makaranta ce ma haka ne. Ya koma ya kwanta tare da janyo pillow ya rungume a ƙirjinsa gami da lumshe idonsa. A daa ya bar Neehal ta ƙarasa school ɗinta kafin ya tura a yi maganar auransu, amma a yanzu sai yake ganin kamar ba zai iya jiran watannin da suka rage mata ba ta ƙarasa karatun, ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba. A ɓangaren Neehal itama lumshe ido ta yi ta kwanta a jikin a kujera bayan ta katse wayar da murmushi ɗauke akan fuskarta. ‘Uncle rigima.’ Ta faɗi haka a ranta. Ƙarar shigowar text message cikin wayarta yasa ta buɗe ido ta ɗauki wayar ta duba, kamar yadda ta zata shine yay mata text ɗin, ta shiga karantawa a zuciyarta kamar haka. Thank You so much Princess, you make me Happier, I love you so much. Ta yi murmushi ba tare da ta yi masa reply ba ta tashi ta haye upstairs………✍️



