NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

5️⃣7️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..Bayan Sallar Magriba Neehal tana zaune a falon ƙasa tana sauraren karatun Alkur’anin dake tashi a cikin speaker, wanda ta yi connecting ɗinsa da wayarta. A hankali take bin karatun idanunta a lumshe. Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo tare da yin Sallama cikin kamilalliyar muryarsa. Bata ji sallamar ba ma hankalinta yana kan karatun, har ya nemi guri ya zauna, k’amshin turarensa ne ya fargar da ita zuwan sa. Ta buɗe idonta da sauri tare da tashi daga kishingid’en da take. Ta waro Ido cikin murmushi tana kallon sa, kamar yadda shima yake kallon ta. Ta saka stop a karatun, sannan ta tashi ta koma ta zauna a kusa da shi. A hankali ta ce “Ina yini Yaya.” Ya ce “Lafiya k’alau.” Ta ce “Ya Aunty Hafsah?” Ya ce “Tana nan k’alau.” Ta murmusa ta ce “Yaya na ga sak’on ka, thank you so much, Allah ya ƙara buɗi mai albarka.” Ya lumshe ido ya buɗe a kanta ya ce “Amin.” Ta miƙe tare da faɗin, “Bari na kira Mama.” Bai ce komai ba har ta haye upstairs. Ta shiga ɗakin Mama da sallama, Mama dake shiryawa ta amsa mata, ta ce “Mama Yaya ya zo, yana ƙasa.” Mama ta ce “Okay I will come.” Ta juya ta koma ƙasa ta zauna a kusa da shi, ta shiga aikin kallon sa, shi kuma yana ta aikin latsa waya. Sai ta ga kamar ƙara kyau yake, ko dan ƙarshe ne shi a iya wanka da iya ɗaukar dressing. Ta kalli bak’ar sumar kansa wadda daga gani babu tambaya ba ƙaramin kuɗi ake kashe mata ba. Ta lumshe ido a ranta tana faɗin ‘Ba a ƙasa ya ɗauki gayu ba, dan Mama ƙarshe ce itama a wannan fannin. Mama ta shigo falon tare da faɗin, “Neehal ki kawo masa abinci mana.” Ta miƙe tare da amsawa ta nufi kitchen ɗin. Mama ta zauna a kujerar dake fuskantar sa, fuska a sake ya ce “Ina yini Mum.” Mama ta ce “Lafiya k’alau, ya Hafsah?” Ya ce “Tana nan k’alau.” Mama ta ɗan ƙura masa ido na wasu sakanni sannan ta ce “Ameen! Is everything okay?” Ya ce “Komai lafiya Mum, me kika gani?” Mama ta ce “You look so worry.” Ya yi murmushi ya ce “Nothing Mum, idan ma da akwai wani abu yanayin aiki ne kawai.” Mama ta ce “Allah ya taimaka ya bada sa’a, sai a cigaba da dagewa da addu’a.” Ya ce “Insha Allah Mum.” Dai-dai lokacin Neehal ta fito daga kitchen ta ajiye tray a gabansa, ta tsugunna dan sarving ɗinsa, Mama ta dakatar da ita da faɗin. “Barshi Daughter, je ki gyara mun bedroom i will save him.” Ta ce “Toh Mama.” Tare da nufar sama. Mama ta sakko ta zuba masa abincin a plate, ta dube shi ta ce “Sakko ka ci, and no more excuse or saying you are full.” Ya yi murmushi tare da saukowa ya zauna a kusa da ita, ya jawo abincin gaban sa ya ce “Yaushe da rabon da ki yi save ɗina Mum?” Mama ta harare shi ta ce “Kasan jariri ne ai kai, da sai na zuba maka abinci zaka ci.” Ya yi murmushi ya ce “Before you getting a Daughter ai kina mun, tunda kika yi ƴa kika daina yayi na.” Mama ta yi murmushi ganin yanda ya wani marairaice ta ce “Au har wani daina yayin ka na yi?” Ya lumshe kyawawan idanunsa ya buɗe ya ce “Eh mana.” Mama ta ce “Never Ameen, ai babu wani abu da zai yi replacing ɗinka a zuciyata, kai ɗin ne sometimes nima ba gane kanka nake ba.” Ya yi murmushi bai ce komai ba ya yi Bismillah ya fara cin abincin sa. Mama ta bishi da kallo cike da k’auna, a ranta ta ce “My Son you will never change daga miskilanci.” Ta yi zaton idan ya yi aure zai rage, amma sai ta ga jiya i yau, kamar ma ƙara masa a kay. Kaɗan ya ci abincin ya ajiye spoon ya ce ya k’oshi, sannan ya sha ruwa yay mata sallama ya tafi. Mama ta tattara kayan ta kai kitchen bayan ya fice.

Sai da suka yi Sallar isha’i sannan Mama ta zaunar da Neehal a ɗakinta akan maganar da ta ce zasu yi. Tana duban ta seriously ta ce “Neehal ɗazu kawunki Malam Musa ya zo, yaso ya zauna ya jira ki dawo ku gaisa amma akai masa kiran gaggawa a gurin aikin su. Kuma dalilin zuwan nasa ya zo ne akan ya kamata idan kina da tsayayye ya fito a yi maganar auran ku.” Ta d’ago ta dubi Mama da sauri amma batai magana ba. Mama ta cigaba da magana da faɗin, “Na ce masa akwai wanda yake zuwa gurin ki, dan kun ma daɗe kun kusa shekara tare, amma mu da muna jiran ki kammala karatun ki ne sai mu yi masa magana idan da gaske yake sai ya fito a yi maganar biki.” Neehal ta sauke numfashi tare da yin ƙasa da kanta, Mama ta ce. “Ya ce duk wannan ba matsala ba ce, idan gasken yake ya turo a yi maganar auran naku, bayan kin kammala karatun naki sai a yi bikin.” Neehal ta d’ago ta dubi Mama gabanta na fad’uwa ta ce “Mama duk yanda kuka yanke dai-dai ne, kuma duk abun da kuka ce shi zan bi.” Mama ta ce “Haka ne Daughter, Allah yay miki albarka, yanzu idan Daddy ya dawo zamu tattauna ni da shi, yanda muka yi zan sanar miki sai ki faɗawa Sadik ɗin.” Neehal ta gyaɗa mata kai, tana son tay mata maganar Ahmad amma kuma ta rasa ta ina zata fara. Mama dake nazartar ta, ta ce “Neehal me kike son cewa? Ko baki son Sadik ɗin ne?” Ta girgiza mata kai cikin sanyin jiki. Mama ta ce “To ya na ga gaba-ɗaya yanayinki ya sauya, kamar ba ki yi farinciki ba, kin ga Daughter idan da akwai wata matsalar ki faɗa mun.” Ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce “Uncle Ahmad.” Mama ta yi murmushi ta ce “Me ya faru da shi?” Ta buɗe baki kamar zata yi magana sai ta fasa. Mama ta ce “Na san soyayya kuke yi da shi ai, na zuba miki ido ne kawai in ga iya gudun ruwanki.” Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunya. Mama ta ce “Amma Neehal me yasa kina tare da Sadik kike kula Ahmad da sunan soyayya? Hakan ba dai-dai ba ne.” Ta sauke numfashi ta ce “Mama i can’t reject him, saboda shi ma ya taimake ni a lokacin da nake buƙatar taimako.” Mama “You are right, but you did a mistake.” Ta ce “Mama na sani, amma ban san yaya zan yi ba ne a time ɗin.” Mama ta ce “Shikenan, yanzu shi kike so ko Sadik ɗin. Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama ta ce “Uhm? Ke nake sauraro.” Ta ce “Mama na rasa wanda zan zab’a a cikin su, kowanne a cikin su yana da good quality, amma Mama ki zaɓar mun ɗaya a cikin su Please, duk wanda kika zaɓar mun i will accept him.” Mama ta girgiza kai tare da dafa ƙafaɗarta ta ce. “Neehal miji fa, abokin rayuwarki wanda zaku yi rayuwar da baku taɓa yin irinta da kowa ba a duniyar nan. Dan haka ke ya kamata ki zab’arwa kanki wanda hankalin ki ya fi kwanciya da shi. Wanda kika yaba nagartar shi kuma kuka fahimci juna, wanda kike ganin zai baki farinciki ya kuma riƙe ki amana. Duk da mazan yanzu sai addu’a, amma ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, akwai nagari wanda muke fatan Allah ya haɗa ku da su. Dan haka ki je ki nutsu ki yi shawara ki tantance wanda kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi, kafin mu gama magana da Dad sai ki sanar mun wanda kika fitar, sai na faɗa musu a san abun yi. Sannan kuma ki dage da addu’a da neman zaɓin Allah.” Neehal ta sauke numfashi cikin rashin sanin abun yi ta gyaɗawa Mama kai. Mama ta tashi tana faɗin. “Bari na je part ɗin Daddy.” Ta gyaɗa mata kai kawai still bata yi magana ba. Bayan fitar Mama ta kwanta akan gado ta faɗa duniyar tunani. Ta fara tuno farkon haɗuwar su da Sadik da irin mutuncin da yay mata, ta kuma tuno irin tarin soyayyar da yake mata, da kuma damuwar da yake shiga a sanadin ta, domin ta san komai da ya faru a gidansu ya sanar mata babu abun da ya ɓoye mata. Ta tuna alkawarin da tay masa lokacin da ta je asibiti dubo shi da ba shi da lafiya, ya kama hannunta ya ce mata. “Neehal dan Allah duk runtsi karki bari a raba mu, Wlh idan na rasa ki mutuwa zan yi.” Tana hawaye ta ce masa “Baza ka mutu ba Ya Sadik ɗina Insha Allahu kai ne mijina, na maka alƙawarin indai kana raye ba zan taɓa aurar wanin ka ba.” And then ta komar da tunanin nata kan Ahmad, mutumin da yay ta dakon soyayyarta tsawon shekaru, kuma ya taimaka mata a lokacin da take da buƙatar taimako, ga kuma Ƴaƴansa wanda suke k’aunarta take k’aunar su, zata so ta auri Ahmad ko dan ta kula da twins, ta maye musu gurbin mahaifiya da suka rasa. Ta gyara kwanciyarta tana son ta tantance wa tafi so a tsakanin su amma ƙwaƙwalwarta ta kasa yi mata wannan aikin. Ganin ta kasa samun mafita sai ta yanke shawarar zata tunkari ƴar’uwa kuma Aminiyarta wadda bata da kamar ta wato Haneefah da wannan maganar, domin ta bata shawara. Da wannan tunanin ta miƙe ta koma ɗakinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button