NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Mama kuwa sai da ta zubawa Daddy abinci ya ci sannan ta sanar masa da zuwan Kawu Musa da kuma yanda suka yi da shi. Daddy ya numfasa ya ce “Haka ne, kuma abun da ya faɗa gaskiya ne, nima da na so na ce ta turo mun shi yaron mu yi magana, amma sai na ce mu bari ta gama karatun ta, ta ɗan huta tukunna. Ko dan damuwar da ta shiga kwanaki akan rasuwar sauran samarinta.” Mama ta ce “Haka ne, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya kawar da duk wata fitina a wannan karon a yi lafiya a gama lafiya.” Daddy ya ce “Amin, yanzu ta fara turo mun shi yaron mu yi magana da shi, kafin akai ga maganar turo magabatansa.” Mama ta ce “To ai ita yanzu wai ta rasa wa zata zaɓa, ka san baban Twins shima son ta yake.” Mama ta kwashe duk yanda suka yi da Neehal ta sanar masa. Daddy ya yi murmushi ya ce “Daughter mai farin jini.” Mama ta ce “Hmm, Allah ya kyauta, amma ni nafi mata sha’awar Ahmad ɗin, tunda shi babba ne, ga kuma yaransa suna buƙatar kulawar uwa, amma kuma idan ta zaɓe shi ta bar Sadik shi kuma bata kyauta masa ba, tunda ya riga Ahmad ɗin zuwa.” Daddy ya ce. “Allah ya zaɓa mafi Alkhairi kawai.” Mama ta ce “Amin Amin.” Dad ya ce “Ɗazu Saratu ta kira ni, tana mun shirmen ku na mata.” Mama ta ce “Shirmen me kuma?” Dad ya ce “Ita fa har yanzu bata haqura da batun Ameen da Hameedah ba, na ce mata ban da abunta Ameen fa ko shekara bai rufa da yin aure ba, idan ma auran zai ƙara ai ba yanzu ba, ballantana ma na san halin Ameen da ƙyar zai yarda ya ƙara aure.” Mama ta ce “Allah ya kawo mata miji nagari ta yi auranta, amma Ameen a farko ma ya ƙi auren ta balle kuma yanzu.” Daddy ya ce “Nima shi na gani dai Doctor.” Mama ta ce “Allah ya kyauta.”
Washegari ta kama Friday lecture ɗin safe gare ta 8_12. Kafin ɗaya ta dawo gida, bayan ta yi Sallah ta ci abinci ta shirya tay wa Mama Sallama ta tafi gidan Haneefah kamar yadda ta k’udurta. Haneefah tana kitchen tana suyar wainar fulawa ta ji ana knocking ƙofar falo, bata fita ta falo ba ta buɗe ƙofar kitchen ta baya ta lek’a dan ganin waye. Hango Neehal da ta yi yasa ta waro ido da ƙarfi ta ce, “Kan uban nan, zuwa babu sanarwa.” Neehal ta yi murmushi tare da ƙarasowa ƙofar kitchen ɗin ta juya ido ta ce. “Ko in koma ne?” Haneefah ta rungume ta cikin murnar ganin ta ta ce, “Wa ya isa ke da gidan ki.” Neehal ta ce “Shi na gani dai.” Haneefah ta jata suka shiga kitchen jin wainar data bari akan wuta tana kamawa. Neehal ta riƙe hab’a ta ce “Unborn me cin wainar fulawa ne kenan?” Haneefah ta ce “Rufa mun asiri da wani batun unborn, ina da sauran shekara biyu da watanni kafin na kammala school, a hakan ma idan ba’a tafi strike ɗin ƙasar nan na gado ba. Wannan wainar fulawar ta Ya Faruq ce ya saka ni in yi masa, kin san masoyiyarsa ce.” Neehal ta ce “Faɗi gaskiya dai, wannan murjewar da kyawun da kika yi duk na mene ne?” Haneefah ta ce “Auran kenan Yarinya.” Neehal ta waro Ido ta ce “Hmm, ya kk ya gida da school?” Haneefah ta ce “Lafiya k’alau, Alhamdulillah ya Mamana? Duk da fushi nake da Mama ta ƙi zuwa gidana.” Neehal ta ce “Kin san Mama, ita fita wahala take mata.” Haneefah ta ce “Daga gida kike ko school?” Ta ce “Daga gida mana, takanas na zo dan na gan ki.” Haneefah ta yi murmushi ta ce “Kin kyauta kuwa, ki shiga falo ki huta kafin na ƙarasa.” Neehal ta ce “Toh, Ya Faruq yana nan ne?” Haneefah ta ce. “Eh yana ɗaki, da na ji shigowar mota ma na ɗauka abokansa ne, ashe my Besty ce ta mun surprised.” Neehal ta yi murmushi ta wuce ciki. Bayan Haneefah ta kammala wainar ta kaiwa Ya Faruq ɗaki tare da sanar masa zuwan Neehal, ya fito suka gaisa cikin fara’a. Haneefah ta kawowa Neehal abinci da drinks da wainar data toya, tana ci suna hira. Sai da suka yi Sallar la’asar lokacin Faruq ya fita sannan Neehal ta zayyanowa Haneefah problem ɗinta.
Haneefah data ƙura mata ido tana sauraren ta, ta numfasa ta ce “Yanzu Neehal ke a karan kanki kin kasa zaɓar wanda zuciyarki ta fi so, ta yaya wani zai iya zaɓar miki? Ke baki san wa kika fi so a cikin su ba?” Cikin damuwa Neehal ta ce “Wallahi ban sani ba Besty, na kasa tantancewa, idan ina tare da wannan sai in mata da waccan.” Haneefah ta ce “To duk ba son su suke ba.” Neehal ta dube ta cikin mamaki tare da faɗin “Kamar ya?” Haneefah ta ce “Kamar yadda kika ji na faɗa, ai shi wanda zuciya take so baya b’uya, Neehal da ace kina son Sadik ko Ahmad idan kina tare da ɗayan su ba zaki taɓa mantawa da wanda kikewa son gaskiya a ba a cikin su. Daga Sadik har Ahmad tausayin su kawai kike ji, ko kuma wani a cikin su yana miki wani abu da yake burge ki, and kuma kina duba halacci ko kyautatawar da sukay miki a rayuwarki, amma so dai da k’auna na soyayya ba kya yiwa Sadik da Ahmad. Ni nafi tunanin akwai wanda zuciyarki take so, wanda ke kanki baki sani ba.” Neehal ta ɓata fuska ta ce “Ni babu wani wanda nake so daban kuma, to wani saurayin ne dani bayan su da zan so shi?” Haneefah ta ce “Wanda ba kya taɓa mantawa da shi a cikin ranki, ko da kuwa kina tare da Sadik da Ahmad. Indai akwai wanda kike jin haka a kan shi to shi kike so.” Neehal ta tab’e baki ta ce “Babu shi gaskiya, kema kin sani.” Haneefah ta ce “Lokaci ne zai faɗa mana haka, amma now back to our business, wa kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi a tsakanin su?” Neehal ta ce “Wannan ita ce tambayar da Mama tay mun, kuma na kasa tantancewa, shi yasa na zo mu haɗu mu tantance.” Haneefah ta ce “Indai a yanda kika bani labari ne gaskiya zan fi so ki auri Sadik, saboda yanda yake da rauni akan soyayyar ki, kece mace ta farko da Sadik ya fara so a rayuwarsa, idan kika rabu da shi saboda Ahmad kin zalunce shi, saboda sai da ya gama sakankancewa ya samu mata sannan kuma ki canza zance. Time ɗin da Ahmad ya dawo cikin rayuwarki already kuna tare da Sadik, dan haka yanzu idan kika bar shi kin yaudare shi, kuma hak’k’in shi ba zai barki ba. Sannan kuma ki duba yanda danginsa ba kowa ke son ku tare ba, idan kika rabu da shi kika watsa masa ƙasa a ido za ai masa dariya, ace shi yana ta wahala a kanki ashe ma ke ba k’aunar sa kike ba, kuma Sadik ya riga Ahmad fara sonki.” Neehal ta yi sauri ta ce “Uncle Ahmad ya riga, na faɗa miki fa tun ina yarinya farkon haɗuwar mu yake so na.” Haneefah ta ce “Ai wancan lokacin daban, kuma ya wuce. Zancen yanzu ake da girmanki, amma ni dai shawara nake baki, dan ni Baban twins ɗin nan ma bai wani mun ba, ya miki tsufa, gwara ki auri saurayi ɗan shawalwali wanda zaku fi jin daɗin rayuwar auranku. Kuma na lura kalaman Ahmad da iya tsara mace ne suke rud’ar ki a kansa, dan na san ki da son soyayya, da son a nuna miki k’auna.” Neehal ta ce “Ni duk ba wannan nake dubawa ba, ina duba taimakon da yay mun a baya, ni kuma yanzu yana buƙatar nawa sai in ƙi taimaka masa? Kuma ga yaransa da muka shak’u da su, bana son rabuwa da su” Haneefah ta ce “Idan dan Allah yay miki ba zai yi wannan tunanin ba dan baki zaɓe shi ba, su Afrah kuma dan kin yi aure ai ba yana nufin kin rabu da su ba kenan, zaki cigaba da zumuncin ki da su, tunda Allah ne ya haɗa ku.” Neehal ta yi shiru na tsawon mintuna biyu, sannan kamar zata yi kuka ta ce. “Haneefah! Uncle Ahmad yana so na Sosai, kuma duk abun da kika faɗa akan Sadik gaskiya ne, ya cancanci zama miji a gare ni, amma ban san da idon da zan kalli Uncle Ahmad na faɗa masa wannan maganar ba, Allah na yi dana sanin haɗa two dating at one time.” Haneefah ta ce “Haka nan Sadik ɗin shima idan kika zaɓi Ahmad zaki ji nauyin sanar masa kin zaɓi wanin shi a matsayin miji. Neehal! matar mutum kabarinsa, tun kafin ki zo duniya Allah ya riga ya rubuta wanda zaki aura, ki yarda da wannan, ki kuma dage da addu’a da neman zaɓin Allah, tunda kin san dai baza ki auri maza biyu ba ko?” Neehal ta ce “Haka ne ƙawata, daren jiya ma kusan kwana na yi ina kaiwa Allah kukana tare da neman zaɓin sa.” Haneefah ta ce “Yawwa, kisa a ranki kawai wanda kika zab’a shine mafi Alkhairi a gare ki, kuma shi Allah ya rubuta zai zamto mijinki.” Neehal ta ji wani ɗan sanyi a ranta, lallai ta yarda shawara tana daɗi. A hankali kamar wadda aka tilasta mata ta ce “Na zaɓi Ya Sadik, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi.” Haneefah ta ce “Amin ya Allah, shi kuma Ahmad Allah ya bashi tasa matar mai Alkhairin.” Kamar zata yi kuka ta ce “Amin, amma ban san yanda zai ɗauki wannan al’amarin ba, ina jin kamar ban kyauta masa ba.” Haneefah ta ce “He is a Muslim, kuma ya san qaddara mai kyau da mara kyau, Insha Allahu zai fahimce ki. But I’m not forcing you Neehal akan Sadik, kawai ina baki shawara ne kamar yadda kika nema daga gurina, idan kin ji zuciyarki ta fi k’aunar Ahmad karki cuci kanki, ki zaɓi wanda kike so ki aura, dan aure ba abun wasa ba ne.” Neehal ta ce “Hmm, Allah yasa ya fahimta ɗin. No, ni da Ya Sadik da Uncle Ahmad duk ɗaya ne a gurina, duk wanda na zab’a dai-dai ne, saboda duk sun cancanta.” Ta yi shiru tare da ɓata fuska, sannan cikin damuwa ta ce. “Ni duk ba wannan ba ma, ina tsoron abun da ya faru a baya ya kuma faruwa.” Sai ta fara hawaye sannan ta cigaba da magana. “Ina tsoron a kuma kashe mun wanda zan aura yanzu ma.” Haneefah ta ɓata fuska ta ce “Oh my God, Neehal har yanzu baki daina wannan banzan tunanin ba, kin manta Allah ne me rayawa da kashewa.” Neehal ta girgiza kai kawai ba ta ce komai ba, hawaye na cigaba da shatata a fuskarta. Haneefah ta matso ta rungume ta, cikin lallami ta ce. “Insha Allahu, Besty babu abun da zai faru sai Alkhairi, Allah yana sane da ke, ki miƙa masa k’ok’on bararki, shi kuma da yardarsa na san zai kawo miki ɗauki. Kuma duk wanda yake kisan nan matuƙar dan ke ake yi bisa zalunci da son zuciya Ubangiji zai saka miki cikin gaggawa, dan Allah yana karɓar addu’ar wanda aka zalunta. Kuma rayuwar mumuni bata tafiya sai da jarrabawa, ke kuma wannan ita ce taki jarabawar, amma in kika yi haquri sai ki ga komai ya wuce tamkar bai taɓa faruwa ba, be a good Muslim please Dear.” Haka dai Haneefah tay ta nusar da Neehal da nasihohi da kalamai masu daɗi gami da ƙara mata k’warin gwiwa akan Sadik, daga baya kuma ta koma tsokanarta da matar Barrister, an kusa shiga daga ciki. Har ta ji zuciyarta ta mata sanyi, kaso mafi yawa na damuwar da take ciki ya tafi. Shi yasa take son Haneefah, because she is a good person, kuma ta san baza ta taɓa bata shawarar da zata cutar da ita. Amma wani b’arin na zuciyarta sai tambayar ta yake akan anya ta yiwa Ahmad adalci kuwa? Sai bayan Magriba sannan ta bar gidan, shi ma sai da Mama ta kira ta a waya, dan sosai ta ji daɗin kasancewa da Besty’nta_ta………✍️