NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

5️⃣8️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..A falon sama ta tarar da Mama tana kallo. Ta tafi da murnarta ta faɗa jikinta tare da faɗin. “Oyoyo Mamana.” Mama ta harare ta, ta ce. “Aina na ɗauka a can zaki kwana.” Ta ƙara ruk’unk’ume ta tana murmushi ta ce “Sorry My Mum, hira ce ta yi daɗi.” Mama ta ce “Ya yi kyau, idan da Daddy ya dawo sai ki faɗa masa hira ce ta yi daɗi shi yasa kikai dare.” Ta yi dariya kawai, Mama ta ce “Ya kika baro Haneefan?” Neehal ta ce “Lafiya k’alau, tana gaishe ki.” Mama ta ce “Ina amsawa.” Neehal ta miƙe ta shige ɗaki. Kwanciya ta yi akan gado bayan ta ajiye handbag ɗinta da mayafinta. Ta kwanta rub da ciki tare da tallafe kanta da hannunta. Tunanin Ahmad take da irin tarin soyayyar da yake mata, har yanzu ta kasa amincewa da zaɓin da ta yiwa kanta, tana ganin kamar ba zata iya barin Ahmad ba a rayuwarta. To amma Sadik fa, kamar yadda Haneefah ta faɗa idan ta bar shi ta zalunce shi, ta cuce shi ta yaudare shi. Ta runtse ido cikin tsananin damuwa, ita bata taɓa dating two persons at one time ba sai wannan karon, ta yi dana sani mara iyaka, amma kuma babu yanda zata yi wannan ma is another addiction in her life. Ta tashi ta ɗauko jakarta jin wayarta na ringing a ciki, Sadik ne yake kiran ta. Ta d’aga cikin ƙoƙarin ganin bai fuskanci tana cikin wata damuwa ba, gaisawa kawai sukai ya tambayi lafiyarta saboda lokacin Sallah da ya gabato. A daren ranar ta sanar da Mama Sadik ta zaɓa, Mama ta ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Washegari da safe Mama ta ce mata gobe Sunday ta cewa Sadik ya zo Daddy yana son ganin sa. Kamar zata yi kuka ta ce, “Toh Mama zan faɗa masa, amma Mama har yau na kasa sanar da Uncle Ahmad, wallahi ban san ta yaya zan faɗa masa ba, kuma na san zai yi wahala ya ƙi zuwa yau ko gobe.” Mama ta ce “Shikenan idan ya zo ni zan masa bayanin da zai fahimta da kaina.” Ta gyaɗa mata kai tana ƙoƙarin ganin bata bar hawayen idonta ya zubo ba. Ta tashi ta koma ɗakinta dan zata iya fashewa da kuka saboda yanda take jin zuciyarta, ita kuma bata son ta yi kuka a gaban Mama. Tana hawaye ta yiwa Sadik text ta sanar masa abun da Mama ta ce ta faɗa masa. Ta kwanta tana kukan da bata san dalilin shi ba. Tana jin wayarta tana ringing amma bata bi ta kanta ba. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru, ta tashi ta ɗauki wayar ta duba ta ga Sadik ne ya kira ta, da ya ga bata ɗauka ba yay mata reply ɗin text ɗinta, tare da daɗaɗan kalaman soyayya a ƙarshe. Ta yi ɗan murmushi, sannan ta tashi ta je ta wanke fuskarta. Bayan Sallar Azhar tana zaune a ɗakinta da materials ɗin karatun ta tana dubawa. Mama ta shigo ɗakin ta ce mata. “Neehal Ahmad ya zo.” Ta d’ago da sauri gabanta na wani irin fad’uwa saboda razana. Mama data kula da yanayin da ta shiga ta ce. “Ki je ku gaisa, yana ƙasa yana jiranki, kuma karki nuna masa wani abu, idan zai tafi i will explain to him.” Neehal ta gyaɗa mata kai kawai. Kamar wadda k’wai ya fashewa a ciki ta tashi cikin sanyin jiki ta yane kanta da mayafin abayar dake jikinta. Ta ɗan gyara fuskarta sannan ta fesa turare kaɗan, sannan ta fice daga ɗakin cikin matuƙar sanyin jiki.

As always yana zaune akan carpet idanunsa akan steps. Ta sakko cikin nutsuwarta kanta a ƙasa, gabanta na cigaba da faɗuwa ta zauna a kusa da shi tare yin sallama. Yana murmushi ya amsa mata. Ta ce “Ina yini Uncle.” Ya ce “Lafiya k’alau Princess, ya weekend?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce “Ya School da aiki?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya gyara zama tare da juyowa ya fuskance ta sosai ya ce. “Kin yi kyau, kullum kamar ƙara miki kyau ake Princess.” Ta d’ago tare da ƙirƙirar murmushi akan fuskarta a ƙoƙarin ta na ganin bata nuna masa akwai wata damuwa ba, ta ce. “Ni ɗin kuwa?” Ya ce “To da wa?” Ta sake yin murmushi ta ce. “Ina Yarana?” Ya ce “Suna gida.” Ta ce “Da fatan dai suna lafiya, kuma baka barin wani abu yana damar mun su?” Ya kafe ta da ido ya ce. “Suna lafiya, ni kam me zan bari ya damu ƴaƴan Aunty? Ai lallaɓa su nake kar Aunty ta ce ta fasa Aure na.” Ta yi ƙasa da kanta da sauri saboda yanda ta ji bugun zuciyarta ya sauya, ta hasaso yanda yake cikin farincikin nan da nishad’i ya zai ji idan Mama ta yi masa bayanin ta kusa zama mallakin waninsa, daga yau ba zai ƙara zuwa su yi irin wannan zaman ba, duk soyayyar da ya nuna mata ta zama tahiri, a…… “Princess.!” Ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta. Ta d’ago tay masa kallon cikin ido cikin dakiya. Ya lumshe ido ya buɗe su a cikin nata ya ce. “Tunanin me kike?” Ta ce “Babu komai Uncle.” Ya karyar da kai ya ce, “Let me snap you, kin mun kyau sosai yau.” Ya ɗauko wayarsa yay mata pictures, ita kuma tana ta murmushi, sannan ya ɗauke su tare. Ta karɓi wayar tana dubawa, hotunan sun yi kyau sosai. Ta yi murmushi ta cigaba da kallon pictures ɗin wayar, wanda fiye da rabi na twins ne. Ta tura wanda yay musu yanzu sannan ta tuttura wasu na twins da nasa ta whatsapp. Mama da kanta ta sakko ta shiga kitchen ta zubo masa abinci ta kawo masa, ya dinga yi mata godiya cikin jin kunya. Bayan Mama ta koma sama ya dubi Neehal ya ce. “Ina son Mama sosai, saboda kirkinta, da sanin darajar ɗan Adam gami da karamci.” Ta yi murmushi kawai, sannan ta zuba masa abincin, yana ci suna hira, wanda Neehal ta ji kusan rabin damuwarta ta tafi. Sai da aka kira Sallar la’asar sannan ya tashi ya je masallaci ya dawo. Neehal bata sakko ba tana ɗakinta akan darduma bayan ta idar da Sallah, addu’a take yi akan Allah ya sanyayawa Ahmad zuciyarsa, Allah yasa kar abun da Mama zata faɗa masa ya yi hurting heart ɗinsa over.

Jin dawowarsa Mama ta sakko ta zauna akan kujera sannan cikin kulawa ta ce. “Neehal ta faɗa maka za mu yi magana ko Doctor?” Cikin fad’uwar gaban da bai san ko ta mecece ba ya ce “Eh Mama.” Mama ta danne tausayinsa dake cikin ranta ta fara yi masa bayani, cikin tausasan kalamai ta yanda zai fuskanta. Da farko ji yay kansa ya masa wani irin juyawa, yawun bakinsa ya kafe kaf, dak’yar ya iya had’iye wani abu mai ɗaci da ciwo daya tsaya masa a mak’oshi ya ce. “Babu komai Mama, na fahimce ki, Allah kuma yasa hakan shi ya fi Alkhairi a gare mu gaba-ɗaya.” Ya yi maganar cikin tsananin dauriyar zafin da zuciyarsa take masa. Bai kuma fuskantar abun da Mama take kuma faɗa masa ba, ya dai ji kamar haquri take ba shi da kuma ƴar nasiha. Ya gyaɗa mata kai kawai, ita kuma ta tashi ta nufi upstairs tana faɗin bari ta turo masa Neehal ɗin su yi Sallama. At the first bayan barin Mama falon ya d’ago kansa tare da lumshe idonsa yana fatan ya kasance mafarki yake ba gaske ba ne abun da Mama ta sanar masa. Ya yi imagine wai hakan na nufin ya rabu da Princess ɗinsa kenan har abada, nan da wani ɗan lokaci za’ai mata aure da wani ba shi ba. Innalillahi,wa’inna’ilaihirraji’un ya shiga maimaita a fili cikin sanyin murya mai cike da damuwa, har ya ji ya fara ɗan samun salama a cikin ransa. Neehal wadda da ƙyar Mama ta yaƙo ta, ta fito saboda ta ce bata san da idon da zata kalle shi ba, ta ƙaraso falon idanunta na shatatar hawaye, da ƙyar take iya ganin gabanta. Ya ƙura mata ido cikin sarewa da karayar zuci, karon farko a rayuwarta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Ya runtse ido ya buɗe saboda yanda kukan nata yake taɓa masa zuciya. Ya tsotsi lips ɗinsa da suka bushe lokaci ɗaya saboda damuwa cikin marainiyar murya ya ce. “Please Princess Stop crying, ko so kike nima in yi kukan?” Ta girgiza masa kai. Ya d’ago kanta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawaye da shi. Ta bar jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Cikin muryar kuka ta ce, “I’m so sorry Uncle, I…” Ya katse ta da faɗin. “Me kikai mun Princess da zaki bani haquri? Na fuskanci bayanin Mama kuma na gamsu. Princess! Ba mu muke da ikon tsarawa kanmu rayuwa ba, Allah ne yake tsara mana. I’m a Muslim, na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, tabbas rasa ki a cikin rayuwata ba ƙaramin rashi ba ne, amma kuma babu yanda zamu yi da ikon Allah. Karki damu akan wannan Please Princess, I knew you love me so much.” Ta kalli fuskarsa yay mata murmushin da ya fi kuka ciwo tare da kamo hannunta ya ce. “Princess! Sau da yawa abun da zuk’atansu suke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, sai mu ga wanda bama so ɗin ya fi zama Alkhairi a gare mu. Duk da na san kina son guy ɗin da zaki aura ba wai auren dole za’ai miki ba. Amma ko kaɗan ban ji a raina kin yaudare ni ba or something like this, abun da kikai shine dai-dai, kuma shine adalci. Tunda shi guy ɗin he came first before I came, abun da baza ka so ai maka ba kaima karka so kaiwa wani, dan haka ki daina damun kanki indai ni Ahmad ne na haqura, dama rayuwa cike take da farinciki da baƙinciki, idan ka yi haquri kuma zaka ga ribarsa a gaba, kuma komai zai wuce kamar bai faru ba.” Ya yi shiru yana sauke numfashi, dan shi kansa ya san ba ƙaramin dauriya yake ba wajen ɓoye mata damuwarsa. Ta ƙura masa ido cikin mamakin kalamansa zuciyarta cike da tsantsar tausayinsa, ta san daurewa kawai yake dan ya ga ta damu kar ta tashi hankalinta. A hankali ta ce “Thank you so much Uncle, for your cares and everything to my life.” Ya yi irin murmushin d’azu ya ce. “Nima na gode da k’aunar da kika nuna mun Princess, and I will never forget you in my life. Na gode Na gode sosai, da k’aunar kike wa ƴaƴana. Allah ya yiwa rayuwarki albarka, ya baku zaman lafiya ke da mijinki idan kun yi aure, ya kuma baku zuri’a d’ayyiba.” Ta ce “Amin Uncle tare da kai.” Ya ja karan hancinta ya ce, “Zan wuce sai mun zo biki.” Dan ba ƙaramin dauriya yake ba, so yake kawai ya kadaice ya rarrashi zuciyarsa. Ta lumshe ido hawaye ya zirnano daga cikin idanunta. Kamar zai yi kuka ya ce. “Oh My God Princess, dan Allah ki bar kukan nan, baki san yadda nake jin zafi a cikin raina ba idan kina yi. Ta share hawayen bayan ta zare hannunta daga cikin nasa ta ce. “Na daina Insha Allah Uncle.” Ya ce “Promise to me ko na tafi baza ki yi kuka ba.” Ta ja hanci a hankali ta ce. “Ba zan yi ba Uncle Insha Allah.” Ya shafi kuncinta ya ce, “Good lady, yanzu fa kin girma Princess, ko kina so twins ɗinki su gan ki kina kuka?” Ta girgiza masa kai. Ya ƙara kamo hannunta ɗaya ya ce. “Tashi mu je ki raka ni.” Ta kalle shi sannan ta tashi ganin shima ya miƙe. Ya taune lip ɗinsa jin kamar zai faɗi tare da dafa hannun kujera yana ambaton sunan Allah. Ta ƙura masa ido kawai cikin damuwa. Ya d’ago yana murmushi ya ce, “Wannan kallon fa?” Ta ƙara waro masa manyan kyawawan idanunta haɗe da juya masa su sannan ta lumshe su a hankali. Salon nata ya shige sa ba kaɗan ba, bai san sanda ya dafa kafaɗunta ba ya yi kissed saman idanun, a hankali kuma ba tare da ta taɓa zato ba ta ji saukar lips ɗinsa akan nata. Ta sauke wani gwauron numfashi lokacin da ta ji yana kissing ɗinta, kafin a hankali ya janye fuskarsa daga ta_ta. Cikin raunin murya ya ce, “Good bye Princess, I love You.!” Sannan kamar wanda aka tsikara ya juya da sauri ya fice daga falon. Sai buɗe idanunta ta yi ta ga babu shi sai k’amshinsa da ya bar mata a jikinta da falon. Ta ja ƙafafuwanta da sukay mata nauyi ta ƙarasa kujerar dake kusa da ita, ta faɗa kanta ta fashe da kuka, a ranta tana faɗin. ‘This means daga yanzu mun rabu da Uncle, rabuwa ta har abada.’ Ta cigaba da kukan ta a gurin, ta ma manta da alƙawarin data ɗaukar masa na baza ta kuma yin kuka ba, akan rabuwar ta da shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button