NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Da ƙyar Ahmad ya iya jan ƙafarsa ya je parking space, yana zuwa ya buɗe Motar da ya zo da ita ya shiga ya zauna ya ɗora kansa akan sitiyarin Motar, yana jin zuciyarsa tamkar zata soye saboda zafin da take masa. Ganin abun yake tamkar almara, domin bai taɓa tunanin zai ƙara rasa Neehal a karo na biyu ba. Amma ya yadda da ƙaddara, ya kuma yarda wani ba ya taɓa auran matar wani. Zai dage da addu’a akan Allah ya cire masa sonta ko da ba duka ba daga cikin ransa, ya kuma bashi mace ta gari wadda zata kula da shi da marayun ƴaƴansa. Sai dai ya rasa me yasa wani b’arin na zuciyarsa yake tabbatar masa da bai rasa Neehal ba, yake nuna masa zai mallake ta. Ya sauke numfashi tare da addu’ar idan rabonsa ce ita, Allah ya bashi, zai je ya dage da addu’a. Sunan Allah yay ta maimaita a ransa, har ya ɗan samu nutsuwa. Cikin dauriya ya kunna Motar ya fice daga gidan bayan an buɗe masa gate ya nufi gidan Mamy. Yanda Mamy ta ganshi ya shigo a sanyaye kamar mai cuta ta san da matsala, a ɗan rikece ta tambaye shi me nene? Kamar zai ɓoye mata sai kuma ya sanar mata. Itama Mamy ta ji ba daɗi a ranta sosai, domin ta yiwa Ahmad sha’awar Neehal, dan ta yaba da hankalinta da nutsuwarta. Amma sai ta kwantar masa da hankali, ta ce ya je ya dage da addu’a Allah ya zaɓa masa abun da ya fi Alkhairi.
Har bayan Magriba Neehal bata daina kuka ba, Mama ta yi rarrashin ta yi nasihar ta yi faɗan amma ta ƙi barin kukan, har ta gaji ta ƙyale ta. Tana jin wayarta nata vibrate ana ta kiran ta amma ta ƙi bi ta kanta. Ga kanta dake ciwo saboda kukan da take. Bayan Magriban ne Ameen ya zo gidan, lokacin tana ɗakinta a kwance akan gado. Bayan sun gaisa da Mama ya tambaye ta Neehal ɗin, ta sanar masa tana ɗaki tana kuka, ko abinci bata ci ba tun safe. Bai tambaye ta dalilin kukan ba ya tashi ya shiga ɗakin. Ya zauna a gefen gadon ya kira sunanta, ta tashi zaune da ƙyar tana goge hawayen fuskarta, idanunta sun yi jajur. Cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi yay mata Ƴar nasiha, akan kuka ba maganin damuwa ba ne, komai yake damun ka, ka kaiwa Allah kukan ka, shi zai maka magani. Sai gashi ta yi shiru, ya ce ta je ta wanke fuskarta ta zo ta ci abinci. Bata musa ba, ta tashi ta yi abun da ya ce. Mama ta cika da mamakin ganin cikin mintuna ƙalilan ta saki ranta, Alhalin ita tun yamma take fama da ita. Sai da ta ci abincin ta sha maganin ciwon kai sannan Ameen ya bar gidan.
Washegari kamar yadda Dad ya ce, Sadik ya zo gidan da yamma. Har part ɗin Daddy’n akai masa iso ya je ya same shi. Daddy yay masa ƴan tambayoyi, sannan ya ce ya bashi auran Neehal ya turo magabatansa. Ai Sadik ji ya yi kamar ya rungume Daddy dan tsananin farin ciki, yay ta zuba masa godiya. Ranar Neehal ta sha kalamai da soyayya a gurin shi kala_kala, ita kuwa tay ta masa dariya tana tunanin ranar da aka ɗaura musu aure kuma sai ya kusa mutuwa dan farinciki. Bayan sati ɗaya mahaifinsa da abokinsa da Yayan Maamah suka zo nema masa auren Neehal, tare da kuɗin na gani ina so. Daddy da Kawu Musa da Uncle Mahmud, da mijin Aunty A’isha, su suka karb’i kuɗin, aka saka ranar biki bayan ƙaramar Sallah da yardar Allah, lokacin Neehal sun yi graduation ba jimawa. Su Sadik baki ya ƙi rufuwa, saboda farincikin nan da watanni biyar zuwa shida zai angonce da masoyiyarsa. A ɓangaren Ahmad kuwa a washegarin ranar da ya zo ya koma Abuja, yana zuwa ya sanar da su Ummi abun da yake faruwa. Sun ji ba daɗi sosai har Abban su Ahmad, amma suka ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Ahmad ya bawa zuciyarsa haquri, bai bari damuwa ta masa illa ba, duk da ko d’igo babu abun da ya ragu na son Neehal a cikin zuciyarsa. Daga ya ji abun zai dame sa sai ya dinga maimaita kalmar Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un da hasbunallahu’wani’imal’wakil, ga zuciyarsa kullum cikin ƙarfafa masa gwiwar Neehal tasa ce take, kar ya fidda rai da samun ta. Kuma babu abun da ya canza wa Neehal daga yanda suke before, idan ya kira wa su Afrah ita a waya, ta ce su ba shi wayar yana karɓa su yi magana har da ƴar tsokana wani lokacin, sai dai ba ya mata zancen soyayya ko kaɗan, zumunci kawai suke yi. Itama Neehal ɗin ta yi ƙoƙari ta cire damuwar rabuwa da shi daga ranta. Ta yadda cewa Allah ya yi Sadik ne mijinta tun fil azal, ba Jameel, Anwar da Ahmad ba, tunda su sun rasu, Ahmad kuma shi yasa Allah ya raba su tun a farko, dan da ace ba su rabu da shi ba a lokacin da take gidan Aunty Fauziyya, da ko soyayya ba zata yi da Jameel da Anwar ba, tunda ga shi kuma tun lokacin yake son ta. Ta kwantar da hankalinta suna shan soyayyar su da Sadik. Sai dai tunda aka tsayar da lokacin bikin su take jin wani irin feeling a cikin zuciyarta, feeling ɗin data kasa tantance ko na mene ne, sai dai yana mata yanayin kamar tsoro ko fargaba, amma kuma tsoron da fargabar na mene? Sai kuma wani abu guda ɗaya, ɗan sakin fuskar data fara samu daga gurin Ameen da kulawa ya daina mata yanzu, sai ta gaishe shi ma ya ƙi amsawa, ita kuma hakan na damunta matuƙa, bata son ta ga yana yi mata irin wannan shariyar, sai ta ji duk ranta babu daɗi……..✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
6️⃣0️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#
………..Da yamma Haneefah ta zo gidan, duk da tana fama da laulayi amma ta ce ba zata iya kwana bata ga lefen Besty ba. Bayan sun gaisa da su Mama ta hau sama gurin Neehal. A falo ta tarar da ita idanunta a lumshe tana sauraren karatun Alkur’anin da tasa a speaker. Haneefah ta ƙarasa inda take ta taɓa ta, tare da faɗin. “Amarya.” Neehal ta buɗe idonta ta dube ta, ta yi murmushi ta ce. “Na’am Ango.” Haneefah ta zauna a kusa da ita, ta ce. “Ya na ganki wani iri, ko baki da lafiya ne?” Neehal ta ce. “A’a k’alau nake, kawai yanayi ne.” Haneefah ta ce, “Yanayin me? Ke da ya kamata a zo a tarar kina cikin farinciki da annashuwar kin kusa aure.” Ta ƙarashe maganar da dariya. Neehal ta harare ta, ta ce. “Zan bar Maman shine zan dinga farinciki?” Haneefah ta ce. “Wannan duk na ɗan lokaci ne, kina jin zaƙin auren zaki ware, wuyarta ki shiga daga ciki, ke Auran fa da daɗi.” Neehal ta ƙara hararar ta, ta ce. “Allah ya shirye ki, kin fi ƙarfi na.” Haneefah ta yi dariya ta ce. “Ina Barrister? Na ɗauka zan shigo in same ki kina waya da shi kuna soyewa.” Ta sauke numfashi ta ce. “Yana nan k’alau, ba mu jima da yin waya ba, ina Yah Faruq?” Haneefah ta ce. “Yana can Kogi State.” Neehal ta ce. “Yaushe zaki koma ke?” Ta ce. “Next week insha Allah, tunda by Monday zamu gama exam.” Neehal ta gyaɗa mata kai cikin ƙoƙarin ganin ta ɓoye Mood ɗin da take ciki. Ta tashi ta sauka ƙasa ta ɗebo mata snacks ɗin da akaiwa masu kawo kayan lefen, ta haɗo mata da drinks.
Bayan Magriba kamar yadda aka ce, su Daddy suka karb’i lefen Neehal a gurin magabatan Sadik, suka kuma saka lokacin biki sati takwas, bayan Babbar Sallah da sati biyu kenan. Ba su wani jima ba suka tafi, Daddy yasa ma’aikatan gidan suka shigar da kayan part ɗin Mama, aka baje su a falon ƙasa. Aunty Sadiya ta rangad’a guda, gudar da Neehal dake ɗakinta ita da Haneefah sai da suka jiyo. Wata irin fad’uwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta runtse idanunta ta shiga ambaton Hasbunallahu’wani’imal’wakil a cikin ranta. Haneefah dake gwagwiyar goruba ta ajiye ta miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki ta fice daga ɗakin da saurin ta. Neehal ta ji wasu hawaye masu d’umi sun zubo a kan kuncinta, wanda ta kasa tantance na farinciki ne ko akasin haka, yau ita ce aka kawo lefen ta, hakan ya nuna mata ta kusa zama mallakin Sadik kenan? Ta kusa aure itama? Kamar amsar tambayar ta sai ga kiran shi ya shigo wayarta. Ta saka hannu ta ɗauki wayar tare da buɗe idonta, ta ƙura wa screen ɗin wayar ido da idanunta dake ganin dishi_dishi saboda hawayen dake cikin su, ganin Sadik ne yake kiran sai ta mayar ta ajiye wayar, haka kawai ta ji bata son yin wayar da shi.