NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Set ɗin akwati ɗai ɗai ɗai har goma sha biyu Sadik ya yo, sai kuma takalma da jakunkuna a cikin manyan basket ɗin kaba da ake yi yanzu. Su Aunty A’isha fa suka shiga bubbud’ewa suna dubawa cikin farinciki, Haneefah kuma ta shiga yiwa kayan video. Kaya na gani na faɗa masu tsada da kyau aka zuba a lefen, Sadik ya yi ƙoƙari sosai, dan ya kashe kuɗi ba kaɗan ba. Mama ta rasa inda zata saka ranta dan farinciki, ashe za ta ga lefen ƴarta_ta kafin ta mutu, ta shiga addu’ar Allah ya nuna musu ranar bikin lafiya. Har bayan isha’i suna ta aikin kallon kayan, ba su kuma da alamar dainawa, su Dije ma sun fito suna kallon kayan. Sai kod’a kayan da faɗar kyawun su suke. Haneefah dai tana tsakiyar kayan zaune tana ta aikin ɗaukar hotunan su. Suna cikin duba kayan Haneefah ta dubi Mama ta ce. “Mamana yau kina cikin farinciki, dan haka bari na yi amfani da wannan damar na ƙara roƙar ki abun da nake ta nacin roƙon ki in ƙi yarda.” Mama ta yi murmushi ta ce. “Haneefah da naci kike amma.” Ta yi dariya ta ce. “Ni dai Mama ki amince mu ɗan warwasa, biki lami ai babu daɗi, kamar wadda za ai wa auren dole.” Aunty Sadiya ta ce. “Gaskiya Ya Fateemah ki bar su, su warwasa, muma ma je a warwasa da mu.” Aunty Aisha ta ce. “Gaskiya dai.” Mama ta ce, “Shikenan tunda kun dage, sai a yi kamu kawai.” Haneefah ta ce. “Yeee, yawwa Mamanmu, thank you so much, bari mu zo mu zaɓi atamfa mai kyau mu fitar da anko, dan event da anko ya fi kyau.” Mama ta ce, “Kina fama da kanki, amma sai shegen son bidiri.” Haneefah ta yi murmushi ta ce. “Mama bikin Besty ne fa, aiko jego nake na ajiye ɗan a gefe na wasu kwanaki in sha shagali na.” Suka yi dariya Gaba-d’aya, Aunty Sadiya ta ce. “Allah ya shirya ki Haneefah.” Suka ci-gaba da tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, a nan Haneefah ta sanar musu Sadik ma ya ce za’a yi dinner, Aunty Sadiya ta ce, itama Dinner ya kamata a fitar mata da nata ankon. Anan suka zaɓi atamfar da za’a yi ta kamu da kuma kalar yadin da k’awayen amarya za su yi na ranar Dinner.” Haneefah ta haɗa video na kayan lefen da ankunan bikin ta saka a story. Tare da yin ɗan note na Allah ya sanya Alkhairi da kuma nuna farincikin da take ciki. Har da cewa, Yau tana cikin farinciki bikin besty ya kusa, dan haka ko marin ta akai ba za ta ji haushi ba. Neehal dai tana ɗaki bata san me suke ba, Sallar isha’i ce kawai ta tashe ta, ta tashi ta yi sannan ta koma ta yi kwanciyarta.
Sai da tara ta wuce sannan Haneefah ta shigo ɗakinta. Ta rungume ta cikin murna tare da faɗin. “Besty kin ga lefen ki kuwa, ya haɗu Masha Allah, Yaya Sadik ya yi ƙoƙari sosai wallahi, Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya.” Neehal ta janye jikinta daga nata tana murmushi amma bata ce komai ba. Haneefah ta latsa wayarta ta miƙa mata. Ta karɓa ta shiga kallon videon kayan. Sai ta ji wani irin daɗi ya lullub’e zuciyarta, yanzu duk wannan uban kayan nata ne? Gaskiya dole duk wacce aka kaiwa lefe ta yi farinciki. Ta d’ago ta dubi Haneefah ta ce. “Yanzu har kin musu video?” Haneefah ta ce. “Me zan jira, har na watsa su a media ma.” Neehal ta ce. “Sannu uwar azarbabi.” Haneefah ta ce, “Na ji ɗin, ki yi gaba akwai wanda na haɗa da atamfar ankon da muka zab’a yanzu a wayar Aunty Sadiya, ta ce next week zata yi order, duk mai so sai ya siya. Ki tura videon sai ki yiwa duka friends ɗinki sending, ki faɗa musu date ɗin bikin, 8 weeks aka saka.” Neehal ta ce. “Toh.” Tare da ƙara kallon videon. Ta janyo wayarta, first abun da zata yi kafin sending videon ta fara yiwa Sadik godiya. Ta shiga contact ɗinsa ta rubuta masa text mai cike da tarin godiya da kuma addu’oi, sai kuma kalaman soyayya. Sannan ta tura video’s ɗin ta shiga yiwa k’awayenta sending. Nan fa mutane aka yi caaa a kanta, “Dama bikin ki za’ai Neehal babu labari? Wow kaya sun yi Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi. Ai dole mu yi anko bikin ki guda.” Maganganun da ta yi ta sha kenan, ta dinga murmushi kawai. Haneefah tay ta tsokanarta bayan ta yi Sallah. Mama da kanta ta zo ta kama hannunta suka sauka ƙasa ta ga kayan, su Aunty nata tsokanarta. Ita kuma wata irin kunya take ji, bata ma san tana da kunya haka ba sai yau. Ganin yanda Mama take cikin farinciki, sai hakan ya ƙara mata nata farincikin itama. Ta dinga kallon kayan a cikin ranta tana ƙara yabawa Sadik gami da jinjina masa. Sai kusan ƙarfe goma su Aunty A’isha suka tafi gidajensu, Haneefah kuwa ta yiwa Faruq waya, ta ce masa ta yi dare a gidansu zata kwana. Da Daddy ya shigo gidan ya zauna Mama tana bubbud’e masa kayan yana gani, shi kuma yana ta tsokanar Neehal dake cin abinci. Sai dai ta yi murmushi kawai kanta a ƙasa, sosai take jin farinciki, bata jin ko baccin kirki zata iya yi yau, duk wani feeling na damuwa da take ji kusan rabi ya tafi. Ranar kusan raba dare suka yi suna tattauna yanda bikin zai kasance ita da Haneefah, bayan kowacce ta gama shan waya da masoyinta. Da yake Neehal har Zahra ƙanwar Ahmad ta tura wa lefen, data kunna data sai ta ji voice ɗin su Afrah wanda ya sata dariya ba kaɗan ba. Dan gaba-d’aya yaran sun ruɗe da murna ganin kayan, sai zaɓar abubuwan da suke so a cikin kayan suke tun kafin su zo. Washegari tun safe mak’ota suka fara shigowa ganin kayan, ranar wuni su kay cikin karɓar baƙi ƴan ganin kaya, k’awayen Neehal da k’awayen Mama gami da ƴan’uwa, cikin baƙin har da Hafsat da Hajiya da Matar Uncle Mahmud, da matar Kawu Musa. Neehal dai ta sha tsokana a gurin mutane. Ummin su Ahmad da Mamy sun kira ta a waya sun mata Allah ya sanya Alkhairi. Shima Ahmad ɗin ya kira ta, yay ta tsokanarta kuwa. Da daddare Ameen ya zo gidan, Mama ta bubbud’e masa kayan ya gani, duk da, da farko cewa ya yi ba sai ya gani ba. Amma Mama ta ce, ya dai gani ɗin yasa Albarka. Haka su kay ta shan baƙi ƴan ganin kaya, ƴan aikin gurin su Neehal dana gurin su Mama. Amaryar Uncle Umar ta zo, amma banda Aunty Fauziyya. A gurinta Neehal take jin ashe Uncle Umar ɗin ya saki Aunty Fauziyyan, a dalilin cikin shegen da Iman ta yi, ya haɗa su duka ya kore su. Neehal bata ji daɗi ba har da kukan ta. Shi kuma Uncle Umar ya gama haɗa kuɗaɗen sa zai yo sarin kaya ya zuba a shago b’arayi suka tare shi suka k’wace kuɗaɗen. Aunty Hauwa tana faɗawa Neehal har cuta ya yi saboda tashin hankali da damuwa. Ita kuma ta k’wace duk wasu takardun kadarorin Neehal, kuɗaɗen ta kuma suna account ɗinta. Ta ce ba zai ci kuɗin marainiyar Allah ba, sai dai ya fita ya nemi nashi ko dako ne ya yi. Neehal ta cewa mata ta ba shi dukiyarta ita ta bar masa duniya da lahira, Aunty Hauwa ta ce. Abun da ba zai yiyu ba kenan, dan ta gama yanke shawara ana yin bikin Neehal ɗin zata tattaro mata dukiyarta ta damk’a mata a hannunta, ta juya abunta ta nemi kuɗi. Shi kuma Uncle Umar tunda yana koyarwa zasu cigaba da jalautawa a haka. Neehal dai bata ji daɗin abun ba sam, dan sosai tausayinsu ya cika mata zuciya.
Babbar Sallah saura sati ɗaya Mama ta ɗauko matar da zata yiwa Neehal gyaran jiki daga Maiduguri, sunan matar Hajja Gana, dan Mama so take a gyare mata ita sosai ciki da waje. Da ƙyar Neehal take zama a yi mata gyaran jikin, sai Mama ta mata jan ido tukunna, mai gyaran jikin tay ta dariyar dramar Mama da Neehal, wadda tunda bikin ya matso ta koma so silent, abun kaɗan sai kuka da k’unci. Mama kuwa ta tattara ta, ta watsar shirye-shiryen biki kawai take ba kama hannun yaro. Siyayya ba kaɗan ba take jibgowa Neehal ta kayan kitchen. Daddy kuwa ya ce, a je a duba gidan Sadik sannan Neehal da Mama su je duk inda take so ta zaɓi kayan ɗakinta da kanta wanda zai cika gidan. Ameen kuma Mama ta ɗaura masa nauyin siyayyar duk wani kaya da Neehal zata saka na fitar biki shi zai siya mata, tun daga kan ɗan’kunne da sarka har zuwa takalma, ta ce ba zata saka komai a cikin kayan lefen ta ba. K’awayen Neehal da ƴan’uwa suna ta kara suna ta siyen anko, ƴan NEEHAL FAN’S GROUP ma ba’a bar su a baya ba, sun ce ba’ayi ba su ba. Neehal ta kasa tantance yanayin da take ciki, bikin na ƙara kusantowa tsoron da zuciyarta take ciki na ƙara tsananta. Ta rasa tantance tsoron ko na mene ne, tana jin kamar wani abu mara daɗi na shirin faruwa, duk da kullum Aunty Sadiya cikin rarrashin ta da ƙara jaddada mata cewar haka kowacce amarya haka take jin irin wannan feeling ɗin, ta kwantar da hankalinta ba wani abu ba ne. Ita dai ta ƙara k’aimi gurin dagewa da addu’a, kamar yadda Mama take tunatar da ita a kullum. A ɓangaren Sadik kuwa zai iya cewa tunda ya zo duniya bai ɓata riskar kansa a farinciki irin na wannan lokacin ba, kullum cikin lissafin kwanakin bikin da suka rage yake, tare da ƙara dagewa gurin farantawa Neehal da nuna mata k’auna. Zuwa yanzu Ahmad ya cire rai da samun Neehal, kuɗi masu kauri ya turo mata a matsayin gudunmawarsa, dan ya rasa mai zai sai mata. Da tay masa complain ɗin kuɗin ya yi yawa sai ya yi fushi ya ce bata ɗauke shi a matsayin Uncle ɗin da take kiran shi ba kenan. Da ƙyar ta lallaɓa shi ya haqura sannan tay ta zuba masa godiya kamar ba gobe, Mama ma ta kira shi tay masa godiya.