NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan Babbar Sallah da sati ɗaya an gama soyasoyen nama da shan bukukuwan Sallah wanda ya kama bikin Neehal saura sati ɗaya. Ranar Alhamis da daddare Neehal tana ɗakinta tsaye a gaban mudubi, fitowarta kenan daga wanka bayan da aka gama mulke mata jikinta da haɗin gyaran jiki da ake mata. Tana shafa mai amma kallon fatar jikinta kawai take yi, yanda ta canza ta yi wari irin laushi hami da haske, har wani pink_pink jikinta yake yi saboda an mata halawa. Ita kanta bata gajiya ta taɓa jikinta, dan ji take kamar ba jikinta ba tsabar sulb’i da kyau, dan tana shan gyara bana wasa ba. Ga wani irin fitinannen k’amshi dake tashi a jikinta, duk inda ta gilma kuwa sai an ji shi. Dan ma bata fita yanzu kwata_kwata, tun satin da za’a fara mata gyaran jiki ta ɗauki hutu a gurin aiki. Jiya da Sadik ya zo kawo mata invitations card kamar zai cinye ta saboda santi da kyawun da tai masa.
A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakin tare da yin Sallama, ta juyo ta kalli ƙofar da sauri. Ganin Ameen ne ta yi saurin tashi ta ɗauki hijabin dake gefen gado ta zira a jikinta cikin rawar jiki. Shi ko bai ko kalli inda take ba, ya ajiye ledodin hannunsa a kusa da ƙofa. Ya juya yana ƙoƙarin fita ta ce. “Yaya!” Ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Ta ƙarasa ta tsaya a kusa da shi. A hankali ta ce. “Thank you so much, Allah ya ƙara buɗi.” Ya juyo ya zuba mata ido, itama idanun ta zuba masa ganin yanda yake kamar wani mara lafiya. Lokaci ɗaya idanunta suka kawo ruwa, cikin damuwa ta ce. “Yaya baka da lafiya ne? ko kuma wani abun ne yana damun ka?” Ya yi mata ɗan murmushi tare da girgiza mata kai. Ta fara hawaye ta ce. “Yaya i know baka da lafiya, ko kuma wani abun yana damun ka, Yaya You look so worry.” Ya tako a hankali ya matso daf da ita, a hankali ya kama fuskarta da hannuwansa duka ya saka idanunsa cikin nata ya ce. “Nothing Miemerh, Just pray for yourself and me.” Ta gyaɗa masa kai a hankali cikin rashin fahimta. Ya saki fuskarta sannan ya kuma yi mata murmushi ya juya ya fita. Ta bi shi da kallo tana maimaita abun da ya faɗa a cikin zuciyarta, a ƙoƙarin ta na ganin ko zata gane mai yake nufi amma bata gane ba. Addu’a abu ne mai kyau akan kowanne mutum, may be shi yasa ya ce tay musu addu’a ita da shi. Ta sauke numfashi ta ƙarasa inda ledodin da ya ajiye suke ta tsugunna ta shiga fito da kayan ciki tana dubawa. Kayan da zata yi fitar biki ne da su, kuma gaba-d’aya kalolin da ta ce masa tana so ya siyo. Babu abun da zata saka wanda bai sako ba, har da su undies da pant da bra. Ta yi murmushi ita kaɗai cikin jin kunya. Wedding gowns ɗin da zata saka ranar kamu, Dinner da ranar D’aurin Aure da safe. sun fi komai burge ta da yi mata kyau a cikin kayan, gashi daga ganin su masu tsada ne. Ta cire hijabin jikinta cikin murna ta fara gwada kayan.
Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga bayan ya fita, ya tarar da ita da Aunty Sadiya suna haɗa kayan da suka siyo d’azu a kasuwa. Tunda bikin ya gabato ba’a kwana biyu ba su je kasuwa ba. Bayan ya yi sallama ya zauna a kujerar dake gefen gado. Suka bi shi da kallo, Ba tare da Mama ta amsa gaisuwar da yay mata ba ta ce. “Al’ameen! Meke damun ka ne?” Ya lumshe idonsa bai ce komai ba. Mama ta shiga yi masa masifa akan wannan shegen muskilancin nasa da zurfin ciki, idan wani abu ke damun shi ai sai ya sanar mata, ko baza ta magance masa ba sai tay masa addu’a, amma ya gwammace ya bar abu a ransa yay ta damun sa, ita mahaifiyarsa ce baza ta so ta dinga ganin shi cikin damuwa ba, idan ma wata matsalar ce tsakanin sa da matarsa ai ya kamata ya sanar mata a san abun yi. Tunda ba shi da kamar ta a duk duniyar nan. Faɗa sosai Mama tay masa, Aunty Sadiya na bata haquri amma bata yi shiru ba sai da ta kai aya. Ganin yanda ran Mama ya ɓaci ya dinga bata haquri, ya sanar mata yanayin aiki ne kawai. A k’ufule Mama ta ce. “Aiki, aiki. Daga an yi magana ka ce aiki, kamar kai kaɗai ke aikin duk duniyar nan, a gurin aikin yankar naman jikinka ake ai. Amma ka cigaba idan ganin ka cikin damuwa ya haifar mun da wata damuwar nima ai ka ji daɗi.” Bata jira amsar shi ba ta tashi ta fice daga ɗakin, Ya bita da ido. Aunty Sadiya ta dawo kusa da shi ta zauna cikin rarrashi ta ce. “Ameen! Rayuwar nan cike take da k’alubale da kaddda kala_kala, kowa ka gan shi ka kalle shi kawai, amma shi kaɗai ya san abun da ke damun sa, kuma bawa ba ya taɓa kaucewa ƙaddarar sa, ka saka wannan a ranka, sannan kuma ka rage damuwa, Please Ameen.” Ya sauke numfashi ya ce. “Insha Allah Aunty Sadiya I will try.” Aunty Sadiya ta tsaya kawai tana kallon sa kamar yadda shi ma yake kallon ta, kallo mai kama da na tausayi tare da jiman ta wani al’amari.” Ta ɗauke idonta daga kallon sa cikin raunin murya ta ce. “Ka je ka bawa mahaifiyarka haquri, ka ga ranta ya ɓaci sosai.” Ya ja numfashi mai huci ya sauke sannan ya miƙe bai ce komai ba ya fice, Aunty Sadiya ta girgiza kanta cikin damuwa, alamun something is hurting her heart. Bayan ya tafi Aunty Sadiya suna falo zaune ta cewa Mama. “Ki yi haquri Yaya Fateemah akan al’amarin Ameen, na ga kamar har yanzu ranki a ɓace yake.” Mama ta girgiza kai cikin sanyin jiki ta ce. “Ko ɗaya Sadiya babu d’igon ɓacin ran Ameen a raina, dan ya wanke mun shi tass kafin ya tafi. Amma Sadiya ni na haifi Ameen, na san halinsa ciki da waje, tabbas ko tantama bana yi akwai abun da ke damar mun yaro.” Aunty Sadiya ta ce. “Tunda ya ce miki babu, a matsayin ki na mahaifiyarsa wadda babu hijabi a tsakanin addu’arki a gare sa, ki yi masa addu’a, Insha Allahu in ma da akwai abun da ke damun sa to Allah zai yaye masa.” Mama ta ce, “Haka ne, Allah yasa mu dace. Mu je kiga kayan fitar bikin da ya kawo wa Neehal kafin ki wuce, ya ce mun ya kawo mata.” Aunty Sadiya ta ce. “Masha Allah, Allah ya saka masa da Alkhairi. Mama ta ce, “Amin.” Tare da miƙewa.
Washegari Neehal suka fita da Freind’s ɗinta guda biyu na B.u.k rabon I.v, ba’a son ranta ta fita ba Mama ce ta tilasta mata. Da cewa ta yi zata turawa kowa ta waya, gate pass ɗin dinner kuma zata wakilta wasu su bayar a ranar. Mama ta ce, bata isa ba yara su yi mata anko sannan ta ƙi kai musu kati har gida. Sai yamma liss suka dawo, tana cin abinci kuma aka ɗora mata daga inda aka tsaya a gyaran jiki. Washegari ma ta fita, ta je gurin aikin su ta kai musu katin, sai kuma sauran Freind’s ɗinta da ba su ƙarasa jiya ba. Ranar talata mai ƙunshi ta zo har gida tay musu ita da Mama da su Aunty Sadiya da Haneefah. Saboda Washegari ran Laraba za’a fara bikin, a yi Kamu Laraba, Alhamis a yi Dinner, Juma’a a daura aure akai ta gidan mijinta. Tun yau da taga an yi mata lalle ta ga tabbas da gaske dai auren zatai zata bar gaban Mama ta fara kuka sosai. Mama ta tsaya kawai tana kallon ikon Allah, ta rasa hali irin na Neehal, ta ga dai yara ma ƴanv17_18 years ana musu aure amma basa damuwa haka, sai ita mai 24_25 years. Aunty A’isha ce mai aikin rarrashinta. Tun yau gidan ya fara wadatuwa da baƙi, ciki har da Uncle Usman da matarsa da yaransa guda biyu. Neehal ta rungume shi cikin tsananin farincikin ganin sa. Ta ce “Uncle ɗina na yi kewar ka sosai.” Ya yi murmushi ya ce, “Nima haka Daughter, rabo na dake tun kina ƙarama, gashi har kin girma kin zama ƙatuwa.” Ta yi dariya cikin jin kunya. Aunty Hauwa ma amaryar Uncle Umar tun yau ta zo, su Hajiya ma da wasu ƴan Gombe haka. Ƴaƴan Ummi (Yayar Abba) Maza guda biyu su ma sun zo tare da matansu daga Lagos. Can yamma kuma sai ga Zahra da twins. Farincikin ganin yan’uwa da mutane anata zuwa ya ɗaukewa Neehal hankalin damuwar da take ciki. Ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud da Haneefah da Zahra, duk inda ta yi suna biye da ita, dama amarya akwai farinjini.