NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ranar Kamu da safe sai ga Hameedah da Mommy’nta sun zo, abun ya bawa Mama mamaki amma bata nuna ba, ta karɓe su hannu bibbiyu. Saboda yanda suke nuna tsana ga Neehal bata yi zaton za su zo tun yau ba, ta ɗauka sai ranar D’aurin Aure za su zo. Kafin ka ce me gida ya ƙara cika da baƙi, ƴan’uwan su Mama da ƴan’uwan Daddy. Ba ya ma na Mama, dan Familyn su Mama suna da yawa Masha Allah. Ga shi dama Mama ita ta kowa ce, ko bata je inda kake akai_akai ba, akwai kira a waya ta sadar da zumunci. Hafsah ma ranar tun safe ta zo. Mama zuciyarta fari k’al da farinciki, yau Allah ya nuna mata zata fara taron bikin Neehal, duk da ba’a daura aure ba, amma yanzu zuciyarta babu fargabar komai kamar a baya da suke cike da tsoron kar a kuma kwata kashe wanda Neehal zata aura. Duk da sun fi alaƙanta hakan da shawarar da Uncle Mahmud ya bayar ta ɓoye batun auren sai da ya zo daf sannan aka bayyana. Gidansu Sadik ma ya fara harama da baƙi ƴan biki, suna ta nasu shirye-shiryen su ma. Amma fa har yanzu Hajiyarsu da Kawu ba san bikin suke ba, babu yanda za su yi ne kawai dan suna matuƙar jin kunyar Mahaifin Maamah, baza su iya yin jayayya da shi ba. Umma kuwa ta yi makircinta da kisisina akan ganin an fasa Auren amma bata yi nasara ba. Tun a jiya da safe bayan an gama yiwa su Aunty ƙunshi suka tafi gidan Neehal dake unguwar Tarauni yi mata jere, yau da sassafe kuma suka koma dan ƙarasawa. Masha Allah Gidan ya yi kyau, falo biyu ne da three bedrooms. Sai kitchen da store. Sai kuma ɗakin mai gadi kana shigowa gate daga gefe. Su Mama da Daddy kuma sun cika mata gidan da kaya na gani na faɗa.

Ƙarfe biyu na rana Aunty Sadiya ta saka Neehal ta yi wanka. Ta fito ta zira doguwar riga ta saka hijabi suka ɗauki kayan da zata saka suka tafi gurin kwalliyar da already an yi bucking. Aunty Sadiya ta ce, ta kira Sadik ana yin Sallar la’asar saboda ba su san African time, ƙarfe huɗu aka saka a jikin kati amma kamar biyar haka su taho. Neehal ta amsa mata sannan ta je ta yiwa Mama Sallama suka tafi ita da Haneefah. Gurin kwalliyar ya haɗu sosai, shago ne a cikin wata ƙatuwar plaza dake nan cikin Nasarawa. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka fara yi musu kwalliyar, dan ba mutum ɗaya ce ke yi make up ɗin ba. An riga gamawa Haneefah saboda ita casual make up akay mata. Neehal kuma bridal ake mata. Masha Allah Haneefah ta yi kyau sosai, sai ma data saka kayanta akai mata dauri. Sai biyar aka gama shirya Neehal, faɗar irin kyawun da ta yi ɓata baki ne. Ta yi kyau ƙarshen kyau. Ita kanta ta kasa ɗauke idonta daga kan mirror, sai tambayar kanta take anya kuwa ita ce, ba wata aka canza ba. Aka yiyyi mata pictures da video’s, sai 5:30 Sadik ya zo ɗaukar su shi da wani abokin sa. Ya yi kyau abunsa cikin dakakkiyar shadda sai maik’o take, kalar adon jikin kayan Neehal da head ɗinta. Zuwa lokacin Aunty Sadiya har ta fara kiran su akan su yi sauri su taho, saboda gurin biki fa ya ɗauki harama an fara shagali, amarya da ango kawai ake jira. Mai kwalliyar tasa dole sai da Sadik ya shiga cikin gurin, tana son tay musu pictures tare da Neehal and kuma tana son ta caze shi kuɗi. Yanda Sadik ya ruɗe da ya ga Neehal ba zai misaltu ba. “Wifey ke ce kuwa? Kai Masha Allah na yi dace da kyakkyawar mace.” Su Haneefah da masu kwalliyar su kay tay masa dariya. Ya zaro kuɗi masu yawa a aljihun sa ya bawa mai kwalliyar, duk da already su Neehal sun biya ta, amma ya ƙara mata. Wai ta iya kwalliya babu ƙarya, bayan auran su zaina kawo Neehal ta dinga yi mata. Ita dai Neehal murmushi kawai take, a ranta tana jin abun kamar a mafarki. Wai yau ita ce a matsayin amarya, yanda take zuwa bikin wasu itama an zo nata. Sai 6 suka bar a wajen. Haneefah da abokin Sadik sune a gaban Motar, ita kuma da shi suna baya, ya addaba mata da kallo kamar zai cinye ta. Haneefah kuma na yi musu video da pictures daga inda take a wayarta. Suna isa gurin bikin ta ji gabanta ya faɗi, ta lumshe ido tana ambaton sunan Allah, tare da ƙoƙarin ganin ba ta yi kuka ba. Tana jin Sadik yana mata magana, da kai kawai take iya amsa masa. Sun yi 15 minutes a Motar kafin a gama arranged k’awayen Amarya da abokan ango da za su shiga tare da Amarya da Ango. Daga cikin ball ɗin kuma MC nata b’ab’atun sanarwar isowar ango da amarya. Aka buɗe mata Motor ta fito, tun daga lokacin Camera ta ce mata salama alaikum, aka fara ɗaukar ta a hoto. Kowa na yaba kyawun da ta yi. Ta ƙarasa ta tsaya a inda aka ce mata, Sadik na gefen ta yana ta zuba murmushi. K’awayen amarya ne a gaba, suka fara tafiya cikin tsari suna ɗan yin rawa ta cool music ɗin da aka saka, wadda ta dace da shigowar amarya da ango. Su Neehal suka mara musu baya cikin taku ɗai_ɗai, abokan Ango na take musu baya. Abun dai gwanin burgewa mutane duk an tattashi ana musu video. Ango da amarya suka ƙarasa gurin zaman su, mutane da masu hoto suka baibaye su, kowa na san ya ɗauke su. Sai a lokacin Neehal ta ga twins ɗinta Zahra ta kawo mata su, wanda suke ta kuka tun yamma su sai an kai su inda take. Sun yi kyau sosai cikin shigar da akai musu, hannayensu da ƙafafuwansu sun sha lalle. Afrah ta zauna a gefen Neehal, Amrah kuma a gefen Sadik. Haka aka cigaba da gudanar da shagali a gurin, amarya da ango suka shigo tsakiyar fili aka dinga zuba musu lik’i kamar kuɗin ba su da wahalar samu. Su Haneefah da sauran k’awayen Neehal sun jajige sun ci rawa abin su, amarya dai ƙin takawa ta yi. Shigowa ta musamman aka yiwa Mama wadda ta yi kyau abun ta sosai, kana ganin ta ka ga uwar amarya. Duk yadda Neehal ta so daurewa sai da ta yi hawaye a lokacin, ana saka wak’ar wayyo Allah Mamana ta Ali jita ta ji zuciyarta ta karye, ta tuno Ummanta da Abbanta da basa raye, Allah ya yi baza su ga Auren ta ba. Hawaye take yi sosai, da ƙyar Aunty Sadiya ta lallaɓa ta, ta bar kukan. Mama ta yi musu lik’i sosai ita da Sadik su ma su kai mata, k’awayen Mama sun mata kara sun musu lik’i ita da Neehal. Sai a lokacin Neehal ta ga Ameen ya zo ya yiwa Mama lik’i, haka kawai ta ji daɗi a ranta dan bata yi tunanin zai zo ba, saboda sanin halin sa. Suka haɗa ido yay mata murmushi ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, ya matso kusa da ita ya shiga yi mata lik’in rafar ƴan dubu_dubu. Itama ta zari wasu a hannunsa ta dinga lik’a masa suna kallon juna cikin wani irin yanayi. Ahmad ma ya zo, ta yi mamakin zuwansa dan bai faɗa mata zai zo ba. Haka dai akay ta gudanar da shagali a gurin, a gefe guda kuma masu rabon abinci da drinks suna ta yi. Can na hango ƴan NEEHAL FAN’S GROUP an ci anko an kame akan kujera, su Meerah, Rachel, Ummu Hanif, Hany, Zainab AA, Zainab Aliyu kkm, Miemie Afreen, Aunty ruky, Maman Zahrah, Hauwa’u Sani, Fulani, Hafsat Garba da sauran team ɗin Ameen suna ta kai laumar shinkafa baki suna korawa da drinks. (????????????)Sai hararar Sadik suke tare da gulmar sa wai ko kyau bai yi ba, bai ma dace da Neehal ba. Gefe guda kuma su Ummul Amina ne ana ta yagar naman kaza. (????????????????????????????) Ita da sauran team ɗin Ahmad irin su, Aysha Rawayau, mrs Suraj, mrs Jay, Ruk’ayya, Momyn ruky, A’ishat Abubakar, Aysha Khalil da sauran su dai. Su kuma Ameen suke zabgawa harara dan shi ya tsole musu ido. (????????) Ummul Amina har da gulmar sa wai dan baƙin hali a gurin bikin ma ba zai yi fara’a ba sai haɗe rai yake. Sai da tara ta wuce aka tashi daga taron, bikin yau ya yi daɗi Alhamdulillah an yi lafiya an tashi lafiya saura kuma na gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button