NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare, bayan Neehal ta yi wanka ta saka kayan bacci, tana ƙoƙarin kwanciya duk da ƴan’matan dake ɗakin suna ta hira ba su da niyyar kwanciyar su, ita kuwa ta gaji bacci kawai take buƙatar yi a yanzu. Mama ta aiko Aunty Sadiya ta kira ta. Ta zira hijabi ta fito ta nufi part ɗin Daddy inda Maman take. Ta same ta zaune a falo da kayan fruits a gaban ta. Ta zauna a kusa da ita tare da kwantar da kanta akan ƙafaɗarta. Mama ta ce. “Bacci kika fara ne?” Ta girgiza kai. Mama ta ce. “To sauka ki sha fruits ɗin nan, na san yau ba ki ci wani abincin kirki ba.” A hankali ta ce. “Bana jin yunwa.” Mama ta ce. “Ai ba cewa na yi kina jin yunwa ba, cewa na yi ki sauka ki ci.” Ta zare jikinta daga na Mama a hankali ta sauka ta janyo plate ɗin da suke ciki a yayyanke ta ɗauki yankan Apple ta fara ci, ta yamutsa fuska lokacin da take taunawa. Mama ta ce, “Ya dai?” Bata ce komai ba sai hawaye. Mama ta girgiza kai ta ce. “Oh Allah, Neehal meke damun ki ne? Dan zaki yi aure sai ki koma kamar wadda aka cewa zaki mutu, haba Neehal karki ki kaini bango fa da wannan banzan kukan naki, sai kace a kanki aka fara Aure, duk wanda ake yiwa Auran haka kika ga suna yi?” Neehal ta fashe da kuka ta ce. “To ni Mama id’ont want to leave you.” Mama ta yi murmushi kamar ba ita ta gama faɗa yanzu ba, ta sakko ta zauna a kusa da ita, tare da janyo ta jikinta. Tana ɗan bubbuga bayanta kaɗan ta ce. “Haba ƴar Mamanta, ai kina tare da Mama babu wanda zai raba ki da Ita, dan kin yi aure Neehal ai hakan ba yana nufin kin daina gani na ba ne. Nima dauriya kawai nake, dan ban ma san irin kewar ki da zan yi ba in kin tafi. Amma kuma ina cikin tsananin farincikin nuna mun lokacin Aurenki da Allah ya yi. Neehal burin kowace uwa idan tana da ƴa wadd ta girma ta isa aure to ta aurar da ita, ki yi haquri kin ji, kowa da haka yake sabawa, ai Aure ya zama dole.” Neehal ta gyaɗa mata kai tana ƙara matso hawaye. Mama ta d’ago kanta ta yago tissue ta share mata hawayen. Cikin tsokana ta ce. “Ki rage wannan kukan naki, ko haka zaki haifa mun jikoki suna kuka ke kina yi?” Ta mayar da kanta jikin Mama tana murmushin jin kunya tare da turo baki. Mama ta ƙara d’ago ta, ta ce. “Taso in baki a baki, kin ji ƴar autar Mama.” Ta tashi zaune, Mama ta fara bata fruit ɗin a baki. Sai da ta sha sosai sannan Mama ta ƙyale ta, ta koma part ɗinsu ta kwanta. Mama ta shiga ɗakin Daddy ta tarar da shi yana kaiwa da komowa cikin damuwa. Mama ta dafe kai ta ce. “Yanzu na gama da ƴarka kai ma gaka, sau nawa zan faɗa maka Gen. Ka kwantar da hankalinka, babu abun da zai faru Insha Allahu sai Alkhairi, za’a yi bikin nan lafiya a gama lafiya.” Daddy ya zauna a bakin gado cikin damuwa ya ce. “Wallahi Doctor bana son a kuma samun wata matsalar at this time, na rasa me yasa hankalina ya ƙi kwanciya, bana son a ƙara cutar da marainiyar Allah.” Mama ta ƙarasa kusa da shi ta ce. “Ka saka abun a ranka ne shi yasa, ni duk damuwata tunda na ga bikin ya matso na kwantar da hankalina, addu’a kawai nake kuma na san Ubangiji yana sane da mu, duk wani mai ƙoƙarin cutar da mu Allah ya mayar masa da cutar kansa.” Daddy zai kuma magana Mama ta hana shi, ta hanyar kama hannunsa tana faɗin. “Mu je ka yi wanka, ji bi yanda duk ka haɗa zufa.” Ya miƙe ya bi bayan ta zuwa toilet ɗin, amma shi kaɗai ya san abun da yake ji a ransa na damuwa. Washegari aka yi Dinner bayan Magriba, a wani had’ad’d’en hall. Yau Neehal har tafi jiya kyau, gurin bikin ma ya fi na jiya tsaruwa sai dai bai kai shi girma ba, da yake ba kowa aka gayyata ba, bai fi rabin mutanen jiya ne suka je ba. Shima an warwarsa an ci an sha, Haneefah dai yau bata more da rawa ba kamar jiya, saboda zuwan Faruq gurin. Ya zaunar da ita ya ce baza ta ce ta jawo masa asarar ɗa/ƴa a banza ba. Ta zauna ta dinga ɓata fuska shi kuma yana mata dariya.

Yauma kamar jiya Sadik ne ya kawo ta gida da aka tashi daga gurin bikin, time ɗin 11 na dare ta wuce. Suna zaune a bayan Mota abokinsa da ya yi driving ɗinsu yana gaba. Sadik ya ƙura mata ido tare da kama hannunta. Ta yi ƙoƙarin k’wace wa amma ya ƙi sakar mata. Ta turo masa baki gaba. Ya yi murmushi murya ƙasa ƙasa ya ce. “Wifey gobe by this time muna tare a gidana an kawo mun ke.” Ta d’ago ta kalle shi tana murmushi, sun jima suna kallon juna ido cikin ido, kallo mai cike da k’aunar junan su. A hankali ta fara janye nata idanun tare da lumshe su. Sadik ya lumshe nasa shi ma tare da sakar mata hannu. Cikin matuƙar sanyin murya ya ce. “Mu je in raka ki, kar Mama ta ga kin daɗe, duk da dai na san baza ta damu ba, tunda ta san kina tare da mijin ki.” Tay masa wani kallo ta ce, “Ka bari a ɗaura dai.” Ya yi ƴar dariya sannan ya ce. “Yau da gobe duk ɗaya ne a gurin Allah.” Bata ce komai ba, ya buɗe Motar ya fita sannan ya zagaya ya buɗe mata ta fito itama. Sai da ya raka ta har bakin part ɗin Mama sannan ya juya, yana jin kamar kar su rabu. Dare ya tsala amma Neehal ta kasa bacci, duk hirar ƴan ɗakin sun gaji sun yi bacci. Ita kuwa sai juyi take akan gado, sosai gabanta ke faɗuwa duk bayan sakanni, ta rasa na mamaki ne ko na tsaron Ɗaura mata auren da za’a yi gobe. Sai tambayar kanta take wai da gaske ita za’a d’aurawa aure gobe, abun kamar almara haka take jin sa. Jin wayarta na vibrate ta tashi zaune da sauri ta ɗauka dan ganin wake kiran ta cikin tsakiyar daren nan. Ganin Sadik ne ta cika da mamaki, ta yi pick sannan ta ƙara a kunnenta amma bata yi magana ba. Cikin raunin murya ta ji ya ce. “Neehal baki bacci ba?” A hankali ta ce. “Uhm.” Ya ce, “Why? Ko d’okin za’a kawo ki gidana gobe ne?” Cikin shagwab’a ta ce. “Ni ba haka ba ne, kawai na fara missing Mama ne.” Ya ce. “Ki daina damuwa Wifey, idan Mama ce koyaushe kike so ki gan ta zan kaiki ki gan ta, I promised.” Ta yi shiru tana sauke numfashi. Ya ce, “Nima zumud’i da farinciki sun hana ni bacci, idona murtsitsi babu alamar d’igon bacci, amma yanzu zan je in yi alawala in yi sallah in roƙa mana Allah ya wanzar mana da zaman lafiya a zaman auren mu, ke ma idan kin ji baccin ya ƙi zuwa ki je ki yi, mu raya daren kin ji Wifey.” Ta ce. “Toh Husby.” Suka yi sallama ta katse wayar, duba time ta yi ta ga uku na dare saura. Ta kunna light ɗin wayarta sannan ta sakko daga kan gadon, dan ta san ko ta cigaba da kwanciya baccin ba zuwa zai yi ba, gwara ta bi shawarar Sadik ɗin…..✍️

6k plus words, ten read more. Gaskiya na yi typed yau, sai dai ban yi edit ba, ku yi haquri da typing errors.

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

5️⃣9️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..Haka rayuwa tay ta tafiya, bikin Neehal na ƙara kusantowa. Ɓangarorin biyu na amarya dana ango suna ta shirye-shiryen bikin, duk da dangin Angon ba kowa ke son auren ba. Sai dai kamar yadda Uncle Mahmud ya roƙi alfarma tun ranar da aka kawo kuɗin Auren, akan a ɓoye batun auren sai abun ya matso daf sannan a bayyana saboda tsaro, a cewar sa idan ma wani ne yake kashe samarin da Neehal zata aura kamar yadda ake hasashe, to lokacin da zancen bikin zai fito kafin ya gama duk wani shirinsa an yi bikin an gama Insha Allah. Hakan ce ta kasance kuwa domin ba kowa ya san da maganar bikin ba, sai na jiki_jiki wanda ya zama dole. Ita Mama kam ta ce babu wani shagali da za’ai da bikin, ɗaurin Aure kawai za’ayi akai amarya gidan ta. Sai dai fa shi Ango Sadik da bai san da shirin Mama ba yana ta shirye-shiryen haɗa gagarumar dinner shi da abokanansa. Haneefah ma ta ce baza su yi biki lami ba, sai sun cashe ko da na rana ɗaya ne, tana nan tana ta yiwa Mama naci da magiya akan ta amince. Ita kam Neehal tsarin Maman ya mata dai-dai, dan ita ba gwanar son harkar taro ba ce dama. A wannan azumin na bana Neehal suka ziyarci ƙasa mai tsarki ita da Mama, Mama ta cika alƙawarin data ɗaukar mata tun last year. Sun je sun yi Umrah, satin su biyu a can suka dawo. Bayan Sallah da sati ɗaya suka fara final exam ɗinsu. Neehal ta maida hankalinta sosai akan karatu, ta watsar da duk wani feeling da take ji a cikin ranta ta duk’ufa ga karatu, domin tana son yanda ta fara karatun ta successfully ta gama successfully. A gefe guda kuma zuciyarta cike take da murnar kammala karatunta da zata yi this year.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button