NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Yau Friday wadda ta kama sati uku da fara exam ɗinsu, kuma yau ne za su yi final exam. Exam ɗin safe gare su, hakan yasa tun asuba ta fara shirinta. Ta shirya cikin Black Tomy skirt ɗin da suka yi anko na ƴan class ɗinsu da farar t_shirt wadda aka yi rubutu a gaban rigar, aka rubuta sunan department ɗinsu da year da suka gama school. Ta zauna ta tsara ɗaurin ɗan_kwali a kanta da wani plan yadi Black. Ta saka ɗan kunne mai rawl white colour. Ta ɗaura tsadadden agogon hannu mai kyau Black a left hand ɗinta, sannan right kuma ta saka white abun hannu da k’aton zobe mai stone a ɗanyatsanta na tsakiya. Ta kalli kanta a mirror tare da yin murmushi, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin farinciki a yau. Ta tashi ta ɗauko sabon Black shoe ta zira kyakyawan ƙafuwanta dake sanye cikin socks a ciki. Bayan ta feshe jikinta da sanyayan turarukanta masu daɗin k’amshi ta ɗauko madaidaicin mayafi white colour ta yafa a jikinta, sannan ta ɗauki ƙaramar handbag mai ɗauke da exam card ɗinta da pen da kuɗi da phone’s ɗinta a ciki.Ta riƙe jakar a hannun damanta, hannun hagunta kuma leda ta riƙe mai ɗauke da rigar graduation ɗinta a ciki. Ta fito ta nufi part ɗin Daddy domin Mama tana can. A falo ta tarar da su a zaune akan carpet Daddy yana breakfast. Ta ajiye kayan hannunta ta tafi da gudu ta rungume Mama tana murmushi. Mama tana murmushin itama ta shafi gefen fuskarta ta ce. “Congratulation my Daughter, Allah ya albarkaci karatunki da rayuwarki baki ɗaya.” Tana murmushi ta ce “Amin, Thank you so Much Mum.” Sannan ta tashi ta koma kusa da Daddy ta zauna ta ce. “Good Morning Dad.” Yana murmushi cike da kulawa ya ce. “Morning Daughter, how was your preparation of been a graduate?” Ta ce “Alhamdulillah.” Daddy ya ce, “To Masha Allah Daughter, Allah ya bayar da sakamako mai kyau, ya nuna mun ranar da zaki zama professor.” Ta ce “Amin My Dad, than you so much.” Ya ce “You are welcome Dear.” Mama ta dube ta, ta ce, “Dafatan kin yi breakfast, ba saurin tafiya school ba.” Ta girgiza kai ta ce. I’m full.” Daddy ya ce, “A’a Daughter, ba’a yi celebration ciki babu abinci ba, zauna mu ci a nan taree.” Ta ce “Toh Daddy na.” Ta haɗa tea ta sha tare da bread. Ƙarfe bakwai da mintuna tay wa su Mama sallama ta tafi, su kuma suka bi ta da addu’a tare da fatan samun nasara. Bayan ta ƙarasa school ta tarar da classmates ɗinta cikin irin shigar jikinta, mata da skirt maza da wando. Cikin farinciki Freind’s ɗinta suka tarb’e ta, kowacce tana yaba kyawun da ƴar’uwarta ta yi. Ƙarfe takwas da mintuna suka shiga ɗakin jarrabawa, Alhamdulillah exam ɗin ta yi mata sauƙi dan jiya kusan raba dare ta yi tana karatu. After 1 hour waɗan da suka gama suka fara submit na exam sheet, itama submitted ta je ta yi dan already ta gama. Tana fitowa suka rungume juna ita da wasu classmates ɗinta da suka riga ta fita, suna taya juna murna. Ta ɗauko wayarta ta shiga WhatsApp ta yi story da Alhamdulillah. Dai-dai nan sak’on text message ya shigo wayarta daga Ameen. Ta buɗe da sauri ta karanta. Murnar graduation yay mata tare da tarin addu’oin nasara a rayuwarta. Ta yi murmushi cikin jin daɗi, a ranta ta ce. “One like no other, My Yaya.” Tay masa reply da thank you. Daga nan suka shiga ɗaukar pictures ita da classmates ɗinta, har time ɗin gama exam ɗin ya yi, kowa ya fito daga exam hall, suka sassaka rigunan su na graduation mai ɗauke da sunayen kowa a jikin tasa. Rigar white and black colour ce, sai ta dace da dress ɗin jikinsu. Sun sha hotuna yau kamar ba gobe, Haneefah ta zo mata har yamma suna tare a school, whites t_shirt ɗin jikinsu gaba-ɗaya ta ɓaci da sign out, dan ma ita Neehal bata bari an mata ba sosai ba, k’awayenta mata ne kawai su kay mata. Sai kusan Magriba ta koma gida, ta tarar Mama ta haɗa delicious for Dinner na taya ta murnar graduation. Sai bayan ne Magriba ta kunna datar wayarta dan tun safe da tay posted pics ɗinta bata kuma kunnawa ba, ta tarar da tarin messages daga mutane ana mata congratulations, ciki har da Sadik da Ahmad, sai kuma waɗanda suka ɗora ta a status da pics ɗin da ta yi posted. Ta yiyyi screenshot ta ɗora a story tare da godiya. Sosai take cikin farinciki yau, today is another unforgettable Day in her life. Bayan ta yi wanka ta canza kaya tana zaune a falon ƙasa kan dinning table tana cin delicious ɗin da Mama ta haɗa mata Ameen ya shigo falon. Kasancewar tana dinning area hakan yasa bata ga shigowar shi ba. Ya zauna suka gaisa da Mama. Sai da ta miƙe domin ɗauko juice dake ɗan nesa da ita akan dinning ɗin, sannan ta hango shi. Ta ɗauko juice ta tsiyaya ta sha idanunta na kansa, sannan ta ajiye cup ɗin ta nufo inda suke. A kusa da shi ta zauna duk zuciyarta cike take da tsoron kar ya share ta, amma sai ta ga saɓanin abun da ta yi tsammani. Ya juyo yana kallon ta fuskarsa ɗauke da murmushin da ta manta rabon da yay mata, kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin. “Congratulation.” Ta yi murmushi cikin daɗi ta ce. “Thank you Yaya.” Ya gyaɗa mata kai sannan ya ɗauke kansa daga gare ta. Ta gaishe shi ya amsa mata cikin kulawa, sannan ta tashi ta ɗauki wayarta ta tafi upstairs dan amsa kiran da Sadik yake ta zuba mata. Tana shiga ɗakinta wani kiran nasa yana ƙara shigowa. Ta d’aga tare yin sallama. Ya amsa mata tare da faɗin. “Graduate.” Ta yi fari da ido tana murmushi ta ce. “Yes Barrister.” Ya yi murmushi ya ce. “Congratulation once again Dear.” Ta ce “Thank you, Husband to be.” Ya ce, “Wow kina fasa mun kai fa, idan kika ce Husband to be ɗin nan.” Ta yi ƴar dariyar dake bayyanar da farincikinta ta ce. “To na daina faɗa maka.” Ya kwaikwayi muryarta ya ce, “Ai bakinki ne ya iyar faɗar Husband, ina son ki kira ni da sunan.” Ta murmusa ta ce, “To Husby, Ya Maamah da Abba?” Ya ce “Suna nan k’alau, suna taya surukar su murnar been a graduate.” Ta ce “To ina godiya sosai.” Ya ce “Diarlin ya kamata mu haɗa wani ɗan special party fa, na taya ki murna.” Ta ce, “Hmm Daddy ya so haɗa mun amma Mama ta hana, ta ce ita bata son wannan bidi’a_bidi’an, ka san halin Mama sai ita. Sadik ya yi dariya ya ce. “Mama tamu, Allah ya bar mana ita.” Ta ce. “Amin.” Suka ci-gaba da hirar su, suna cikin wayar kira ya shigo wayarta, ta duba ta ga Ahmad ne yake kiran ta. Ta cewa Sadik zata ɗan d’aga waya mintuna kaɗan, ya ce babu damuwa. Ta d’aga kiran cikin sauri ganin yana ƙoƙarin katsewa.

Ahmad ya ce “Princess!” Ta ce “Na’am my uncle.” Ya ce “Kina waya da my in-law shine kika katse kika daga kira na?” Ta yi murmushi ta ce. “To ai kai Uncle ɗina ne, dole ya yi haquri in yi waya da kai, tunda cikin biyayya yake karka fasa ba shi auren ƴarka.” Ya yi murmushi mai sauti ya ce. “Yaranki ne suka ce na kira ki they want to congratulate you.” Neehal ta ce. “Allah sarki ƴaƴan albarka, amma fa sun so su yi late.” Ahmad ya ce, “Lefin Daddy ne bai kira musu Aunty da wuri ba, yau kuma a gidan Ammi suka wuni babu mai Numbern ki a gidan.” Neehal ta ce. “To a basu wayar in ji muryoyinsu ko hankalina zai kwanta, in ji sa’idar kewarsu dake cike a raina.” Ahmad ya cire wayar daga kunnensa ya saka a speaker, ya ajiye a gaban su Afrah da suka zuba masa ido amma babu damar su yi magana, dan ya ce duk wanda ya yi masa surutu yana waya ba zai yi magana da Aunty ba, kuma ba zai ci cake ɗin celebration ɗinta ba. Cikin rige_rigen Magana suka ce. “Aunty congratulation.” Neehal ta yi murmushi ta ce, “Thank you so much my kids, Allah yay muku albarka, yaushe zaku zo Aunty ta gan ku, dan I missed you over.” Afrah ta yi saurin fara magana da faɗin. “Aunty Daddy ya ce sai bikin ki zamu zo, wai kin kusa zama amarya.” Neehal ta murmusa ta ce. “Toh Shikenan Daughter, ya school?” Amrah ta ce. “Aunty now we are in primary one.” Neehal ta ce “Masha Allah, yarana sun girma har sun shiga primary, what about islamiyya?” Afrah ta ce. “Muna suratul Jin.” Ta ce, “Masha Allah, ku dage da karatu kun ji yaran kirki, ban da over play, idan kuna karatu sosai I will give you something special.” Suka ce. “Toh Aunty, Daddy ya ce zaki yanka Cake for your celebration, Aunty ki kawo mana mu ci.” Na ce. “Insha Allah, zan kawo muku.” Ahmad ya ɗauke wayar jin za su kuma wata maganar ya ce. “Ya’isa haka kar a ƙarar mun da credit.” Neehal ta ɓata fuska kamar yana ganin ta, cikin shagwab’a ta ce. “Kai Uncle, muna hirar mu mai daɗi zaka katse mana?” Ya ce. “Sorry Aunty, zan mayar da su gidan Ummi ne, idan na bar su kuma surutunsu ba ya ƙarewa sai mu yi dare, kuma i want to tell you something.” Neehal ta ce. “What?” Ya lumshe ido ya buɗe ya ce. “I was engaged today.” Cikin razana ta waro Idanunta waje tare da dafe saitin zuciyarta da hannunta, saboda wani abu da ta ji mai zafi ya soki zuciyarta. A hankali ta shiga sauke numfashi amma ba ta ce komai ba. Ahmad ya cigaba da magana. “Neehal! Zuwa yanzu na riga na fitar da ran samun ki a rayuwata, duba da yadda bikin ki ya rage bai fi saura 1 month ba. Amma kuma zuciyata ta kasa daina tunanin ki, ta kasa rage sonki ko da kaɗan ne. Neehal! Ina tsoron ki yi Aure na dinga tunanin ki ina kwasar zunubi, hakan yasa na yanke shawarar yin aure nima nan da watanni kaɗan, na san idan ina da mata zata ɗauke mun hankalin tunanin ki.” Ta lumshe idonta hawaye ya biyo ta ƙasan idon, ta sani ita macece mai kishi, yanzu ma kuma ta san kishin Uncle ɗin nata ne yake damun zuciyarta. Ta daure sosai dan ganin bai fuskanci halin da take ciki ba, ta ce. “Masha Allah My Uncle, Allah ya sanya Albarka, Allah yasa matar rufin asirinka ce, Allah ya kau da duk wata fitina dake cikin auren ku. Allah ya bata ikon riƙe ka da amana kai da twins.” Cikin jin daɗi ya ce. “Amin, Amin Princess, na gode sosai. But one thing Princess, Twins naki ne, babu matar da zan iya bawa ta riƙe mun su matuƙar kina raye. Dan haka bayan aurenki idan kun gama cin amarcin ku, Indai mijinki ya amince zan kawo miki su, ki riƙe ƴaƴanki har auransu idan Allah ya nufa.” Ta buɗe idonta hawaye na cigaba da zuba daga idanun, bata jin zata samu wanda zai so ta kamar Uncle ɗinta, tana son twins sosai, amma ta san duk k’aunar da take musu ya fita son su, amma ya sadaukar da nasa son saboda ita, saboda ta yi farin ciki a rayuwarta. “Me yasa baza mu yi aure ba mu mori soyayyar da muke wa juna?” Ta yi maganar da a tunaninta a zuci ta yi, sai da ta ji Ahmad cikin raunin murya ya ce. “Allah ne bai yi ba Princess.” Sannan ta yi realising ashe a fili ta yi maganar. Ta ja gwauron numfashi tana hasaso irin kulawar da zata samu a gurin Ahmad data aure shi. A hankali ta ce. “Thank you so much Uncle, Allah ya biya ka da Aljannah.” Ya ce “Amin Princess, and you too.” Ta kawar da damuwar dake cin ranta ta ce. “Ya sunan Auntin tawa?” Ya ce, “Kina so ki sani?” Ta ce. “Eh mana, idan da hali ma har da pics ɗinta domin in ga ko ta dace da kyakkyawan Uncle ɗina, one in the million.” Ya yi murmushi ya ce. “Yanzu kuwa Princess, dan idan ba tay miki ba dole a canza ta, a samo duk kalar wadda kike so.” Ta yi ɗan murmushi mai ciwo, a ranta ta ce. ‘Da son samu ne ni nake so ka aura Uncle.’ amma a fili sai ta ce masa. “Na san ma ta yi, Uncle ɗina ba zai yi zaɓen da zai bani kunya ba.” Ya murmusa ya ce, “Sai dai kin gani zaki tabbatar, zan tura miki pics ɗinta yanzu ta WhatsApp.” Ta ce. “Toh Uncle.” Ya ce, “Good night, ki je ki cigaba da waya da in-law kar ya yi fushi, ga yaranki har sun fara bacci.” Ta ce, “Ka shafa mun kansu, and my regard to Ummi, Abba, Zahra and my Aunty.” Ya ce “Duk za su ji Insha Allah, ki gaishe da Mama.” Ta ce, “Zata ji Insha Allah.” Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Ta zare wayar daga kunnenta tare da zuba mata ido, tana jin zuciyarta babu daɗi sosai akan auren da Ahmad zai yi. Kenan duk soyayyar da yake cewa zai nuna mata idan sun yi Aure yanzu wadda zai aura zai yiwa ita. Sai ta ji wani kishi ya ƙara cika mata zuciya, a ganinta kamar ya yi sauri, ai da ya bari ya ga an ɗaura mata Aure sannan sai ya fara tunanin yi shi ma. Ta ɓata fuska tare da kunna data ta shiga WhatsApp dan ganin pics ɗin da ya ce zai tura mata. Ya turo kuwa kamar yadda ya faɗa, da sauri ta buɗe ta kalla, wata Black beauty ce, amma daga gani ta girme mata. Tana ta zuba murmushi a hoton, tana da kyawunta dai-dai gwargwado. Ta yi back, ta karanta gajeran bayanin da yay mata akan yarinyar, Nurse ce a asibitin da yake aiki, a nan suka haɗu sunanta Khadijah. Neehal ta masa reply da Allah ya tabbatar da Alkhairi. Sannan fita daga WhatsApp ɗin ta kira Sadik suka ci-gaba da hirar su. Washegari Sadik ya kawo mata prame mai ɗauke da hotonta, tare da banner mai ɗan girma, da turaruka as her graduation gift. Ranar Sunday wanda ya kama kwana biyu da yin graduation ɗinsu, ranar za su yi Graduation dinner da suka haɗa iya ƴan class ɗinsu, a wani tsadadden hall ƙarami. Ƙarfe biyar da mintuna na yamma ta sakko cikin shirinta na tafiya. Tana sanye cikin wani had’ad’d’en less kalar black and red. Ɗinkin riga da skirt akai mata wanda ya zauna dass a jikinta. Ta kafa kwatancen dauri mai V a kanta. Ta yi kyau sosai kayan ya ƙara haska farar fatarta. Turus ta tsaya a falon ganin Ameen zaune shi da Mama, dan ɓata tunanin ganin shi at this time ba, tunda ba ya zuwa gidan sai dare. Mama ta dube ta, ya ce. “Me ya faru na ga kin tsaya? ke da tun d’azu kike ce mun sauri kike.” Ta ƙaraso cikin falon tana kallon sa wanda sai a lokacin ya d’ago ya dube ta. Kamar mara gaskiya ta ce. “Yaya Ina yini.” Bai amsa ba sai cewa ya yi. “Where are you going?” Ta kalli Mama ba ta ce komai ba, Mama ta ce. “Party suke yi yau na graduation ɗinsu.” Ya dubi Neehal yana ɗan haɗa rai ya ce. “Party kuma na me?” Mama ta ce. “Na ƴan class ɗinsu mana.” Ya kafe ta da ido bai ce komai ba, tay saurin yin ƙasa da kanta cikin tsoron kar ya hana ta zuwa, dan ta san kaɗan daga aikinsa ne ya hana tan.” A hankali ta ce. “Mama zan tafi.” Mama ta ce, “Allah ya kiyaye a hanya, ki kula fa sosai kuma karki yi dare.” Ta miƙe tana faɗin. “Insha Allah Mama, sai na dawo.” Ameen ya haɗe rai sosai yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ce. “Wai wanne irin party ne da ba’a yi shi tun rana ba sai daf da Magriba za’a tafi? A dawo yaushe kenan?” Neehal ta yi raurau da ido kamar zata yi kuka, dan ta saddaqar hana ta zai yi.” Mama ta ce, “Bayan Magriba zata dawo.” Sannan ta mayar da kallonta ga Neehal ta ce. “Wuce ki tafi Daughter, saura ki bari hawayen idonki su zubo ki ɓata kwalliyar ki.” Ta gyaɗa mata kai. Ameen ya miƙe yana faɗin, “Mu je in kai ki.” Ta kalle shi ta ce, “To Yaya wa zai dawo da ni?” Ya mata wani kallo ya ce. “Ban sani ba.” Mama ta ce, “Ku je Daughter, zan zo in ɗauko ki, kafin ku tashi ki kira ni.” Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fice daga falon. Mama ta dube shi tana taɓa baki ta ce. “Yarinya tana cikin farincikinta zaka canza mata mood, ta kusa dai hutawa da takurar ka, tunda in ta yi aure baza ka bi ta gidan mijinta ka nuna mata iko ba.” Bai ce Komai ba, ya fice daga falon. A bakin Motarsa ya tarar da ita tsaye tana jiran sa. Bai mata magana ba ya buɗe Motar ya shiga, itama buɗewa ta yi ta shiga tana tutturo baki gaba. Ya kalle ta sau ɗaya ya ɗauke kai sannan ya kunna Motar suka tafi. Sai da suka hau kan titi ya tambaye ta gurin da za su, ta faɗa masa. Suna cikin tafiya ta ce, “Yaya.” Ya ce. “Uhm.” Sai kuma ta yi shiru, ya ce. “Mene ne?” Jin yanda ya yi magana cikin sanyin murya sai ya bata k’warin gwiwar tambayarsa abun da yake damunta a rai. “Yaya wai dan Allah me nake maka sometimes sai in ga kana ta shashshare ni.” Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Ya juyo ya kalle ta, sannan ya yi ɗan murmushi ya ce. “Kina son in daina miki hakan ne?” Da sauri ta ce. “Eh.” Ya mayar da duban sa ga titi sannan ya ce. “Why?” Ta ce. “Saboda kai kaɗai ne Yayana, ina son na ga muna rayuwa kamar kowanne Yaya da ƙanwarsa.” Ya yi shiru na tsawon mintuna biyu, kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce. “Yanzu kamar yaya muke rayuwar? Ai kamar kowa ne dama.” Ta ce. “Ni dai bana son yanda muke, sai nake ganin kamar wani laifin nake maka.” Ya juyo ya mata wani kallo da lumshashshun idanunsa, cikin wata irin so cool voice wadda tasa Neehal lumshe ido ba tare data shirya ba, ya ce. “Yes akwai abun da kikai mun.” Ta buɗe ido da sauri tare da waro su cikin mamaki ta ce. “Mene Yaya, ka faɗa mun ba zan kuma yi maka ba, Insha Allah.” Ya murmusa ganin yanda ta ruɗe ya ce. “I will tell you, but not now, kuma don’t ask me again, idan lokacin da ya dace ki sani ya yi zan sanar miki da kaina ba tare da kin kuma tambaya ta ba.” Ta shagwab’e fuska ta ce. “Please Yaya ka faɗa mun yanzu.” Ya ɓata rai ya ce, “Ba ki ji mene na ce ba ne?” Bata kuma magana ba, a ranta tana jinjina halinsa, yanzu zaka gan shi faran_faran take kuma sai ya canza. Ta kwantar da kanta a jikin kujera tana tunaninta ita kuwa wanne irin abu tay masa da yake mata haka? Har suka ƙarasa gurin babu wanda ya kuma magana. Sai bayan ya yi parking ne ta ce masa. “Thank you.” Ya ce, “Saura kuma ki je ki ta rawa.” Ta turo baki a ranta tana faɗin. ‘Ko yaushe ya taɓa ganin ta tana rawa ma da zai ce kar ta yi.” Ta buɗe ƙofar ta fita, ta kalle shi ta d’aga masa hannu. Ya gyaɗa mata kai kawai tare da bin ta da kallo harta shige gurin. Sai bayan isha’i sannan aka tashi, partyn ya yi musu daɗi da armashi yanda suke so. Ga mamakin Neehal Ameen ne ya dawo ya ɗauke ta, sai ta yi tunanin ko Mama ce ta tilasta masa ya zo, dan ta san halinta zata iya cewa tunda shi ya kai ta sai ya koma ya ɗauko ta……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button