NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan Kwana Uku ya kama ranar Laraba, ranar ne kuma za’a kawo lefen Neehal daga gidan su Sadik. Tun safe tana kwance akan gado ko falo bata fito ba, balle ta sauka ta ci abinci. A kwanaki ukun nan da suka wuce gaba-ɗaya bata jin daɗi, yanayin feeling ɗin data ke ji a cikin zuciyarta na ƙaruwa. Ji take kamar ta ce ta fasa Auran Sadik Ahmad take so, amma akan me to? Idan so ne ta san tana son Sadik, kuma babu wani abu da yake mata wanda bata jin daɗin sa, kullum cikin ƙoƙarin faranta mata yake, bare ta ce ga dalilin da yasa ta fasa auren sa. Sai daga baya ta gane Auren take tsoro gaba-ɗaya ba Sadik ɗin ne bata so ba. Mama bata bi ta kanta ba ayyukan ta kawai take, ta lura abun nata har da iskanci. Aunty Saudiya ce da suka zo tun safe ita da Aunty A’isha dan taya Mama aiki da kuma jiran masu kawo kayan lefen, duk da Maza ne za su kawo, amma sai an kawo za su tafi. Wajen sha biyu na rana ta shiga ɗakin Neehal, ganin tunda suka zo ba ta ga gilmawar ta ba. Ta zauna a gefen gadon tare da yaye bargon data lullub’e jikinta da shi, ta ce. “Neehal baki da lafiya ne?” Ta buɗe ido jin muryar Aunty’n, ta yunƙura ta tashi zaune tana hawaye. Aunty Sadiya ta ce. “Subhallahi! Neehal meke damun ki?” Ta girgiza kai ta ce, “Babu komai Aunty.” Aunty Sadiya ta ce. “Babu komai amma kike kwance kin ƙi tashi kuma gashi kina kuka?” Ta yi shiru ba ta ce komai ba. Aunty Sadiya ta kamo hannunta ta ce, “Please talk to me, ko da akwai wata matsala ne?” Ta ce. “No Aunty, just I’m scared” Aunty Sadiya ta ce. “Tsoron me kuma Neehal?” Ta ce. “Na auren nan.” Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. “Ki daina jin wani tsoro babu abun da zai faru Insha Allah, wannan emotions ne da kowacce mace take feeling idan Aurenta ya gabato, wani lokacin kuma shaid’an ne, sai yay ta saka maka wasu abubuwa a cikin ranka game da Auran, ka ji kamar a fasa.” Ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. “Ki daina damuwa, ki yi ta addu’a kawai, muma duk mun ji irin wannan yanayin a namu lokacin Auren.” Neehal ta gyaɗa mata kai. Aunty Sadiya ta ce, “Yawwa Daughter, ke fa amarya ce, farinciki ya kamata ki dinga yi, kin kusa tafiya gidan masoyinki.” Ta rufe fuskarta da duka hannayenta biyu, Aunty Sadiya ta yi dariya tare da miƙewa ta ce. “Ki tashi ki shirya, sai ki sakko ƙasa ki yi breakfast, yau ai ranar farinciki ce bata damuwa ba.” Ta amsa mata, tare da saukowa daga kan gadon ta nufi toilet. Zuciyarta na tuna mata exactly day like this, ranar da za’a kawo lefen ta daga gidan su Anwar, amma Allah bai nufa ba aka kashe mata shi. Ta tambayi kanta da faɗin. ‘Ko wannan karon za’a bari a kawo mata lefen har a yi bikin nata? ko kuwa shima Sadik ɗin kashe mata shi za’ai?………✍️

Ban yi edit ba Yau, a yi haquri da typed errors.

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

6️⃣1️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………Toilet ta shiga ta ɗauro alwala ta fito, tun a toilet ɗin ta ji wayarta ta yi vibrate alamar shigowar message. Bata bi ta kanta ba, ta tayar da Sallah. Har aka fara kiraye_kirayen Sallar Asuba tana kan darduma tana lazimi, zuwa lokacin ta fara jin bacci na fizgar ta, daurewa kawai take saboda bata so ta rasa Sallah akan lokaci. A lokacin ne kuma ƴan ɗakin suka fara tashi daga bacci. Tana nan zaune har aka yi kiran assalatu aka shiga sallah. Ta miƙe dak’yar dan jin ta take kamar mai cuta ta yi Sallah, tana idarwa ta haye gado ta kwanta, tana jin tsiyar da su Haneefah suke mata ta share su, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauke ta. Sai da bakwai na safe ta wuce sannan Aunty A’isha ta shigo ta tashe ta. Ta tashi ba dan baccin ya ishe ta ba, dan har ciwo kanta ya fara mata. Aka cigaba shirye_shirye ana ta dafe_dafen abinci a bayan gidan, kowa nata hada_hada cikin farinciki, amma ita tana zaune ta yi tagumi, so take ta yi kuka ko zata ji sauƙin abun da take ji a ranta, amma bata son faɗan Mama dana su Aunty Sadiya shi yasa take ta daure kukan. Ta ɗakko wayarta ta kunna data ta shiga media. Ƴan’matan dake ɗakin suna ta tsokanarta tare da yin hirarsu, amma ko ƙala bata ce musu ba, dan ta san tana buɗe baki da nufin magana kukan da take ta ƙoƙarin dannewa ne zai taho. Haneefah ta shigo ɗakin da plate ɗin wainar shinkafa ɗauke a hannunta. Ta zauna a gaban Neehal ta fara ci tana faɗin. “Bebinki ya mayar da ni uwar ci, duk abincin dana ci kafin na kwanta amma ina tashi na ji cikina na mun ƙugi”. Neehal ta d’ago daga lallatsa wayar da take, cikin sanyin murya ta ce. “Dama can ke acici ce, karki yiwa ɗana ko ƴata sharri.” Haneefah ta ce. “Hmmm, kwana nawa ne kema kin yi inda rai, a lokacin zaki tabbatar sharri na yi ko gaskiya na faɗa.” Neehal ta ce. “Me zan yi?” Haneefah tana dariyar mugunta ta ce. “Cikin mana.” Neehal ta ɓata fuska bata ce komai ba, a ranta tana tunanin abun da Haneefah ta faɗa, kamar tana mamakin abun. Haka kawai ta ji tana son jin muryar Sadik, ta shiga phone ta yi dialing Numbern shi, tay ta ringing amma bai ɗauka ta ba. Sai ta yi tunanin wataƙila bacci yake tunda jiya bai samu ya yi ba. Ta lumshe idonta kawai tana sauke numfashi. Haneefah ta dube ta da kyau ta ce. “Lafiya kike kuwa Neehal? yau fa ranar farinciki ce a gare ki, amma na ga duk kin yi kamar wata mai cuta.” Ta buɗe idonta tare da girgiza mata kai. Haneefah ta ce. “Are you sick? Ko kewar Maman ce kika fara tun yanzu?” Kamar zuga ta, ta yi sai ga hawayen da take ta ƙoƙarin mayarwa sun zubo. Cikin lallami Haneefah ta ce. “I’m sorry Besty, Dan Allah ki bar kukan nan kar hankalin mutane ya dawo kan ki.” Ta share hawayen tare da gyaɗa mata kai. A hankali ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet ta yi brush, sannan ta fito ta tafi part ɗin Daddy, dan anan kayanta na sakawa suke. Mama da kanta ta kawo mata ruwan zafi da kayan haɗin tea, ta haɗa mata ita da su Afrah dake mak’ale da ita suka sha. Sannan ta kawo musu abubuwan toye_toye irin su, waina, sinasir, funkaso suka ci. Duk da ita Neehal kaɗan ta ci, dan da ƙyar suke iya wuce mak’oshinta, cusawa kawai take ganin idon Mama. Wajen ƙarfe tara Aunty Sadiya tasa ta, ta yi wanka, ta shirya cikin wani had’ad’d’en less ɗinkin riga da zani, ta yi kyau sosai duk da ba ai mata make up ba. Sai anjima mai make up ɗin zata zo har gida tay mata, tunda d’aurin Auren sai ƙarfe biyu na rana za’a yi, bayan an idar da sallar juma’a za’a daura. Ta dawo part ɗin Mama ta zauna suna ta yin pictures da su Haneefah. Abokan wasa nata tsokanarta. Ƙarfe goma na safe sai ga Aunty Fauziyya da Iman da Aiman sun zo. Neehal ta tarb’e su cikin fara’a, har da musu tsiyar shine tunda aka fara bikin ba su zo ba sai yau. Aunty Fauziyya ta bata haquri da cewar Iman ce bata jin daɗi shi yasa ba su zo ba. Neehal tay mata sannu cikin tausayawa, yarinyar duk ta rame ta d’ashe, ana kallon ta an ga mai ƙaramin ciki, itama Aunty Fauziyyan kamar me jinya ta k’anjale ta yi baƙi. Sai ga Hafsah ba kunya ta zo tana yiwa Neehal magana cikin fara’a, abun ya bawa Neehal mamaki, amma sai ta ɗauki hakan a matsayin fuska biyun da take mata. Kamar ta tambaye ta Ameen da kuma dalilin da yasa bai zo dinner jiya ba sai kuma ta fasa. Gida fa sai ƙara cika yake da baƙi mata da maza. Neehal har ta fara gajiya da gaisawa da mutane. Ƙarfe goma sha biyu na rana mai make up ta zo gidan ta fara yiwa Neehal kwalliya, wadda zuwa lokacin hankalinta gaba-ɗaya yana kan angon ta. Ta ƙara kikkiran sa bayan kiran da tay masa na safe amma bai ɗauka ba kuma bai kira ta ba har yanzu. Duk da ta masa uzurin may be ya shiga cikin hada_hada da mutane ne. A dai-dai lokacin Mama tana bedroom ɗin Daddy tana shiryawa cikin shigarta ta biyu a ranar, fuskarta ɗauke da farincikin nuna mata ranar D’aurin Auren Neehal da Allah ya yi. Tana zira sark’a Daddy ya shigo dakin kamar an jeho shi, kallo ɗaya tay masa ta cikin mudubi ta san akwai matsala. Gabanta ya yi mummunar fad’uwa, ta miƙe tsaye har wayarta dake kan cinyarta na faɗuwa a ƙasa ta juyo tana kallon Daddy dake ta goge gumin fuskarsa, in ba gizo idanunta ke mata ba har yar rama ta ga ya yi. A ruɗe ta ce. “Gen. Lafiya kuwa?” Daddy ya sauke zazzafan numfashi cikin tsananin damuwa ya ce. “Akwai matsala Doctor.” Wani irin sarawa Mama ta ji kanta yay mata, jikinta har rawa ya fara, cikin rawar murya ta ce. “Matsalar me?” Daddy ya kamo hannunta kamar zai yi kuka ya ce. “Yanzu Mahifin Sadik ya kira ni, wai an neme shi an ransa.” Mama ta waro Ido waje tare da k’wace hannunta daga na Daddy, cikin matuƙar tashin hankali ta ce. “Kamar ya an neme shi an rasa? Ina kuma zai tafi ranar Auren sa?” Daddy ya ce. “A yadda ya sanar mun ya ce, suna zargin sace shi aka yi, dan jiya har cikin dare yana gida cikin ƴan’uwa, amma tunda asuba mahaifin nasa ya shaida mun aka lura baya gidan, kuma ga wayoyinsa duka da komai nasa a ɗakin da ya kwana, harta silifas ɗinsa gashi nan a bakin toilet.” Mama ta ji wani abu luuu ya gilma ta ƙwaƙwalwarta, zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfin gaske, cikin sark’ewar numfashi ta ce. “Me hakan yake nufi Daddy? Dan Allah karka ce mun an sace Sadik a yau ranar Auransa da Neehal, dan Allah Daddy kace mun kunnena ne bai ji dai-dai ba.” Daddy ya riƙe ta ganin tana ƙoƙarin faɗuwa suka zauna a bakin gado. A gigice ya ce. “Calm dawn Doctor, jikina yana ba ni Insha Allahu za’a gan shi kafin time ɗin d’aurin Auren, may be wani gurin ya tafi zai dawo.” Mama ta girgiza kai cikin hawaye ta ce. “Tunda har Mahaifinsa ya kira ka ya sanar maka to da akwai babbar matsala.” Bata jira cewar Daddy ba, ta tashi cikin sauri ta ɗauki wayarta data faɗi ƙasa, ko gani bata yi sosai saboda tashin hankali ta shiga contact ta lalubo Numbern Maamah ta yi dialing. Kamar yadda ta yi zato bata ɗauki kiran ba. Ta juyo tana duban Daddy amma bata ce komai ba, Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un kawai take maimaitawa a cikin ranta. Ta dafe bango saboda jirin da take ji yana ɗibar ta. Aunty Sadiya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a tunaninta Mama ce kaɗai a ciki kamar yadda ta fita ta bar ta. Da mamaki take kallon su, ganin fuskokinsu cikin tashin hankali. Da mamaki ta ce. “Yaya Tafida lafiya?” Daddy ya sauke numfashi ya ce. “Babu lafiya Barrister, an sace Sadik.” Aunty Sadiya ta yi jimm tana kallon Daddy sannan ta ce. “Sadik dai Ango wanda za’a d’aura musu aure da Neehal yau? Na ma kasa gane wane Sadik ɗin.” Daddy yay mata bayanin abun da Abban Sadik ya sanar masa kamar yadda yay wa Mama bayani. Aunty Sadiya ta dafe kai tana ambaton Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un a fili. Kusan 5 minutes suna haka babu wanda ya kuma magana, Mama dai sai addu’a take a ranta Allah yasa mafarki take, ba gaske ba ne abun da yake faruwa yanzu. Wayar Daddy ce ta dau ƙara, suka kalle shi gaba-ɗaya cikin alamar tambaya. A sanyaye ya zaro wayar ya duba, sannan ya dube su ya ce. “Alhaji Suraj ne.” A hanzarce Mama ta ce, “D’aga mu ji ko an gan shi ne.” Daddy ya yi picked ya saka wayar a handsfree. Cikin damuwa ya ce. “Alhaji Suraj an gan shi ne?” Cikin muryar dake nuna tsantsar damuwa Abba ya ce. “Har yanzu dai babu wani labari ranka ya daɗe, duk inda muke tunanin zai iya zuwa an je baya nan, ga dukkan alamu fa sace Abubukar akai, dan ƙofar ɗakin da ya kwana a ciki a ɓalle muka tarar da ita.” Daddy ya ce, “A ɓalle kuma? Kenan ɓalla ta akai aka shiga?” Abba ya ce. “Haka muke tunani, ga darduma nan a shimfid’e alamun abu na ƙarshe da ya yi sallah ce.” Daddy ya ce. “Hasbunallahu’wani’imal’wakil, Alhaji gani nan zuwa gidan naka, wannan maganar bata waya ba ce, bari na kira a haɗa mun jami’an sojoji su zo mu san abun yi, Insha Allahu za’a gan shi.” Mama ta durk’ushe a gurin da take tsaye numfashinta na fita da ƙyar. Ta rasa tunanin me ma zata yi, ƙwaƙwalwarta gaba-ɗaya ta toshe, ta ma daina fahimtar abun da Daddy yake faɗa. Aunty Sadiya ta yi wani murmushin takaici ta ce. “An canza salo kenan? saboda a ɗauke hankalin mutane.” Cikin rashin fahimta Daddy ya ce. “Kamar Yaya?” Aunty Sadiya ta ce. “Lokaci da ikon Ubangiji na tonar asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al’amari zai bayyana.” Daddy ya ce. “Me kike nufi ne Barrister, dan Allah karki danganta ɓatan Sadik da mutuwar su Anwar.” Aunty Sadiya ta ce. “Ban danganta ba, amma ina zargin haka.” Daddy ya miƙe yana gyara hular kansa ya ce. “Bari na je na dawo sai mu yi magana, yanzu hankalina ba ya jikina.” Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin. Dan shi damuwar Daddy ɗaya kar a ce an fasa d’aurin Auren nan a yau. Aunty Sadiya ta ƙarasa inda Mama take ta riƙo ta, Mama tana duban ta, ta ce. “Sadiya an sace Sadik kamar yadda aka kashe Jameel da Anwar, kenan hakan yana nufin akwai wani da yake bibiyar rayuwar Neehal da wata mummunar manufar? Me tay masa haka da ya zaɓi cutar da ita da mu da iyayen yaran da yake kashewa? Akan me ba’a son aga ta yi Aure kamar kowacce mace?” Aunty Sadiya ta ce. “Yaya Fateemah yanzu duk ba wannan ne a gaban mu ba, addu’a kawai zamu yi Allah ya bayyana mana Sadik a duk inda yake. Kila ma abun da muke tunani ba haka ba ne, wani gurin Sadik ɗin ya je. Ko kuma idan ma sacen shi aka yi hakan ba shi da alaƙa da Neehal.” Mama ta sauke wani gwauron numfashi mai tattare da tsantsar damuwa ta ce. “Ya Allah ka bayyana mana yaron nan, ya Allah ka kare shi a duk inda yake, Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan al’amari.” Aunty Sadiya ta ce. “Ameen ya Allah.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button