NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Neehal tana kwance idonta a lumshe tana tunanin da bata san ranar daina shi ba. A hankali ya turo ƙofar dakint ya shigo, ya tsaya yana kallon ta tare da hard’e hannayensa a ƙirji. Bata ji shigowar shi ba saboda bata duniyar da yake, daddaɗan k’amshinsa da ba ya taɓa buya matuƙar yana guri shi yasa ta buɗe idonta, saboda yanda ta ji gaba-ɗaya ya mamaye mata hanci. Ta waro Idanunta waje waɗanda babu d’igon hawaye a cikin su, tunda ta kwanta take son ta yi kukan ko zata ji daɗin radadin da zuciyarta take mata amma kukan ya ƙi zuwa, sai yanzu ta gane ashe kukan ma rahama ne, ashe idan damuwa ta kai damuwa nemar shi ake a rasa? ta yunƙura tana ƙoƙarin tashi zaune cikin matuƙar dauriya. Ganin haka ya ƙarasa bakin gadon da sauri. Cikin marainiyar murya ta ce. “Yaya!” Ya rank’wafawa ya ce. “Na’am Miemerh!” Ta faɗa jikinsa da sauri tare da fashewa da kukan da take ta fatan ya zo mata tun d’azu sai yanzu ta ji sa. Ya runtse idanunsa tare da taune lip ɗinsa da ƙarfi, a hankali ya saka duka hannayensa ya zagaye bayan ta da su. Kuka take yi sosai mai taɓa zuciya gami da karyar da zuciyar mai saurarensa, wanda idan mutum mai saurin kuka ne zai iya taya ta. Numfashinta har wani sama_sama yake kamar zai ɗauke. Da sauri Ameen ya zare ta daga jikinta jin yanda take kukan kamar zata mutu, ya zauna akan gadon sosai sannan ya d’ago fuskarta yana fizgar da huci mai zafi ya shiga girgiza mata kai. Ta kwantar da kanta akan ƙafaɗarsa ta cigaba da rera da kukan ta. Ya jinjina bayansa da prame ɗin gado tare da lumshe idonsa zuciyarsa na wani irin bugawa. Bai ce mata komai ba kuma bai yi yunƙurin hana ta kukan ba, sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru ta shiga sauke ajiyar zuciya. Jin ta yi shiru ya buɗe idonsa ya zuba su akan fuskarta, wadda ta yi jajur saboda kuka. Ya ɗora hannunsa akan fuskar ya ji zafi zau kamar garwashi. Ta cire hannunsa daga kan fuskarta ta rike da nata hannun ta d’ago kanta daga jikinsa, cikin magana da ƙyar ta ce. “Yaya sun sace Sadik, Yaya me nay musu? Please Yaya ka karb’o mun shi dan Allah kar su cutar da shi, kar su kashe mun shi kamar sauran, ka ji Yaya.” Ameen ya shiga goge mata hawayen fuskarta ya ce. “I promised to you Miemerh, zan nemo miki Sadik a duk inda yake Insha Allah.” Ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tana ƙara riƙe hannunsa. “Thank you Yaya, dama na san kai kaɗai ne zaka dawo mun da shi, Yaya ka je ka karb’o mun shi yanzu_yanzu karka bari ya kwana su kashe shi, Yaya in ya mutu nima mutuwa zan yi, ka yi sauri ka ji Yayana.” Ya ƙura mata ido ganin yanda take magana kamar bata cikin hayyacinta, ga dukkan alamu tashin hankalin da take ciki ya rud’ar da ita ba kaɗan ba. Ta saki hannunsa ta mayar da kanta ta kwantar a jikinsa tare da lumshe idanunta tana sassauke ajiyar zuciya akai_akai. A lokacin Mama ta dawo ɗakin da ledar drugs a hannunta, kallo ɗaya tay musu ta ɗauke kanta. A hankali Ameen ya zare Neehal daga jikinsa ta koma ta kwanta, wadda ta yi wani irin shiru jikinta kamar na wadda ta suma duk ya shika, sai numfashinta dake fita da sauri da sauri. Mama ta ɗauki mug ɗin tea tana faɗin. “Taso ki sha Daughter kar ya yi sanyi.” Neehal ta buɗe idonta a hankali ta zubawa Mama su, Mama ta dubi Ameen ta ce. “Taimaka mata ta tashi zaune.” Ya amsa mata da kai sannan ya tayar da Neehal zaune, ya saka mata pillow a bayan ta Sannan ya miƙe. Mama ta ce. “Ka je gurin matarka kuwa? Yarinyar nan yau gaba-d’aya cikin zullumi ta wuni.” A hankali ya ce. “Yanzu zan je na gan ta, daga nan sai mu wuce gida.” Mama ta ce. “Shikenan Allah ya kiyaye hanya.” Ya amsa da Amin sannan ya fice daga ɗakin. Mama ta zauna a bakin gadon tare da miƙawa Neehal mug ɗin hannunta ta ce. “Take it.” Neehal ta girgiza mata kai, Mama ta ce. “Ki yi haquri ki daure ki sha ko kaɗan ne, baki da lafiya Neehal ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba.” Ta buɗe baki da ƙyar ta ce. “Bakina ɗaci Mama, ba zan iya sha ba, ko na sha ma amai zan yi.” Da ƙyar Mama ta lallaɓa ta, ta sha tea ɗin kaɗan, sai dai kamar yadda ta faɗa kurb’a uku kawai ta yi ta dawo da shi. Dole Mama ta haqura ta ƙyale ta, magungunan ma fasa bata ta yi, dan ta san su ma in tasha amansu zata yi. Tana son tay mata allura amma saboda cikin ta babu abinci yasa batai mata ba dan kar ta galabaitar da ita. Sai ruwa ta ɗebo ta goga mata a jikinta da towel saboda zafin da jikin nata ya yi, ta kuma kama mata kanta ganin yanda take ta dafe kan da hannunta. Goma saura Hafsat ta zo ta yiwa Mama Sallama, wai za su wuce gida ita da Ameen. Mama tay musu addu’ar Allah ya kiyaye hanya. Neehal dai tana kwance idanunta a lumshe amma ba barci take ba, tunanin Sadik da rashin sanin halin da yake ciki a yanzu kawai take. Ko yana raye ko a mace sai Allah. Tana ji su Aunty A’isha da Aunty Sadiya da Hajiya suka shigo ɗakin suna tambayar jikinta tare da yi mata sannu, amma ko ido ta kasa buɗewa ta kalle su.
Sha ɗaya saura Daddy ya shigo ɗakin, Mama tana zaune ita kaɗai akan darduma tana jan carbi. Ya zauna a bakin gado yana duban Neehal ya ce. “Bacci take ne?” Mama ta ce. “Ehh.” Daddy ya girgiza kansa ya ce. “Allah ya kawo miki ƙarshen wannan abun Daughter.” Mama ta ce. “Amin, bari na kawo maka wani abun ka ɗan saka a cikinka, na san yau babu abun da ka ci.” Ya ce. “Doctor bar abun cin nan, babu abun da zai iya shiga cikina a yanzu.” Mama ta ce. “Daurewa zaka yi ka ci ko kaɗan ne, yau ɗaya amma ba ka ga yadda ka faɗa ba.” Daddy ya ce. “Ina cikin tsananin tashin hankali ne Doctor.” Mama ta ce. “Addu’a ce mafita Gen.” Daddy ya ce. “Haka ne ita muke ta yi, yanzu ma masallaci zan tafi, na saka a kwana yau ana karatun Alkur’ani, to na san ko na zauna a gida ba bacci zan yi ba, shi yasa na ce gwara na je kawai a yi karatun tare da ni, ko na ji daɗi a raina.” Mama ta ce. “Shikenan, Allah ya amsa mana addu’oin mu, ya bayyana mana wannan yaro.” Daddy ya ce. “Amin Amin.” Sannan ya shafa kan Neehal yay wa Mama Sallama ya tafi masallaci. Daren yau mutane da yawa ba su rintsa ba, Mama kwana ta yi tana Sallah tana kaiwa Allah kukan ta, haka ma Maamah mahaifiyar Sadik da Abbansa, Aunty Sadiya ma kwana ta yi tana bincike a system ɗinta da wayarta. Neehal kuwa wannan daren da tunanika ta raya shi. Ta fara tunanin farkon haɗuwar ta da Jameel har zuwa lokacin da ya rasu ya bar ta da tarin k’aunarsa a ranta, ta tuno Anwar shi ma da irin soyayyar da suka sha kamar babu gobe, ta tuno Ahmad da tarin k’aunar da ya nuna mata, ƙarshe kuma suka rabu. Sai Sadik wanda ta saka a ranta shine mutum na ƙarshe wanda zata yi soyayya da shi a rayuwarta, ta sakankance shi zai zamto abokin rayuwarta na har abada. Amma shi ma sai da BAK’AR ƘADDARA ta raba su a ranar d’aurin Auren su. Ta gane bata da sa’a a soyayya kamar yadda ta fitar da rai da yin aure a rayuwarta. Ta haqura da soyayya balle har ta yi tunanin yin aure, tunda aka sace Sadik a ranar Aurensu to babu makawa ko da ta yi aure mijin data aura ma ba zai tsira ba, za’a iya biyo shi har cikin gidansu a kashe shi. Ita kuma abun da zuciyarta baza ta kuma ɗauka ba kenan, ta san idan hakan ta faru bugawa zuciyarta_ta zata yi ta mutu. Ta gaji da sai ta shak’u da mutum sannan a raba su, rabuwa ta har abada. She accepted her destiny, zata k’are rayuwarta a haka babu aure, wannan ita ce ƙaddarar ta. Tana fata da kuma addu’ar Allah ya bayyana Sadik cikin k’oshin lafiya, amma ba dan ya dawo su yi aure ba, sai dan farincikin ahalinsa. Sai wajen asuba bacci mai kama da suma ya ɗauke ta, a cikin barcin mafarkai ta dinga yi barkatai, wani wai gashi an ga Sadik cikin mawuyacin hali, wani kuma gawarsa aka gani an kashe sa, wani kuma ya dawo cikin k’oshin lafiya har an yi auransu suna rayuwarsu cikin farinciki. Duk mafarkan nata dai akan Sadik ne da kuma halin tashin hankalin da ake ciki game da ɓatan sa. Da asuba da Mama ta tashe ta da ƙyar ta iya tashi ta yi Sallah a zaune. Kafin safe jikinta ya rikice sosai da zazzafan zazzaɓi, jikinta har rawa yake ga matsanancin ciwon kai. Hankali a tashe Mama da Aunty A’isha suka ɗauke ta suka nufi asibiti da ita. Suna zuwa aka ba su gado, wanda zuwa lokacin Neehal ta galabaita matuƙa. A asibitin suka wuni, yayin da ƴan dubiya da suka samu labarin ciwon nata suke zuwa ko ta ina duba ta. Ahmad da su Ummi ma sun zo sun duba ta, Ahmad ya tsaya a bakin gadon marasa lafiyar da take kwance yana kallon ta cikin tsananin tausayin ta. Ya shafi gefen kuncinta ya ce. “Allah ya baki lafiya Princess.” Kamar kar ya tafi ya zauna yay jinyar ta haka yake ji. Sai can yamma Ameen da Hafsat suka zo asibitin amma har dare ba su tafi ba. Da daddaren Mama ta matsa aka sallame su daga asibitin, ta ce zata cigaba da kula da ita a gida. Neehal dai bata um bata Um’um, sai dai tay ta kallon mutane. Hajiya ta ce, al’amarin nan nata fa sai an haɗa mata da rubutun dangana ta sha. Haka kuwa aka yi Daddy yasa akai mata rubutun ya zamto ruwan shan ta. Kwana uku da ɓatan Sadik amma shiru babu wani labari har yanzu, addu’a kam an dage yinta ake, a gefe guda kuma jami’an tsaro suna ta aikin nasu binciken. Zuwan su biyu gidan Mama domin yiwa Neehal tambayoyi a matsayin ta na wadda suka yi wayar ƙarshe da Sadik kafin a sace shi, amma halin da take ciki yasa ba su samun damar yin magana da Ita ba. Baƙin da suka yi saura a gidan tuni kowa ya koma gidan sa, su Aunty ma sun koma gidajensu amma kullum sai sun zo, dan ita kanta Maman tausayi take ba su, dan za’a bata gado tsaf Ita ma zata kwanta, dauriya da ƙarfin hali kawai take. Hajiya ce kaɗai bata tafi ba. Mommyn Hameedah ma ta gama yada habaibaice_habaicen ta tasa tuzuruwar ƴarta a gaba sun tafi. Uncle Usman da iyalansa ma basu koma Nijar ba, suna gidan Uncle Umar, a part ɗin Aunty Fauziyya suke zaune tunda bata gidan. Neehal ta fara magana kaɗan_kaɗan, idan aka yi mata magana yanzu tana amsawa da um ko um’um. Doguwar maganarta kuwa sai idan Ameen ya zo gidan, ta dinga ce masa. “Yaya ka karb’o mun Sadik ɗin? dan Allah Yaya ka karb’o shi kar su cutar da shi.” Shi kuma sai ya lallaɓa ta tare da tabbatar mata da Insha Allahu Sadik zai dawo cikin k’oshin lafiya. Sai karatun Alkur’ani da kullum suke yi tare da Mama safe da dare, shine yake ɗan sanyaya mata zuciya yasa ta ji damuwarta na raguwa. Haneefah ma idan ta zo gidan tana iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta rage mata damuwar dake ranta, ta hanyar yi mata hira da nasihar yadda da ƙaddara cikin sigar rarrashi.



