NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ranar juma’a wanda ya kama sati guda cif da ɓatan Sadik, da yamma Maamah suna zaune a main Parlour’n gidan ita da ƴan’uwanta da ba su koma gida ba har yau, sai Hajiya kakarsu Sadik. Suna zaune jigum_jigum kamar gidan zaman makoki, ko da yake su da mutuwa ma Sadik ɗin ya yi sai hankalinsu ya fi kwanciya tunda sun san ba ya raye, akan wannan zullumun da fargabar rashin sanin halin da yake ciki da suke. Mai gadin gidan ne ya faɗo Parlour’n yana ta zuba haki babu ko sallama. Hajiyarsu Sadik ta ce. “Lafiya kuwa malam Ayuba ka faɗo mana cikin gida a ruɗe babu sallama?” Sai a lokacin Maamah dake jan carbi ta d’ago kanta tana jin zuciyarta na wani irin bugu. Waje malam Ayuba yake nuna musu da hannunsa amma ya kasa magana sai rawar baki yake alamun yana so ya ce wani abu maganar ce ta ƙi fitowa. Hajiya ta buɗe baki zata kuma magana amma shigowar Sadik Parlour’n a matuƙar sanyaye ya hana ta faɗar abun da tay niyya……..✍️

Na so page ɗin ya fi haka tsayi, amma rashin caji ya hana yiyuwar hakan, and ban yi edit ba a yi haquri da typing errors.

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

6️⃣2️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

……….Kafin Yamma Labarin sace Sadik ya baza ko ina a cikin jihar nan da ma mak’wabtan ta. Sakamakon hotunansa dake ta yawo a social media tare da note ɗin ɓatan da ya yi. Abun da yake ƙarawa labarin nasa armashin yaɗuwa sace shin da akai a ranar D’aurin Auren sa, and kuma amaryar tasa wadda yake shirin angoncewa da ita fitacciyar ƴar jarida ce wadda duniya ta san ta. Su Daddy sun so a ɗaura Auran a yau ko dan jama’ar da aka tara amma dangin Sadik suka ƙi amincewa, haka suka dawo gida jiki a sanyaye. Kawu Musa ya ce, suna da gaskiya, kuma ko waɗanne iyaye ne ɗansu ya ɓata abun da zasu yi kenan, suna cikin zullumi da damuwar ɗansu baza su bi takan wani d’aurin Aure ba. Uncle Usman ya bayar da shawarar a ɗaurawa Neehal Aure da wani saurayin idan tana shi kowa ya huta da wannan fargabar. Amma Daddy ya ce baza a yi haka ba, domin Dangin Sadik zasu ga kamar ba su damu da ɓatan Sadik ba, tunda har suka iya ɗaurawa Neehal Aure a yau, idan suka yi haka ba su yi musu kara ba. Gidan bikin Mama ma ya koma kamar na zaman makoki like gidansu Sadik, Haneefah ta ci kuka ta k’oshi, haka ma Aunty A’isha da Hajiya. Aunty Sadiya mai ɗan dauriya a cikin su, Mama kuwa ko magana bata iya yi, tana zaune kawai ta tafka tagumi. Neehal kam tun bayan data suma aka dinga shafa mata ruwa a fuska da ƙyar ta farfaɗo tana ambaton sunan Sadik tare da roqon kar ya tafi ya bar ta. Ganin bata cikin hayyacinta kuma a firgice take yasa wata abokiyar aikin Mama tay mata allurar bacci, aka ɗauke ta aka kaita ɗakin Daddy aka kwantar.

Bayan Sallar la’asar gaba-ɗaya ƴan’uwa na jiki suka hallara a main Parlour’n Daddy dan tattaunawa akan al’amarin, tunda zuwa yanzu sun fuskanci saboda Neehal aka sace Sadik. Daddy, Kawu Musa, Uncle Usman, Uncle Umar, Uncle Mahmud, Uncle Ahmad (Mijin Aunty Sadiya) Abba, (Yayan Daddy) Mama, Hajiya, Aunty Sadiya, Aunty A’isha da Umma. Kawu Musa ya yi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka. “Zamu fara da Addu’ar Ubangiji Allah ya bayyana mana wannan yaro a duk inda yake, ya kuma kare shi yasa yana hannu na gari, idan kuma kamar yadda ake tunanin sace shi aka yi, to Ubangiji Allah ya toni asirin waɗanda suka sace shin cikin gaggawa.” Gaba-ɗaya suka amsa da “Amin ya Allah.” Daddy da hannunsa ke dafe da kansa ya d’ago yana girgiza kai ya ce. “Amma fa wannan abun akwai rikitarwa da tayar da hankali ba kaɗan ba.” Mama ta sauke numfashi tare da janye tagumin data rafka, cikin sanyin murya mai nuni da tsantsar damuwar da take ciki ta ce. “Tabbas a yau na yarda da maganar Sadiya 100%, ko shakka babu wanda ya kashe Jameel shi ya kashe Anwar, haka nan kuma shi yasa aka sace Sadik yanzu ma, kuma duk saboda Neehal.” Daddy ya ce, “Ni kuma bana tunanin hakan gaskiya.” Cikin takaici Uncle Usman ya ce. “To idan ma hakan ne waye yake aikata hakan? kuma akan me? Me yarinyar nan tay masa?” Cikin dashashshiyar muryar da ta ci kuka ta k’oshi Aunty A’isha ta ce. “Na fi tunanin koma waye son ta yake, shi yasa baya son kowa ya aure ta.” Aunty Sadiya ta ce. “So?” Sai kuma ta yi ɗan murmushi ta ce. “Hmm, duk wanda yake aikatawa Neehal wannan abun ba son ta yake ba, wata mummunar manufar ce da shi a gare ta.” Uncle Mahmud ya ce. “Me yasa zaki ce haka Haleemah? Nima zuciyata ta fi yarda da abun da A’isha ta faɗa na wani ne yake son Neehal ɗin, shi yasa yake kashe duk wanda zata aura, yanzu kuma sai ya sace Sadik ya canza salo.” Aunty Sadiya ta miƙe ta yi taku hannayenta cikin juna tana zira yatsunta a tare tana zarewa, sannan ta ce. “Idan har dagaske son ta yake son Allah ba ƙoƙarin cutar da ita ba me yasa ba zai bayyana kansa a gare ta ba? Me yasa ya san idan har ya bayyana kansa a matsayin wanda yake kashe mata duk wanda zata aura saboda yana son ta ya san baza ta taɓa amincewa da auren shi ba, amma kuma yake aikata hakan?  Ya kamata Ku yi tunani da kyau akan wannan idan har son ta yake da gaske ba zai taɓa aikata mata haka ba, kamar yadda na faɗa wata mummunar manufar ce da shi a gare ta, ko kuma akwai wani abun da yake son gudanarwa da ita, amma kuma Allah bai ba shi sa’a ba har yau, kuma ga dukkan alamu mummunan kudirin sa a kan ta da zarar ta yi aure ba zai samu ba, shi yasa yake aikata hakan.” Gaba-ɗaya suka yi shiru suna kallon ta kowa yana auna maganganun ta a mizanin hankali. Ta koma ta zauna sannan ta dubi wani sashi na Falon ta ce. “A binciken da nake gudanarwa fiye da shekara akan al’amuran Neehal akwai wanda nake zargi, kuma a Ƴan kwanakin nan wasu alamomi suka ƙara ƙarfafa mun zargin nawa a kansa.” A hanzarce Daddy ya ce, “Wa kike zargi Barrister? Ki yi gaggawar sanar mana in saka a damk’o sa a bincike sa.” Uncle Umar ya ce, “Wannan haka ne, kuma shine abun yi, domin kuwa wannan abun ya yi yawa, mun gaji, muna san sanin gaskiyar al’amarin.” Suka gyaɗa kai gaba-d’ayan su alamun haka ne. Aunty Sadiya ta ce. “Zargi nake ban tabbatar ba, shi yasa ba zan sanar muku a yanzu ba, na fi son sai na samu cikakken evidence k’wakwk’wara.” Uncle Mahmud ya tari numfashinta da faɗin, “Amma ai a tsarin doka ma ana gudanar da wanda ake zargi a gaban shari’a, ko da ba’a tabbatar ya aikata lefi ba, ke me yasa baza ki faɗa ba?” Hajiya da bata yi magana ba tun d’azu sai yanzu ta ce. “Gaskiya ne, ya kamata ki faɗi wanda kike zargin, in ma ba shi ba ne wataƙila sanadiyyar hakan sai ki ga an gano gaskiya.” Umma ta ce. “Haka ne, Sadiya ya kamata ki faɗa mana wanda kike zargi domin a san abun yi a kansa.” Aunty Sadiya ta numfasa ta ce. “Ku yi haquri, na san zuciyoyinku a zak’e suke da sanin ko waye, amma ku sani wannan case ɗin na Neehal ya sha banban da case ɗin laifukan da muka saba ji da gani, idan har ban yi takatsantsan ba to zan iya kwana a ciki.” Abba ya ce. “Kamar ya? Ba bincike ba ne? Ai idan aka gane mutum ba shi da hannu a ciki sakin sa za’a yi.” Aunty Sadiya ta ce. “Ku dai yi haquri, Insha Allahu nan ba da jimawa komai zai bayyana, mu dai kawai mu dage da addu’a.” Kawu Musa ya ce. “To Allah yasa mu dace, amma ba kwa tunanin ko akwai wani da suka samun saɓani da yarinyar nan ya k’ullace ta yake aikata mata wannan abun?” Mama ta ce. “Bana tunanin haka gaskiya, dan Neehal bata da abokin faɗa a rayuwarta, na san wani lokacin bata da haquri idan aka ɓata mata rai, amma bana jin zata yiwa wani babban abun da zai sa ya dinga bin ta da wannan mummunan abun a matsayin ɗaukar fansa ko hukunci.” Kawu Musa ya ce. “To idan ba haka ba kuwa zata iya yiyuwa ko shi Gen. da ya kasance babban mutum mai tare da ƴan adawa a ƙasar nan saboda shi ake aikata wannan abun, domin a ɓata masa suna ko kuma dan wata manufar daban.” Suka yi shiru cikin alamun nazari. Daddy yana jinjina kai ya ce. “Kuma fa Alhaji Musa zancen ka akwai k’amshin gaskiya, dole ne in tsaurara bincike akan wannan al’amarin, domin kuwa na san zuwa yanzu sunana dana iyalina ya fara ɓaci a idon duniya.” Uncle Mahmud ya ce. “Wannan shawarar ta yi, kuma ita ma Neehal ɗin ya kamata a tuntube ta akan maganar da Alhaji Musa ya yi ta farko, akan ko sun taɓa samun matsala da wani, like criminal person haka, ko kuma wani da suka samu saɓani ya taɓa yin wani mummunan ƙudiri a kanta a matsayin ɗaukar fansa.” Abba ya jinjina kai ya ce. “Ya kamata kam, domin komai zai iya faruwa, tunda mu har yanzu lalube muke a cikin duhu, muna neman gaskiyar al’amari.” Umma ta ce. “Har wannan ƙawarta_ta itama a tuntube ta ko san wani abu akai, tunda kodayaushe suna tare.” Aunty A’isha ta ce. “Wai Haneefah kike nufi?” Umma ta ce. “Ehh.” Aunty A’isha ta ce. “Insha Allahu duk zamu yi ƙoƙarin yin hakan, Allah Ubangiji dai ya toni asirin masu aikata wannan abun da gaggawa, ko zuciyoyinmu zasu samu salama.” Suka amsa da Amin, kuma kowa ya yi na’am da wannan shawarwarin da aka bayar. Aunty Sadiya dai kawai kallon su take bata ce komai ba, cikin ranta tana tunanin wani abu daban. Uncle Usman ya ce, “Ni Neehal ɗin ma nake tausayawa, yarinya duk za’a sa ta tsani kanta da rayuwarta, dan babu wanda zai so a ce ana rasa rai ta dalilin sa, ko kuma an cutar da wani.” Kawu Musa ya ce. “Wallahi fa, tunda k’uruciyarta za’a ɗora mata tension ɗin da ya fi ƙarfin kanta.” Umma ta ce. “Ƙaddara ce, wadda ta riga fata, babu yanda zamu yi, sai dai mu yi addu’ar Allah ya tsayar haka, kuma da izinin Allah komai zai zo ƙarshe, zai kuma zama tarihi kamar ba’ai ba.” “Haka muke fata.” Cewar Uncle Umar. Hajiya ta ce. “Tana kwance har yanzu ko?” Aunty A’isha ta ce. “Eh, tunda akai mata allurar bacci bata farka ba har yanzu.” Mama ta ce. “Bari mu gama sai in je in tashe ta, na ga yamma ta yi sosai Magriba ta gabato, gwara ta tashi ta yi sallolin dake kanta.”  Hajiya ta ce. “Ni fa da wannan abun ya faru na yi zargin ko dai aljanu ne da yarinyar nan.” Kawu Musa ya ce. “Zata iya yiyuwa su ɗin ne ma, amma kuma shi sha’anin jinnu ba haka yake ba akan al’amarin Aure, yawanci tun kafin maganar aure ta yi nisa suke tarwatsa abun, ko kuma ki ga yarinya ta girma sosai babu mashinshini, amma indai ba turo su akai ba zai yi wahala su yi kisa, in ma zasu yi kisan ba ta hanyar harbi ba, sai dai kawai a wayi gari a ga mutum ya rasu.” Umma ta ce. “Tabbas haka ne, dan na taɓa ganin yarinyar da irin wannan ya faru da ita, ita auranta aljanin ya yi, da farkon ƴan’matancinta tana samari, daga baya kuma sai suka daina zuwa dif, sai daga baya aka gane aljanin ne ya aure ta.” Aunty A’isha ta ce. “Subhallahi, Allah ya kiyaye mu da zuri’armu baki ɗaya. Suka amsa da Amin. Uncle Mahmud ya ce. “Hakan ma zata e yiyuwa, kin san su ma aljanun babu abun da ba za su iya ba, sai a gwada yi mata magani a ga ko Allah zai sa a dace.” Kawu Musa ya ce. “Allah yasa mu dace, yasa mu fi ƙarfin zuk’atanmu, ya kare mu daga abun da yafi ƙarfin mu, ya raba mu da mummunar ƙaddara.” Suka ƙara Amsawa da Amin. Abba ya nisa ya ce. “Ni fa ina da wata shawara, a gani na tunda duk wannan abun da ake yi mun fahimci saboda kar yarinyar ta yi aure ne, auren ne ba’a son ta yi, me zai hana a ɗaura mata Auren kawai ta tare a gidan mijinta ba tare da duniya ta sani ba, kun ga kenan daga lokacin da tai auran koma waye yake bibiyarta da mugun nufinsa ta yi auranta, magana ta ƙare.” Uncle Usman ya ce. ,”Tunanin dana yi d’azu kenan nima, na ce a ɗaura mata auran a yau, amma Daddy’n ta ya hana.” Dad ya ce. “Ba wai na ƙi ba ne, abubuwa guda biyu na duba, na farko iyayen yaron Sadik  nan baza su ji daɗi ba idan muka ɗaurawa Neehal Aure a yau, zasu yi tunanin ba ma mu damu da ɓatan ɗansu ba ta auran ƴarmu kawai muke, alhalin kuma duk mun fuskanci ko na ce muna tunanin saboda da ita aka sace shi, duk da ba ma fatan hakan. Na biyu kuma ita kanta yarinyar bazai yiyu tana cikin halin baƙin ciki da tashin hankalin ɓatan Sadik sannan mu ƙara mata da wata damuwar mu daura mata aure da wanin sa ba da sanin ta ba, may be wanda zamu aura matan bata son shi, kun ga mun jefa ta a cikin wata damuwar bata gama fita daga wata ba.” Suka  jinjina kai gaba-d’aya cikin gamsuwa da bayanan Daddy. Mama ta ce, “Maganar ka gaskiya ce Gen. Amma in dan wanda Neehal zata aura ne ba mu da matsala da wannan, dan ta son yaron nan Ahmad Baban twins, shima kuma yana son ta, gashi yaron kirki ne ba shi da matsalar komai haka ma iyayensa, amma kamar yadda ka faɗa koda za’ai mata auran ba yanzu ba, mu ɗan jira zuwa wani lokaci kafin nan Insha Allahu mun warware daga cikin wannan matsalar, dan yanzu babban burin mu Allah ya bayyana mana Sadik cikin k’oshin lafiya.” Haka dai suka ci-gaba da tattaunawa, shi Daddy yana ganin gwara a jira bayyanar Sadik idan ma Auren za’ai wa Neehal a aura mata shi. Uncle Mahmud ya ce, kamar hakan da wuya, tunda a rabuwar da suka yi ɗazu da danginsa sun nuna ko Allah ya bayyana shi ba zai auri Neehal ba, kuma ba ya jin yanda suka ɗauki zafi akan al’amarin zasu amince ta cikin ruwan sanyi. Suna cikin tattaunawar ne Aunty Sadiya ta ce. “Wai ina Ameen ne? Yau gaba-d’aya duk wannan abun da ake ban gan shi ba.” A ɗan firgice Daddy ya ce. “Bai zo gidan nan ko da safe ba? Ni sai ma yanzu da kikai magana na yi released ban gan shi ba yau kwata_kwata ko a gurin d’aurin Auren.” Cikin damuwa Mama ta ce. “Nima rabo na da shi tun jiya da rana, to ina yaron nan ya shiga?” Hajiya ta ce. “Matar shi ma haka ta ce, kuma tun safe take kiran wayarsa a kashe.” Kawu Musa ya ce. “Subhallahi, Allah dai yasa lafiya yake.” Uncle Ahmad ya ce. “Insha Allahu yana lafiya k’alau, kun san halin Ameen, may be ya samu wannan labarin ne shi yasa bai zo ba saboda tashin hankali.” Daddy ya ce. “To kuma sai ya kashe wayoyinsa, Ameen da koyaushe wayoyinsa a kunne suke.” Mama da gabanta ke faɗuwa ta ce. “Bari na dauko wayata na kira shi mu ji ko zata shiga yanzu.” Uncle Mahmud ya ce. “Bari na kira shi ba sai kin tashi ba.” Ya ƙarashe zancen tare da zaro wayarsa daga aljihun gaban rigarsa. Yana kira ta shiga, sai dai har ta katse bai ɗauka ba. Mama ta ce, “To ina Yaron nan ya shiga ya bar wayar tasa kuma?” Daddy da yanayinsa ya nuna rud’ewa ya ce. “To shi kuma me ya faru da shi?” Umma ta ce. “Babu komai Insha Allahu, tunda wayar ta shiga zai biyo bayan kiran ko anjima ne, wataƙila ba ya kusa da wayar ne, ku kwantar da hankulanku, kar ƙarawa kanku wata damuwar, mu yi masa addu’a kawai.” Sukay shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button