NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A ɓangaren su Abban Sadik su ma bayan dawowar su daga masallaci suka zauna zaman cigaba da tattaunawa akan al’amarin. Suma kamar su Daddy sun amince dalilin Neehal aka sace Sadik, har wasu k’annen Abba na cewa k’ila ma da haɗin bakinta, tunda ita ce last wanda ya yi waya da ita cikin dare. Abba ya ce, ya yarda ta sanadin Neehal aka sace Sadik, shi ma hakan zargi yake ba wai ya tabbatar ba ne, amma sam ba zai taɓa yarda da saka hannunta ko haɗin bakinta a sace shin ba, dan ya san baza ta taɓa cutar da Sadik ba. Kuma batun waya da suka yi, ai idan aka duba Sadik ɗin ne ya kira ta ba ita ta kira shi ba, bare ace akwai abin da ta shirya a wayar suka yi. Abby ya ce duk wannan maganganun ba su ne mafita ba, mafita kawai a dage da addu’ar Allah ya bayyana Sadik. Maamah ta farfaɗo, amma ko magana bata iya yi, ƴan’uwan ta na kanta suna yi mata firfita. Ƴan’biki kuwa duk an watse cikin alhakin abun, sai ƴan’uwa na jiki ne da baƙin nesa sukay saura, al’amarin dai babu daɗin ji ko kaɗan, abun tausayi da rud’ani.

A ɓangaren Ahmad al’amarin ya rud’a shi fiye da tunanin mai karatu, musamman da Zahra ta sanar masa abun da ta ji ana faɗa a gidansu Neehal lokacin da suka riski labarin ɓatan Sadik, cewar samarinta biyu na baya ma kashe su aka yi. Abun ya matuƙar ɗaure masa kai da jefa shi cikin tunani, Neehal ta sanar masa samarinta biyu sun rasu, amma bata ce masa kashe su akay ba. Idan kuwa har haka ne ya tabbatar da akwai wata b’oyayyiya kenan a rayuwar Neehal ko kuma ya ce wata babbar matsala. A gefe guda kuma tausayinta mai tsanani ne ya cika masa zuciya, a ransa ya dinga faɗin wannan wanne irin zalunci ne ake mata haka? Wunin yau gaba-d’aya cikin tunanin al’amarin ya yi shi, ya kulle kansa a ɗakin da yake sauka a gidan Mamy, Sallah ce kawai take fito da shi. Hankalinsa in ya yi dubu yau a tashe yake, ba ya son wani mummunan abun ya samu Princess ɗin sa, yanda yake jin zuciyarsa ba abun da yake buƙata sama da ya je ya ga halin da take ciki, dan ya san tana can tana kukan nan nata, ya san hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, abun da yake ƙara d’aga masa hankali da Zahra ta ce har suma ta yi. Twins ma waɗanda su Ummi suka taho da su gidan Mamy sai kuka suke suna kiran Aunty, da ƙyar Ummi ta lallame su suka ci abinci. Ummi saukar su kenan ita da Abban su Ahmad suka tarar da wannan mummunan labarin, hakan yasa ba su wani jima ba a gidan Mama suka yo gidan Mamy tare da Mamin da ta je bikin ita ma, tunda maganar biki kuma ta tashi tunda babu Ango. Zuciyoyinsu babu daɗi ko kaɗan, wuni suka yi suma suna jimanta wannan al’amarin mai rikitarwa. Neehal da ahalinta sun ba su tausayi sosai, more especially ma Neehal da ƙarshe komai a kanta zai ƙare.

Mama tana zaune a bakin gadon Daddy, ta saka Neehal dake kwance a gaba tana kallon ta cikin tsananin tausayawa bayan ta idar da Sallah. Tunanin rayuwar Neehal kawai take da irin jarrabawoyin da take gamuwa da su a rayuwarta, tun tana ƙarama aka kashe mata iyayenta, ta tashi a wahalce a hannun iyayen riƙon ta, bayan ta dawo hannunta da zama kuma danginta suka nuna suna ƙin ta ƙuru_ƙuru ba k’aunarta suke ba, ta san wannan abun ma yana damun ta, boyewa kawai take tana barin abun a cikin ranta. Bayan ta isa aure kuma ta fara fuskantar wannan challenges ɗin, abun ya yi mata yawa a ƙananun shekarunta. Daga nan Mama ta fara tunanin abun da suka tattauna d’azu, and she noticed one thing a zaman d’azu da akai game da Aunty Sadiya, tana magana ne kamar mai habaici a gurin, tana kuma yin wani irin kallo kamar na gargadi’ ko kuma na tuhuma. Gashi ta ƙi faɗar wannan ta ce tana zargin, Mama ta kasa gane me Aunty Sadiyan take nufi da kuma inda ta dosa, amma ta k’udurce a ranta zata tambaye ta idan sun keɓe. Sai kuma ta juyar da akalar tunanin nata kan Ameen bugun zuciyarta na ƙaruwa, tana tambayar kanta ina ya shiga? Me yake yi har yanzu bai zo gidan ba? Kuma ana ta kiran shi ba ya pick. Bayan shigowar ta ɗakin ta masa kira ya kai sau biyar amma bai ɗauka ba.

A hankali Neehal ta buɗe idonta da yay mata nauyi ta sauke su akan fuskar Mama. Cikin muryar marasa lafiya dake fita da ƙyar ta ce. “Mama!” Mama ta sauke wahalallen numfashi muryar Neehal ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi. A hanzarce ta ce. “Na’am, Daughter kin tashi? sannu kin ji.” Ta ƙarashe zancen da kama hannayen Neehal duka a cikin nata. Neehal ta gyaɗa mata kanta wanda take jin sa kamar dutsen dala saboda nauyin da yay mata, ta fara hawaye ta ce. “Mama da gaske ne ba mafarki na yi ba Sadik ya ɓata an sace shi?” Mama ta mayar da k’wallar data tarar mata a ido dan kar ta ƙara karyar wa Neehal zuciya ta ce. “Eh Daughter, amma za’a gan shi Insha Allah, ana nan anata neman sa da cikiyar sa tare da addu’a.” Neehal ta fashe da kuka mai karyar da zuciya ta ce. “Me nay musu Mama? Su waye suka ɗauke mun Sadik? Me yasa basa san na yi aure kamar kowa? Ya Allah in wani laifin nay maka ka yafe mun w…..” Mama tay saurin rufe mata baki tana faɗin. “Ya isa haka Neehal, ki bar wannan maganganun kar ki je ki yi sab’o, gashi baki da lafiya. Ki yi haquri komai kika gani ya samu bawa rubutacce ne a rayuwarsa tun fil azal daga Ubangijin sa, wannan abun ƙaddarar ki ce da mu baki ɗaya, amma baza mu gaji da kaiwa Allah kukan mu ba, da shi kaɗai muka dogara kuma shi zai yaye mana, jarrabawa ce Neehal, kowanne Mumini akwai irin tasa, ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu za’a ga Sadik.” Ta lumshe ido hawaye masu d’umi na zubo mata, bata taɓa jin ta tsani rayuwarta irin yau ba, ta gaji da cutar da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da ake yi saboda ita. “Ya Allah kar ka ba su ikon cutar mun da Sadik, My Sadik where you? Ka dawo gare ni karka tafi ka barni kamar yadda su Anwar suka tafi suka bar ni Please, i’m in needing you in my life, please my Sadik come back to your wife.” Abun da take faɗa a ranta kenan cikin ɗacin zuciya, kamar ta cire zuciyarta ta yar haka take ji saboda zafin da take mata. Har yanzu bata bar fatan ace zata farka daga wannan mummunan mafarkin da take ba, zuciyarta ta kasa yarda cewar da gaske ne abun da yake faruwa. Mama ta d’ago ta tana faɗin. “Tashi mu je ki  yi wanka ko zaki ji daɗin jikinki, ki kuma rama sallolin dake kanki, sai ki sha ko tea ne ki sha magani, na ji jikin naki da zafi zau alamun zazzaɓi.”  Bata musa wa Mama ta ɗaure ta sakko dak’yar tana cize lip ɗinta hannunta dafe da kanta, Mama ta taimaka mata ta kai ta toilet ta yi wanka tare da brush ta ɗauro alwala sannan suka fito, kayan data cire ta mayar ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah, a zaune ta yi sallolin da ake bin ta duka ta haɗa isha’i da ake yi yanzu, ta daɗe tana addu’a cikin kuka a sujjadarta ta ƙarshe akan Allah ya bayyana Sadik, ya kuma kawo mata ƙarshen wannan al’amarin. Bayan ta idar ta lallaɓa ta koma kan gado ta kwanta, Mama bata ɗakin ta fita hado mata tea, wanda tana da yaƙinin a halin k’uncin da take ciki a yanzu ba zai iya shiga bakinta ba balle har ya wuce ta mak’oshinta ya tafi cikinta. Bata san musawa Maman ne kawai, amma ita a yanda take jin zuciyarta da Allah zai ɗauki ranta a yanzu da ta yi murna da hakan fiye da wannan rayuwar da take ciki. Mama ta dawo ɗakin ta ajiye mug ɗin hannunta ba tare da yi magana ba, sannan ta juya ta kuma fita dan ɗauko mata magani, sauri take saboda tana son ta yi ta kawo mata maganin sannan ta je gurin baƙin da suke rage a gidan, dan fiye da rabin mutanen d’azu duk sun koma gidajensu tunda maganar biki ta tashi. Ta buɗe ƙofar falon kenan da nufin fita suka yi karo da Ameen dake ƙoƙarin shigowa………..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button