NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Haka na wuni ni kaɗai a ɗakin cikin tunanin mafita, Sallah ce kawai take tayar da ni idan na ga lokacin ta ya yi. Har bayan Magriba ko ruwa ban kurb’a na saka wa cikina ba, yunwar ma da ƙishirwar ko jin su bana yi, ko ma ina ji bata su nake ba. Kafin isha’i mutumin ya ƙara dawowa ya kawo mun wani abincin da ruwan. Na tashi da sauri cikin ƙarfin hali dana zuciya na cakumi mutumin ina tambayar sa dalilin yasa suka kawo ni nan? Me nay musu? Kamar wani kara haka mutumin ya yakice ni daga jikinsa ya dank’wafar da ni a ƙasa ya juya ya fice. Na rarrafa a ƙoƙarina na ganin na riƙe ƙofar kafin ya rufe, amma tuni ya ja ta sai motsin saka mukulli a jikinta na ji. Na kwanta akan carpet ɗin dake malale a ɗakin cikin tsananin damuwa. Sai da takwas ta wuce sannan na miƙe ina layi na shiga toilet na ɗauro alwala na yi Sallar isha’i, na ƙara da nafila a cikin kowacce sujjada ta ina roƙon Allah ya fitar da ni daga cikin wannan riskin da nake ciki. Ina kan sallaya mutumin ya sake shigowa, na zuba masa ido in ga mai kuma ya shigo yi, da yake ɗakin akwai hasken wani farin k’wan wuta guda ɗaya dake sak’ale a bango. Ga mamakina sai na ga ya kama ni ya kai ni kan gado ya kwantar, na bishi da kallon mamaki, ban gama mamakin ba na ji ya juya ni gefe ya d’aga jallabiyar jikina ya tsikara mun allura. Daga nan na fara ganin bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan bacci ya yi gaba da ni. Ban farka ba sai ƙarfe shida saura na safe, na bi ɗakin da kallo, sai na ga fankar sama tana wulwulawa, na juya b’arin damana sai na ga Television ta bango manne a bangon dakin, sai wani abu mai kama da GO TV a ƙasan ta da remotes biyu a kansa. A gefen ta kuma wani ɗan table ne an ɗora Alkur’ani izifi sittin akai. Mamaki fa ya kusa kashe ni, na shiga tambayar kaina  abun da mutanen nan suke nufi da ni? Ko duk a cikin salon cutarwar da za su mun ne? Ko kuma wani abu suke nema a guri na? Na yunƙura na tashi sai a lokacin na lura da bargon dake lullub’e a jikina, kaina kuma ashe akan pillow yake. Sai na rasa da yaran da zan fassara wannan al’amarin da na tsinci kaina a ciki. Haka na yunƙura na sakko daga kan gadon, jikina a matuƙar sanyaye kamar jiya na nufi toilet. In tak’aice muku zance haka na kasance a cikin ɗakin nan, kullum za’a kawo mun abinci da ruwa da lemo safe, rana, dare. Da farko bana ci, sai daga baya dana ji yunwa na neman yi mun illa sannan na fara ci ba don daɗi ba. Kuma duk dare sai mutumin nan ya mun allurar nan, wanda na fuskanci ta bacci ce, amma asuba tana yi zan farka. Hakan yasa jikina kodayaushe babu k’wari, ya yi mun wani irin lagwab. Ban taɓa wanka ba sai sau ɗaya da na ji kamar zan mutu saboda k’aik’ayin da jikina yake mun, a toilet ɗin akwai kat’on soap na wanka da toothpaste da brush sabo. Tun ina tambayar mai kawo mun abinci wanda ban taɓa ganin fuskarsa ba dalilin da yasa suka ɗauko ni suka ajiye ni a gurin, har na haqura na daina na zubawa sarautar Allah ido da ganin iya gudun ruwan su, amma har na baro gurin ba su taɓa ƙoƙarin cutar da ni ba, Alkur’ani nan shi ya zamo abokin hira ta, shine nake karantawa wuni guda cur, hakan yasa nake samun nutsuwa a cikin zuciyata. Kwana na huɗu aka kawo mun jallabiya guda biyu da ƙaramin wando, da har na ƙi sakawa sai kuma na ɗauka na saka, da na yi tunanin ina Sallah kar kayan jikina su yi dattin da baza su yi Sallah ba, Tunda ban san ranar fita ta daga gurin ba. Jiya da ya kasance kwana na shida a wannan ɗakin na lek’a waje ta window, sai na fuskanci kamar gida ne inda nake ciki, saboda dana lek’a like bayan gida na gani. Yau na tashi kamar kullum na yi Sallah na ɗan taɓa abincin da aka kawo mun kaɗan, sannan na ɗauki Alkur’ani na fara karatu. Wajen sha biyu lokacin na ajiye Kur’anin inata ta tunane_tunane na, mutumin nan ya shigo ɗakin. Ya ɗauke Alkur’anin gaba na ya ajiye akan table ɗin nan, sannan ya fito da wani baƙin k’yalle ya ɗaure mun idanuna tamau, ina tirje_tirje da yi masa ihun ya rabu da ni amma bai kula ni ba. Na ji an ƙara buɗe ƙofar ɗakin an shigo, daga nan kuma sai ji na yi sun kama ni mun fice daga ɗakin. Inata tambayar su ina zasu kai ni, amma babu wanda ya ce mun kanzil. Har suka saka ni a cikin mota suka ɗaure mun hannuna ta baya muka fara tafiyar da ban san inda za’a kai ni ba. Addu’ar neman tsari kawai nake karantawa a raina. Mun yi tafiya sosai sannan na ji mun tsaya, suka fito dani muka shiga wari guri, sai da muka shiga suka kunce mun daurin fuskata dana hannuna, suka buɗe wata ƙofa suka kaini bakinta, ina shiga na ga toilet ne. Mamakin waɗan nan mutanen nake da basa wasa da Sallah, dan na gane tsayawa suka yi da tafiyar dan na yi Sallah. Na ɗauro alwala na fito na tayar da Sallah akan carpet ɗin dake tsakiyar gurin mai kama da ɗaki, amma babu komai a cikin sa, ko labule babu. Na tayar da Sallar kenan ɗaya daga cikinsu ya taso ya juyar da ni, da alama ban fuskanci alk’ibla dai-dai ba, tunda dama shata kawai na yi. Ina idarwa suka mayar mun da k’yallen fuskata suka kuma ɗauren hannuna, suka kama ni muka fice daga gurin. Muka koma motor aka cigaba da tafiya, wadda har sai ana la’asar muka shigo cikin gari, nan ma sai da suka tsaya suka shigar da ni wani gida da babu kowa a cikinsa na yi Sallah, sannan muka fito, tafiya kaɗan muka yi suka sauke ni tare da kunce mun d’aurin fuskata dana hannuna cikin sauri sannan suka juya suka shiga cikin Mota suka manne ta da mugun gudu. Na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi lokacin dana fuskanci a bayan gidan nan nake. Jikina har rawa yake dan murna da zumud’i na miƙe na nufo gida, ina son na yi gudu dan ƙarasowa da wuri amma rashin k’warin jikina ya hana ni, dole sai a hankali na tako na zo, ina tafe ina tunanin mutanen nan da tambayar kaina menene fa’idar ɗauke ni da sukay? Kuma gashi sun dawo da ni gida ba tare da cutarwar ko ƙwarza ne a jikina ba? Wannan shine abun da ya faru da ni.”

Gaba-ɗaya mutanen Parlour’n suka yi shiru kowa yana jimanta al’amarin a cikin ransa cikin tsananin mamaki. Abban Sadik ne ya fara magana a cikinsu cikin matuƙar mamaki ya ce. “To fa, ka ji kuma wani ikon Allah, amma wannan abun da ɗaure kai yake, to su waye waɗan nan mutanen, mene kuma fa’idar su na yin hakan?” Kawu ya ce. “Shine abun tambayar.” Hajiya ta ce. “Yo wanne abun tambaya kuma ga abu nan a zahiri? An sace Sadik ba dan komai ba ne sai dan kawai akan wannan yarinyar, saboda kar auransu ya yiyu, Allah ya rufa mana asiri shi ba’a kashe shi ba kamar na bayan da aka kashe.” Cikin sauri Sadik ya kalle ta amma bai ce komai ba. Hajja (Mahaifiyar Maamah) ta ce. “Gaskiya ne zargin mu ya zama gaskiya, saboda yarinyar ne.” Kawu ya ce. “Lallai Sadik ka auna arzik’i, Allah ya yi da sauran kwanan ka a gaba kana da rabon shan ruwa, Eh, Alhamdulillah mun godewa Allah, fatan mu Allah ya baka wata matar ta gari, wannan yarinya kam ba matar Aure ba ce.” Abba ya ce. “Nima na tsorata gaskiya, gwara da ba mu yarda an ɗaura Auren ba, wataƙila da waɗan da suka sace shin sun ji labarin an ɗaura Auren da tuni sun kashe shi.” Hajiya ta ce. “Zancen yaushe kuma? Ai Allah ne yay mana gyaɗar doguwa, gobe in Allah ya kai mu sai a karb’o kaya da kuɗin da aka kai gidansu yarinyar, maganar aure kuma ta ruguje, tunda yarinya ta zama annoba.” Abba ya dubi Sadik dake cikin tashin hankali ya ce. “Ka yi haquri Abubukar, tun kafin ka dawo mun gama yanke hukunci baza ka auri yarinyar nan ba, dan alamu sun nuna kota yi auren ma za’a iya bi har gida a kashe mijin.” A ruɗe Sadik kamar zai yi kuka ya ce. “Abba ni na san ba domin Neehal aka sace ni ba, abun da kuke tunani ba haka ba ne Abba, ka manta aikina, ka manta wani zai iya yin komai dan yana jin haushi na, may be mun samu wata matsalar akan wani case daban, ko kuma…..” A zafafe Hajiya ta katse shi da faɗin. “Lallai Sadik na yarda baka da hankali, ka ci akai ka dawanau a duba ƙwaƙwalwarka, yarinyar da kafin kai samarinta biyu an kashe su, kai kuma aka sace ka ana i gobe d’aurin Auren ku shine kake ƙoƙarin kare ta? Saboda Kai ne Majnoon sarkin soyayya, ko kuma in ce sarkin hauka? To yarinyar nan in ma mayya ce ta lashe maka kurwa sai ta sake ka wallahi, kai da ita kuma haihata_haihata kun rabu, rabuwa ta har abada, in ma zaka cire ta daga ranka ka cire ta, na san wannan farar fatar ta_ta da dogon hanci da manyan idanu su suke rud’ar ka a kanta, to indai wannan ne zaka samu wadda ta fita sau dubu a duniyar nan.” Sadik ya dafe kansa dake sara masa kamar zai tsage lokaci ɗaya. Abba ya ce. “Abubakar ka yi tunani da hankalinka mana, idan dan jin haushin ka ko dan ɗaukar fansa aka sace ka baza a barka lami lafiya ba sai an cutar da kai, amma wannan fa dubi yadda aka kula da kai, harda saka maka kayan kallo dan su ɗebe maka kewa. Amma na jinjinawa koma waye ya sace ka, yanda bai bari ka yi wasa da Sallah ba, kuma yake baka abinci akai_akai, tabbas ya san darajar ɗan Adam. Sai dai ba mu san mene a cikin zuciyarsa ba daya aikata hakan.” Ɗaya daga cikin k’annen Abba ya ce. “Abun da mamaki ba kaɗan ba, ita kuwa wannan yarinya wa yake yiwa rayuwarta haka, ni tausayi take ba ni dan na san su ma ba su da masaniya akan mai aikata mata wannan al’amari.” Hajja ta ce. “Abun da tausayi gaskiya.” Umma ta ce. “Wataƙila aljanu gare ta.” Kawu ya ce. “Koma mene ne Allah ya yaye mata, mu dai an yi walk’iya mun gani, ɗanmu ba zai aure ta ba, fak’at.” Sadik zai yi magana Kawu ya katse shi cikin faɗa ya ce. “Karka ce komai, indai mun isa da kai daga yau ba kai ba wannan yarinyar.” Sadik ya kalli Maamah da bata ce k’ala ba tunda ta zauna yana marairaice fuska, a ƙoƙarin na son ta roƙar masa su Kawu akan kar su raba shi da Neehal, amma sai ya ga ta sunkuyar da kanta ƙasa alamun tana bayan su Kawu, ta goyi bayan a raba shi da Neehal kenan ita ma? Ya ɗauke kansa daga kanta cikin ƙarfin halin radad’in da yake ji a zuciyarsa ya ce. “Shikenan Kawu, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi.” Yana gama faɗar haka ya miƙe cikin sanyin jiki kamar zai faɗi ya fice daga falon. Suka bi shi da kallo dukan su. Maamah ta ji tausayin ɗan nata ya cika mata zuciya, sai ta ga kamar su Kawu ba su kyauta masa ba, daga dawowar shi su tarye shi da zancen rabuwa da abar son sa, wanda kowa ya san zai ji ciwon hakan ba kaɗan ba. A ganin ta aida sun bari an kwana biyu ya ƙara hutawa ya dawo cikin nutsuwarsa. Baza ta iya barin ɗanta a cikin halin damuwa ba tare da rarrashe shi ta faɗa masa abun da zai ji sanyi a ransa ba, hakan yasa ta miƙe ba tare data kalli kowa ba ta bi bayan shi. Umma ta tab’e baki. Hajiya ta shiga mita da masifar Neehal ba haka ta bar mata jikan ta ba, asirce shi ta yi, ban da haka mutum yana ganin mutuwa muraran amma yana ƙara kai kansa gare ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button