Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yana shiga a gaggauce ya shiga wanka ya fito yana goge jikinshi da towel wayanshi ya fara ringing,yana yin picking tace dady kayan da zakasa suna kan bed dinka”tana gama fada ta kashe wayan shi Kuma ya juya Yana kallon pure white expensive suit din dake ajiye kan gadon nashi…bai bata lokaci wurin shiryawa ba don yasan shi ake jira,bayan ya gama combing gashin kanshi ya tsaya kawai Yana kallon kanshi ta mirror,shi kanshi baisan he si this handsome ba sai yau,wani irin kyau yaga ya kara na musamman,ya feshe jikinshi da designer perfumes snn ya nufi inda suke.
Bayan ya zauna aka fara gudanar da abubuwan da suka shirya,Layla ce tayi welcoming speech tareda wishing daddyn nata happy birthday snn aka shiga ciye ciye daga nn Kuma akaje sallah bayan an dawo akai cutting cake Layla ce ta fara ajiye gift dinta snn kowa yazo yai wishing dinshi hbd snn ya ajiye birthday present dinshi,haka mutane sukaitayi har suka kare.
Su Layla suka shiga kwasan gifts din daya samu suna shiga dasu ciki bayn kowa ya tafi.

9:00pm dai dai wnn lokacin duk suna zaune parlor suna maida yadda akayi sai dariya suke,Taheer kam Allah Allah yake ya kebe da Layla yanason tambayanta inda ta samu kudinda ta siya mai Rolex wrist watch din da ta bashi as gift dinta,baya tunanin zata samu kudin ta hanya da bai dace ba but he still needs to ask.
Bayan su ummi sun kwanta shima ya mike har fita sai Kuma ya doshi dakinta,fitowanta a wanka knn tana kokarin sa sleeping dress dinta ya shigo dakin… welcome dady…ta fada yayinda ta gama sa kayan ta karasa gefen gadonta da yake zaune ta zauna dab dashi tana cewa”Happy Belated Birthday once again daddy na…Allah ya karo shekaru masu albarka”ya Dan kakalo murmushi snn yace”Ameen”sai Kuma ya tamke fuska yace baby bakijin mgn na koh?…ba na hanaki yin any how dressing kice Zaki shiga cikin mutane dashi ba??…ta wani rausaya Kai tace”ka hanani daddy,Amma gani nai it’s ur birthday so I have to look good”….wato you have to look good…you have to look good for others right?..da sauri tace “not at all dady,why will I dress for someone?..I did it only bcox it’s my daddys birthday shikenan,Amma am sorry”ya firzar da wani iska snn yace”naji amma kar ki sake yin irin haka”…I won’t InshaAllah…yace good girl,,now tell me Ina kika samu kudi kika siyamin such an expensive wrist watch?…it’s my money daddy,kudin da kake samin account Dina ai ba tabawa nakeba shine naga wani friend dina yayi posting dinsu a Instagram na tanbayeshi yace min na saidawa ne shine na siya maka..don’t you like it dadyy?…ya kamo hanunta yace of course No baby I like it so much infact nafi sonshi ma dake..ta wani turo baki kmr zatayi kuka tace”are serious daddy”yace I was only kidding babyna I love you the most,and am sure babu abinda zanso a duniyan nn fiyeda ke,I love you so very much my little princess muuuaah”ya karasa tareda manna mata peck a forehead dinta ita Kuma sai blushing take daddynta yafi sonta fiyeda kowa…ya mike zai tafi yace oya kwanta Nima zanje in kwanta,ba musu ta kwanta ya rufeta da duvet tareda yi Mata addu’a snn ya Mata off din light ya rufe Mata dakin as always shima ya wuce nashi.

One Week ltr…

Yau Nafeesa suke Shirin komawa sbd hutun yara ya kusa karewa umma kuwa dama yau kwananta biyu da komawa kano..Layla ta shigo daki ta samu nafeesa dake kokarin sama hibba hula akai duk sun gama shiri Taheer kawai suke jira ya kaisu airport,,ta zauna kusada ita idonta har ya kawo kwalla tace”Mami don Allah ko kwana biyu ne ku Kara I don’t want you to go plss”Mami ta janyota jikinta duk sai taji ta bata tausayi ciki lallami tace”hutun su Al’ameen ya kare Layla Ramadan ma har sun koma kinga bazai yiwu mu Kara kwana ba and abbansu shima yau zai dawo daga Singapore kiyi hakuri kinji,kuyi mgn da daddynki idan ya amince sai kizo ki kwana biyu kafin time na post ume dinku yayi”Layla ta daga Mata Kai tace”toh…yawwa babyn daddy kukan ya isa haka kinji,nan ma Kai ta daga Mata tana murmushi ta kama hanun hibba suka fito…su Al’ameen ma duk sun fito kowa rikeda trolley dinshi,ga ummi ma a tsaye jikinta duk yayi sanyi ita kanta bason tafiyan nasu takeba,,Taheer na shigowa suka fara fita da kaya bayan duk sunyi sallama da ummi suka fito,ita kanta nafeesan Saida tayi hawaye hakama ummi.
Taheer na driving yana kallonsu ta mirror duk sunyi wani sanyi ya saki murmushi yana cewa”to kukan ya isa haka madam wa zai rarrashi ‘ya’yan naki..duk kukazo garin nn da kuka kuke rabuwa dagake har ummin kmr wanda bazasu Kara ganin junaba..nidai pls kukan ya isa haka kar ‘yata tayi ciwon Kai”ta galla mai hara tace”ai ba wani yasa ‘yar taka kukan ba”murmushi ya sake saki sai Kuma in a serious note yace to kukan dai ya isa haka for God sake we are all going to miss each other.. beside kwanan nn zamu sake haduwa fa idan Ramla ta haihu..haka dai yaita consoling dinsu har suka isa airport,suna zuwa ba bata lokaci suka shiga jirgi don time yayi,haka suka tasya har Saida jirgin ya fara tafiya snn suka shiga mota suka tafi..ko a hanya layla sai share hawaye take,jefi jefi Taheer ke kallonta duk ta bashi tausayi,a hankali ya gangara gefen titi yai parking ganin bafa dena kukan zatayi ba..baby..ya Kira sunanta a hankali..Saida ta share hawaye ta snn ta dago ta kalleshi..come here…ya fada tareda bude mata hanunshi aiko kmr jira takeyi ta fada jikin nashi tana ci gaba da kukanta..bai hanata ba don yasan tsakanin ‘da da uwa sai Allah ga Kuma siblings dinta dole zatayi missing dinsu..a hankali yake shafa bayanta har ta dan tsagaita da kukan snn ya dago fuskanta yana kallonta ya manna Mata peck a both cheeks dinta yace”to kukan ya isa haka nan baby kar kanki yayi ciwo plss”..ya gama share Mata hawaye yace ay zakije musu holiday kema tunda time na post ume din baiyi ba so stop crying kinji..Kai ta daga mai snn ta koma ta zauna inda take shi Kuma ya cigaba da driving.

Mum Ashraf✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

08

Ranan Thursday Layla na zaune sai sharan hawaye take sakamakon kalaban da ummi ke Mata…Sam bata son a taba Mata kai.
Saura befi hudu su gamaba Taheer ya shigo parlon…ya kalli Layla dake ta aikin kuka snn ya kalli ummi data daure fuska tana cigaba da kalaban….yanason yin mgn amma yasan ummi fada zata haushi dashi don haka yayi shiru kawai ya zauna yana kallonsu….kasa hakura yai da ganin yadda Layla ke kukan yace”ummi sannu da aiki…ko Zaki kawo in karasa Mata”…banza tayi dashi batace komai ba….Saida ya sake maimaitawa snn ta dago tana hararanshi tace”in baka ka karasa salon ka kyaleta ta gudu koh…to baka isaba….kullum Kai kake lalata yarinyan nn duk wani abun daya kamata bazaka barta tayi ba….ynxu wnn kan nata kusan watanshi hudu ba kitso sai kace ba mace ba….to na dena Bari wlh… daga yanxu every two two weeks zan dinga tsefe kan da kaina snn inyi Mata wani….idan bata saba da kitson ba haka zaayi Mata aure taje tanayi a gidan miji….to ba zaayi haka daniba…tunda ta fara mgn shiru yayi kawai Yana kallonta….Saida ta gama kalaban tsaf snn ta mike tana karkade jikinta ta wuce daki abinta….da gudu Layla ta fada jikinshi tana cigaba da kukanta tace”daddy don girman Allah ka tsefe min wlh kaina har ya fara ciwo”….ya rungumeta sosae a jikin nashi ya shiga shafa dogon gashin nata yace” shushh ya isa to dena kukan….kinsan ummi bazata Bari a tsefe ba….so kiyi hakuri bazai dade yana miki ciwonba…kafin tayi mgn wayanshi ya fara ringing….”Alhajin Dutse”shine sunan dake kan screen din wayan nashi(N.B Alhajin Dutse shine kakan Layla,shine ya haifi mahaifinta snn Kuma yayan kakanta Wanda ya haifi mamanta)….ya dan janyeta a jikinshi snn yayi picking…”Assalamu alaykum”…aka fada daga daya bangaren… Taheer ya amsa tareda gaisheshi…mutumin yace”Alhamdulillah Taheer ya mahaifiyar taka….tana nn lfy alhaji….”MashaAllah dama wani mgn ne ya taso shine nace let me call you anytime ka samu chance sai kazo muyi mgnr….da sauri Taheer yace alright zanzo gobe InshaAllah…mutumin yace no ba sauri ake ba Taheer….u can take ur time duk ka sama dama sai kazo….da sauri Taheer yace….ba damuwa sir….zan taho gobe in Allah ya kaimu….alhajin yace”shknn Allah ya kaimu goben…ka gaida amaryar tawa…Taheer ya amsa da zataji InshaAllah snn ya ajiye wayan….da sauri layla dake jin me sukace tace “daddy kaje Dani plss….nadade banje Dutse ba daddy don Allah zan bika”….mikewa yai yace”alright idan an samu tickets biyu sai muje…let me talk to ummi first…yana shiga ya fadama ummi yanda sukayi snn ya tafi clinic…ya Kira wani friend dinshi dake airport yace yanason tickets biyu zuwa kano gobe….cikin saa Kuma an samu zasu sauka a kano daga nn sai su karasa Dutse a mota.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button