Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

“Ice on my neck….ice on my wrist….many days I neva sleep….Hotter Hotter….Hotter Hotter….everyday am chasing good life….Tire Tire….Tire Tire…. Rollercoaster Never Tire….I never Tire….yeah yeah….back to sender…. back to sender….you wish me bad….back to sender….yeah Mami….higher higher….higher higher….I never come down going higher….Shoni CC….load am….Cash App….Cash Out….Oni maga….bill am….small money….ball out….usain bolt run am….you get sure client lock am….if you no get money live am….EFCC Mbo japa”…ko ba komai Kun dan shaqata????

A hankali suka fara shiga cikin hall din..suna tafe suna irin step dance haka..amarya da ango dai suna tsakiya…suna shigowa wurin kallo ya koma kansu… almost everybody was like”wow!!what a perfect couple”…babu Wanda basu burge ba a wurin…Layla dai kanta qasa..har yanxu Kuma hanunta na cikin na Taheer..har suka isa inda aka tanadan ma bride n groom suka zauna…brides maids ma suka zauna inda aka tanadar musu likewise grooms maids…bayan amarya da ango sun zauna Mc ya bukaci Hajia Nafisa da tazo ta bude musu taro da addu’a…Nafisa ta fito ta gabatar da addu’a snn ta koma seat dinta…Mc ya juya ga amarya da ango yana fuskantarsu snn ya fara mgn”ga Jakada angon Jakada…wato gskyr mgn tun da nake ban taba ganin amarya da angon da suka dace da juna kmr wadan nn ba…ango Dr.Taheer kayi Dace da zankadediyar amarya..son kowa kin Wanda ya rasa..Hajia Maryam farar mace alkyabbar Mata…ance idan kaga Zara zakaga wata…to yau ga Layla snn ga Majnoon dinta”..Taheer dake zaune yanajin yanda Mc ya dage sai koda mai Mata yake..sai yaji kmr yaje ya rufeshi da duka…shiko Mc da bai San ma yanayi ba..sai yaci gaba da sana’arsa”Hajia Maryam Jakada amarya a gidan Alhaji Taheer Jakada…Allah yasa shekara kmr haka mu dawo taron sunanku”…mutanen dake wurin suka shiga rige rigen fadin”Ameen..Ameen..Ameen”…Mc ya sake dubansu snn yace yanason ganinsu a tsakiyan fili..yanaso yaga adadin masoyan da suke dashi…Taheer da har yanxu yakejin haushin Mc sbd koda mai Mata da yai..ya galla mai wata uwar harara a fakaice snn ya dauke Kai…Layla ce kadai taga abunda yayi…batasan lokacinda ta fara dariya ba…shima ya zuba Mata idanunshi kawai Yana kallon yanda ta dora hanunta kan bakinta tanata faman yin dariya…sai ya sunkuyo daidai kunnenta yace”you are laughing at me right?..don’t worry Zaki shigo hannuna ne”..da sauri ta shiga girgiza kai ta matso saitin kunnenshi itama tace”am sorry plss..bazan Kara ba”…kmr daga sama sukaji Mc na fadin”don Allah amarya da ango idan an gama kus kus din sai a sakko muna jira..kaf mutanen wurin nn ku sukeson gani sbd dominku suka taru”..Taheer ne ya fara mikewa snn itama ta mike..Saida Taheer ya rikota jikinshi sosae snn suka shiga saukowa daga steps din…Mc na kallonsu yace”Allahu Akhbar kaga Layla da Majnoon iyayen kauna”…Taheer ya dan yatsine fuska..cikin ranshi ko cewa yake”waishi wnn Mcn bai iya komai bane sai mgn”..(what do u expect Dr..mutumin da sana’srshi ce mgnr????)…ummi dake kallon abinda yai itama ta girgiza kai tana murmushi tace”mara kunya kawai”

Bayan sun sauko sun tsaya a wurin..sai Mc yacema Dj yanaso a samo waqan da zai dace da couple din nn ayi playing dinta… without wasting time kuwa Dj yai playing waqar Enisa(Love Cycle)…umma ce ta fara zuwa inda suke ta shiga yi musu barin kudi..snn ta rungumeshi gaba daya tana kokarin maida hawayen idonta…sai ummi ma ta taso..sai Nafisa da Ramla.. inshort a hankali mutane suka fara tasowa suna musu likin kudi…can na hango Hajia Amina maman Maimunatou tanata barin kudi kmr bata san ciwonsu ba????abun dai sai Wanda ya gani.

Daga nn Kuma aka bada filin rawa..bayan amarya da ango sun koma mazauninsu…Hanna an dage sai tikan rawa ake..

Finally akazo cutting cake…Umma ta fito as uwar ango…ummi Kuma as uwar amarya..bayan an gama Mc ya sake Kiran amarya da ango stage…hakika dai Abu yayi kyau sai Wanda ya gani…anci ansha snn an dirki rawa.
inshort dai baa tashi a dinner ba sai after 11..shima sbd Taheer ya matsa wai lallai a tashi don shi ya gaji…su ummi basu tafiba Saida suka tabbatar da kowa ya samu mota snn suka wuce…amarya da ango ko dama tun dazu suka tafi…sauran friends dinshi sukaita jigilan daukan mutane suna maidasu gida.

Gobe bazaku samu update ba sbd zanje biki…sai Monday in Allah ya kaimu????

Mum Ashraf ✨

[06/04, 21:21] Mrs Abba Sarkee❤????: ????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

31

Kai tsaye ummi ta wuce da ita bathroom bayan ta hada mata ruwan wanka da kanta…tace”yi sauri kiyi wankan ki fito..ki tabbata kin wanke ko ina na jikinki”…Layla dai batace Mata komai ba..don gani take wankan ma sai ance ga yanda zatayi…ummi Kuma na fita ta janyo trolley da aka cikashi da some of kayanda zata fara amfani zasu tafi dashi..ta fiddo Mata kayanda zata sa da inner wears snn ta jiyesu kan gado ta sake rufe akwatin…tana nn zaune Nafisa ta shigo da kabbasa a hanunta tace”yawwa ummi gashi”…ummi ta Mika Mata kayanda Layla zata Sanya jikinta tace”amshi kiyi maza ki turarasu Nafee…bansan meya dauke hankalina baayi turaren ba tun dazu wlh..da yanxu yasha iska”…ba musu Nafisa ta mike tareda jona burner dake ajiye kan bedside a socket..ummi ta miko Mata turarenda zaayi amfani dashi ta zuba cikin burner din..in no time qamshin turaren mai sanyin dadi ya fara tashi a dakin…ta dauki kayanda ummi ta bata tareda dorasu kan kabbasa..ta ajiye burner din a karkashin kabbasan…ta lullube ko ina ruf ya zamana bata inda iska zai shiga ciki.. hakan shi zai sa turaren yaita hawa kan kayan…after ike 10 mins ta sake juya kayan snn ta Kara turaren..nanma ta barshi Yana tayi…Layla kuwa Saida ta kwashi almost 11 mins snn ta fito daga bathroom…idonta ya kada yayi jajir don ba karamin kuka taci a cikin bayin ba…tana fitowa ummi ta mike tareda komawa bathroom din..wani ruwan ta sake hada Mata mai daukeda madarar turare kala kala..snn ta fito ta sake tura Layla kan ta dauraye jikinta dashi…ba musu Layla ta koma bayin tayi kmr yanda ummi tace…ita kanta taji yanda lokaci daya jikinta ya sake dumamewa da kamshi..bayan ta fito again ummi ta sake bata wani Humra nan ma tabi duk loko da saqo na jikinta ta shafeshi tass da Humra din…zuwa yanxu zaka iya jiyo kamshin da jikinta keyi ko baka kusa da ita…bayan Nafisa ta gama turara kayan ta mikama ummi tana fadin”ummi ga kayan an gama”…ummi ta amsa kayan tareda shinshinasu…Saida ta lumshe ido don jin kamshin dake fita jikin kayan…ba bata lokaci ta ba Layla kayan kan ta sa ajikinta…Layla da keta kokarin danne hawayenta ta amsa kayan…Saida ta fara sa pant da bra snn ta saka kayan…atampa ne blue da touches din yellow a jiki..dinkin riga da skirt ne daya zauna a jikinta das kmr a jikin aka dinka..ummi ta zaunar da ita gefen gado kafin a gama turara lafayan da zaa nadeta dashi…kawai saita fada jikin ummin tareda fashewa da matsanancin kuka…ummi ta shiga shafa kanta tana kakalo murmushi…ita kanta duk abunda takeyi dauriya kawai take..Allah ya sani ba karamin missing dinsu zatayi ba idan suka tafi…ta riga ta saba dasu tun suna kanana…tasan idan suka tafi dole kewarsu ya dameta…tabbas ba don aureba da babu abinda zai rabata dasu sai dai ko mutuwa..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button