Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari suka sake fita yawo hadda umma da ummi…Ramla cedai batajin dadi ta zauna a gida tareda mai aikin umma…sunje parks da dama snn sukai shopping daga karshe suka koma gida.

First thing in the morning driver ya kaisu airport suka wuce Abuja.

Yau Monday Layla ta gama shirinta tsaf don yau zatayi post ume…Taheer kawai take jira…shima bai bata lokaci ba ya shirya…ya dauketa suka nufi Baze University bayan sunyi sallama da ummi tana binta da addu’an samun nasara.
Tun a hanya taji cikinta ya Dan fara ciwo har suka isa school din…9 daidai suka shiga exam din…Taheer na waje yana jiranta tareda yi Mata addu’a Allah ya bada sa’a.

After 11 ta fito daga exam din…kmr jira ake ta fito maranta ya kulle sosae…da kyar ta karaso inda yake ta bude motan ta shiga…ya rikota da sauri Yana tambayan meya faru…amma ta kasa mgn…da sauri ya kunna motan suka tafi…don ya manta shaf date din period dinta ya cika.
Basu dade a hanyaba suka isa gida sbd gudun da yakeyi duk ya gigice…yana parking ya kinkimeta yai cikin gidan da ita…taimako ya shiga bata kmr yanda ya saba duk in ta fara period…Saida ta samu bacci snn ya samu yaje masallaci shima…duk ya zama wani kala kmr shine mara lafiyan.
Bayan kwana uku ta warke garass snn shima ya samu nutsuwa…sai a lokacin ya koma normal activities dinshi.

Alhamdulillah am back guys..thank u all for the prayers..I really appreciate????????♥️

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

15

Kamar yanda Alh Adam Jakada(uncle din Taheer)yai alqawari yau ya dira garin Abuja…da safiyar gobe Kuma shi da wani friend dinshi dake nn Abuja…sai old friend din mahaifin Taheer din InshaAllah zasuje nema ma Taheer auren Sameera kmr yanda ummi ta bukata.

Daren yau Yana zaune part din mahaifin Taheer…inda a nan ne yake sauka duk yazo Abuja…ummi da Taheer na zaune cikin parlorn suma… Alh Adam na kallon Taheer yace”for the last time ina tambayanka watanni nawa kakeso a sanya maka bikin?…Taheer dake zaune kan carpet idanunshi a kasa yace”kmr nan da shekara ko zuwa da rabi haka”…a tare ummi da Uncle din nashi suka kalli Taheer din…”Kai bakada hanakali ne…are you mad…ya zakace a sa maka biki shekara daya da rabi…what’s your problem?…a hankali Taheer da har yanxu kanshi ke kasa yace”ai ana sawa uncle..har shekara biyu ma ana saw…bai karasa ba uncle din ya katse da fadin”you are not serious…Kai me kake jira da zakace a Sanya maka shekara…akwai abunda baka gama bane?..ka shiga hankalinka Dani wlh…idan bakai auren yanxu ba sai yaushe knn zakayi…you are not getting any younger so in zaka dena wnn mafarkin ma ka dena…ummi dake gefe ta tabe baki snn tace”ai na fada maka dama Alh…indai Taheer ne 6ata mana rai da lokaci kawai zaiyi…ni inta nawa nema nanda wata biyu nakeso ayi bikin…ay shi ya kawota yace zai aureta ba dole akayi mai ba”…cikeda gamsuwa uncle ya girgiza kai snn yace “shikenan…tashi ka tafi”ba musu Taheer ya mike ya fita daga dakin…ummi ta bishi da harara????

The following day Alh Adam sukaje neman aure gidansu Sameera…an Kuma sa biki next two months kmr dai yanda sukayi da ummi…farin ciki a wurin ummi baya misaltuwa…sai Kiran family and friends take a waya tana sanar dasu ansa bikin Taheer wata biyu…duk wanda ta kira yakan tayata murna snn yayi addu’ar fatan alkhairi.
Ta ko wane bangare murnan sa wnn biki ake…umma ma da taji ba karamin farin ciki ta samu kanta ciki ba… finally Taheer zaiyi aure..Allah ya basu zaman lfy…Nafeesa ma da labarin ya risketa ji tayi tamkar tayi tsuntsu tazo Abuja don farin ciki…haka Layla ma baa barta a baya ba…she’s super happy daddy zaiyi aure…shknn shima daddy zai haifa ‘da ko ‘ya and she can boldly call him/her”kanina ko kanwata”

Bangaren Taheer kuwa baiji dadin sa bikin watanni biyu ba Sam…har ga Allah yaso a sa ko 6 months ne idan ma bazaa sa shekara ba…tun daga lokacin kuma ya zama wani iri…gaba daya baida walwala sosae…Kuma sai karewa yake kmr kudin guzuri…duk ummi na lura dashi amma taki kulashi…ko me zaiyi sai anyi auren nn Bi’iznillahi…Allah ya gani shi ya fara kawota a matsayin wadda zai aura so ba auren dole zaa mai ba.

Suna zaune dinning Layla na kokarin serving dinshi…for the 5th time wayanshi ya sake daukan ruri…a fusace yai picking yana cewa”for God sake menene haka Sameera…idan kika Kira kikaga banyi picking ba Ina wani abun ne and in naga missed call zan kiraki…why kiketa jera min Kira haka sai kace mara aikin yi”… Sameera ta Dan goge hawayen daya zubo mata snn a hankali tace”am sorry”…ba tareda ya sake cewa komai ba yai hanging wayar tareda Jan tsaki…ummi dake zaune parlor tanajin duk abunda ke faruwa ta karaso dinning din tana mai mugun kallo tace”wato bakada kirki ko Taheer…matar taka kake ma wnn ihun kawai sbd ta damu da kai ta kiraka a waya…you are trying to become stubborn koh…to kaci gaba Allah ya baka sa’a…and let me remind you..in har kan mgnr auren nn kake haka…to wallahi kaji na rantse ba fashi…sai anyi auren nn…idan yaso in an daukota an kowa maka sai kayi gunduwa gunduwa da ita tunda baka shirya yin auren ba..shahsasha kawai”…Layla ta dan rausaya Kai tace”Kai ummi…yanxu da girmanshi zakina mai fada irin haka”…tun bata karasa ba itama ummi tace”kinci ubanki kema…komai girman nashi ai bashi ya haifeni ba…nice nan na haifeshi…sbd haka ki kama kanki kema tun kafin in hadaku keda uban naki incicci ubanku wlh…shashasha kema mara kunya..duk sai nayi maganinku wlh…tana gama fadanta ta wuce abinta…Layla ta bita da kallo tana turo baki kafin ta maida kallonta ga Taheer daya dafe Kai da hanunshi…ta dawo kusa dashi tareda kamo hanun nashi ta rike cikin sigan lallashi tace”kayi hakuri daddy pls”..a hankali shima ya dago yana kokarin yin murmushi ya daga Mata Kai snn ya mike kawai ya bar dinning din…direct part dinshi ya wuce ya wulla kanshi kan gado yana sauke numfashi.

Ummi na shiga dakinta ta dauko waya ta shiga Kiran umma… ringing biyu ta daga tareda sallama…ko gaisawa basuyi ba ummi ta fara mgn”yanxu tsakani da Allah Aisha abinda kike kinyi daidai knn…asa maki bikin ‘da kusan sati biyu knn amma har yanxu kin kasa zuwa garin nn…abubuwan da suke gabanmu fa yawa ne dasu”…Saida ummi tayi shiru snn umma tace”kiyi hakuri Yaya don Allah…akwai abunda ya tsai Dani Amma InshaAllah wani satin zan shigo”…ummi tadan tabe baki snn tace”shknn Allah ya kaimu..snn ki Kira Taheer ki gaya masa idan baiyi wasa ba bazamu rabu dashi lfy ba a cikin gidan nn…yaro duk yabi ya lalace sai iskance iskance yake tsirowa dasu duk sbd yanaso a fasa biki.. to wlh tun wuri ma ki sanar dashi bazaa fasa bikin nn ba..snn ya shiga hankalinshi dani don idan ya kaini bango ba jin dadina zaiyi ba dagashi har ‘yar tashi wlh”ummi ta karasa mgnr tana huci(easy ummi..ai abun baiyi zafi haka ba????)umma data gama sauraranta dariya tayi snn tace”InshaAllah zanyi masa fada Yaya..kiyi hakuri zai gyara”…ummi tace shknn Allah ya bamu alkhairi…daga nn ta kashe wayarta.

Two weeks later…

Taheer ya shigo bedroom din ummi sakamakon kiranda tayi masa…ya samu wuri ya zauna kanshi a kasa snn yace”gani ummi”…ba tareda ta kalleshi ba tace”makullin gidanka nakeso ka bani…zan aika a gano min gidan idan akwai bukatar wani abun ayi tun lokaci bai kureba…naga idan na tsaya bi ta kanka batamin lokaci zakayi”…ba tareda ya dago kanshi ba yace”dama yau nakeso inje gidan ummi…ki barshi kawai idan naje sai in duba”…ummi ta kalleshi da kyau snn tace”bana son bata lokaci Taheer…idan kasan bazakayi akan Kari ba ka bani key zan aika a gano min”…yace”InshaAllah zaayi yanda kikeso ummi…kiyi hakuri”…shiru ummi tayi kmr bazatace komai ba….sai Kuma tace”shknn tashi ka tafi”…baiyi musu ba ya mike kafin ya karasa kofa tace”saura Kuma gobe kaje kayi zamanka a clinic…kasan Aisha jirgin rana zata biyo…so make sure kayi picking dinta on time”…yace InshaAllah ummi”snn ya fita a dakin…ummi ta bishi da kallo zuciyarta cike da tausayinshi…Allah ya sani idan tace rashin walwalan nn nashi bai damunta tayi karya… pretending kawai take kmr bai damunta…but Allah ne kadai yasan yanda abun ke damunta…kullum cikin tunanin dalilin wnn damuwan nashi takeyi amma ta rasa…har rama taga yayi cikin kwanakin nn…wani lokacin sai taji kmr zatace idan auren ne bayaso a fasa amma tasan inhar tace hakan to Taheer bai San Annabi ya faku ba…snn Kuma bazai tsaya ya maida hankali yayi auren ba ita Kuma babban burinta shine taga auren Taheer…snn taga ‘ya’yanshi…shi kadai Allah ya bata don haka dole taso ganin jininshi itama…shi kadai gareta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button