Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

toh snn ya fita,,koda ya shiga bedroom dinshi bacci ya samu Layla nayi,ya karasa gadon a hankali a tsaya yana kallonta,fara ce sosae irin farin nn mai sirkin ja,hancinta dogo dan siriri dashi idanunta so Masha Allah dake daukeda yalwataccen gashin gira me sansti,ya sauke idonshi kan bakinta dake nan dan tsut dashi kmr an sammata,a hankali ya haura kan gadon yana shafa dogon gashinta daya hargitse sbd kwanciyan da tayi,ta dan turo baki ta sake rungume pillow tana Shirin juya mai baya ya mikar da ita zaune,ta wani narke tana kallonshi da sexy eyes dinta tace dady plss bacci nakeji wlh,yaja hancinta yace to ki tashi ummi ce tace a kiraki,,ta zaro ido da sauri hadda rufe baki da hannayenta tace la’ilaillallahu dady bakace zaka bata hakuri ba,Yana murmushi yace don’t worry na bata hakurin ai kuma tace ta hakura kawai cewa tai in turoki maybe wani abun Zaki mata,ta kamo hanunshi tace are you sure dady?ya gyada Mata kai yace am pretty sure baby,tashi kije ba abinda zata miki Nima ynxu xan shirya in tafi clinic,,da sauri tace dady Dan girman Allah zan rakaka clinic din ay dama na dade banje ba,yace to je kiji me ummin zata saki idan kin gama kafin in fito sai mu tafi tare ta Mike da sauri tai hanyar fita tace toh daddy Allah yasa dai ummi ba fada zatamin ba,yabita da kallo yana murmushi saida ta fita ya sauke ajiyar zuciya snn ya nufi toilet don yin wanka.

Washe gari Wednesday cikin shirinshi na tafiya aiki ya shiga parlor bai samu kowaba sai tv dake aiki sai Kuma Mama hauwa dake shirya abinci a dinning ya gaisheta da Respect kmr yanda ya saba snn ya shiga dakin ummi,zaune ya samesu su biyu a gefen gado Layla nama ummin mgn kasa kasa yana shigowa tayi shiru,ya karasa kusada su yana kallonsu da alamar tambaya yace ummi me kuke cewa ne haka naji Ina shigowa kunyi shiru,tace meko muke cewa Taheer hira ne kawai takeyimin na yan skul dinsu,ya kalleta kmr dai bai yadda da abinda tace ba snn ya kalli Layla daketa faman murmushi yace ohk!ni zan wuce aiki yanxu,,da sauri Layla ta mike tace daddy ni zan bika clinic din don Allah,yace baby idan naje ma ba zama zanyiba theatre zamu shiga,,tace eh nidai zan bika daddy sai in zauna aboffice ko kuma inje wurin anty Sara daddy zaman gidan boring wlh idan baka nan nidai kar kace aah plsss,yai murmushi kawai yace to je dauko hijab dinki Ina jiranki,ta Mike da gudu ta fita a dakin

tana fadin thank u dady,,yai dariya kawai ya kalli ummi yace to ummi zamu tafi,ummi ta tabe baki tace a dawo lfy ita Kuma zataci ubanta tunda cewa take gidan ba dadi idan baka nan,yace ummi bafa haka take nufi ba kawai dai tana nufin tafi jin dadi idan Ina nn,,koma dai menene sai naci ubanta wlh,yace ummi kawai wayon zagina ne wnn ni banga laifi a mgnrta ba,ummi tai dariya kawai tace wayon zagin nakne kaima don ubanka,ya kyalkyale da dariya kawai ya fice daga dakin.A bakin mota ya sameta har ta dauko mayafi tana jiranshi,ya kalleta from head to toe pencil trouser ne jikinta blue sai shirt dinta red ta dora kimono mai red n black kan kayan snn ta yafa veil dinta red duk rabin gashinta a waje,ya karasa still idonshi a kanta yace baby bana hanaki yin irin wnn dressing din kice zaki fita dashi ba ne?ta marairaice tace dady ai naga fa mota zamu fita Kuma muna zuwa clinic a office zan zauna ai ba cikin mutane zan shigaba,,ya daure fuska yace su mutanen dake clinic din ba mutane bane

knn,ko Kuma su muharraman kine da Zaki shiga cikinsu a haka,,zatai mgn yace common go back and wear hijab before i knock u,,ta Dan turo baki tace to dady nidai kar ka tafi ka barni pls,sai ta juya ciki da sauri ta sako hijab dark blue me hannu ya dan wuce guiwanta kadan,ta dawo ta tarar har ya shiga mota itamata bude front seat ta shiga,yaima motan key mai gadi ya bude mai gate suka fita,sunyi nisa da tafiya wayanshi dake hanunta tanayin game ya fara ringing,ta Mika mai wayan tace daddy ana Kira,ya Dan kalli wayan ganin unknown number ne ya danja tsaki yace barshi ya gama ringing ki cigaba da game dinki,tai shiru tana kallonshi kmr zatace wani abu sai Kuma ta fasa,yana gama ringing ta cigaba da game dinta wani Kiran ya sake shigowa ta sake mikomai hankalinshi na kan titi yace reject it”a hankali tace why dady?yai mata shiru yacigaba da tukinshi,cikin sanyin murya tace daddy aunty Sameera ce koh,ya daga mata Kai kawai ita Kuma taci gaba,daddy meyasa kake Mata haka don

Allah wlh tana sonka,she loves u sosae shiyasa Nima nake sonta daddy,,meyasa baka sonta pls?murmushin gefen baki ya saki ya juyo ya kalleta snn yace”wato ke ynxu baby har kin wani San so koh”ta Dan turo baki tace na sani mana dady Allah tana sonka,Nima Kuma tanasona kuma duk wulakancin da kake Mata tana hakura sbd tana sonka nidai Dan Allah kaima ka sota daddy,Allah inaso inga kayi aure Nima a haifamin kanne,,dariya sosae yayi daidai lokacin suka isa clinic din,ya gama parking suka fito,ya kalli hijab dinta da bai karasa kasa ba yace baki da wani hijab din daya Kai maki har kass ne?tace inadashi,guda nawa?two”yace kafin mu koma gida zamuje a siyo wasu naga wadan nn duk sun maki kadan,itadai batace komai ba,tunda suka shigo dama mutane keta gaisheshi Yana amsa musu da faraa kmr yadda ya saba,itama tana gaishesu don kusan duk clinic din ba Wanda bai santa ba sbd Yana zuwa da ita time to time haka,,suka shiga personal elevator dinshi da zai kaisu 3rd floor inda office dinshi yake,suna shiga office kmr jira take tace daddy nidai am serious kan mgnr da mukeyi fa, seriously inason inga kayi aure ka samu mai kwantar ma da hankali kaim…tai shiru da mgnr ganin irin kallon da yake Mata,ta rufe bakinta da hannu tana dariya,ya dawo kusada ita ya zauna yana kallonta face dinshi da murmushi yace so babyna har tasan wani kwanciyan hankalin aure koh?ta boye fuskanta a kirjinshi tace Noo daddy niba abinda nake nufi kenan bafa,ya dagota Yana kallon fuskanta yace to fadamin me kike nufi,tasa hannayenta biyu ta boye fuskarta snn tace nidai kawai daddy

inaso kayi aure Nima Kuma in samu siblings,,yana shafa gemunshi still face dinshi da murmushi yace alright zanyi auren nn dai tinda ynxu har babyna ma mgnr auren takemin,ya mike ya koma seat dinshi akai knocking kofa,come in”ya fada yana duba time wata nurse ce ta shigo ta risina ta gaisheshi ya amsa snn tace mgnr theatre din nan me doctor everything is ready Kai kadai ake jira,yace ok kice musu su shiga da ita theatre gani nn zuwa ta amsa da yes sir snn ta kalli Layla tace ‘yar gidan daddy yau an tuna damu knn?Layla tai dariya tace Ina kwana anty Sara,,lfy Lou babyn daddy ya sch?ta Dan wara ido tace aunty Sara nayi graduation ai,shiyasa ma kikaga bana zuwa sbd Ina exams ne,,to Masha Allah Ashe babyn daddy an fara girma to Allah ya Sanya alkhairi ta amsada ameen snn ta fita,ya mike tareda daukan lab coat dinshi yace baby zamu shiga theatre ynxu ki zauna nan sai ki kunna kallo,ta makale kafada tace dady nidai zanje wurin aunty Sara,yace ohk ki kullemin office din tohta amsa mai snn ya fita don ana jiranshi.
Yan fita ta dauki phone dinshi da har ynxu ke hanunta ta fita tai locking office din kmr yanda yace dnn ta tafi Nurses Station,,tana gab da shiga wurin taji an kirata,ta juya a hankali tana neman me Kiran nata,lokaci daya ta saki murmushi tace laa uncle Salees(Salees student doctor ne yake house man ship dinshi a asibitin)ya karaso kusada ita Yana murmushi shima yace umh ‘yar gidan daddy dama ana ganinku?tace ana ganinmu mana uncle ay sbd Ina exams ne daddy ya dena xuwa Dani Amma ynxu na gama,yadan wara ido yace wow!congratulation sweetheart Allah yasa albarka,tace Ameen,,kallonta kawai Salees keyi don ba karamin burgeshi yarinyar keyi ba,ba karamin missing dinta yai ba da bata zuwa,,ganin kallonta kawai yake tace umh uncle bari inje wurin aunty Sara har ta juya yai saurin tsayar da ita yace wait mana,,inason muyi wata mgn fa dake dama,ta wara ido kadan sai Kuma tace mgn Kuma uncle?wace irin mgn kenan?yace let’s go to my office,,tayi shiru kmr bazata jeba tace ai daddyna fada zaiyimin,yace daddynki ya shiga theatre madam and I assure u bazai fitoba sai nan 2 hours beside Saida na fara tambayanshi ma kafin inxo wurinki,are u sure?ta fada tana kallonshi yace am very very sure,,tace alright muje,nan suka tafi office din nashi.
Da kanshi yaja Mata kujera yace bismillah ba musu ta zauna shima ya zauna opposite to her yace baby I missed u sosae,,dayi Dan murmushi tace sunana Layla yace to Layla nayi missing dinki da yawa da yawa hope dai ynxu kullum zaki ringa biyo dad dinki kuna tahowa tunda exams ya kare,ta daga mai kai alamar eh,ya wani sauke ajiyan zuciya hadda Dora hanu a saitin heart dinshi yace thank God,,ya cikata da surutu tun bata saki jikiba har daga karshe ta ware yanata bata labarai ita Kuma tana dariya sai admiring kyanta yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button