Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bayan Sati 3…

Yau tun safe Layla ke zuba idon ganin Taheer tanason yimai mgnr komawanta school amma shiru bata ganshi…tun last week take so tayi resuming amma datayi mgn da ummi sai tace wai sai sunyi arba’in..ita harga Allah ta gaji dayin missing karatunta…yanxu satinta hudu knn da haihuwa..Kuma Alhamdulillah daga ita har Nawal din basu da wani matsala…ita ta maida jikinta tayi kyau tayi fresh abunta..kana ganinta zakasan batada wani problem..ta Dan Kara kiba da yayi suiting dinta…itama Baby Nawal tayi kiba ta Kuma Kara haske sosae…in ka gantasai kayi tunanin takai 2 months..gashi tayi wayo ga Kuma kyanta dake Kara fitowa..kowa ya ganta sai yayi sha’awanta…haka uban ke sata a gaba yayita Mata wasanni kala kala..tun tana kukan bata so har tazo ta saba..idan kaji yanda yake mgn da ita zakayi tunanin da babban mutum yake mgn…ummi tayita fada wai so yake ya lalata ta kmr yanda ya lalata mata Layla…

Tana cikin daki ta gama shirinta tun dazu..tana zaune da wayanta a hannu tana tunanin ko kiranshi zatayi ta fada mishi mgnr komawa school din..sai Kuma taga it’s better suyi mgn face to face…tana nn zaune tana tunane tunane tajiyo kmr muryanshi a parlor…da sauri ta ajiye wayan nata ta fita…yana zaune parlon shida umma..Yana sanye cikin kananun Kaya sai taga ya koma yaro sosae a idonta..gaba daya hankalinshi na kan Nawal da yake wasa daita..ita Kuma sai babbaka dariya dake har dimples dinta suna lotsawa…umma na gefe tana kallonsu tana dariya..dawowanshi knn daga Clinic ko abinci baici ba ya fara wasa daita…ta kuma San tunda suka fara wasan nn yanxu cin abincin ma sai illah MashaAllahu…
Karasowan Layla yayi daidai da shigowan ummi parlon itama…Layla ta zauna opposite to him snn a hankali ta Kira sunanshi don hankalinshi na kan Nawal bai ma ga shigowanta ba…a hankali Taheer ya dago idanunshi tareda saukesu a kanta…wani irin difff yaji cikin brain dinshi kmr irin an kawo wuta am dauke…ya zuba Mata idanun nashi sosae yana binta da wani kallo mai wahalan fassarawa… zuciyarshi yaji tana wani fat fat fat..gashi kuma ta koma bugu da sauri sauri..idanunshi sun kada sunyi jajir…ya Kuma kasa dauke idanun nashi daga gareta..it’s like akwai wani force of attraction dake Jan idanun nashi zuwa gareta…lokaci daya komai da komai nashi ya tsaya cak kmr ansa musu brake…ita Kuma Layla kallon da taga yana Mata ne ya haifar Mata da abubuwa da dama a cikin heart dinta..gaba daya sai taji ta kasa fadan maganan da yake bakinta…yawun bakinta taji ya kafe kaff ba tareda sanin musababbin hakan ba…ummi Kam zuba musu ido tayi tana kallon ikon Allah…ta kalli wnn ta kalli wancan ta rasa kallon me akeyi ne haka..ita Kuma umma dama tun da taga yanda Taheer ya kafeta da ido tasan karshen zancen…Kamar kiftawa da bismillah kawai sukaga Taheer ya mike ya kama hanyar fita daga dakin…da sauri ummi tace”Kai Ina zakaje da jaririya bakada hankali ne”…a hankali ya juyo tareda mikama umma Nawal snn ya fice daga dakin..shi gaba daya ma ya manta tana hannunshi Saida ummin tayi mgn…duk suka rasashi da kallo bayan ya fita ummi na tabe baki tace”yaro sai kace mai iskokai..iskanci iri iri ya iyashi…yanxu dubi yanda ya wani mike a zabure sai kace bashi ya cika mana kunne yana wasa da ‘yarsa ba dazu”…daga umma har Layla baby Wanda yace kala..ita Layla ta mike tareda komawa daki tanajin gaba daya jikinta a sanyaye..bata yadda da kallon nn da taga Yana Mata ba Sam…tasan for sure something is fishy..da akwai abinda ke damunshi…ita Kuma umma gaba daya sai taji ya bata tausayi…tasan yanda Taheer yake son Layla Allah ya sani yamayi kokari da aka kawo har yanzu bai gaza ba…tun kafin ta haihu fa take gida Kuma bai taba cewa komai ba..ko ganinta ma watarana ummi hanashi takeyi..batasan meyasa ummin kemai haka ba wlh..ko don ta lura Yana matukar son Laylan ne oho…ta maida idanunta kan Nawal data fara yan koke koke..ta dan saci kallon ummi taga hankalinta ma na kan tv..a hankali ta mike zuwa dakinda Layla ta shiga..ya kamata tayi wani abu..bai kamata tasa ido tana kallon danta yana kokarin zaucewa kan abinda is his ba..bazata zuba ido ba gsky..she really must do something idan ba haka zasu shiga hakkin yaran nn… especially ma Taheer da tasan bashida hakuri ko kadan akanta..saukin abun ma yanzu shine Nawal…ko ya yake cikin bacin rai yana fara wasa daita sai ya mance..amma dukda haka zata duba taga abunda zatayi..

A kwance ta samu Layla tayi daidai kan gado..ta rufe face dinta da hannayenta so bata ganin face dinta…umma ta zauna gefen gadon snn tace”tashi muyi mgn”…da sauri Layla ta mike zaune don bata ji shigowan umman ba…umma ta Mika Mata Nawal tace”fara bata tasha naga zata fara rigima”…ba musu Layla ta amsa Nawal da umma ke miko Mata snn ta fara feeding dinta…

Ku Dan Kara hakuri saura kiris mu gama InshaAllah????????????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

You are highly welcome to the world of islam my baby girl????Allah ya rayaki ya maki albarka..she is our family’s first grand daughter????

55

Umma na nn zaune tana jiran Layla ta gama feeding Nawal suyi mgn kawai sai ga ummi ta shigo dakin…ba don umma taso ba ta mike tareda fita daga ciki…tanata ayyana yanda zaayi ta tura Layla part din Taheer ba tareda ummi tayi noticing ba…wnn shine kadai hanyan da tasan zai dan samu sauki cikin ranshi…ta San Yana bukatar kebewa da matarshi tunda ta dade a gidan..ba kuma abinda yake shiga tsakaninsu…snn itama Laylan ta lura akwai maganan da take sonyi dashi don haka wnn ne kadai solution…

Saida ta daidaici ummi tayi bacci snn ta sake komawa dakin…kmr yanda tayi zato ummi tana kwance kan gado tana bacci…ita Kuma Layla ta gama Shirin kwanciya itama zata kwanta sai ga umma ta shigo…zatayi mgn umma ta dora hannu kan bakinta tace”shhsshs”…ba musu Layla taja bakinta ta tsuke…ita Kuma umma ta kama hanunta a hankali suka fita daga dakin…Saida suka shiga parlor snn umma ta sake hannun Laylan…tayi kasa muryarta tace mata”kina jina..so nake kije ki dauki abincin ki kaima Taheer yana bangarenshi.. duk yau ya kasa cin abinci ban San meke damunshi ba”…a hankali Layla tace”umma ko dai bashi da lfy ne”…umma tace”ke da kike matarshi ai ke ya kamata ki sani Layla..haka nn kike biyema Yaya kuna azabtar da yaron nn..ko gaisheshi fa baki zuwa har can part din nashi kiyi..kullum kina daki bayan Kuma kinsan yanada bukar ganinki amma kike iskanci..ki cigaba da biye mata duk ya gaji da wulakancinki yace zai Kara aure bazan hanashi ba wlh.. instead ma zanyi supporting dinshi tunda ke kina nuna baki damu dashi ba”…da sauri Layla da idanunta har sun raina fata jin maganan da umma ta fada tace”Kai umma dn Allah…Ni wlh ba Wulakanci nake mishi ba ummi ce..kinsan halinta bazata na barina Ina kulashi ba..wai sai na gama jego”…umma ta saki tsaki kafin tace”ai sai Kita yi…kici gaba da biyema Yaya kina banzatar da mijinki..shi namiji kulawa yake so kuma idan bai samu wurin matarshi ba yana iya zuwa koma inane ya samu..idan kinga zakiyi hankali sai kiyi”…tana gama ta nuna kofa tana cewa”yi sauri kije ki dawo kar Yaya ta tashi taga bakya nn”…da sauri kuwa Layla da kayan bacci kadai ne a jikinta sai hula ta fita daga dakin…Kai tsaye part dinshi taje..a hankali ta tura kofan parlonshi luckily tajishi a bude…duhu sosae ta gani a dakin don ya kashe bulbs din ko Ina…a haka ta karasa bedroom dinshi…nan ma tana tura kofan tajishi a bude ba bata lokaci ta bude ta shiga…Saida tayi switching light din dakin snn ta shiga bin dakin da kallo tana so taga a inda zata ganshi…ta wara ido sosae tana waige waige ganin baya cikin dakin…a hankali tace”to Ina ya shiga a Daren nn Kuma”…zuciyanta ya buga da karfi data tuna mgnr da umma ta fada Mata yanxu…”shi namiji kulawa yakeso Kuma idan bai samu a wurin matarshi ba yana iya zuwa koma inane ya samu”… innalillahi badai daddy fita yayi cikin Daren nn ba…to Ina zaije..wajen wa zaije at this time of the night…gaba daya ta gigice har bataji time din da ya fito daga bayi ba…abinda taji kawai shine an rungumota ta baya…ta lumshe ido lokaci guda kuma ta sauke ajiyar zuciya mai karfi…koda bataga face dinshi ba tasan shine…taji kamshin perfum dinshi and taji yanda hug din nashi yayi affecting duk body systems dinta..a hankali ta juyo tana facing dinshi…zatayi mgn ya sake hugging dinta gam yana cewa”baby I missed you…am about going crazy..baby dn Allah stop all this drama..ki dena biyema ummi kizo mu koma gidanmu dn Allah..wlh na gaji..na gaji da boye mn Mata da akeyi sai kace wanda bashida gata..duk ummi ta maidani gwauro ta karfi da yaji”…Yana gama mgn sai ya jata suka zauna kan gado yana kallonta da kyau yace”Yama akai kikazo nan..ummi ta sani?..”da sauri Layla na girgiza mishi kai tace”bata saniba..umma ce tace inzo..wai ko abinci bakaci ba”…Taheer na murmushi yace”Allah yaja zamanin ummata..she is one in a million..I love her so much”…sai Kuma ya kwabe fuska yace”baby am starving..yunwa nakeji sosae wlh”…da sauri Layla ta mike tana cewa”let me get you something..idan kaci sai muyi mgn”…tana kokarin barin inda yake yasa hannu ya jawota ta fada jikinshi..ya kwanta kan gadon tareda dorata itama ta kwanta a samanshi…murya can kasa yake cewa”Ina Kuma zakije”..tace”zanje in kawo maka abinci mana daddy”…ya dan bata rai snn yace”Ni ba abinci nake bukata ba..I want you”…Layla ta zaro idanu sosae tana kokarin mikewa daga jikinshi tace”Aa daddy kar kayi haka plss..wlh ummi zata gane nidai ka kyaleni in tafi dn Allah..Kuma Nawal zata iya tashi daga bacci bana nan”…a hankali taji ya saketa daga rikon da yayi Mata..lokaci daya jikinshi yayi sanyi jin ta kira Nawal..ya sani tabbas zata iya tashi daga baccin idan bata kusa Kuma zatayi kuka..shi kuma baison kukanta..dn haka zai hakura ko dan sbd ita..amma indan ta ummi ne bazai damu ba..tunda yasan kota tashi baza tace zata biyo Layla har part dinshi ta dauketa ba..iyakaci dai da safe idan sun hadu ta sauke masu kwando kwando wnn Kuma sun riga sun saba dashi so bazai dameshi ba..amma Nawal kam yasan definitely zata iya tashi daga bacci and babu wanda keda nonon da zai bata sai Layla so wnn shine kadai dalilin da zai sa ya hakura komai matsuwar da yayi kuwa..bazai taba dora bukatarshi kan ta yarinyarshi ba..no.. Never..yana yi mata sonda ko yaya yaji kukanta hankalinshi na matukar tashi so bazai so ya zama source of yin kukan nata ba…a hankali ya koma tareda kwanciya kan gadon ya juya ma Layla da tayi tsai tana kallonshi baya…murya can kasa yace mata”kije..Saida safe”…kmr zatayi kuka tace”daddy”…ya juyo yana kallonta ba tareda yayi mgn ba…ita Kuma ta sake langabe Kai tace” daddy am sorr”…bata karasa ba ya mike zaune tareda dora hannunshi kan bakinta…yana girgiza kai yace”u don’t have to apologise ay ba laifi kikayi ba..kawai nace ki tafi ne because I don’t want sweetheart ta tashi daga bacci Kuma baki koma ba..so kiyi sauri ki tafi kar ta tashi baki kusa”…a hankali ta sake cewa”but daddy I want to talk to you”…a takaice yace Mata”umhumm inaji”…tace”mgnr komawa school ne dama…ya kamata in koma daddy inata missing abubuwa masu muhimmanci”…Taheer ya shiga girgiza kanshi yace”No baby..ba yanxu ba”…kmr zatai kuka tace”but daddy why”…yace”sbd Sweetheart bata yi kwari sosae ba..ban so kije kina wahalar min da ita a school so it’s better ki bari ta dan Kara girma”…lokaci daya Layla ta fara hawaye tace”ai dama ni yanzu nasan baka Sona..Allah daddy nasan yanzu kafi son Nawal a kaina”..dafa goshi Taheer yayi yanajin yanda take sake dama mishi lissafi da wnn kukan da takeyi…tanaso ta sake hargitsa mashi ‘yar ragowan nutsuwar da yai saura a tare dashi…har ya Kai hannu zai kama nata sai kuma ya fasa..murya a hankali yace Mata”baby mene abun kuka dn Allah..to kiyi hakuri ki bari idan kuka karasa 40 days sai ki koma..and stop saying na dena sonki okay?..yanxu ki tashi ki koma kar ta tashi a bacci baki nn”..Layla na share hawayenta tace”gashi nn har wani korana kakeyi sbd ita”…Taheer ya sake dafa goshi before yace”to naji am sorry..bazan Kara koranki ba..are we good now?..”ta murguda baki tareda dauke kanta gefe..shi Kuma ya saki murmushi snn ya sake komawa ya kwanta..shi kadai yasan what he’s feeling right now..yasan idan taci gaba da zama a nan komai na iya faruwa..shi Kuma baison abinda zai sa sweetheart dinshi kuka..ya tabbata ba dan Nawal ba yau da Layla bata isa tabar dakinshi batareda ya aikata wani abun ba…ita Kuma Layla a hankali ta mike ta kama hanyan ficewa daga dakin…har takai bakin kofa sai Kuma ta tsaya tana tunani…anya kuwa ya kamata ta tafi ta barshi bayan tasan ko abinci baici ba..sai taga kmr bata kyauta ba idan tayi hakan..tasan for sure yana cikin damuwa…sai ta juya a hankali tareda komawa cikin dakin…ta zauna kusa dashi tana bubbuga bayanshi da hannunta tace”daddy”…Taheer yayi Mata banza bai amsa ba..ta sake cewa”daddy”…nan ma baiyi mgn ba…sai tasa duk hannayenta tana kokarin juyo dashi tace”daddy mana..I want..”tun kafin ta karasa mgnr Taheer ya mike zaune yana kallonta da idanunshi da sukai jajir yace mata”ki dena tabani baby indai baso kike ki karar min da dan hakurin dayai min saura a tareda ni ba..na fada maki ki tafi..banason Nawal ta farka baki koma ba”…ta rausayar da Kai snn tace”daddy to in kawo maka abinci”…ya girgiza Mata kai..ta sake cewa”amma daddy kace min bakaci abinci ba”…yace”am not hungry any more”…ta mike zata fita tace”nidai bari in kawo maka ko tea ne kasha”..tana rufe baki yace”ko kin kawo ma baby ba iya cin komai zanyi ba..I lost my appetite so dn Allah kije ki kwanta nima I want to sleep”…Layla bata sake cewa komai ba ta juya tareda ficewa daga dakin…zuciyarta taji na Mata wni irin zafi..wato ma ita yake Kora daga inda yake..kawai sbd Nawal shine yake Mata wnn Koran Karen…tana tafe tanata tunani ita kadai har ta karasa part dinsu ta shiga…bata samu umma parlor ba don haka ta wuce dakin ummi…suna kwance suna baccinsu daga ita har Nawal kmr dai yanda ta tafi ta barsu..a hankali ta haura kan gadon itama ta kwanta tareda lumshe idanunta..har yanxu idanunta basu bar gano Mata shi cikin yanayin da ta baro shi ba..duk sai taji ta gagara sukuni..duk haushin ummi taji ya kamata don ita ke hanata zuwa inda yake wai kar ya lallaba ya sake dirka Mata wani cikin..ita Kuma Allah ya sani tsoron haihuwa take..tunda tayi bataji dadinta ba..gani takeyi har abada bazata sake haihuwa ba sbd tunda take bata tabajin ciwon da yakai nakuda azaba ba a duniya..ta wahala ne fiyeda tunaninta..ta dade tana tunane tunane sai juyi takeyi kan gado baccin yaki daukanta..sai can dare sosae snn wani barawo ya lallaba yayi gaba da ita..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button