Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Taheer kuwa yawo ya shigayi kawai Yana zaga gari ba tareda yasan inda ya nufa ba..baison komawa gidan ne yanzu sbd ummi zata iya zargin wani abu…Saida ya shafe almost an hour yana gantali a titi daga wnn layin ya shiga can…daga karshe dai ya shiga wani store ya siya mata uban chocolates masu yawan gaske…dukda bai sonta da Shan chocolate din amma haka ya siya kmr ba gobe…baima San me ya kamata yayi don ya faranta mata rai ba…ana gama ma packaging ya dauka snn ya koma mota…Kai tsaye gida ya nufa don yasan zuwa yanxu dai ummi bazatayi tunanin komai ba.

Yana isa gidan bayan yayi parking ya fito daga motan..ya bar chocolates din nan cikin mota snn ya nufi cikin gidan…gaba dayansu suna dinning suna Shirin fara lunch ya shigo…ya karasa dinning din shima yaja kujeran dake next to umma ya zauna snn ya karyar da murya Yana kallon umma yace”serve me pls”…umma na murmushi ta mike tai serving dinshi snn ta koma ta zauna… Taheer ya shiga cin abincinshi hankali kwance..yanayi Yana Satan kallon Layla..ita kuwa Yana zuwa wurin taji gabanta ya Fadi…haka nan taji wani kunya ya lullubeta..tama kasa cin abincin dake gabanta..batasan wane irin al’amari bane wnn bayan da ba haka take ba…ta ajiye spoon dake hanunta a hankali snn ta mike zata bar wurin…umma na kallonta tace”Ina Kuma zakije”…tace”umma daki zan koma..na koshi”…kafin umma ta sake mgn ummi tace”yi tafiyarki kinji..idan ma baki koshi ba zan kawo maki daki sai ki karasa ci”… Layla namurnushi tace”yawwa my ummi”snn tabar dinning din da sauri…Taheer shima duk sai yaji abincin ya fice daga ranshi…ko baa fada ba yasan sbd shi tabar wurin..to meyasa..badai yarinyar nan tsoronshi ta faraji ba Kuma..no ko zaiyi tolerating komai bayajin zai iya tolerating wnn gudun da takeyi sbd shi..don Allah ya sani cutar dashi zatayi…a haka dai har suka gama cin abincin yanata tunane tunane…suka koma parlor suka zazzauna..still Taheer yaki tafiya don yana tunanin zata fito ya ganta amma shiru…har yaje sallahn asr ya dawo nan ma babuta ba alamarta… inshort haka Taheer yaita zaman parlor wai ko zata dito ya ganta amma har dare lokacin kwanciya bacci yayi bata fitoba..ranshi ba karamin baci yai ba…ya ringa Satan kallon kofar dakinta yasan dai ko giyar wake yasha bai isa ya doshi hanyar dakin bama don ummi saita tara mai jama’a…haka ba don yaso ba ya tafi part dinshi bayan duk sun tafi sun kwanta suma…ko cikin dare yanata tunanin ko zuwa zaiyi ya sameta yanxu tunda yasan kowa na bacci amma tsoron abunda zai biyo idan ummi tai ram dashi yasa baijeba…haka ya kwana wnn daren ranshi bace..zuciya cikeda tunani kala kala.

Washegari ma same thing happens…tun safe Taheer ke parlorn ummi amma ko keyarta bai ganiba…gaba daya ranshi ya gama baci…Sam bazai dauki wnn halin ba wlh..dole ya nema mafita..
2 nayi ya koma part dinshi don yin shrin tafiya aiki…har ya gama shrin ya fito ya sake komawa yai sallama dasu umma bai ganta tafito ba…ya wuce ya tafi clinic kawai..amma yasa a ranshi yau duk abunda zai faru sai dai ya faru..amma bazai kwanta bacci ba sai ya sanyata a idonshi..sai kuma ta fada mai dalilinda yasa take tserewa daga gareshi…gaba daya yinin yau cikin kunci yayishi har dare.

9pm ya baro clinic…bai karasa gidaba sai around 10…bayan yayi duk abubuwan daya saba before going to bed..sai yai zamanshi nan part din nashi yaki zuwa can..yasan ko yaje dinma ba ganinta zaiyi ba so it’s better yai zamanshi.
Saida ya tabbatar da kowa ya kwanta snn ya mike ya nufi part dinsu..lokacin 12 ya wuce…bai samu kowa parlor ba as he expected..gaba daya bulbs din parlon ma kashe suke…a hankali ya taka zuwa dakinta..ya bude kofar ya shiga…sai yaga ba kowa a ciki..baiyi mamaki ba ya juya ya fito don dama Saida yai tunanin hakan.
A hankali ya tura kofar dakin ummi ya shiga ciki…suna kwance su biyu a kan gadon…ummi na daga farko..ita Kuma Layla na ciki..yabar kofar a bude snn ya shiga tafiya Sadaf Sadaf har ya zagawa inda Laylan ke kwance..yasa hanu ya yaye duvet din data rufe har fuskanta dashi…sai ya saki murmushi ganin idonta nata motsi yasan ba bacci takeyi ba..ya sunkuyo saitin kunnenta murya can kasa yace”saura Kuma kimin ihu”…itadai Layla batace komai ba sai gabanta dake dukan tara tara…a hankali Taheer ya sunkuyo tareda daukanta cak ya rungume a jikinshi…snn ya fara tafiya a hankali har ya fita daga dakin Kai tsaye ya isa dakin Laylan ya bude kofar ya shiga ciki..ya ajiyeta gefen gado snn ya koma yai locking kofar hadda sa Mata key.

Me mutumin nn ke Shirin aikatawa ne????

Masoyan doctor yace yana gaisuwa..yana godia da supporting dinshi da kukeyi kan baby????

Mum Ashraf y

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

26

Yana gama rufe kofan ya juya tareda komawa cikin dakin..ya zauna kusada ita..fuska a tsuke yace”fadamin dalilin da yasa kike guduna baby..ko tsanar da kikamin ne yasa ko ganina baki sonyi”…Layla ta girgiza kai da sauri..har kwalla ya ciko idonta…Taheer ya sake hade rai yace”karki kuskura kimin kuka..kinsan banaso”..aiko ta hadiye kukan nata tareda Kai hanu tana goge hawayen dake kan fuskanta…yasa hanu tareda riko nata..idanunshi a kanta yace”ki fadamin baby..baki son ganina ne in dena zuwa inda kike”…Layla da kuka ke Shirin kufce Mata tace”ba haka nake nufi ba daddy..kawai dai”..kmr zata fada sai Kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya…yasa hannu yai cupping face dinta ya sake cewa”kiyi mgn baby..dare na karayi”…Saida ta lumshe idanuwanta snn tace”ni kunya nakeji daddy..Kuma inajin tsoro”…yai shiru na tsawon secs yana kallonta..sai can Kuma ya nisa yace”meyasa kikejin tsoro na Kuma..kina tunanin zanyi maki wani abun ne”…batace komai ba sai hawaye da takeyi…ya matso da fuskanshi ya hada da nata..hancinshi na gogan nata.. idanunshi shima a lumshe yace”idanma kina tunanin zanyi maki wani abun ne baby to ki dena..bazan taba yi maki abunda bakiso ba..I promise babu abinda zai shiga tsakanina dake sai da amincewarki..am not after that baby..am after your love..so ki dena jin tsorona ki saki jikinki dani don Allah”..Layla da idanunta ke lumshe har yanxu..tace mai”toh daddy”..ya dago fuskanshi yana share Mata hawaye yace”promise me daga yau baki kara guduna”…Layla ta saki murmushi snn tace”I promise”…yasa hanu ya janyota jikinshi sosae..idanunshi kan lips dinta da sukayi ja as a result of kukan da tayi..murya can kasan makoshi yace”saura kunyar..bari in cire maki itama kinga saik…bai karasa mgn ba Layla tai saurin dora hanu kan bakinshi dake gab da hadewa da nata…kirjinta na sama da qasa tace”shima na denaji daddy..bazan karaba”…wani malalacin murmushi ya saki yana kallonta yace”are you sure baby..da ki bari kawai indan rage maki ita”…ta sake kai hanunta bakinshi tana girgiza kai kmr zatasa kuka tace”Allah na dena daddy..kayi hakuri pls”…Taheer yasa hannu ya sake manne ta da jikinshi yana smiling yace”na hakura my baby..amma daga yau duk kika sake cewa kunyana kikeji sai nayi..kin yadda”..ta daga mai Kai a hankali…ya dagota daga jikinshi yanata kallonta yace”alright na gode sosae baby..I love you”…Layla ta sake fadawa jikinshi tana murmushi..ta bude baki zatace I love you too sai Kuma ta maida bakin ta tsuke da sauri..murya can kasa tace”nayi missing dinka sosae”…ya dagota tareda kama cheeks dinta yace”and I missed you more…yanxu tashi kije ki kwanta tunda mun gama kar ummi ta farka taga bakya nan”…Layla murmushi ta saki data ayyano kawai ace suga ummi a kansu ynxu..ai tasan ba daddy ba ita kanta Allah ne kadai zai rabata da ita.
Taheer ya fara mikewa itama ta mike..ya kama hanunta suka fita daga dakin..ya rakata har kofar dakin ummi tareda yi Mata peck a goshi snn yace daita”sweet dreams”…tana murmushi itama ta gyada kanta tace”Allah ya tashemu lfy…Yana tsaye yana kallonta har ta bude kofar ta shiga..shima ya juya a hankali zuwa part dinshi…har ya fara missing dinta wlh..Allah dai ya dorashi kan ummi ta bashi matarshi su tafi gida abunsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button