Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

samunshi kan Wanda kake da tabbas?look at me mana,age mate dinka ne ni amma shekarana 10 da aure da yara 4,ita kanta uwar yarinyar nn qanwarka cefa ka bata good 2 years dukda dai ita mace ce amma yaranta nawa ynxu,kafiso kayita zama a haka kana batama umminka rai knn,,ynxu ko bakason auren nn kodan farin cikin ummi bai kamata ka ajiye wnn batu ka samu mace ka auraba,meka nema ka rasane a rayuwa?”Babu,komai Allah ya baka,kanada kyau kanada kudi kanada ilimi snn ga Mata nn dake sonka duk kaki basu dama kan yarinyar da ka raineta a hannunka Taheer wane irin sone wnn don Allah da yake neman zautan min da abokina,I want my old friend back,u have to think about this Taheer pls,”tunda ya fara mgn idanun Taheer a lumshe Amma jin duk wata mgn daya yake tamkar saukan guduma kan kirjinshi,yasan duk abinda abokinshi ya fada gsky ne Amma abinda Yusuf ya kasa fahimta shine da ace zai iya rabuwa da wnn tunanin da tuni ya yakiceshi a zuciyarshi kodan shima ya samu sukuni Amma hakan ba mai yiwuwa bane,it’s not that easy ace ka rabu da abunda ka kwashi tsahon shekaru kana kauna,shi kanshi at times yakan ce zuciyarshi bata mai adalciba ta rasa wa zataso

duk fadin duniya sai yarinyarda ya raina a hannunsa,yarinyarda ta daukeshi matsayin mahaifi,so kuma mai tsanani irin wnn”Taheer”Yusuf ya katse mai tunani ta hanyar Kiran sunanshi,yq bude idanunshi da sukai ja yana kallon Yusuf din mgn yakesonyi Amma ya kasa,sai kawai ya komar da iadanunshi ya rufe tareda jingina da bayan kujera for some minutes snn yai gyaran murya a hankali yace”naji duk abinda ka fada friend and nasan gsky kke fadamin Kuma InshaAllah zanyi kokari inyi kmr yanda kace but please ka tayani da addu’a kaji,Ni kadai nasan me nakeji wlh InshaAllah Allahn daya doramin shi zai yayemin,,maganganunshi ba karamin tausayi sukaba Yusuf yai Dan murmushi yace InshaAllah zan tayaka and kayi kokari ka rage damuwan nn cox it will affect ur health,ya gyada mai Kai alamar zaiyi,ya jima a gidan don jiyayi bayason komawa gidan gaba daya,sai wurin 6 snn ya nufi gida,shima bai shigaba sbd anyi magrib yana hanya sai kawai ya wuce masjid bai shigo gidan ba Saida akayi

isha’i,,a hankali yake tafiya tamkar mara lfy har ya iso parlor,ummi ce zaune da system kan laps dinta tana video call Banda murmushi ba abinda takeyi,ya karaso ya zauna yana leka system din don ganin da wa take mgn,,wasu kyawawan yarane suka bayyana babban cikinsu baifi 15 yrs ba sai dayan da bazai wuce 12 sai Kuma ‘yar karamarsu da bazatafi 7 ba,yaran na ganinshi suka fara rige rigen Kiran daddy kowa na gaishesi,dukda bacin ran da yake tare dashi Saida ya saki murmushi yana kallonsu suka gaisa Yana tambayansu skul,babban cikinsu ne yace daddy next week zamuzo Abuja muma idan anyi holiday,still Yana murmushi yace to Allah ya kaimu Al’ameen ina maminku?tana kitchen,yaron ya fada,yana Shirin mikewa zai kirata sai gata ta fito ta zauna gefen yaran ta matso da system din gabanta yanda zata gansu da kyau tana kallon ummi da fara’a tace “ummina barka da dare,,barka dai nafisa ya gida ya yara?wlh alhamdulillah ummi muna nn zuwa next week da zaran yara sunyi

hutu,ummi tace to Allah ya kawoku lfy ta amsa da ameen ummina snn ta kalli Taheer dake kallonta shima ta daga mai gira tana fadin ba gaisuwa?ya zare ido sasai ya kalleta snn ya kalli ummi yace ummi kinji yarinyar nn wai Ni zan gaisheta niba yayanki bane?ummi ta tabe baki tace to mene ne idan ka gaishetan Taheer,,ya sake zare idon yace ummi qanwa tace fa,,to da take qanwarka ai tafika daraja ko a wurin Allah ynxu,kalleta fa da aurenta harda ‘ya’ya nta mene laifi idan ka gaisheta,ai ta karbe girman ynxu,,nafisa dake dariya tace yawwa fada masa ummina,itadai bata sake cewa komai ba ta mike ta barshi a wurin,ya janyo system din ya dora gab dashi yace wato rainin da kikaimin har yakai haka koh?tana dariya tace wasa nefa bro yanxu fadamin ya kke ya aiki,,aiki alhamdulillah ya kids dina,tace suna nn lfy Ina babyn taka yau ban ganta kusa dakai ba,ya Dan shafa Kai yace laifi tayi nake fushi da ita nasan tana daki a kwance,,nafisa tace haba koda naji,Ashe ana fushi da ‘yar lelen dama,dariya

kawai yayi yace kinga je kiji da yaranki nima ynxu xanje in kaimata abinci nasan duk yau bazataci komai ba indai bani na bata ba,,tace to ay shknn sai ka dawo ni yarana ba shagwababbu bane irin taka sai anjima,sukai sallama snn ya ajiye system din ya mike zuwa dinnig,abinci ya xuba a plate yasan for sure bataci komaiba yau ya nufi dakinta dashi,tana zaune ta hada Kai da gwuiwa sai kuka take,zuciyarshi ba karamin karyewa tasoyi ba ganinta a haka Amma ya daure ya karasa ciki,Saida ya ajiye abincin kan stool snn yace”zo kici abinci”ta dago da sauri don bataji shigowarshi ba,ta matso a hankali ta sauke legs dinta kasa tana share hawaye tana kokarin mgn yace I don’t want to hear anything,just eat,ta sunkuyar da kanta tana shesheka kafin a hankali ta faracin abincin kmr tanacin magani Kuma bata bar hawayen da takeba,,duk yana jinta yai pretending sai Danna waya yake yanata yaki da tausayinta dayakeji,,kadan taci tace ta koshi yace saita Kara haka nan da kyar yaci rabi tace ya isa,bai Mata musuba ya bata ruwa Tasha snn yace shiga kiyi brush ki fito Ina jiranki,,jiki ba kwari ta nufi toilet tayo brush din kafin ta fito ya dauko Mata sleeping dress ta karba tana Shirin cire kayan a gabanshi yace shiga bayi ki cire,,nn ma ba musu ta shiga tasa kayan ta fito”kwanta”ya fada yana nuna Mata godon,a hankali ta hau ta kwanta ya janyo duvet ya rufeta dashi yai addu’a ya tofa Mata kmr dai yanda ya saba snn ya kashe wutan dakin ya fita,aiko Yana fitata sake rushewa da kuka,,shima dakin ummi ya shiga yi Mata Saida safe tace Layla fa takicin abinci babu yanda banyi da itaba wlh takici wai batada lfy,nadai bata paracetamol nace ta kwanta idan ka dawo saika dubata,yace eh na bata drugs ynxu,,to taci abincin ne?shima taci nasan ynxu bacci zai dauketa,,to Allah ya sawake kaima ka kwantar da hankalinka don Allah zata samu sauki ai naga duk ka zama kmr mara lafiyan kaima,yace InshaAllah ummi Saida safe,Allah ya tashemu lfy,har ya fita ummi na binshi da kallo tasan for sure wani abun na damunshi.

Daren nan dai dagashi har ita ba Wanda ya samu baccin kirki,shi ya kwana tunanin maganganun da sukai da Yusuf tareda neman mafita ita Kuma ta kwana tana kukan fushin da yakeyi da ita dama duk ranar daya dauke mata wuta haka take rasa sukuni har sai sun shirya.

Wurin karfe sha daya yana tsaye gaban mirror yana combing gashinshi yayi kyau sosae cikin faran shirt daya Dan kama jikinshi long sleeve,sai trouser dinshi black,dogo ne sosae irin mazan da ake cema masu zatin jiki,kalan fatanshi ba me haske ba Kuma ba fari tass ba,yanada manyan idanu farare qal dasu sai dogon hanci dayai daidai da fuskarshi,bakinshi madaidaici sai qasimba me daukeda gemu da suka sake qawata fuskan nashi,ya gama ya feshe jikinshi da designer perfumes dinshi ya dau phone dinshi snn ya fita zuwa part din ummi,tana zaune parlor suna kallo itada Mama hauwa,ya gaishesu Yana kokarin zama ummi tace Layla fa batayi bacci ba jiya,bayan ka tafi naje dakin zazzabi ya rufeta sosae dashi ma ta kwana wlh,sai safiyar nn baccin ya dauketa,,da sauri ya mike yana dafa goshi yace ya Salam!meyasa baki kirani ba ummi,,ita ta hana in kiraka wlh wai kar in tasheka a bacci gaba dayama ta hanani tashi in dauko wayan wai bazan barta ita kadai ba,ya nufi dakin da saurinshi ya shiga,tana kwance tsakiyar gado tana rungume da teddy dinta,,lokaci daya murmushi ya kubce mai,ganinta kawai can flush his sadness,a hankali ya zauna gefen gadon yana kallon duvet din data tattareshi gefe,murmushi ya qara saki ya rasa me yasa batason lulluba ba ko kadan,haka take tun tana karama,lokacin tana kwana tare dashi yana lullubeta dama zata yaye,ya shafa kanshi yama nemi bacin ran da yake ciki yarasa,dama yasan fushin nashi ba wani tsayi zaiyi ba yamayi kokari daya iya jurewa har haka,yakai hanu yana feeling temperature dinta yaji normal ya sauke ajiyan zuciya me karfi ta farka firgigit don kmr a mafarki taji ajiyan zuciyan nashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button