Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari….

Taheer na zaune parlo shida ummi ya gama shirinshi tsaf…Layla ta fito daga dakinta itama ta gama shiryawa hanunta rikeda Arabian gown dinta da zata Sanya gobe…sai pant da bra dinta data Dora kan rigan…..ta karaso parlon tasa hannu ta dauko Dan jakan da Taheer yasa kayanshi a ciki ta shiga sa natan a ciki itama…ummi daketa kallonta da mamaki taja tsaki tace”kedai zanga ranarda Zaki nutsu kisan kin girma Layla…ynzu breziern ne kika dakkoshi haka gagal gagal ko Dan sakayawa babu??..Layla na cigaba dasa kayanta a jakan tace”to ai naga ba kowa a parlon dagake sai daddy fa….ai ba kunyanku nakeji ba…ummi ta girgiza Kai kawai tace”Allah ya kyauta…Taheer dake nan zaune yana jinsu murmushi kawai yai don baisan me zaice ba….suna gamawa driver yayi dropping nasu a airport suka shiga jirgi zuwa Birnin dabo.

Bayan isansu kano gidan umma suka sauka…saida sukaci abinci suka Dan huta snn driver dinta ya daukesu zuwa jigawa….basu saukaba sai around 4 na yamma….bayan driver yayi parking suka nufi entrance din gidan….wata mai aiki ce ta bude musu kofa bayan Danna door bell da sukayi….tayi musu iso zuwa central parlor snn ta tafi Kira musu matar gidan….bayan mintina kadai sai gata ta sauko daga sama….dattijuwar Mata ta karaso parlon da fara’arta suka gaisa da Taheer….snn ta kalli Layla tace to tsohuwa da fatan dai ba zama kika zoyi gidana ba….Layla na murmushi tace”ay idan baki wasaba har mijin kima sai na kwace kafin na bar gidan….matar ta zaro ido tace”lallai Layla kinyi baki yanxu….ya ummin taki…ummi na nn lfy tace a gaisheki…tace Ina amsawa bari ayi muku mgn da alhajin….ta mike xuwa sashen maigidan nata….bayan minti kaman biyu ta fito tace musu bismillah muje….sukabi bayanta har zuwa part din….yana zaune kan daya daga cikin royal chairs din dake parlon….dattijo ne wanda kallo daya zakamai kagano yanada tarin ilmi….bayan sun zauna Taheer har kasa ya durkusa ya gaidashi hakama Layla da yaketa faman tsokanarta wai bata ajiye komai ba sai tsayi….hajiya ta mike tacema Layla”to tashi muje ‘yar nema ki barsu suyi mgnrsu…ba musu Layla ta mike suka fita tare….alhaji na kallon Taheer yace”yanzu ka fara huta gajiya Taheer….in anjima sai muyi mgn….shidai Taheer ba haka yaso ba….kmr yace baya tareda gajiya Kuma yai shiru….alhaji ya daga waya ya Kira wani….bayan few minutes wani saurayi ya shigo dakin….kyakykyawa dashi ya risina ya gaida Taheer snn alhaji yace”yawwa Usman ka kaishi masaukinshi snn ka tabbatar ka Kai mai duk abinda yake bukata…Usman ya amsa snn ya dauki jakan dake gefen Taheer ya fita….a hankali Taheer ke binshi a baya baisan dalilinda yasa jikinshi yai sanyi hakaba….ya kagu yaji wani mgn ne zasuyi….boys quarter Usman ya kaishi….Saida ya tabbatar ya mai duk wani abu daya kamata snn ya mai sallama ya tafi….Taheer kwanciya kawai yayi yana tunani sai can ya dauko waya ya sanar ma ummi sun sauka snn ya Kira umma itama ya fada Mata ya sake komawa ya kwanta.

Layla kuwa tana can sashen kakarta sai labarai take bata ita Kuma tanata faman dariya….mahaifinta ya Kira a wayar kakar bayan sun gama gaisawa dasu Al’ameen tace mai ga Layla ma sunzo dazu itada uban nata….Layla ta wani turo baki tace ni ki dena cewa ubana….babana zakice ko daddyna….in kikace ubana kmr zagi nefa….hajiya ta Mika Mata wayar tace ungo ni uwar kinibibi….bazaace daddyn naki ba….Awwal dake jinsu ta waya murmushi kawai yake…Layla ta amsa wayan da fara’arta tace Abba Ina yini….yace”ba wani Ina yini keda ko nemana bakyayi…ta zaro ido tace”Allah Ina nemanka Abba…idan tafiyane bana samunka a waya shiyasa…yace shknn ai Ina daddynki….tace”daddy Yana nn lfy abba tare mukazo nan dashi….yace iyye yar gidan daddy wato ko Ina sai anje dake koh…tana dariya tace eh mana….daddyna yanaji Dani sosae…haka sukaita hira da mahaifinta daga baya su Al’ameen suka amsa nanma suka cigaba da hirarrakinsu sai da akai magrib snn sukai sallama.

Bangaren Taheer ma bayan ya dawo daga sallahn magrib kwanciya ya sakeyi…bai San meyasa har ynxu yakejinshi very week ba…bai dade da kwanciya ba aka kawo mai abinci da drinks kala kala amma babu abinda ya taba…ana Kiran isha’i ya sake mikewa zuwa masjid dake nn kofar gidan.

Bayan sun idar tare suka dawo da alhaji da kuma Usman…shi usman ya shiga part din hajiya yayinda Taheer Kuma yabi alhaji zuwa nashi part din…bayan sun zauna alhaji na fuskantar Taheer yace”dama wata mgn ce muhimmiya nake muyi dakai Taheer…da kaina naso zuwa Abuja in sameka sai wani al’amari ya bullo Wanda shi hanani zuwa…Taheer da ya matsu su fara mgnr yace”ba komai alhaji…ai nine ya kamata inzo dama tunda nine karami…Kuma kmr mahaifina na daukeka…. don haka duk lokacin da kakeson gani na just give me a call ni Kuma zanzo InshaAllah…Alh ya jinjina kai cikeda gamsuwa yace hakane Taheer….na Kuma gode Allah ya saka ma da alkhairi…Saida ya danyi shiru ya fara mgn kmr haka”dama mgn ce akan ‘yar wajen taka…wnn yaro Usman shine yazomin da batun yanasonta da aure….da farko ban bawa mgnr tashi muhimmanci ba Amma da naga yanda ya damu Kuma yakemin magiya naga ya kamata in duba…wani irin faduwar gaba ya riski Taheer a lokacin…ya sunkyar da kanshi qasa yana mai karanto sunayen Allah a ranshi…alhaji ya gyara zama snn yaci gaba”Taheer kar kace zaka duba alakar dake tsakanina da yarinyar nan…aah ka daukeni a matsayin wanda yake nemawa dansa auren ‘yarka….kaga yaron nan maraya ne…nina haifi mahaifinsa snn tun rasuwar mahaifin nashi ni na rikeshi snn namai tarbiyya…don haka bashi da Wanda zai shigemai gaba kan mgnr nn sai ni….amma hakan ba yana nufin ayima yarinya doleba Sam ba haka bane….kafin ma mgn yaje kunnen yarinya inaso Kai ka fara dubawa ka gani…a matsayinka na uba Kuma waliyyi a gareta…kayi bincike kmr yanda addinin musulunchi yace ayi…idan har Usman bayada qualities din da zaka dauki yarka ka bashi…to kar kaji komai ka sanar dani kuma nayima alkawarin cewa bazan taba ganin laifinka ba…sbd nasan irin sonda kakema yarinyar nn…. Kuma bazaka taba zaba Mata abinda zai cutar da itaba…sbd haka kar kaji komai…ni matsayin dana na daukeka…don haka na baka lokaci kaje kayi tunani…snn nafiso itama yarinyar ta farajin mgnr a bakinka tunda tafi sabawa da Kai…Kuma idan har bata aminceba to bazaa taba yi Mata dole ba…nasan kuma bai zama lallai kanada burin yi Mata aure nan kusaba….don haka koda an daidaita…to bazaayi aureba har sai zuwa lokacinda kaji zaka iya aurar da ita sai ayi sbd bana son a shiga hakkinku…Allah ubangiji ya zaba mana mafi alkhairi….Taheer tunda ya sunkuyar da kai bai sake dagowaba…zuciyarshi yaji ta tattare waje daya kmr ta dena aiki….jin alhaji yayi shiru ya samu ya tattaro ragowar nutsuwarshi yana murmushin yake yace”na gode sosae da wnn karramawar taku a gareni…Allah ya saka da alkhairi…Kuma InshaAllah zanyi tunani kmr yanda kace snn in har baby ta amince nima na amince ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi…na gode kwarai…ya karashe mgnr cikin sanyi…nan alhaji shima yai masa godiya snn ya mike yace zaije ya kwanta…sukayi sallama da alhaji snn ya fita…har zai nufi masaukinshi ya tuna ummi tace ya hadata da Layla suyi mgn….sai kawai ya nufi part din…yana shiga parlor abinda idanunshi suka gani yaji kafafunshi sun kasa daukanshi…yai saurin zama kan kujera dake kusa dashi yana kokarin saita kanshi..
Layla ce zaune a parlon kanta ba dankwali itada Usman din da yasan yana sonta…da sauri Layla tazo inda yake tace daddy baka da lfy ne??kasa cewa komai yayi kawai ya mike yana takawa a hankali ya fita a parlon…yana isa masaukinshi ya fada kan gado tareda lumshe ido…wasu hawaye masu dumi suka shiga bin kuncinshi…a hankali yakai hannu fuskanshi ya taba yaji fa tabbas hawayene yakeyi…hawayen tausayin kanshi…ya tabbata yanason abinda bazai taba samuba…idan ya tuno maganganun da alhaji ya fada sai yaji zuciyarshi ta sake tsinkewa…irin kara da mutanen nn sukamai ai komai sonda yake ma Layla basu cancanci ya musu butulci ba..sbd sun fishi iko da Layla amma basu yanke hukunci Kai tsayeba sai da aka kirashi snn Kuma akace shi zaiyi deciding idan zai bada aurenta idan ma bazai bayarba….ya sani Yana son Layla Amma baya ganin sonda yake Mata zai kaishi ga aikata tsantsar butulci irin haka…yes zai bashi ita kmr yanda suka bukata amma Kuma yasan tamkar tashi rayuwar zai dauka ya bayar…ya sake lumshe ido har yanxu bai Dena hawayeba daya tuno a yanayin da ya samesu zaune a parlor sai yaji kmr ya cire zuciyarshi ajiyeta gefe…yanxu tana can tana hira dashi…ya gama ganin gashinta maybe har rike mata hannu yayi…”innalillahi wainna ilaihi rajiuunnn”ya fada da karfi yayinda yake buga kanshi da jikin gado…sam bayason zuciyarshi ta dinga ayyana mai abubuwa irin haka don a yanda yakeji din nn zai iya hadiyan zuciya ya mutu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button