Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari ma da kanshi ya taimaka Mata tayi wanka snn ya sake sawa ta shiga ruwan zafi..shi yayi mata komai har Shirin tafiya school…ita kuma har yanxu bata dena kumbure kumbure tana fadin jikinta na mata ciwo ba..Taheer saidai yayi dariya kawai hadi da girgiza kai…rigimar baby sai ita wlh.

Tun dazu yake zaune cikin mota yana jiranta..daga taje ta dauko hijab su tafi shine har yanxu bata fito ba kusan minti biyar yana jiranta…ya duba agogon hanunshi yana sauke numfashi..bai son yai lattin zuwa clinic don yanada abubuwan yi sosae…can sai gata ta fito bakin nn a tsuke..Taheer ya bita da kallo mayafi ta yafa orange Wanda ya shiga da riga da skirt na atampa dake jikinta maimakon hijab da yace mata…Saida ta karaso inda motar ta bude ta shiga snn yace”baby wnn ne hijab din Kuma”..tana sake turo dan bakinta tace”daddy ni jikina namin ciwo..idan nasa hijab nauyi zaimin wlh..so plss let me”…Taheer ya jinginar da kanshi kan kujera yana binta da kallo..dukda ba make up tayi applying sai yaga tayi mai wani shahararren kyau kmr tayi heavy make up..uwa uba daurin dankwalinta daya zauna das a kan nata sai kace ba hannu ne yayi shi ba…bai sake ce Mata komai ba ya kunna motar suka tafi…har ga Allah ba da son ranshi zataje makaranta a haka ba..yasan ba kowane namiji ne zai iya dauke ido a kanta ba..amma bazai iya da rigimarta ba..yasan duk tanayi ne sbd taji haushin wahalan daya bata jiya…haka yaita Satan kallonta yana danne dariya dakeson kufce mai..ita wai bata yadda ba ta daure fuska????

12 saura ta kirashi a waya tace mai ta gama abinda zatayi yazo ya kaita gida…yace Mata gashi nn zuwa…ba bata lokaci kuwa sai gashi yazo…maimakon su nufi gidan ummi kmr yanda tayi tunani sai taga sun dauki wani hanyan.. tana dubanshi tace”daddy Ina Kuma zamuje..ummi fa tace ka kaini gida”…yana cigaba da tukinshi yace”zan kaiki mana baby amma ba yanxu ba..so nake sai dare idan mukayi picking su Nafeesa daga airport sai mu wuce gidan gaba daya”…ta marairaice mai tace”nidai dn Allah daddy ka kaini ynxu”.. ya juyo ya dan kalleta snn yace”baby kin gaji da ganina koh..Ina takura maki abi?..”tace”Ni ba haka nake nufi ba..kawai dai inaso inje gidan ne”..Taheer shiru yayi mata..kmr bazai sake mgn ba sai can Kuma yace”to ynxu muje wani wurin muci abinci..muna gamawa sai mu koma gida ki hada kayan naki sai in kaiki can”.. Kai kawai ta daga mai tareda kwanciya kan seat din da take..har yanzu bata bar jin jikinta kmr anyi mata dukam tsiya ba..ba karamin wahala tashaba jiyan nn..dukda bai kai na first encounter dinsu ba still tanajin jikinta a gajiye..ga bayanta da cinyanta har yanx basu dena yi mata ciwo ba..ta lura gaba daya daddy ficewa hayyacinshi yakeyi duk yake mu’amala da ita… murmushi ta saki data tuna mgnr da suka tabayi da Hanna…wai idan mijinki bai takura maki baki cika a kiraki da mace ba…haka tayita sake sakenta har suka isa wani restaurant mai kyau..bayan ya samu wuri yayi parking sai ya bude mota ya fita…ta bude ta fita itama snn suka shiga ciki.

Karfe 8 daidai yayi musu a airport don daukan su Nafee… jirginsu bai sauka ba sai 8:15..suna nn zaune cikin mota mutanen dake cikin jirgin suka fara fitowa…Taheer ne ya fara bude motan ya fita snn ya bude mata itama ta fito…yaran ne suka fara hangosu…aiko sukayo wajen da suke da gudu..gaba daya kan Taheer sukayi suna rungumeshi kowa yana fadin”daddy..daddy”…shima rungumesu yayi sosae yanabinsu da kiss a goshinsu daya bayan daya..Nafeesa ma ta karaso inda suke face dinta da murmushi tace”angon baby”.. Taheer ya dan kalleta ta gefen idonshi yana dan kauda Kai…wai ita batasan yanajin nauyinta bane..shi kanshi bai taba tunanin akwai rananda zatazo yaji yanajin kunyar Nafeesa ba..yarinyar da suka taso tare tun suna kanana..ya tuna irin fadan da sukeyi tun da can…ya saki wani murmushi yana shafa kanshi..bai taba tunanin Nafeesa ce zata haifi macen da zaiyi ma matsanancin so irin haka ba..ko da yake Allah ba yanda baya al’amuranshi…Layla ce ta karasa tareda daukan hibba dake kusada Maman nata tana fadin”Mami sannunku da zuwa”… Nafeesa na gyada kai tace”yawwa”..shi Kuma Taheer ya bude ma yaran mota suka shiga..itama Nafeesan ta shiga..Layla da shi duk suka shiga snn yaja motar suka bar wurin.

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

44

Suna isa gida yaran suka bude mota suka shiga ciki a guje..Taheer ya fito tareda zagayawa ya budema Layla itama ta fito…Nafeesa dake kallon abinda yakeyi tai murmushi kawai tana girgiza Kai..wai yarinya karama yakema wnn abun sai kace wata babba.. ta bude itama ta fito..tare suka nufi entrance din gidan..

Su ummi na zaune parlor da alama dama suna jiran zuwan nasu ne…yaran ne suka fara shiga snn suma suka shigo..Kai tsaye Nafeesa ta karasa inda ummi take ta bata kyakykyawar runguma tana fadin”fatan mun sameku lfy ummina”…itama ummi ta rungumeta tana cewa”lfy Lou muke Nafee”..sai Kuma ta saketa ta shiga dube dube tace”ina wnn mara mutuncin take”… Al’ameen ne yace”gata can a bayan daddy”…ummi tasa hanu ta janyo Hibba dake boye bayan Taheer tace”zo nan don gidanku..ke baki iya gaida mutane bane..duk yayyenki sun gaisheni kece mara kunya koh”…gaba daya suka sa dariya…bayan sun zauna gaba daya suka shiga gaisawa dasu ummin…Taheer ya mike ya fita tareda su Al’ameen suka shigo musu da kayansu ciki…daga nn Kuma suka nufi dinning sukayi dinner tare..sunayi suna dan taba hira..shikam Taheer kacokam hankalinshi na kan babynshi…kawai tunanin yanda yau zai kwana ba tareda itaba yakeyi…Anya kuwa zai iya..tunda akai bikinsu zuwa yanxu in ka cire case dinsu da AY bai taba kwana ba tareda itaba..ko a wancan karon ma yaji jiki balle yanxu da suka riga suka zama daya..duk sai yaji abincin ma ya fita a ranshi..Sam bai wani ci sosae ba ya mike tareda komawa parlor..
Bayan sun gama suma duk parlon suka koma..nan Kuma aka sake dasa sabon hira kmr irin sun shekara basu hadu ba…umma ce ta lurada yanda Taheer duk baida walwala sai tace”kai lafiyanka kuwa”..maimakon yayi mgn sai ya karyar mata da kai kmr karamin yaro.. exactly yanda yake mata idan yanaso ta tausaya mishi… murmushi kawai ummi tayi don tasan da kyar idan ba kan tafiyansu da Layla yake wnn abun ba…sai ta mike tareda kama hanunshi shima ya mike..tace”muje ka fadamin menene matsalanka”…haka Taheer ya shiga binta a baya kmr bindi…ummi da Nafee suka bisu da kallo..ummi na tabe baki tace”ai ko me zakayi saidai kayi wlh..baka isa ka hana yarinyar nn zuwa bikin ‘yar uwarta ba”…Nafee tace”ummi hanata zuwa yayi”… still bakin ummi a tabe tace”yo meye banbancin abinda yake shirinyi da hanata zuwa din..wani wai bazamu tafi da itaba saidai in zaizo daurin aure ran asabar ya tafi da ita..ranan lahadi kuma ya sake dauko kafa ya dawo da ita..sbd ance mai na farajin tsoronshi”…Nafeesa dariya ta danyi kafin tace”Ummi da kin barshi Mana..matarshi ce fa”…itama harara ta samu daga wurin ummi tareda fadin”bai isaba wlh..ko zai mutu sai mun tafi da ita gobe”

Suna shiga daki umma ta zaunar dashi itama ta zauna snn tace mai”to inajinka..menene matsalan”…Saida ya narkar da murya kafin yace”umma dan Allah kicema ummi ba sai kun tafida baby ba..tsakani da Allah umma har tsawon kwana nawa akeso inyi ba tareda itaba..ni bazan iyaba wlh.. dn Allah kuje ku kadai abinku.. inyaso mu sai mu taho ranan Friday”…dariya umma ta saki dama tatsuniyar gizo ai baya wuce koki…ta kama kunnenshi da kyau snn tace”wato ko kunyana bakaji koh”…Taheer ya kama hanunta dake rikeda kunnen nashi yace”auchh umma akwai zafi”…”zafin nakeso kaji dama ai”umma ta fada tana sakin kunnen nashi…shiko yana shafa kunnen ya sake cewa”Allah umma da gaske nakeyi..yanxu gobe Wednesday ni kuma bazan zo bafa sai ranan Saturday.. seriously bazan iya spending 3 whole days without seeing her ba..do something plss”…da mamaki sosae umma ke dubanshi tace”ban san yaushe ka zama mara kunya haka ba wlh..ynxu kwana ukun kakema wnn abun sai kace shekara uku”…cikin zuciyarshi yace”umma bazaki gane bane”..a fili Kuma yace”nidai umma do something plss..ki taimaka kima ummi bayani”…umma ba tace komai ba Saida ta mike..tana kokarin fita daga dakin tace”to tashi muje ka fada Mata da bakinka”…Taheer ya zaro idanu waje yace”kema kinsan rufeni da fada zatayi”…umma tace”to shawaran da zan baka shine kawai kayi hakuri..tun jiya nace mata ta bari ku taho tareda ita amma taki yadda..Kuma kasan halin Yaya da kafiya..so gara ma ka sama ranka dangana tun yanxu”…tana gama mgn bata jira me zai ce ba ta fita daga dakin…Taheer ya shiga hargitsa gashin kanshi yayinda ya bita da ido har ta fita….da kyar ya mike shima ya fita daga dakin…Yana isa parlor ummi tace”Kai wai sai yaushe zaka tafi gida ne..dare na karayi fa”…tana rufe baki yace”a nan zan kwana ummi”…tana binshi da kallon mamaki yace”a nan zaka kwana Kuma”…Taheer ya daga mata Kai..ummi kmr zata sake mgn sai kuma ta fasa ta cigaba da hiran da sukeyi itada Nafeesa…shiko Taheer idonshi na kan Layla dake nunama su Al’ameen abu a wayanta ya fita daga parlon…Kai tsaye part dinshi ya nufa don da gaske bazai iya komawa yaje ya kwana gidanshi while ita Kuma tana nn gidan ba…da zaa mai adalci sai a turo mai ita ace suje su kwana tare amma yasan ba Wanda zaiyi hakan..Saida yaje part din nashi ya tuna bai amso key a wurin umma ba…dan tsaki yaja snn ya sake juyawa ya nufi part dinsu…wnn karon Al’ameen da Ramadhan kadai ya samu a parlor… yana dubansu yace”Ina baby take”…Ramadhan yace”ynxu ta shiga dakinta”…tun kafin Ramadhan ya rufe baki ya kama hanyar dakin nata da sauri…Yana budewa kuwa ya ganta a ciki ita kadai..tana kokarin cire kayan jikinta…”am one lucky man”ya fada yayinda yake karasawa kusa da ita…Layla na ganinshi ta zo inda yake tareda juya bayanta tace”daddy budemin zip dina plss”…baiyi mgn ba yasa hannu ya bude mata zip din..ta juya zata koma inda kayan nata suke kawai taji ya kamo waist dinta da both hands dinshi…ta juyo tana kallonshi a marairaice tace”daddy plss..kayana fa nakeso in cire”…still baice komai ba yasa hannu ya shiga cire mata rigan nata a hankali..ya zare both hands dinta daga ciki snn ya cire rigan gaba daya daga jikin nata..ya zama daga ita sai bra..sai Kuma skirt dinta…ya sake sunkuyawa a hankali ya bude zip din skirt din shima ya shiga janyeshi daga jikinta a nutse..saida ya saukeshi har kasa snn yasa hannu ya dagata sama cak..skirt din ya fita daga kafafunta snn ya ajiyeta gefe..ya risina tareda dauko skirt din sai ya karasa gefen gado dasu a hannunshi..ya zauna snn ya fara ninke Mata kayan..yana gamawa ya ajiyesu nn gefe snn ya maido da idanunshi kanta…tana nn tsaye kmr gunki daga ita sai pant da bra a jikinta tana binshi da idanu kawai..ita kanta tunanin yanda zata debi tsawon kwanaki haka ba tareda Shiba takeyi..ya riga ya sabar mata da kwanciya a jikinshi always…ta saba da yanda yake kulawa da ita kmr baby..ta saba tayita mai shagwaba yana biye mata..tasan definitely ba karamin missing dinshi zatayi ba…tana tsaka da tunanin kawai taji yayi sama da ita..Saida ya koma gefen gadon ya zauna snn ya dorata kan laps dinshi tareda rungumeta tsam a kirjinshi… idanuwanshi lumshe yana shaqan daddadan kamshin da gashinta ke fitarwa muryanshi a shake yace”baby plss..kar ki tafi ki barni don Allah..i can’t live without you..kiyi wani abu plss”…muryanta very low itama tace”nima ban San me zanyiba daddy..am going to miss you too”…Taheer ya dago idanunshi da suka kada sukai jajir sbd wata wutar fitina dake cinshi…ya kamo fuskanta ya hada da tashi…still muryanshi can kasa ya sake cewa”kawai cewa zakiyi bazaki bisu ba shknn..kina fadan haka nasan ummi zata kyaleki..ko kinaso kije ki barni ni kadai ne”…ta girgiza mai kai a hankali…yace”then do something..kiyi wani abu indai ba so kike inyi sabuwar budurwa ba idan kin tafi”…da sauri ta bude idanunta tana kallonshi..ta tsuke baki kmr zata sa kuka tace”Allah ban yadda ba..kuma wlh kanayin budurwa na dena kulaka infact kwaso kayana ma zanyi in dawo nn gidan”…ta karasa mgnr tareda murguda dan bakinta da tun dazu Taheer yai kurii yana kallonshi..ya lumshe ido tareda dora lips dinshi kan nata..itama lumshe idanun nata tayi luf as tanajin dadin yanda yake sarrafa bakin nata..har ga Allah bata isa tace daddy is not romantic ba..he is extra romantic.. kawai dai tanajin zafin abinda yakeyi Mata kuma ga tsoro shiyasa bata cika sakin jiki har da zataji dadin abin da yakeyi din ba…sun dauki almost 10-12mins suna abu daya…da kyar Taheer ya raba bakinshi da nata gudun kar yakai limit dinda bazai iya controlling kanshi ba Kuma..yasan wani na iya shigowa dakin at any time so yayi stopping kanshi ba don yaso ba…rungumeta ya sakeyi a jikinshi yana sauke numfashi da sauri da sauri…idanuwanshi rufe yanajin tamkar ya zubar da hawaye yace”bazan iya spending almost a week ba tareda keba baby..I just can’t..do something dn Allah”…Layla ta zame jikinta daga nashi..tana goge tears dake fitowa idonta tace”badai cewa kayi zaka sake budurwa ba..dena kulaka zanyi wlh”…ta karasa mgnr tana kokarin mikewa daga jikin nashi ya dawo da ita da sauri..ya sake matseta sosae..dukda he’s emotional hakan bai hanashi dariya ba..duk tace ta dena kulashin nn dariya take bashi wlh..but he’s happy she’s jealous..at least yanxu yasan bashi kadai yake kishinta ba..itama tana kishinshi and he’s happy to know that…Layla ta shiga mutsu mutsu tanason barin jikinshi..tana kuka tace”let go of me daddy..ka sakeni inyi tafiyana ni”… maimakon ya saketa sai ya sake Rungumeta gam…still yana smiling yace”ohk ohk naji..am sorry da wasa nake maki..kema dai kinsan bazan taba kallon wata mace da sunan so ba baby..not after inada kamarki..so stop crying kinji”…bata sake yin mgn ba..ta dai dena kukan da takeyi..a hankali tace”to ka sakeni insa Kaya kar wani yazo ya sameni a haka”…baiyi musu ba ya saketa snn ya mike zuwa inda kayanta suke…cotton dogon riga ya dauko mata armless mara nauyi..ya dawo inda take tareda kamota ya shiga sa mata rigan da kanshi..tayi shiru tana binshi da kallo har ya gama sa Mata..ya kamota tareda manna Mata kiss a forehead dinta yana fadin”you look gorgeous my baby..I love you”…Layla ta saki kasaitaccen murmushi itama tace”I love you more..yanxu kazo ka tafi daddy kaga ummi zata iya shigowa”…ya kama hanunta suka fita dakin yana cewa”baby muje ki tayani bacci dn Allah kinji”…ta zaro idanu tana dariya tace”Tabb..kanaso ummi tayi min kaca kaca knn”…shima dan dariyan ya saki jin abinda ta fada..wai kaca kaca…suna zuwa parlon suka samu duk sun dawo..su Al’ameen ne dai duka tafi daki suka kwanta…hanunta cikin nashi suka karasa ciki…ummi tabi hannayensu dake sarke da kallo kafin tace”ikon Allah..kai Kuma daga Ina..ba munyi sallama dakai ka tafi ka kwanta ba..me Kuma ya dawo dakai nn”…Taheer ya shafa goshi jin tambayoyin da ummi ke jero mai..sai kace ba ita ta rike mai matarshi ba…a zuciya yace”ki bani matata mana kiga bazaki sake ganin keyana ba sai garin Allah ya waye”..a zahiri Kuma ya nuna Layla da hanunshi cewa yai”Kaya na bata ta canza ummi..zamuje mu kwanta”…ummi ta zaro ido tace”la’ilaha illallahu muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasallam..kai wai meke damunka ne..meya shiga kanka haka..yanxu Taheer ko kunya babu kake duban tsabar idonmu kana wani cewa zakuje ku kwanta..to ka saketa snn ka wuce ka bar min parlor tun ban gaggala maka mari ba wlh..fitsararre kawai”…a hankali Taheer ya saki hannun Layla dake cikin nashi snn ya fita daga dakin..ko key din ma bai karba ba aka koroshi…saiya Kira umma a waya yace ta bada key din a kawo mai.
Bayan fitanshi Nafeesa da taji kunyan abinda ummi tayi mai…tana duban ummi tace”ummi da baki mai haka ba wlh..ni tausayi yake bani..kuma meye amfanin ajiyeta a nn tunda gashi yana gidan”…ummi tace”ni rashin kunya ne banso..dubi fa ya ketare mu yabi yarinyar nn har daki sbd bashida ta ido”…sai ta maida kallonta ga Layla dakejin kmr tasa kuka sbd abinda ummin tayi mai..tace”kema kuma kika biye mai sbd ba kunyan ne ya isheki ba koh”…batace komai ba sai ma mikewa da tayi ta koma daki abunta… ummi ta rakata da harara tana tabe baki tace”ba laifinki bane wlh..duk shi ya lalata ki da dabi’unshi..duk halayen Taheer ba wanda ta mance bata dauka ba..Allah ya shiryeku”…Nafeesa shiru kawai tayi hadda su tagumi tana kallon ummi da karfin hali…ita kuwa umma mikewa tayi tana dariya kasa kasa..ta tafi daki don dauko mai key din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button