Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bayan Wasu Shekaru…

A takaice dai rayuwar auren Layla da Taheer rayuwa ce da suka ginata kan soyayya da Kuma kulawa da juna..rayuwace sukeyinta na tsakani da Allah babu munafurci Kuma babu ha’inci a cikinta…suna matukar so da Kuma kulawa da junansu sosae…Layla ta kammala karatunta inda tayi specialising bangaren gynecology…yanxu hake she’s a medical doctor and sunyi aiki tare da Taheer a Clinic dinshi…kafin daga baya ya bude Mata Clinic nata na kanta itama take running dinshi da sauran employees dinta…rayuwarsu na tafiya cikin farin ciki da kwanciyan hankali…

Yanxu Layla ta zama big madam don yara hudu gareta..bayan Nawal Saida tayi maza biyu snn ta kara mace guda daya…akwai mai sunan dad din Taheer ana ce mishi khaleel…sai Abdallah sai Kuma auta mai sunan Nafeesa ana kiranta Neehal…gaba daya yaran Kuma da babansu suke kama haske ne kawai suke dauko na Layla..banda Khaleel dake kamada Taheer sak..hatta skin colour dinshi irin na babanshi ne…wani lokacin Layla saita zauna tayita kallonshi don har acting dinshi irin na Taheer ne..ita Kuma Neehal ce ta dauko rigimanta…halinsu iri daya itama da Layla shiyasa wani lokacin Taheer ke kiranta da His little baby…su Nawal Kuma yanxu an girma don mostly ma bata cika zaman gidan ba…idan umma ta Kira tace a kawo Mata namesake dinta haka Taheer zai sauketa ya kaita ba don yanaso ba..shi Sam baison rabuwa da ‘ya’yanshi..

Yau Friday Layla ta tashi daga aiki 12 sbd tanaso taje gidan ummi ta dubata da jiki don tayita fama fever kwana biyu…Saida ta tsaya tayi picking yaranta a school snn suka nufi gidan..shima Taheer zaizo after Jumu’at prayer…tunda suka isa gidan yaran suka shiga da gudunsu suna rungumar su umma dake parlor suna musu kiss suna fadin”we missed you grannies”…Nawal kam tana makale jikin umma da take kirada Namesake…ita Kuma ummi tana zaune sai tabe baki take tana cewa”Yaran Taheer Kuma dama idan basuyi haka ba wane zaiyi ni Maryam…idan basu iya runguma da kissing goshin mutane bama ai Allah saiya tambayesu tunda ba abinda ubansu ya iya sama da wnn..banajin duk duniya akwai Wanda ya kaishi iya kissing da hugging din mutane”…umma na dariya tace”Kai Yaya..shi hugging da kissing din ai sign of love ne..so banga laifi a ciki ba..besides itama Layla tanayi ai..ba Taheer din ne kadai ya iya ba”…ummi dai tabe baki tace”ai dama baki son gaky Aisha..Sam bakison kiji an Fadi laifin Taheer..Kuma dai Shiba waliyyi ba dole Yana yin ba daidai ba”…Layla dai na gefe tana ta musu dariya..sauran yaran suma suna tayata..

Karfe biyu daidai Taheer ya shigo gidan..da gudu yaranshi suka fita sunajin dirin motanshi…Layla ta bisu da kallo with so much love..sun riga sun saba ko a gida dama Yana dawowa har rige rigen tafiya mishi oyoyo akeyi..ita kanta daurewa kawai tayi taci gaba da zama amma da a gida suke Kam itama binsu zatayi…
Taheer bayan yayi parking ya fito sai ya shiga daukan yaran daya bayan daya hugging da kissing dinsu..suma suk suna maida mishi da martani…Saida suka gama rungume rungumensu snn ya jasu suka shiga cikin gidan…Yana shiga ya saki hannun yaran tareda karasawa inda umma take yayi hugging dinta yana gaisheta…ummi tace”kaidai Allah ya shiryeka wlh..duk kabi ka lalata yaran nn da rungume rungume..basuki su rungume kowa ba wadann yaran”…Taheer na murmushi ya karasa kusa daita..itama kawai sai ji tayi yayi hugging dinta…sai tayi shiru kawai tana girgiza Kai..a fili ta furta”Allah ya shiryeka Taheer”..shi kuma yace”Ameen Ameen Ummi”…Saida ta saketa snn ya dauki Neehal daketa faman miko mishi hannu tana dariya..ya dagata sama yana juyi da ita cikin parlon..duk suka zuba mishi ido Saida ya gama snn ya zauna kusada Layla ya dora Neehal din kan cinyanshi yana Jan kumatunta yace”Nafee ‘yar lukuta”…ummi ta galla mishi harara tace”wato bazaka dene kiranta Nafee ba koh..sai kace sirikarka ba kake wnn iskancin”…Taheer na dariya yace”ummi ko sirika tace ai she’s still my younger sister…so ni a kanwar na dauketa ba sirika ba”…ummi tace”dole kace haka mana tunda ta Haifa maka ‘ya ka aura”…umma dake gefe tace”to Yaya abun gori ne Kuma”…ummi tace”dole in mishi gori ai tunda har yanzu daukanta yake matsayin kanwarshi”…Taheer kuwa hannun Layla ya kamo cikin nashi snn ya faki idonsu ummi yayi kissing hannun nata before saying”I love you so much babyna..bazan taba iya rayuwa babu ke ba”…itama idon nasu ta faka snn tayi kasa da murya tace”I love you too hubby..I love you so much”…Taheer ya lumshe ido tareda kissing forehead dinta..

Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!

A nan na kawo karshen Littafina mai suna Dr.TAHEER..Allah ya bamu ikon yin amfani da darussan dake ciki…Kura kurai dake ciki kuwa Allah ka yafe Mana????????

Ina Mika dimbin godia ga daukakin masoya Wanda suke bin wnn littafi nawa…nagode nagode nagode muku sosae da soyayyan da kuke nunama littafin…Allah ya kasa da alkhairi Allah Kuma ya bar zumunchi…i want you all to know that Ummu Ashraf loves you more than you could imagine wlh..I love you guys so much and am going to miss you sosae..????????????????????????

Yanxu xamu Dan huta sbd Ramadan Amma in Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya zaku jini ciki n sabon Novel Dina mai taken”INA ZAN GANTA”…it’s another interesting love story..Ina fatan zaku bishi Kuma ku soshi kmr yanda kuke son Dr.TAHEER..thank you all once again..I love you so much♥️♥️♥️

Mum Ashraf ✨

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94

Leave a Reply

Back to top button