Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Har yamma Taheer bai fito ba…duk anje part dinshi Kuma yaki bude kofa…both umma da ummi are very worried…Layla kuwa dama baa mgn..don tun dazu take musu kuka wai a Kira doctor yazo gida ya dubashi…Saida umma ta kusan maketa snn tayi shiru…but har zuwa yanxu bata bar hawaye ba…she is so worried about halinda taga daddy a ciki..she can’t stand seeing him like that…she can’t.
Suna nan zaune jigum sai gashi ya shigo bayan isha’i…yanata kokarin boye damuwan dake fuskarshi ya shiga binsu da kallo…kawai sai ya fashe da dariya ganin yanda suke zaune kmr gidan mutuwa…a fusace ummi tace”bakada kirki wlh Taheer…ya zaka sanyamu a damuwa snn kazo kana mana dariya sai kace abokan wasanka…Taheer ya Dan tsgaita da dariyan…ya samu wuri ya zauna snn yace”well am sorry ummi…kune kuka bani dariya Naga kunyi jigum kmr gidan makoki…tsaki ummi taja snn ta mike zuwa dakinta…cikin ranta kuwa tasan duk dariyan nn da yakeyi…yake ne…zuwa yanxu ba karamin tausayi yake bata ba…she prays maganin da aka bashi yayi aiki…tasan InshaAllah zai Dena duk damuwan da yakeyi..don ita har ga Allah tunaninta baida lfy ne…shiyasa baya sha’awan yin aure.

Bayan ummi ta tafi ya koma kusada umma ya zauna tareda kamo hanunta yace”ba komai fa umma..bacci ne kawai ya daukeni”…dukda umma bata yadda da abinda yace ba…bata nuna mai ba…sai ta shafa kanshi tace”shknn…but don’t try anything like this again Taheer…you scare the hell out of us”…Taheer na murmushi yace”bazan Kara ba umma”…bata sake mgn ba ta mike itama zuwa daki… Layla ta taso a hankali ta dawo kusa dashi tace”daddy are you sure ba abinda ke damunka Kuma”..Saida yai pecking dinta snn yace”am pretty sure baby..so ki dena damuwa okay?…tana murmushi ta daga mai Kai itama snn ta fada jikinshi tace”I love u daddy”

One week ltr…

Bikin Taheer da Sameera saura sati 3 ciff…both bangarori nata shirye shiryen biki amma Banda Taheer…Saida ummi tayi da gske snn aka samu yaje ya ba Sameera duk abunda take bukata na biki…ya kuma tabbatar Mata da ko event daya bazaiyi attending ba…ita kuwa ummi cewa tayi a Dena bi takanshi…shirye shiryensu sukeyi hankali kwance itada umma.

Akwai events da suke arranging…ranan Thursday zasuyi mother’s Eve… Friday bayan daurin aure zaayi dinner da dare…bayan an kawo amarya staurday Kuma zaayi traditional day snn ayi welcoming amarya into their family.

Daidai da kayan da Taheer din zaiyi amfani dasu a bikin duk ummi ta tanada…don yadda taga yake iskancin nn tsaf zata iya tara mutane shi Kuma yazo ya bata kunya…Sam bazata yadda ya kunyatata gaban mutane ba.

Ana kawo invitation cards dama Yusuf ta Kira ta damkasu a hanunshi…tace lallai lallai ya rabama friends dinsu snn har clinics din da Taheer din ke aiki duk yaje ya Kai musu…harkan gabanta kawai takeyi batabi ta kanshi don bata son bacin rai…she have made up her mind Taheer indai ba mutuwa yayi ba…to bazaa fasa wnn auren ba(wlh kiyita shirinki ummi..muma duk kika gayyacemu biki zamuzo miki????)…bazai yiwu suyita zuba mai ido yana zaune ba auren ba…shekara arba’in ai ba nan kusa bane..so yake sai ya tsofe Mata a gida..inaa Sam bazai yiwu ba.

Yau Taheer na zaune parlonshi bayan tafiyan Yusuf abokinshi…yazo kan arrangements din biki da zaayi amma Sam Taheer yace ba abunda zaiyi…Yusuf sai hakura yai kawai ya tafi…ya Kira ummi a waya ya sanar da ita yanda sukai da Taheer din…tace ya rabu dashi kawai…duk abunda ake ciki zata nemeshi.

Layla ta shigo dakin da tab dinta a hanu ta zauna kusa dashi tana nuna mai tab din tace”daddy tayani zaban gown din nn plss…inaso inyi order ne…next week kayan zasuzo”…ya amsa tab din ya shiga duba gowns din da take nuna mai…maimakon ya zabar Mata din saiya tabe baki yace”me zakiyi da wnn kayan baby?…ta Dan wara ido tace”na biki ne mana daddy…as your daughter ya kamata da bikinka ace nafi kowa yin kyau…nasan idan nasa kayan nn duk Wanda ya kalleni sai ya sake kallona sbd ba karamin kyau zasumin ba”…Taheer ya daure fuska tamau tareda kashe tab din ya ajiye a gefe yace”wato duk Wanda ya kalleki ya sake kallo abi?to bazaa sai kayanba”ta marairaice tace”daddy karka hanani plss…ba abinda nake nufi knn ba…Ina nufin ya kamata inyi kyau ranar bikinka”…ya sake girgiza Kai yace”na fada maki bazaki sa kayan nn ba…zan kaiki ki sai duk abinda kikeso kikai a dinka maki…amma bazan Bari ki sai wnn gown din kisa in public ba”…da sauri tace”daddy ummi fa duk ta siyamin irin wadan nn…shi wnn daban ne daddy…don Allah kar ka hanani…ya sake girgiza Kai yace”na fada maki bazaki sa wnn gown din ki shiga cikin mutane dashi ba baby…so kima dena pleading don ba canxa mind dina zanyi ba…nace bazaki sa ba and that’s final”…shiru kawai Layla tayi tana kallonshi kafin tace”toh”…da ganin yanda tai mgnr ba yanda zatayi ne…Taheer ya mike tareda daukan car key dinshi yace”tashi muje in kaiki ki siyo yanxu”…ba musu ta mike..Saida ta Sanya hijab dinta katoto snn sukama su ummi sallama suka fita…sai turo baki take ita a dole ya bata Mata plan…bata San me zata siyaba bayan uban kayan da ummi ta siya Mata Kuma…tasan ko zata shekara cemai tanada su ba yadda zaiyi ba so gara ma ta bishi ta zabo wasun kmr yanda yace don ko zata shekara mai bayani ba hakura zaiyi ba.

Gidan su Sameera suka fara zuwa…basu wani dadeba suka tafi don dama sako yaje Kai Mata…ran Sameera ba karamin baci yai ba…wai shi duk inda zaije dole sai ya tafi da wnn yarinyar me kamada aljanu ne??..dole ma tayi mgnin yarinyar nn wlh…

Kai tsaye inda suka saba siyayya suka nufa…Saida ta zabi duk abinda takeso ya biya kudin snn suka tafi.
Suna tafe a hanya ya kalleta yace”can I ask you something?..ta juyo tana fuskantarshi tace”of course daddy”…Saida ya maida kallonshi kan titi yace”will u miss me idan nayi aure?…lokaci daya mood dinta ya canxa…idonta har ya kawo ruwa…ita kadai inta zauna tana wnn tunanin har hawaye takeyi…bata taba nuna mai bane sbd tasan zai fita damuwa…tace”sai nafi kowa missing dinka daddy…am going to miss you like crazy…shknn idan kayi aure daddy ba Wanda zaina kaini skul…ba Wanda zaina zuwa dakina duk dare yamin addu’a snn ya kashe min haske…ba Wanda zai na petting dina idan nayi fushi…snn ba Wanda zaina kula Dani idan bani da lfy…duk kafi kowa iya kula dani in bani da lfy daddy…ummi tai tamin fada tana cewa na fiya raki da shagwab…sai ta kasa karasawa ta rushe da kuka…da sauri Taheer ya gangara gefen titi yayi parking…yasa hannu ya janyota jikinshi…shima kmr zaiyi kuka yace”no baby stop crying plss…I promise I won’t let you miss me even for once…I will come every night in saki bacci snn in maki addu’a in maki duk abinda na saba…first thing in the morning Kuma zanzo in kaiki skul…idan bakida lfy ma I will always be there for you…duk kike bukatan wani abu just let me know…zanyi maki without wasting of time…I will never let you miss me okay?so stop crying plss…I will talk to ummi ta bani ke kawai mu tafi tare…da sauri Layla ta girgiza Kai tace”ummi bazata yadda ba daddy and nima I don’t want to leave her all alone…she will be lonely without the two of us…so I prefer to stay with her”…Taheer na goge Mata tears yace”then stop this crying baby kinsan banaso… InshaAllah you won’t miss me okay?..ta daga mai Kai tana murmushi…shi Kuma yaja kumatunta yace”my cry cry baby…kuka baya maki wahala”…tai murmushi kawai snn ta koma seat dinta…shima ya gyara zama snn ya kunna motan suka cigaba da tafiya…deep down he’s thinking ita missing dinshi kawai zatayi…amma shi loosing dinta zaiyi for good.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button