Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Saida suka sake tsayawa a chicken republic ya sai mata burger da pizza kmr yanda ta lissafa mai snn suka kama hanyan gida…har yanxu bai dena godema Allah kan such a very huge blessing da yayi mashi ba…sai nanata Alhamdulillah yakeyi yanajin tsantsar farin ciki na sake ratsa kowace kafa ta jikinshi.

Umma suna gama waya da Taheer ta nufi dakin ummi da saurinta…sukaci karo da ummin tana Shirin fitowa parlon itama..saura kadan umma ta bugeta sai Kuma tayi saurin ja da baya..she’s very happy that bata lurada ummin ba saida suka kusa bugan juna…ummi na dubanta tace”lfy kike kuwa Aisha..tunanin me kikeyi haka har kika kusa kaini kasa baki saniba”…umma ta saki dariya jin abinda ummin ta fada..wai ta kusa kaita kasa…ta kamo hannayen ummi tareda rikesu gam cikin nata…fuskanta dauke da farin cikin daya mamayeta tace”Alhamdulillah Yaya mun kusa samun karuwa..jikarki dai cikine da ita”…ummi ta dan tabe baki kafin tace”jikata Kuma Aisha..wacce jikar tawa daga ciki”…da sauri umma tace”Yaya wace jika kike daita mai aure Wanda ta wuce Layla..yanxun Taheer ya kirani yake fadamin she is two months pregnant”…wani irin sandarewa ummi tayi a wurin baki a bude…tsananin mamaki da Kuma farin ciki da zumudi suka baibayeta lokaci guda…bawai tana mamaki da ikon Allah bane..aah kawai dai tana mamakin yanda basu taba kawo Layla zata samu ciki yanxu ba Kuma sai gashi Allah ya kawo…a hankali ta cire hanun umma dake cikin nata…sai ta durkusa nn kasa itama tayi sujoodushshukhoor…bayan ta gamata dago tana duba umma cikeda tsantsar farin ciki tace”Allah mungode maka..Allah Alhamdulillah..kai wnn kyakykyawan albishir ne Aisha..Allah ya zaunar da cikin nn lfy Allah rabasu lfy..kema da kika fada mn Allah ya biya maki bukatunki duniya da lahira..Allah mun gode maka”…tana gama mgn Kuma sai tayi hugging umma tana kokarin maida hawayen farin ciki dake kokarin zubo Mata..bata taba tunanin Layla na iya samun ciki nan kusa ba..Ashe akwai ranar da zatazo ta riski wnn abun farin cikin..Ashe akwai ranarda zataga gudan jinin Taheer..her only son…kai Allah abun godia….sun dauki tsawon lokaci rungume da juna kafin suyi breaking hug din…still ummi na dariya tace”Ashe akwai rabo a tsakanin yaran nn shiyasa duk yanda nayi kar aurensu ya yiwu sai da akayi..kice dana zura jiki ma karshenta wnn rabon sai ya kasheni kuma snn ayi bikin..Allah mun gode maka”…umma itama nata murmushi tace”wlh fa rabone Yaya..Allah ya nuna mana lokacin haihuwarta lfy..Allah Kuma ya rabasu lfy”…ummi ta amsa da ameen..cikin ranta tana tunanin da kyar idan ba dauko Layla zatayi ta dawo da ita nn gabanta ta ringa kulawa da ita ba..gani takeyi Taheer Sam bai San yanda zai na kula da ita da kuma bayn cikin dake jikinta ba.(Hajia Ummi badai karfin hali ba????)

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

49

Suna karasawa gida Layla ta baje kayan daya siyo mata a nn parlor ta fara cin kayanta…Taheer yana daga zaune gefe yana kallonta with adoration..kawai yana imagining ta Haifa mashi very cute baby kmrta..he just can’t wait for this day.. Allah ya bashi tsawon rai da zaiyi witnessing wnn rana…Kiran sallah da akai ne ya tasheshi a wurin..ya shiga bathroom ya dauro alwala snn ya tafi masallaci.

Lokacin da ya dawo bai sameta a parlon ba sai ya wuce zuwa dakinta..tana zaune kan sallaya itama ta idar da sallah knn ya shigo dakin..ya karasa ciki ya zauna yana kallon yanda take addu’a..Saida ta gama ya tayata shafawa snn ta mike daga inda take tareda maida sallaya ta ajiye inda yake..ta cire hijab din jikinta shima ta ajiye..ya rage daga ita sai kayan baccin da tasa…Taheer ya Mika Mata hannunshi ta kama snn ya zaunar da ita kusa dashi..ya dora hannunshi kan cikinta..idanunshi kuma na kallon fuskan ta yace”har kin koshi da abincin?..”a hankali ta daga kanta alaman ta koshi…ya sake janyota jikinshi kafin yace”kin tabbata kin koshi baby..ban so kina barin babyna da yunwa ne”…ta murguda mai baki tareda cire hannunshi daga kan cikin nata tace mai”ni ka kyaleni”..tana gama mgnr Kuma ta juya tareda kwanciya kan gadon… Taheer ya matso ta sosae yana cewa”Hey ki ringa bi a hankali fa kar wnn juyin da kike yayi affecting babyna”…a fusace ta sake mikewa zaune..ta shiga tureshi har ta fara hawaye tana cewa”leave me alone..ai dama kafi son cikinka dani..nima ka kyaleni”…ta juya zata koma ta kwanta Taheer ya matseta a jikinshi gam..Allah ya sani har cikin ranshi yakejin wnn juye juyen da takeyi gani yake kmr idan tayi kwakkwaran motsi wani abu zai samu babynshi…a hankali ya shiga shafa kanta yana cewa”baby am sorry..pardon my manners kinji..I love you both..you two are my family so ina sonku equal”…yana rufe baki tace”Allah kafi son cikin nn a kaina..gashi nn tun yanxu ka fara dena damuwa dani”…Taheer ya dafa goshi kafin yace mata”na fada maki duk ku biyun are my babies..ki dena wnn kukan pls”..ba musu ta share hawayenta..shi kuma yaja dogon hancinta yana murmushi yace”that’s my good girl”

Washegari sukayi Shirin fita tun safe..shi zaije Clinic ita Kuma zataje school..Allah ya sani ji yake kmr ya hanata zuwa makarantan nn..gani yake kmr idan tasha wahala wani abu zai samu cikinshi..yasan yanxu yana cewa ta hakura da zuwa school ballo ma kanshi ruwa zaiyi..don idan ta fara kuka har sai ya gaji da lallashi zata hakura…a haka ya gama shiryata da kanshi..duk yanda taso ya barta tayi Shirin da kanta kin yadda yayi..ko breakfast ma a waje ya siyo musu don baiso tana yin aiki mai yawa sbd babynshi…bayan ya sa mata Hijab dinta ya dauka hand bag dinta snn ya kama hanunta suka fita…ya bude mota ya sata ciki snn shima ya zagaya ya shiga ya tada motan suka tafi…Saida suka fara tafiya snn yace”baby ba wani abun da kikeso?..”ta daga kanta kawai don ta gaji da bashi wnn amsan..tunda garin Allah ya waye yake tambayanta Kuma tace mai batason komai…shima sai yayi shiru da mgnr ganin yanda ta daure fuska..yasan idan ya matsa zatace ai dama yafison cikinshi akanta..shi bai taba ganin rigimammiya irin baby ba wlh..

Bayan sun isa school din yayi parking..sai ya juya yana facing dinta ya kamo hanunta ya rike snn yace Mata”Kun tabbata ba abinda kukeso koh”…Layla na dubanshi da alamar tambaya tace”Ni da wa Kuma?..”Saida ya saki murmushi snn yayi pointing chest dinta yace”this baby”..sai Kuma ya sake pointing cikinta yace”and this baby”…ta tura baki tana hararanshi tace”ai saidai ku nemi wani sunan kuma badai baby ba wlh”…Taheer ya wara idanu still smiling yace Mata”why..ba babyna bace itama?..tace”to nidai baka isa ka kirata da sunan da kake kirana dashi ba..itama kuma bata isa tace zata kiraka da daddy ba”.. ta karasa mgnr tareda murguda mai dan bakinta…Saida ya lumshe ido yayi kissing bakin snn yace”itama fa ‘yata ce baby..dole zan kirata da baby mana..she is your younger sister”…yana rufe baki tace”she is not my younger sister”…still Taheer na murmushi yace”why..kema ba ‘yata bace”…tace”ka taba ganin inda uba ya auri ‘yarshi ne”…yace mata”of course ba gashi kin gani a kanmu ba..you are my baby..itama kuma she’s my baby”… Layla bata san lokacinda murmushi ya subuce Mata ba jin abinda ya fada…ta danja gemunshi dake dab da face dinta tace”haka kawai ka gama rainona wai kuma daga baya kazo kace zaka aureni..ni ban taba ganin inda akayi haka ba”…yace”kuma tun Ina rainon naki Allah ya dora min sonki ba..Ina sonki tun bakisan waye ke ba..gashi kuma yanxu na gama rainonki zan fara rainon sister dinki”…tadan harareshi snn tace”nifa she’s not my sister..she is my kid..kuma na fada maka baka isa kace zaka kirata da baby ba..wnn sunana ne ni kadai”…Saida ya dora hannunshi kan cikinta kafin yace”baby sbd me wai..ba dai kishi zakiyi da itaba..kinsan dai ita bazai taba yiwuwa inzo ince Ina sonta daga baya ba”…Layla ta saki dariya tana cewa”to wa ya sani daddy..ni din ma ai ba wanda ya taba tunanin zakace kana son nawa kuma ka fada”…tana rufe baki yace”ai ita she’s my blood”…tace”umhhh su blood manya..nidai yanxu kar barni in tafi kar inyi missing class”…yayi kissing goshinta snn yace”you can go..amma da kinji kinason cin wani abu just give me a call zan bar duk me nakeyi in kawo maki kinji”…tana murmushi ta daga mai kai tana cewa”toh”…shi Kuma ya shiga binta da kallo fuska daukeda murmushi har ta fita daga motan..saida ta bacema ganinshi snn ya tada motan shima ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button