Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Yana nn tsaye suka fito gaba dayansu…suka shiga mota driver yaja motar suka fita…shima ya karasa tashi motar ya shiga snn yai Mata key ya fita daga gidan.
Suna tafe Yana binsu a baya har suka isa airport..bayan anyi parking duk suka fiffito daga motan…ya fito daga nashi motan shima ya karasa inda suke…ya shiga bama yaran hannu suna musabiha snn yai pecking dinsu kowa a forehead…tun kafin yazo kan Layla dama ta juya tareda barin wurin da suke…ya bita da kallo kawai…Nafisa ta karaso kusa dashi tace”to mu zamu tafi bro Allah ya saukaka al’amura”…yana kokarin murmushi yace”Ameen..Allah ya saukeku lfy”…ta amsa mai da Ameen snn tace”Bari in turo maka ita kuyi sallama”…yai murmushi kawai tareda komawa cikin mota…ita Kuma ta wuce inda yaran suke…ta turo Layla wurinshi kmr yanda ta fada…ta taho tana turo baki..idonta har sun kawo kwalla…tana isa jikin motar yasa hannu ya bude mota kofar daga ciki…ba musu ta shiga kafafunta a waje…ko rufe motar batai ba…ya saki murmushin takaici yana kallonta…inshort dai juya mai baya ma tayi…bata son ganinshi…Saida yai gathering courage snn yace”nasan yanxu ba Wanda kika tsana a duniya kmr ni..and as I have told you zan sawwake maki if hakan will make u happy..kiyi hakuri”…banza tai dashi taki kuma juyawa ta kalleshi…ya sake sakin smile snn yace”u can go..Allah ya kiyaye hanya”…kmr jira take ta shiga kokarin sauka daga motan…ya kamo hanunta da sauri..hawaye na kokarin saukowa kan fuskanshi yace”won’t you miss me baby..you are eager to leave me right?…lumshe idanu Layla tayi hawaye na sake wanke mata fuska…a hankali yai kokarin maida nashi hawayen shima snn ya saki hanunta…ya koma ya gyara zamanshi snn yace”am sorry”…bata ce komai din ba tabude motar ta fita..har tana hadawa da gudu…Taheer ya lumshe ido allowing tears din da suka cika mai ido suka saukan kan fuskarshi…ya zaro handky a aljihunshi ya goge snn ya rufe motar tareda dora kanshi ka starring…bai bar airport dinba Saida jirginsu ya tashi.

Kai tsaye clinic dinshi ya wuce don baison komawa gida kwata kwata…yai kokarin yakice damuwarshi snn ya fara duba patients kmr ba abunda ke damunshi…she’s trying his best ya boye abunda ke cikin ranshi but ya kasa mantawa dashi.

Around 3 Yusuf yazo office din nashi…bayan ya shigo ya zauna ko gaisawa basuyi ba yace”man I’ve heard abunda ka aikata..baka kyauta ba gsky..bakayima Sameera adalci ba”…Taheer dafa kanshi yai don ya gaji dajin mgnr nn…a hankali yace”Ni banyi haka don cutarta ba…nayine sbd in tseratar da kaina snn in tseratar da ita itama”… Yusuf ya daga kafada snn yace”shknn Allah kiyaye gaba…yanxu fadamin…Ina amaryar taka…Taheer Ibraheem Jakada angon Maryam Taheer Jakada..what a couple!!!…Taheer yaja tsaki snn yace”ban son irin wnn wasan ka sani”…da sauri Yusuf ya tsaida dariyar da yake snn yace”sorry ango..bazaa Kara ba..yanxu ya amaryar taka”…Dan tabe baki Taheer yai snn yace”sun tafi porthacourt”… Yusuf ya zaro idanu yace”ban gane ta tafi porthacourt ba..don’t tell me iyayenta sun kwace kayarsu ne”…wani dogon tsaki Taheer ya sake yi snn yace”Kai matsalana dakai watarn bakada hankali Yusuf…like how on Earth zakamayi wnn tunanin”… Yusuf ya daga hannaye yace”easy doctor…bani fa na kar zomon ba…naji kace ta tafi porthacourt ne so ban gane me kke nufi ba”…Taheer ya sauke ajiyar zuciya snn yace”ummi ce wlh..kasan har yanxu bata bada consent dinta a auren ba..shine kawai ta hada Mata kaya wai su tafi da ita sai tace a dawo da ita zata dawo”… Taheer ya danyi shiru for some secs snn yace”do you know the worst part of al’amarin nn?…Yusuf na girgiza Kai yace”No”…Taheer yace”wai uncle cewa yai bazasu bani ita ta tare gidana ba har sai lokacinda ta kammala karatu..kaji wani mgn fa don Allah Yusuf.. medicine fa take Shirin karanta..for how many years sukeso inyita zama Ina jiranta tsakani da Allah…kawai don sunga Ina sonta shine suketa bani wahala haka”…

Yusuf da mgnr Taheer din ya bashi abu biyu..wato tausayi da Kuma dariya..sai ya zabi yai dariyarsa kawai don bazai iya rikewa ba…Taheer yai shiru yana kallon yanda ya dage Yana mai dariya..ranshi ba karamin baci yai ba… there’s no point in talking to wnn Dan iskan wlh… Yusuf ya tsaida dariyar snn yace”like yanxu knn da Kai da tuzuru Wanda bashida aure matsayinku daya knn..gsky su ummi basu kyauta maka ba..just when kake shirye shiryen angoncewa zasu yanke ma danyen hukunci irin haka”sai ya sake fashewa da dariya…Saida yai me isarsa snn ya sake cewa”Ni har na fara lissafin nan da 9 month ku haifo mana junior doctor ko junior baby ashe haukan banza na nakeyi ma”…Taheer bai tanka shi ba..ya shiga duba files din dake gabanshi… Yusuf don kanshi ya gama snn yace”gsky am not happy da wnn hukuncin nasu ummi..like suna son suce maka kayita jira har nanda 6 or 7 years nan gaba..inaaa..gsky da sake..haka sukeso kayita zama kana Kara tuzurewa a gida..no..ya kamata mu samu solution..ga shawara zan baka”…ba tareda Taheer ya dago ya kalleshi ba yace”inajinka”… Yusuf hadda gyara zama snn yace”kawai idan sun dawo da ita nan din ka tubure musu…ka nuna kaifa kana bukatar Matarka a kusa dakai.. don haka kosu baka ita..ko Kuma suga danyen aiki”…wani wawan tsaki Taheer ya saki tareda mikewa ya shige bathroom…baiga amfanin mgn da Yusuf ba wlh..gaba daya ya sake lalata mai zuciya…wani wai ya tubure idan basu bashi itaba suga danyen aiki…shi duk ba wnn ne a gabanshi ba yanxu…yanaso ya fara yaki da tsoro da Kuma kiyayyar da yaga suna kokarin rabashi da babynshi…then ya dawo kan ummi itama yayi duk abinda zai iya don ta sauko ta dena fushi dashi…daga nn Kuma yasan karban matarshi zaifi zuwa da sauki don idan ummi ta amince tanayima uncle dinshi mgn yasan zai amince…Allah ya bashi ikon accomplishing wnn plan din nashi????????(Ameen daddy????)

Bayan Sati biyu…

Tsakanin ummi da Taheer dai zaace babu abinda ya sauya…har yanxu gaisuwa kadai ke hadashi da ita..shima Kuma da kyar take amsawa…ya zamana Taheer ba inda yake samun sauki sai a wurin ummah…gaba daya zaman gidan bai mishi dadi..at times sai Yana zaune sai yaga kmr Layla ta fito daga dakinta…cikin sati biyun nn Kuma ko waya bai samu yayi da ita ba..yasan ko ya kirata she won’t pick so baima taba attempting Kiran nata ba..

Yau dai ya kudiri niyyan bazai kwanta ba sai yaji muryanta…sai ya mike zuwa dakin ummah…bai ganta a dakinba..yasan kuma bazata wuce bathroom ba..don haka ya nemi wuri ya zauna…umma na fitowa ta ganshi zaune…ta karasa itama ta zauna tana kallonshi tace”yaushe ka dawo”…a hankali yace”yanxun nn umma…umma pls inaso ki Kira baby ne a wayarki..sai kisa a speaker kuyi mgn inaso ne kawai inji muryanta”…cikeda tausayinshi umma tace”nasan wnn abun ka Sanya a rai yaketa damunka Taheer…wato bazaka saukakama kanka ba koh”…da sauri Taheer yace”ba haka bane ummah…a hakan ma am really trying…umma kinsan dai tun da nake da baby bata taba tafiyan sati ta bar gidan nn ba..and ban taba spending two whole days without seeing her ko without talking to her ba…amma yanxu gashi nayi…yau satina biyu umma ko voice dinta banji ba..and hakan na damuna umma..zuwa yanxu Kuma hakuri na ya kare..kiramin ita kawai zakiyi inajin voice dinta shknn”…umma da tayi zuru tana sauraron shi ta girgiza Kai kawai snn ta dakko wayarta…zuwa yanxu har ta gaji da rarrashin Taheer…ta gaji da bashi baki kan yayi hakuri…she’s now out of words so batasan me zata fada mai ba…don haka kawai sai tayi dialing number din Nafisa tareda sawa a speaker kmr yanda yace…tana shiga tayi picking…bayan sun gaisa umma tace”idan Layla na kusa bata muyi mgn”…Nafisa tace toh snn ta mikama Layla wayar tace”ga umma zakuyi mgn”…Layla ta taso daga inda ta amsa wayan ta Kara a kunne…a nutse tace”umma Ina yini”…umma dake kallon Taheer tanason ganin reaction dinshi tace”lfy Lou Layla…ya porthacourt din”…Layla tace”akwai dadi wlh umma…sai naji kmr kar in dawo Abuja”…daramm Taheer yaji kirjinshi ya buga jin abinda ta fada…umma tace”bakida hankali ai dole kice haka dama”…Layla ta Dan shagwabe murya tace”umma banida hankali kuma”Taheer Saida yasa hannu ya dafa bango don jiri yaji kmr zai daukeshi…he missed her like crazy and bai tabbatar da yayi missing din nataba sai da yakejin muryanta yanzun…he really missed shagwaban nn nata..he missed every single thing about her…umma dake kallonshi kafin tayi mgn Layla tace”umma ya kowa da kowa”…umma tace”duk kowa lfy Lou…baki tambayi daddynki ba”…diff Layla tayi kmr bataji me ta fada ba…Taheer dai yai shiru shima Yana sauraron su…umma tace”ba mgn nayi maki bane Layla kikai min shiru”…a daya bangaren Layla tace”umma ni bansan me zance ba ai”…tun kafin ta rufe baki umma tace”zanci mutunchinki wlh..Taheer din kikema wnn iskancin Layla..wato kin manta duk…bata karasaba Taheer ya mike da sauri ya kwace wayar daga hanunta…yai hanging call din yana kokarin dora murmushi kan fuskanshi yace”umma Mana…ya zakiyi mata fada Kuma…kinga yanxu am happy naji voice dinta idan kikace Zaki Mata fada Kuma spoiling mood din nawa zakiyi ai”…ganin yanda umman tayi shiru tana kallonshi sai ya riko hanunta yace”umma why the blank look?…nidai ko nan gaba don Allah kar kice zakiyi Mata fada a kaina ummah…bazanji dadi ba..Kuma tanada right din jin haushina umma ai kinga ban kyauta Mata ba…so plss kiyi hakuri”…umma kallonshi kawai take totally speechless…cikin ranta tana girmama soyayyan da Taheer ke Mata..tayi imanin ba namijin da zaiso Layla kmr yanda Taheer din ke sonta…ganin ba mgn umma zatayi ba sai kawai ya mike yana fadin”umma Saida safe”…still dai bata iya cewa komai ba ta shiga binshi da kallo har ya fita daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button