Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari ma haka ta tashi sukuku kmr mara lfy…bayan tayi wanka ta shirya kanta cikin skirt da riga na material daya amshi jikinta sosae..sai ta fita parlor sakamakon Kira da ummi keta kwala Mata tun dazu wai Nawal na kuka taje ta bata nono..baki a tunzure ta karasa parlon ta zauna tana cewa”ummi nidai gsky na gaji da halin Nawal wlh..shegen ci gareta..kullum nono kullum nono ko gajiya ma batayi..Muna komawa gida zan fara bata baby formulas don bazan yadda ta karar dani a banza ba”…ta karasa mgnr hadda su murguda baki kmr Nawal din tasan me take fada… ummi Kuma tsaki taja kafin tace”kedai zanga ranar da zakiyi hankali wlh”…daidai nn Kuma sukaji sallamar Taheer a cikin parlon…ya karaso ciki ya gaisa da ummi..umma ta shigo parlon tana dubanshi tace”wuce muje kayi breakfast kafin ka fita”..yace”umma na koshi”…umma na hararanshi tace”ban gane ka koshi ba..ko kaci abinci ne a wani wurin”…a hankali yace”aah”..tace”to wuce muje bana son gardama..naga jiyama haka ka kwana bakaci abincin ba shine yanxu ma kakeso ka tafi aiki ba tareda kaci ba..to da raina da lfyta bazan bari yunwa ya hallaka ka ba wlh..wuce muje”..Taheer ba yanda ya iya haka ya wuce gaba umma na binshi a baya har zuwa dinning..Layla ta bishi da kallo ganin yanda yayi kmr bai San da zamanta a wurin ba…umma taja mai kujera ya zauna snn tayi serving dinshi..ta samu wuri itama ta zauna Saida ta tabbatar da yaci abinci da yawa snn ta kyaleshi..ya mike Yana goge bakinshi da tissue ya koma parlon umma na bayanshi…ya dauki brief case dinshi daya ajiye snn ya kama hanyan fita daga parlon..Saida yakai bakin kofa snn ya juyo ya wani marairaice yana kallon umma fuska a kwabe kmr zaisa kuka..ita Kuma umma ta saki murmushi tana girgiza kai tace”ai ban manta ba” sai kuma ta karasa inda Layla ke zaune ta dauki Nawal dake hannunta ta mikama Taheer ita..da sauri ya amsheta lokaci daya yana Dora murmushi kan fuskan nashi..Saida ya lumshe ido snn yayi kissing forehead din Nawal din..da cheeks dinta snn ya dorata a chest dinshi ya dan matse for almost 2 mins kafin ya mikama umma ita yana cewa”I love you”…umma dake kallonshi tana dariya ta karbi Nawal din tace”an gama sallamar”..Yana murmushi shima yace”an gama ummata”..umma tace”to shknn Allah ya tsare”..yace”Ameen”snn ya juya ya fita daga parlon…kawai Layla saita kifa kanta kan cinyanta ta fashe da kuka…ummi na kallonta tace”ke lafiya”…Layla dake kuka wiwi tace”ummi kalli fa yanda yayi banza dani sai kace bai sanni ba..kawai sbd ya samu ‘ya yanxu shine yake wulakanta ni”…ummi tace”to Kuma shine abun kuka sbd bakida hankali..ba sai ki barshi yaje yayita iskancinshi ba me zai dameki..qanin ubanki ne shi da zaki cika mana kunne da kuka wani wai yayi kmr bai ganki ba..kin haihu amma har yanzu baza kiyi hankali ba…
idan kika barni dashi ai zai dawo har cikin gidan nn ya sameni”…itadai Layla kukanta taci gaba dayi bil haqqi…umma Kuma ta karasa ta zauna snn tace”aah fa Yaya ni Banga laifin Taheer ba a nan”…ummi tace”ai dama bazaki ganiba Aisha..ai har abada bazaki taba ganin laifinshi ba”…umma tace”wlh mgnr gsky ne Yaya..itama da take matarshi take banzatar dashi toshi meye laifi idan yayi Mata abinda takeyi”…ummi tace”kmr ya take banzatar dashi wai..me takeyi mai ne”..dariya umma ta saki kafin tace”nidai banga laifinshi ba gsky..kuma ke dama ya zaayi ki hada son da yake maki da Kuma Wanda yakema diyarshi”…umma ta karasa mgnr referring to Layla…ita Kuma sai ta mike da gudu ta shiga daki tana cigaba da kukanta..ummi ta bita da kallo har ta shige dakin kafin tayi kwafa tace”zaka dawo ka sameni wlh..sai naji dalilinda yasa zaka wulakanta Matarka kawai sbd ka samu ‘ya…sai kace ba ita ta shiga labour room ta haifo maka ‘yar ba”…umma na jinta amma sai tayi kmr bata jiba ta shiga yima Nawal wasa suna dariya abinsu..

Shiko Taheer yana sane yayi mata duk abinda yayi..yaji tana cewa zata fara hadama Nawal da baby formulas and yasan idan ba bacin rai ya nuna mata sosae ba bazata hakura ba..yasan halin kayarshi Sarai..tana komawa school zata iya fara bata formulas din kmr yanda ta fada..shi Kuma bazai taba yadda ta fara bata wani abu ba har sai ta kai 6 months..yasan Kuma hakan da yayi shine kadai maganinta..

Karfe hudu daida ya dawo gidan..bayan ya shiga part dinshi yayi wanka yayi changing sai ya nufi part din ummi…bai samu kowa parlor ba sai tv dake aiki..direct ya wuce dakin umma..ya sameta zaune kan sallaya..idar da sallahnta knn tana addu’a ya shigo..sai ya hau kan gadonta ya kwanta tareda lumshe ido..ita Kuma umma ta mike bayan ta gama addu’an ta cire hijab din jikinta ta hada da sallayan ta ajiyesu inda ya dace snn ta zauna kusa dashi kafin tace”are you alright?..”da sauri Taheer ya mike zaune yana dubanta yace”am fine umma..gajiya ne kawai”…umma tace”to muje kaci abinci sai ka samu ka huta”…har zata tashi daga wurin Taheer yayi saurin kamo hannunta yace”umma Ina baby..nasan tayi maku kuka bayan tafiyana koh”…dariya umma ta saki before saying”wlh kuwa kmr ka sani..kuka sosae wai ka dena sonta yanzu sbd Nawal”…shima dariyan yayi yana girgiza kanshi yace”umma babyn ce batajin mgn wlh..ji nayi fa tana cewa wai muna komawa gida zata fara bama Nawal baby formulas..wai ta fita tsotso da yawa”…umma ta kalleshi snn tace”kaji rashin hankali koh..jariryar zaa fara bama wani abu sbd iskanci”…Taheer yace”abinda na gani knn umma shiyasa nayi kmr ban ganta ba..nasan idan ba da gaske nayi Mata ba zata iya yin abindata fada din”…cikeda gamsuwa umma tace”kayi daidai wlh..ao gara da Kai mata hakan sai ka zama namiji kaima..ba wai ka ringa biye Mata tana iskanci ba”..dariya kawai ya saki jin mgnr da umma ta fada..umma ta kama hanunshi zasu fita daga dakin saiga Layla ta shigo dakin..tana ganinshi Kuma ta juya da sauri zata fita yayi azaman rikota ya dawo da ita ciki..itadai umma ta fice abinta don tasan Taheer ba kunyane ya isheshi ba…shi Kuma Saida ya zauna gefen gado itama tana zaune jikinshi yace”baby am sorry”..ta turo baki tanata kokawan kwatan kanta amma ta kasa..Taheer ya sake cewa”ay mgn zakiyi”…tace”shine daxu hadda yin banza dani..kawai sbd kayi ‘ya yanxu shine kake min Wulakanci”..ya sake rungumeta yana dora kanta a chest dinshi yace”ai kece kika janyo baby..don me zakice zaki fara bata baby formulas”…Layla ta rausayar da Kai kmr zatasa kuka tace”nifa da wasa nake”…mgnr da yake sonyi ya makale sbd bugun da sukaji anama kofan..Layla ta matsa daga jikinshi da sauri tana zazzare ido..shima Taheer din mikewa yayi Yana dariya..muryan umma suka jiyo daga waje tana cewa”bazaka fito daga dakin nn ba ko Taheer”..da sauri ya bude kofan ya fita..itama Laylan mikewa tayi ta fita tana addu’an Allah sa ummi bata tambayeta ba..tasan idan umma tace mata tana tare dashi sai tayi Mata fada wlh.

Sauran mu page daya mu gama sweethearts????idan na samu dama InshaAllah zaku jini gobe idan Kuma ban samuba zakuji shiru..nayi tafiya ne wlh Kuma biki mukeyi..yau dinma sbd na maku alkawari yasa na daure nayi amma gobe ba lallai ku jini ba plss..ku dan kara hakuri kadan..I love you????

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button