Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

A takaice dai har wajen 10 na dare Taheer bai bude kofa ba…ita Kuma Layla bata bar wurin ba tanata faman kuka tana bashi hakuri amma kmr bai San tanayi ba…da kyar ta mike tana jin jiri na daukanta ta koma dakinta..har yanxu towel kadai ne a jikinta..a hankali ta shiga bayi ta dauro alwala snn tazo ta tayar da sallah don batayi sallahn Isha ba.

Shima Taheer din yana son fita yaje masallaci amma bai son haduwa da ita ko kadan..haka yasa yayi sallahnshi shima a cikin daki…har yanxu addu’a yake Allah yasa duk abubuwanda ya gani din ba gsky bane amma inaa..

Wajen 12:30 ya bude kofar dakin nashi tareda fitowa a hankali… downstairs ya fara sauka ya rufe ko Ina snn ya kashe bulbs da komai na wuta kafin ya sake haurowa saman…dakinta ya wuce direct..ya bude kofan a hankali..Saida ya fara lekawa ya hangota kwance kan dadduman da tayi sallah ko hijabin da tayi sallahn ma bata cire ba…a hankali ya shiga takawa zuwa cikin dakin gudun kar yayi making any sound da zai tasheta…wayarta da har yanxu ke yashe a kasa ya fara dauka yasa a aljihunshi snn ya karasa inda take…ya durkusa a hankali yana kallon yanda face dinta yayi jajir sbd kukan da taci…ga shatin hannunshi nn radau a inda ya mareta..wurin ya kumbura sosae..lips dinta ma sun kumbura snn sunyi jaa…bata minti 3 bata sauke ajiyan zuciya ba…haka nn yaji wani irin tausayinta na ratsashi…yaji he regrets Marin da yayi mata…tun tana karama zaice bai taba daukan hannu ya daketa ba amma yau he slapped her…dukda he’s hurt he’s feeling her pain too…sai yaga kmr yayi overreacting daya dora hanunshi kan fuskanta…ya riga yasan dama weakness dinshi knn…amma bazai bari tausayin nn nata yayi tasiri a ranshi ba…a hankali ya dauketa daga nan kasa..snn ya dorata kan gado…yana cikin zare Mata hijab din dake jikinta yaji tayi motsi…sai ya saketa da sauri Yana addu’a Allah sa ba tashi zatayi ba…bayan kmr 2 mins sai Kuma ta koma taci gaba da baccinta…shi Kuma ya karasa zare Mata hijab din..towel din dake jikinta ya zame qasa don har yanxu batasa kayaba..Taheer ya runtse idonshi yanajin yanda zuciyarshi ke bugawa sosae…da kyar ya janyo duvet ya lullubeta dashi tareda yin addu’a ya shafa mata snn yai mata off din light ya bude kofan a hankali ya fita…nashi dakin ya koma amma Sam bacci yaki zuwa inda yake..sai ya shiga bathroom ya dauro alwala snn ya fito ya fara nafiloli.

Da asuba bayan ya dawo daga masallaci..sai ya tura kofar dakin nata ya shiga a hankali…tana kudundune kan gadon..ya dauka ma bacci take amma yana karasawa ciki sai yaji tana shehshekar kuka a hankali..Saida ya tamke fuska tamau snn ya Kira sunanta”Layla”…sai ta mike daga kwancen da sauri..ta yaye duvet din dake jikinta tareda saukowa daga gadon..tana kuka tace”daddy..daddy dn Allah don Annabi kayi hakuri ka ya”..bata karasa yace Mata”enough bana son jin komai daga bakinki…ki tashi kiyi sallah”…yana gama fadan haka ya juya tareda ficewa daga dakin…Layla ta koma tareda zama gefen gado tana bude sabon babin kuka…yanzu shknn daddy ya dena sonta knn..yanxu ya dena treating dinta like baby..ya dena kiranta baby..duk ya kirata da Layla Allah kadai yasan radadin da takeji cikin ranta…sai taji gaba daya sunan baiyi dadi a bakinshi ba…she wants him tobe calling her baby kmr yanda ya saba..Saida tayi mai isarta snn ta shiga bathroom din tayo alwala ta fito snn ta tayar da sallah.

7:30 daidai Taheer ya sauko cikin shirinshi na tafiya aiki…daidai ta fito daga kitchen knn ita Kuma da wormer a hanunta…ta karasa dinning ta ajiye snn a hankali tace mai”daddy Ina kwana”…bai amsata ba sai cewa yai”idan zakije school din kiyi sauri ki fito Ina jiranki a waje”…tayi kokari ta maida hawayen dake son zubo mata snn tace”na gama abinci”..ya shiga girgiza kai Saida ya kusa fita daga parlon yace”am ok”…snn ya fice abinshi…ita Kuma ta hada Kai da gini tana rusa kuka…Saida taji ya fara horn snn ta haura sama ta dauko hijab da bag dinta ta fita..ba don tanason mgn da Hanna ba da ba abunda zai kaita school din…gashi tunda ta tashi bataga wayanta ba da sai ta kirata a waya…
A hankali ta isa inda yake..ta bude motan ta shiga snn yaja suka tafi…ko a hanya ba wanda yacema kowa komai…ita tana Satan kallonshi..tana Kuma so tayi mai mgn amma ta kasa sbd yanda taga ya daure fuska sai taga kmr ba daddynta bane…Har suka karasa school dinsu ba Wanda yace kala…yana gama parking ya cire mata lock tareda dauke kanshi gefe…Saida ta share hawayen da suka zubo Mata snn ta fita daga motan…ko tafiya batayi ba yaja motarshi yai gaba…ita Kuma ta bishi da kallo tana share hawayenta (hmm waya gaya maki borno gabas take)

Wunin ranar nn gabaki daya Layla bataga fuska a gun Taheer ba…ko zuwa daukanta yau baiyi ba..sai ya aiko wani daga clinic dinshi yace ya dauketa ya maidata gida…wnn abu ba karamin daga Mata hankali yayi ba…gashi yauma Hanna batazo makaranta ba..gashi Kuma ba wayan da zata kirata..ko tanada wayan ma batada number dinta a Kai ..tayi kuka tayi kuka har ta godema Allah…bata taba tunanin akwai ranar da zatazo Taheer ya nuna mata bai damu da itaba kmr haka…rabonta da abinci tun jiya kafin incident din ya faru…yau ko ruwa da kyar ta sama cikinta..girkin da tayi kafin ta fito dinma haka ta barshi ba Wanda ya taba dagashi har ita…

Bangaren Taheer kuwa yini yai tunanin abunda ya faru…ya kalla number AY Gambo yafi a kirga…yayi saving number din a wayarshi snn yayi dialing..amma kwata kwata number baya shiga…kafin ya bar office ya Kira yafi sau 50 amma ko sau daya bai shigaba..hakan ba karamin sake tayar mai da hankali yayi ba…ya kuma kudirce a rai lallai bazai bar wnn abun ya tafi in vain ba…ya zama dole ya binciko ko ma waye me wnn number Kuma ya hukuntashi for calling and texting his wife..ya zama dole ya koya mai lesson da har abada bazai sake ganin matar wani yayi marmarin kulata ba…har yanxu zuciyarshi ba karamin Kuna take mai ba…abun da yafi Kona mai rai is yanda ta ringa boye abun daga gareshi sai da ya riga ya gani kuma takeso tayi mai bayani..bayanin me zatayi dazai fahimce ta..ai ko zai saurari abunda zata fada din ba yanxu ba..sai ya tabbatar da ta shiga taitayinta snn zai saurareta.

Har dare bai bar clinci ba Kuma Yana sane yayi hakan..dukda wani bangaren na zuciyarshi na tausayinta amma bai bari tausayin yayi tasiri a kanshi ba…karfe 9 daidai ya shigo ciki gidan…ba kowa a parlon as he expected…ya kalla dinning yaga abincin da ta jera tun safe na nn kmr yanda ta barsu..alaman itama bataci abincin ba knn…ya haura sama zuwa dakinshi..yai wanka snn ya hau gado ya kwanta yana cigaba da tunanin abubuwan da suka faru..harga Allah yanaso yaje ya ganta ya Kuma tabbatar da she’s fine amma ya hana kanshi zuwa..

Ita Kam Layla zuwa yanxu zazzabi ya rufeta ruf…ta kudundune cikin bargo sai rawan sanyi take…ga wani uban yunwa dake cinta amma ko kadan bataji zata iya sa komai a bakinta ba…tanaso taje ta duba ko ya dawo ta sake gwada bashi hakuri ko zai saurareta amma ta kasa tashi…haka tacigaba da kwanciya cikin bargo tana kuka..ga jikinta da ya dauki zafi rau.. temperature dinta yayi rising sosae.

Yauma kmr jiya..bayan karfe daya na dare..ya nufi dakin nata…har yanxu tana dunkule cikin bargo wani wahalallen bacci yayi gaba da ita..saidai zazzabin da har yanxu bai sauka ba…yana zuwa kusa da ita yaji wani hucin zafi..sai yakai hannu da sauri yana feeling temperature dinta aiko yajishi zafi zau…ya dauke hanun nashi tareda zirashi cikin aljihu yana kallonta…kmr zai fita daga dakin..sai Kuma yaga bazai iya barinta cikin wnn halin ba…sai ya fita yaje kitchen ya hado tea mai kauri ya koma dakin nata ya ajiyeshi..snn ya tafi dakinshi ya dauko analgesic da ruwa ya sake komawa dakin nata…ya zauna kusa da ita kafin yasa hanu ya yaye bargon data lullube dashi…sai ta sake dunkukewa waje daya jikinta na rawa sosae sbd sanyin daya ratsata…”Layla”ya Kira sunanta da dan karfi aiko kmr a mafarki taji muryan nashi…sai ta bude idon da sauri…fuska daure..ya dauki tea din da ya hado ya Mika Mata…ta mike zaune da kyar tana hawaye..tasa hanu ta amsa tea din tana kallonshi…tanaso tayi mgn amma ta kasa…yace”shanye ki bani cup din”…ba musu ta kafa cup din a bakinta ta shiga Shan tea din da takejinshi kmr magani…tasha da dan yawa snn ta Mika mai..bai amsa ba yace Mata”shanyewa nace kiyi ai”…a hankali ta sake maida cup din bakinta..Saida ta sanyeshi tass snn ta Mika mai cup din…ya amsa ya ajiyeshi gefe..snn ya ballo drug dake hanunshi ya hada da ruwa ya Mika Mata…nan ma batayi musu ba ta karba…ta sha maganin da kyar snn ta dawo mai da cup din ruwan…Yana amsa ya mike tsaye..har yanxu fuskar nn ba sarari yace Mata”koma ki kwanta”…Saida wasu hawaye suka zubo Mata snn ta koma ta kwanta din…shi Kuma ya janyo balnket ya rufeta dashi idonshi ya sauka inda ya maretan..sai ya dauke idonshi da sauri snn ya juya ya fita daga dakin..hanunshi rikeda cups din daya shigo dasu..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button