Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

51

Tun tana kokawan kwace bakin nata har ta hakura ta dena…lokaci daya tayi luff tana karban saqon da yaketa faman aika Mata… har yanxu Kuma wahaye bai dena sintiri kan face dinta ba…zuwa yanxu tasan ko tacigaba da kokawa dashi din ma ba iya kwatan kan nata zatayi ba..don ji tayi gaba daya wani irin kasala ya rufeta…shiko Taheer tun yanayi don rarrashi sai abin ya fara fita out of his control…duk yanda yake kokarin dakatar da kanshi amma he couldn’t…Saida yayi da gaske snn ya iya zare bakinshi a nata…sai Kuma ya sake rungumeta gagam idanunshi sun sake yin jaa..yanajin yanda heart dinshi ke sauya bugu kafin a hankali yace”baby am sorry..am so sorry for hurting you..but you have to believe me baby.. I love you..only you baby..nasan bazan taba son wata mace a duniya bayan keba..so baki min adalciba if har kika tunanin son da nake maki bai taka Kara ya karya ba..wlh I love you..Ina sonki fiyeda yanda nake son kaina..so dn Allah kiyi hakuri ki dena hurting kanki…I love only you”…a hankali Layla dake rungume jikinshi ta lumshe idanu wasu hawayen farin ciki da kuma dadin kalamanshi suka wanke Mata fuska…lokaci daya ta nemi damuwan da take ciki tarasa..wato Allah yayima daddy baiwan iya tsara kalamai..duk yanda takai ga fushi dashi minti 2 yayi yawa indai zata tsaye ta saurareshi sai yayi winning dinta…ta sake tura kanta a chest dinshi tana smiling kmr ba gobe…shi Kuma Taheer ya dago face din nata yana kallon yanda take sinne kai..sai ya saki murmushi tareda ja dogon hancinta yace”my stubborn baby..kin cika rigima wlh”…Layla ta sake hugging dinshi tana cigaba da murmushinta tace”nidai daddy ko taci gaba da nemaka banaso kana kulata plss..I know she loves you..bazata taba dena sonka ba ni Kuma am scared..I don’t want to loose you to anyone..I love you so much”…a hankali Taheer ya sake maida hannayenshi ya rungumeta a jikin nashi tight..ya lumshe ido yanajin yanda tsantasar farin ciki ke sake lullubeshi..wato ba karamin dadi bane kaso mutum kuma shima ya soka back..ba yau ta fara furta tana sonshi ba amma na yau din sai yajishi different..na yau din sai yajishi very unique and special…yasan har ya mutu wnn moment bazai tana gogewa daga memory dinshi ba..it’s among abubuwanda bazai taba mancewa dasu ba saidai a kaisu kabari tare…a hankali ya matso da bakinshi saitin kunnenta kafin yace”babyna na gode..thank you so much for loving..I love you too..and plss ki dena ma tunanin zanso wata macen apart from you..bama Sameera ba ko wacece zata soni baby saidai tayi hakuri wlh..bazan taba iya hadaki da kowa ba..Ina sonki sosae”…a hankali Layla dakejin tamkar an tsundumata a aljanna don dadi ta shiga mikewa daga jikinshi..har yanxu bata dena murmushi ba…ganin tana kokarin kwanciya Taheer ya riketa yana kallon cikin idanunta yace”what?..”Saida ta dan lanagabar da kanta snn tace”I want to sleep”…ba musu Taheer ya kwantar da ita a kan gadon..sai Kuma ya sunkuya forehead dinta ya sakar mata kiss a wurin..ya sake sunkuyawa yayi ma cikinta ma kiss din kafin ya kamo hanunta a rikeshi gam cikin nashi..murya can kasa yace”kiyi baccinki babyna..am going to watch you sleep”… murmushi Layla ta sakar mishi sai Kuma ta maida idanunta ta lumshe don da gaske baccin taji tanaji…bata dade ba kuwa baccin yayi awon gaba da ita…Taheer kuwa na zaune yana kallonta tana baccin kmr yanda ya fada…bashi ya tashi a wurin ba Saida aka fara Kiran sallahn magrib…

A bathroom dake nn parlon yayi alwala snn ya tafi masjid…ana idarwa ya dawo amma har lokacin bata tashi ba..yanaso ya tasheta tayi sallah amma baison ya katse Mata baccin tunda yasan ba wani baccin kirki take samun yi da daddare ba…haka yacigaba da zama yanata aikin kallonta kmr bai taba ganinta ba…bata farka ba Saida ya dawo daga masallaci sallahn Isha…ta mike tana yatsine fuska kmr zata mai kuka…shi Kuma ya janyota jikinshi yana kallonta yace”menene?..”Saida ta kwabe fuskanta kmr zatasa kuka snn tace”yunwa”…Taheer yayi dariya kawai gamida girgiza kanshi…yanda tayi da fuskan nata sai kace toy sai ya bashi dariya…Saida ya tsagaita da dariyan snn yace”to me zakici?..”ta danyi shiru tana tunani kafin tace”danwake”…ya wara idanu sosae yana kallonta still smiling yace”yau baby ce zataci danwake.. unbelievable”…Yana gama mgn sai ya mike yana kokarin fita daga dakin kmr zatasa kuka tace”daddy ni zan bika”…baiyi Mata musu ba ya dawo tareda kama hanunta cikin nashi snn suka fita daga dakin tare…shi ya fadama su ummi wai tanason danwake..aiko ummi da kanta ta shiga kitchen zatayi mata..shi Kuma ya rakata toilet tayi alwala snn tazo ta fara sallah…bata jima da idar da sallahn ba ummi ta kammala danwaken snn ta kawo Mata..nan tasashi a gaba ta faraci kmr bata taba cin abinci ba…shiko Taheer zama yayi a gefenta yana kallon ikon Allah…a iya saninshi da ita yasan batacin danwake..ko ganinshi ma bata sonshi amma yau danwaken takema wnn cin kmr ba itane ta tsaneshi ba..lallai ciki ba abinda baya haifarwa..

Bayan sati 4…

Layla na kwance dakin ummi tana bacci ita kadai…tun yamma take wnn baccin har zuwa yanxu karfe 8:30 na dare…Ummi da Umma suna parlor…shi Kuma Taheer sai 9 zai baro clinic tunda evening yake…Ummi ta mike tana fadin”bari in dubo yarinyar nn Aisha..najita shiru tun dazu”…umma tace”gsky dai..nima banji motsinta ba”…ummi na shiga dakin ta sameta zaune a tsakiyar gadon sai hada zufa takeyi…takarasa kusa da ita da sauri tana fadin”ke lafiyanki kuwa..meya faru”…da kyar Layla ta iya bude baki tace”ummi bayana ciwo..kmr zai balle wlh”…a rikice ummi ta shiga neman wayanta tana cewa”bari in Kira Taheer infada mishi..da kyar idan ba haihuwa bace”…da sauri Layla tace”ummi ba sai kin kirashi ba ai ya kusa dawowa..yanxu alwala nakeso inyi zanyi sallah”…ba musu ummi ta ajiye wayanta dake hanunta snn ta kamo Layla ta riketa..Saida ta rakata har bathroom snn ta fito…ita Kuma a daddafe tayi alwalan ta fito…ummi ta sake kamata suka koma dakin..ta shimfida Mata sallaya ta bata hijab snn ta tayar da sallah..ita Kuma ummi ta fita parlor ta fadama umma wai Layla na ciwon baya…tare suka dawo dakin suka zauna har Saida ta idar da sallahr..tana idarwa ummi ta sake komawa inda take tana tambayanta ya bayan…tace yayi sauki snn ta yunkura tareda mikewa daga wurin da tayi sallahn..ummi ta taimaka mata ta sake komawa ta kwanta..sudai duk sukai zuru suna kallonta…ita kuwa tana kwanciya ta lumshe idanunta…tanajin yanda ciwon bayan nata ke tsananta..tun tana dauriya har bata san time din da ta fara juye juye a kan gadon ba… ummi tayi kanta da sauri ita Kuma umma ta fida daga dakin don dauko wayanta ta Kira Taheer..

Yana kan hanyanshi na dawowa gidan wayanshi ya fara ringing..bai bata lokaci ba ya samu wuri yayi parking snn yayi picking call din…umma tayi kokarin daidaita muryanta tace dashi”Taheer kana Ina?..”cikin wani irin tsoro da fargaba da Kuma faduwar gaba da suka diran mai lokaci daya yace Mata”am on my way umma..meke faruwa?..”umma tace”it’s nothing..dama inaso inji ko ka taho ne..sai kayi sauri ka karaso”…a rikice Taheer yace”umma please..meyake faruwa Mana..tell me is baby alright”…”she’s alright Mana..na fada maka I just wanted to see you..ka nutsu kayi driving dinka a nutse Taheer..babu abinda ya sameta”..umma na gama fadan haka tayi hanging call din…shiko Taheer sake tashin motar yayi da sauri yaci gaba da tafiya…Allah ya sani dama tun dazu jikinshi ke bashi kmr baby ba lfy..shiyasa ma ya baro clinic din da wuri… yanxu kuma Kiran umma ya sake tabbatar mishi da cewa akwai matsala…”Ya Allah make it easy for her plss..Allah ka bata da sauki..Allah karka wahalan min da ita na rokeka… innalillahi wainna ilaihi rajiun..my baby am coming for you”… abubuwanda yaketa maimatawa knn while Yana driving a guje…gaba daya yayi loosing nutsuwan nashi..dama yasan duk baby tazo haihuwa Allah kadai yasan yanayin da zai shiga..shi din da ko menstrual pain take sai yaji gaba daya duniyar ta mai zafi inaga ciwon haihuwa Kuma..he’s a doctor and he knows exactly how women are suffering duk suka zo haihuwa..ciwo ne wanda duk yanda zaa Kai ga yi maka bayani bazaka taba fahimta ba sai yazo kanka..ciwo ne Wanda bashi da wani magani da zai rage maka ciwon indai ba haihuwa kayi ba…gaba daya tunanin nn ya sake dagula mishi lissafi…da yana cemata da cikin ya shiga 9 months zai mata cs ya dauko abunshi but he never meant it..he was only kidding..Yana fada Mata haka ne don kar hankalinta ya tashi..yanxu kuwa dukda bai je yaga condition din da take ciki ba sai yaji kawai cs din zaiyi Mata ta huta..he can’t watch her suffer like this…da wnn tunanin ya karasa gida…Yana shiga ciki ko parking din kirki baiyi ba ya bude motan ya fita da sauri har yana hadawa da gudu…Yana shiga parlor ya fara jiyo nishinta daga daki…ai baisan time din da ya kara gudun tafiyan nashi ziwa dakin ba…Yana bude kofa ya ganta kwance jikin ummi…numfashi ma da kyar takeyinshi…sai jujjuya Kanta take from one side to another.. idonta ko digon kwalla babu…wato idan azaba yayi azaba ko daman kuka mutum bazai samu ba…idan kaga mutum na kuka kan ciwo to lallai ciwon baikai a kirashi da ciwo ba…gashi dai duk raki da langwai irin na Layla yau ko energy din yin kukan bata dashi…kawai sai ganin Taheer sukayi from no where yana kokarin dago Layla daga jikin ummi…muryanshi a matukar raunane..jikinshi har shivering yakeyi tsabar rudewa..Yana girgiza kanshi Yana cewa”baby am sorry..am sorry you have to go through all these pain because of me..am so sorry plssss”…ya karasa mgnr tareda hade hannayenshi da nata..at this point Yama manta da batun wani asibiti balle Kuma yayi tunanin he’s a doctor…ummi ce tace”asibiti ya kamata mu tafi Taheer..a wnn yanayin da kake nasan ba iya dubata zakayi ba..tashi mu tafi”…ummi na rufe bakinta ya mike zumbur shi sai yanxu ma ya tuna da asibitin ya kamata su tafi…yasa hannu ya kinkimi Layla da har yanxu bata bar girgiza kai tana cije baki sbd azaban da takeji ba…tare suka fita daga dakin…umma ce tayi saurin dauko car key snn suka fita waje…ita ta bude motan..Taheer dake daukeda Layla a jikinshi ya shiga back seat…umma ta shiga driver seat tunda ita zatayi driving din..ita Kuma ummi tana zaune a gefenta…gaba dayansu ba Wanda bai shiga tashin hankali ba…lokaci lokaci suna juyawa su kalli Layla dake jin jiki sosae ko Kuma ta mirror…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button