Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Saida ta daure fuska tamau snn tayi sallama ciki ciki ta shiga office din…yana zaune inda ta sameshi jiya…idanunshi kyar akan kofa har ta shigo…ta karaso ta tsaya gabanshi..idanunta a kasa tace”gani Sir”…AY wani murmushi ya saki snn ya mike daga seat dinshi ya zagayo inda take tsaye…ya tsaya shima yana nuna Mata kujeran dake bayanta yace”sit pls”…banza Tai dashi tareda dauke kanta gefe…bai sake cewa komai ba Saida ya zauna kujeran dake opposite da Wanda ke bayanta… calmly yace”idan baki zauna ba bazaki bar office din nn ba wlh…zamu yita zama dake har sai lokacin da kika zauna Muka gama mgnr da zamuyi snn zaki tafi…koda hakan yana nufin zamu kwana a office din nn ne”…ta maka mai harara snn ta zauna still tana dauke kanta gefe…shikuma Yana smiling yace”naga alama har yanxu kina tunanin da wasa nake sonki…do you think haka nn nace zan raba maku assignment dinku a class the other day?..I did that only because I wanted to know your name…na fara ganinki ba tareda nasan ko sunanki ba..Kuma na kamu da sonki ba tareda nasan komai akanki ba”…Layla da keta faman hararanshi ta gefen ido tace”na rokeka da girman Allah kayi hakuri ka rabu dani..wlh inada aure..Kuma daga yau bazan sake zuwa inda kake ba”…wani murmushi ya karayi hankalinshi kwance..daga yanda yake mgn zakaga shifa baida wata damuwa at all…kmr bazaiyi mgn ba sai Kuma yace”wato princess har yanxu baki gane inda na dosa ba..I’ve told you bada wasa nake sonki bafa..to ban sanar dake Ina sonki ba Saida nayi bincike a kanki..an Kuma tabbatar min da cewa you are not married..so better stop wasting your saliva telling me you are married to someone..I won’t believe that”…lokaci daya hawaye suka shiga sintiri kan face din Layla…tana kallonshi a raunane tace”who told you so dan Allah..wlh karya suka fada maka am married..Kuma inason mijina don Allah kayi hakuri karka shiga tsakanina da mijina plss I beg you”…AY ya runtse idanunshi gam jin mgnr da take fada..he really is jealous..kan me zatazo tana cewa tana son wani a gabanshi..bayan a iya bincikenshi an cemai bata da aure..kuma wadda ta fada mai mgnr nn tace sister dinta ce..so yasan sis dinta bazata taba yi Mata karya ba….”so you are looking into my face kina fadamun you love someone koh..is that fair princess..sbd kinga ina sonki?..”a fusace ta dago tana cewa”am telling you nothing but the fact..this is the only thruth and i have to tell you..inason mijina wlh..don haka ka fita daga harkana..karka kara aikawa a kirani..ko ka aika ma bazan sake zuwa inda kake ba”…tana gama mgnr ta mike zata fita daga office din…har takai bakin kofa taji yace”tunda haka kika zaba zanje in samu wanda kikejin tsoron ya San Ina son naki..zanje in sameshi in fada mashi cewa Ina sonki..Dr.Taheer right?..”a firgice Layla ta juyo tana dubanshi…mamaki sosae kan fuskanta tace”ya akai kasan sunanshi..taya ma akai kasan am related to him?..”yace”as I have told you ba da wasa nake sonki ba..har clinic dinshi na sani..Kuma wlh kikace bazakina amsa kirana ba zanje in sameshi..I’ll tell him ni ina sonki”…”are you mad”…Layla ta fada da karfi…shima ya mike tsaye Yana cewa”yes I am..indai a kanki ne Maryam wlh I’ve gone mad..I’ve gone crazy..in ma akwai abunda yafi hauka muni Zaki iya kirana dashi..I don’t care”…yana rufe baki ta bude kofa tareda ficewa daga office din har tana hadawa da gudu…ta toshe bakinta da hannayenta don kar kukan da take boyewa ya fito…can bayan classes dinsu ta zagaya..ta samu wuri ta zauna ta shiga rera kuka kmr ba gobe..kuka takeyi kmr Wanda akaima mutuwa…ya zatai da wnn masifan..ya zatai idan daddy yaji wnn mgnr..ya zatayi da ranta…wnn sune tambayoyin da takema kanta yayinda take rusa kuka kmr ranta zai fita.

Shima AY Gambo komawa yai tareda relaxing kan kujera…a iya bincikenshi an tabbatar mai da bata da aure..ya dai san ance shi wnn Dr.Taheer din na sonta..iyayensu kuma basu son bashi ita sbd yayi mata girma..amma meyasa take cemai tanada aure..ko don sbd tana son Taheer din ne..ya kasa gane kan al’amarin nn..he really need to do something if not..yana ji yana gani zai rasata..and yana sonta..yana son aurenta..dole bazaiyi folding hands dinshi Yana kallo yayi loosing dinta to someone ba..he can’t.

Ita kuwa Layla ta kwashi almost 1 hour tana kuka nan wurin…gaba daya kwakwalwarta ya cushe..bata san ma tunanin da ya kamata tayi ba yanxu..indai haka al’amura zasu cigaba da kasancewa to gsky gara ta sanar da daddy ya dau mataki a kanshi..in ba haka ba tana kallo zai sanyata cikin matsala…Saida ta gama kukanta ta gyara fuskanta tsaf snn ta koma class..Hanna na ganinta ta fuskanci akwai matsala…Saida ta bari lecturer dinsu ya fita snn ta jata suka fita daga class din…silent area suka samu suka zauna snn tace”ya kukayi dashi..hope dai ya amince kinada aure yanxu”… girgiza kai Layla tayi tana cewa”bai yadda ba..kinsan har cewa yai wai zaije ya samu daddy ya fada masa..ban san ya akai ya Sanshi ba”…Hanna tai shiru na dan lokaci sai Kuma tace”ki barshi yaje ya fada mai din tunda baida hankali”…tana rufe baki Layla tace”Ina ganin zan fada ma daddy kawai..in har ya sake nemana zan sanar da daddy kawai yasan yanda zaiyi dashi”…Hanna tace”yawwa shknn ma..nima tunaninda nake tayi knn”

Yau ma Taheer na kallonta yasan definitely wani abu na damunta..tun a hanya yake tambayanta amma tace mai ba komai..ta riga tasama ranta in har week din nn ya kare AY bai dena kiranta office dinshi yana fada mata cewan yana sonta ba..zata fada mai ko da bai tambayeta ba…Haka suka karasa gida in silence kowa da abunda ke ranshi…shi Yana tunanin abunda ke damunta Wanda har yasa tayi sanyi haka..ita Kuma tana tunanin halinda zai shiga idan ta fada mai abunda ke damun nata.

Da dare ta sauko ta shiga kitchen don yi musu girki…Taheer na zaune parlor yana kallon news…ya bita da kallo har ta shiga kitchen din..shima ya mike yabita a baya…ya kamo hanunta suka fito daga kitchen din suka koma parlor..ya zauna..itama ya zaunar da ita gefenshi..fuskanshi ba alaman wasa yace”fadamin abunda ke damunki”…ta sunkuyar da kanta har ta fara hawaye..yasa hannu ya dago fuskan nata..ya shiga goge Mata tears din yace”I didn’t ask you to cry..cewa nai ki fadamin mene matsalarki”…a hankali yaji tace”Ni banaso kana kula Sameera”…ya dan wara idanu yana Mata kallon mamaki kafin yace”and waya fada maki Ina kulata Kuma..da can da ban sameki bama ban kulata ba sai yanxu da nake dake”…ta dan harareshi tana cewa”ai yanxu naga missed calls dinta a wayanka..har massage tayi maka wai zatazo office dinka gobe”…ya janyota jikinshi murya can kasa yace”missed calls kikace kin gani bani ne na kirata ba..yaushe ma kika missed calls din?..”tace”yanxu nn Mana..ba ka bar wayan naka a sama ba”…ya dago fuskanta yana cigaba da goge Mata hawayen yace”to naji kiyi hakuri..zanyi blocking number dinta ma ko ta Kira bazata sameni ba..are you happy now”…da sauri ta girgiza mai Kai alaman No…ya Dan wara ido yace”to me kikeso again”…tace”so nake kace Mata kar tazo office dinka gobe”…yai yar dariya Yana cewa”an gama ma’am..your wish is my command”…ta murguda mai baki tana kokarin mikewa daga jikinshi…yasa hannayenshi ya maidata..saitin kunnenta yace”to baki min dariya ba”…ta rufe fuska da hannayenta tana murmushi…Taheer ya sunkuyo tareda kissing hannayen nata yace”that’s my love..I love you”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button