Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Layla nata baza ido taga yayi parking a wani babban shop na electronics haka…ya bude mota ya fita itama ta fito suka shiga ciki…inda wayoyi suke ya kaita yace”choose anyone you like tunda kin fasa wancan”…Layla daketa faman doka murmushi ta zaba wayan ta nuna mai…yana kallonta yace”tayi maki”…ta daga Kai da sauri tace”yes daddy…thank you”… murmushi kawai yai mata suka karasa inda zai biya kudin ya biya snn akai musu packaging suja tafi abunsu.

A hanya yana driving yana satan kallonta…he’s just imagining gashi ga Layla as hubby and wifey..yanata murmushi shi kadai…har suka isa gida bai bar tunanin nn ba…yana gama parking yace Mata”ki shiga ciki baby..zanje clinic in dawo”…ba musu ta bude motar ta fita tana daga mai hannu har ya fice daga gidan snn itama ta shiga ciki…su Al’ameen kadai ne a parlor don haka ta wuce bedroom din ummi direct…suna zaune suna wawware wasu Kaya…Layla ta karasa da fara’arta ta shiga nuna musu wayan…ummi ce tadan tabe baki tace”to ba dolema ya sai maki wataba…tunda shi ya fasa maki wancan”…Layla ta kalli ummin tace”ummi bafa shi ya fasamin ba…Ni na yar dashi a kasa da kaina…wnn Kuma ya siyamun ne sbd nayi passing post ume”…ta karashe mgnr da murmushi a fuskarta…ummi taci gaba da abinda takeyi tana cewa”sai kiyi Kuma ai ‘yar nan…ke har abada bazaki taba ganin laifin Taheer ba”…Layla mikewa tai ta fice daga dakin…su kuwa umma da Nafisa ba Wanda yace kala..don har yanxu ummi batasan mgnr nn ba.

Sai yamma snn Awwal ya samu Kiran umma bayan sunyi mgn da mahifinshi…ya sanar da ita shima Alh ya amince…ya kumayi farin ciki dajin wnn mgn…umma rasa inda zatasa kanta tayi sbd farin ciki…she never thought abin zaizo da sauki haka…yanxu fargabanta daya..shine ummi…ba bata lokaci ta Kira uncle din Taheer tayi mai bayani kmr yanda tayima sauran…shima daiki ba…a ganinshi ai hakan ma karfafa zumunchi zaiyi…sedai yace umma ta bari a gama wnn bikin in yaso daga baya sai ayi wnn din…umma taji dadi sosae ta Kuma rokeshi daya Kira ummi ya sanar da ita…yace zai Kira zuwa Safiya tunda yanxu dare yayi.

Cikin Daren umma kasa hakura tayi…tanata zuba idon ganin Taheer tamai wnn kyakyawan albishir din amma bata ganshi ba…mikewa tai kawai ganin har after 9 bai shigoba…ta nufi part dinshi…yana zaune gefen gado…waya kare a kunnenshi…fuskar nn a tamke yake mgn…few minutes back yanajin he’s the happiest man on Earth amma yanxu Sameera duk tayi spoiling mood din…umma na shigowa kmr jira yake yace”my mum is here…I will get back to you”…bai jira cewarta ba yayi hanging tareda ajiye wayan a gefenshi…yana kallon umma da murmushi kan fuskarshi yace”sannu da zuwa umma”…umma ta zauna tana kallonshi tace”tun dazu nake jiranka baka shigoba Taheer”…yace”wlh umma naje clinic ne…I was on call so ban mayi niyyar zuwaba aka kirani wai there’s emergency shine na tafi…yanxun nn na dawo”…umma na girgiza Kai tace”ya kamata dai ka dauki hutu gsky…ta danyi shiru snn ta kamo hanunshi tace”Albishirinka”…ya sake damke hanun nata a nashi yace”goro fari qal ummata”…umma batai wasting time ba tayi masa bayanin yadda sukayi da duk wadanda ta Kira kan mgnrshi da Layla…wani irin farin cikine ya lullube Taheer…ya rasa inda zaisa kanshi don murna sai kawai hai hugging umma tight yace”I love you umma…umma you are the best…umma am lucky to have you…Allah saka maki da gidan aljannah umma…I love you so much”…. murmushi kawai umma keyi tanajin yadda yaketa sambatu…tasan da kyar idan yasan me yake fada…Saida ya gama suburbudo addu’o’in snn ya dago yana kallonta yace”umma am super excited da wnn albishir din naki…you owe me a gift…so tell me duk abunda kikeso I’ll get it”…still umma na murmushi taja cheeks dinshi da hanunta snn tace”babu abinda nake bukata son…wnn excitement dana gani kan fuskan ka kadai is enough to make me happy…Taheer ya sake hugging dinta kafin yace”you are the best ummata…yanxu kina nufin har ummi ma tasan da mgnr nn?…a hankali umma na girgiza Kai tace”gsky bata saniba har yanxu…kasan halin Yaya Taheer Ni ban San ma taya zanyi Mata bayani ba…amma uncle dinka yace zai kirata da safe ya sanar Mata…Saida ta dafa kafadarshi snn tace”ka kwantar da hankalinka don Allah… InshaAllah ma zata amince”…Taheer da lokaci daya farin cikin daya shiga yaji ya fara fading don yasan rigima ne zaa Shashi da ummi…umma ta mike zata tafi tace”a kawo maka abinci?..ya girgiza Kai da sauri yace”am not hungry umma..beside ko inajin yunwa ma wnn good news da kika bani is enough to make me satisfied”… murmushi kawai umma tayi snn tace”to shknn Saida safe…kaima ka samu ka kwanta”…ya biyota da sauri yace”let me escort you umma”…umma batace komai ba suka shiga tafiya tare.
Saida ya rakata har dakinta snn ya fito…har zai fita sai kuma yaji he wants to see her…ya waiwaiga to make sure ba Wanda ke kallonshi…snn ya nufi dakin Layla…a hankali ya bude kofa ya shiga….tana kwance tayi rub da ciki a kan gado tana kallo a system dinta…tana sanye cikin sleeping wears dinta very cotton…wando iya guiwa sai rigan ya Dan sauka kadan…kanta babu dankwali…Saida ya kwashi kusan 5 mins Yana kallonta ba tareda ta saniba snn a hankali ya karasa gefen gadon ya zauna…wani irin kasala yaji ya diran mai at once…hannu kawai yasa ya dauke system din tareda dorawa kan laps dinshi ya shiga kallon abinda take kalla a ciki…ta mike zaune tana mai murmushi tace”yaushe ka shigo daddy”…bai bata amsaba sai cewa yai”mene wnn kike kalla baby”…ta Dana wara ido snn tace”Indian film ne daddy…sunanshi KumKum Bagya….Taheer ya dan tabe daki tareda kashe system din ya ajiyeshi gefe…yana kallonta yace”yau bazakiyi bacci ba knn”…ta Dan daga kafadanta tace”dama am waiting for you to come”… murmushi kawai Taheer yai kafin yace”then ki kwanta yanzu…ai gani nazo…bata sake mgn ba ta kwanta…Taheer kawai tsayawa yai Yana kallonta”tana turo baki tace”daddy cover me pls”…Saida yai murmushi snn yaja duvet dake gefe ya lullubeta dashi…ya risina yayi Mata addu’a ya shafa Mata…snn ya dan ja hancinta murya can kasa yace”sweet dreams”…idanunta a lumshe tana murmushi tace”gud nyt daddy”…mikewa kawai yayi ya kashe Mata hasken dakin tareda rufe Mata kofan snn ya wuce…he’s thinking nan da wani dan lokaci..maimakon ya tafi bayan yayi Mata addu’a sai dai ya kwanta gefenta…this thought kawai yasa yaji mood dinshi is changing????

Washegari…

Tun safe ya tashi amma ya kasa shiga part din ummi…yana tsoron abinda ummin zata iyayi…yasan zuwa yanxu da kyar idan uncle dinshi bai kirata ya sanar da ita abinda ke faruwa ba…gaba daya tsoron haduwa da itama yake…wayanshi ne ya fara ringing…ya duba ganin umma ce yai picking da sauri yana gaisheta…ko amsa gaisuwan nashi umma batayi ba tace”kazo kayi breakfast..and don’t waste my time”bata jira me zaice ba ta kashe wayar…Taheer ya jingina kanshi da gado yana tunanin yanda zasu kwashe da ummi…ba yanda ya iya haka ya mike tareda daukan wayan nashi ya fita da part din..

Ya kusa minti 15 a bakin kofa amma ya kasa shiga ciki…ganin umma na sake Kira yasa yai gathering courage snn ya shiga ciki…
Ummi na zaune tana ma Layla kalaba…ita Kuma sai matsar kwalla take…umma ma na zaune gefe sai Nafisa dake kusada ummi…kanshi a kasa ya karaso parlon ya zauna snn ya gaishesu…cikeda tsokana Nafisa tace”barka da safiya doctor”…wani irin kunya yaji ya lullubeshi…ya dan kalleta ta gefen ido kafin yace”morning…Ina su Hibba”… still tana murmushi tace”hibba na daki tana bacci…su Al’ameen ko bansan meya hanasu fitowa ba”…Taheer ya jijjiga Kai kawai…umma na kallonshi cikeda kulawa tace”ga breakfast dinka can a dinning”…a hankali yace to umma”…yana kokarin mikewa wayan umma ya fara ringing…Saida gabanshi ya Fadi don yasan da kyar idan ba uncle dinshi bane…ummi mikewa tayi bayan picking call din tacema Layla”Ina zuwa”snn ta shiga dakinta…da sauri Taheer ya mike zuwa dinning…don so yake yayi ya gama kafin umman ta fito daga daki…Layla dake zaune nan kasa ta mike itama tabi bayanshi dinning din…Yana zama taja kujeran kusa dashi itama ta zauna…a shagwabe tace”daddy dn Allah inka gama zaka tsefemin??wlh kiston ummi zafi be dashi”…Taheer yadan saci kallon kitson nata snn ya fara cin abincin gabanshi yai kasa da murya yanda su umma dake parlor bazasuji ba yace”zan tsefe miki amma ba yanxu ba…kiyi hakuri ki dena wnn kukan”…a hankali tace”tohm”snn ta matso da kujeranda take kusa da nashi ta shiga cin abincin dake gabanshi itama…Taheer bai wani ci da yawaba ya mike yana goge bakinshi da tissue yace”baby ina zuwa”…bai jira cewarta ba ya wuce…umma na dubanshi tace”Kai badai har ka koshi ba”…yana tafiya yace”na koshi umma…ana jirana ne”…umma bata sake cewa komai ba sai binshi da tai da kallo…ko saurin me yakeyi oho?…abun kmr hadin baki yana fita kuwa ummi ta fito daga dakinta da sauri… fuskanta kadai zaka kalla kasan ta samu lbrin danyen aikinda Taheer din ke kokarinyi…Saida ta fara duba dinning taga Layla ce kadai zaune tanacin abinci…snn ta dawo da kallonta ga umma a kausashe tace”Ina Taheer”…Saida gaban umma ya Fadi ganin yanda yayar tata tayi kicin kicin da fuska…tace”yanxun nn ya fita Yaya…yace wai ana jiranshi ne”….ummi bata sake mgn ba samu wuri ta zauna…ta dubi Layla dake cin abincinta hankali kwance tace”dauki abincin nn kije daki ki karasa ci”…ba musu Layla ta dauki plate din dake gabanta ta wuce dakinta tana fadin”zancen na manyane knn”..(yes na manyane qawata????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button