Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Gaba dayansu sun dauki tsawon lokaci ba mgn..kowa tunanin da yakeyi daban…shi Taheer na tunanin ashe Sameera muguwa ce haka…shi Kuma AY Gambo na tunani da kuma takaicin yanda Sameera tayi using dinshi to her advantage..tasa ya ringa kula matar aure ba tareda ya saniba…Taheer ne ya fara breaking silence din da fadin”yanzu na fahimci inda matala yake..Sameera tayi using dinka don ta raba tsakanina da baby ba tareda ka sani ba…but come to think of it..wnn Class Rep din nasu ban yadda dashi ba..he’s the cause of all these”…yana rufe baki AY yace”yes he is..and he won’t go away with this..i have to teach him a lesson he’ll never forget..zasu san sunyi wasa da intelligent dina daga shi har boss din tashi..and plss am really sorry..da nasan matar wani ce wlh ko da wasa bazanyi gigin kulata ba..don Allah kayi hakuri nasan abun da ciwo so am apologizing”…da sauri Taheer yace”No you don’t have to..kaima ba laifinka bane..ita Kuma Sameera zata gane kurenta”…AY na gyada kai yace”gsky she is an evil person..but zanyi maganinsu..and am sorry once again..itama Jakada ka bata hakuri on my behalf..ba laifinta bane”… Taheer yace”zan fada Mata InshaAllah..kuma na yafe maka sbd duk abunda ya faru..ya farune cikin rashin sani..Allah ya kiyaye gaba”..dan murmushi AY ya dan saki kafin yace”nagode sosae..Ina ganin I have to go don akwai Wanda ke jirana”…Taheer ma ya mike yana cewa”it’s ohk zaka iya tafiya”…Saida suka sake musabiha tareda bama juna hakuri snn AY ya juya ya tafi…

Taheer yaji tausayinshi sosae don ya fuskanci da gaske yake son nata kmr yanda ya fada..Wanda da ace Sameera batai wasa da emotions dinshi ba da maybe tuni ya hakura tunda zai gano tanada aure…jiki a sanyaye shima ya nufi motarshi ya shiga tareda barin wurin…a daya bangaren kuma yana cikin farin ciki sosae…ba karamin relieve ya samu ba da yaji ba fault din Layla a ciki ko kadan..dukda dama bawai yana zarginta bane..kishi ne kawai ya rufe mai ido da kuma takaicin boyewan data ringayi har Saida ya gani da kanshi…lokaci daya regret din abubuwan da yai mata ya sake kamashi…bai kamata ya mata hakaba Sam..yau birthday dinta guda amma ko wishing dinta Happy Birthday baiyi ba..bare ayi mgnr su gift da party da yake shirya mata…sai yaji kmr yai tsuntsu yaje ya sameta ya bata hakuri yakeji…

Kai tsaye wani shopping mall ya tsaya..ya shiga kwasan duk wani abu da yasan tanaso..tun daga kan kayan sawa.. shoes..bags..veils.. perfumes etc.
Saida ya lodi son ranshi snn ya karasa counter ya biya aka Kai mai kayan mota snn ya tafi…

wani bakery ya sake tsayawa ya sai manya manyan birthday cakes guda biyu..ya hada dasu cupcakes..da sauran snacks nanma aka mai packaging ya tafi…

in takaice muku dai har drinks Saida ya tsaya ya siya..ya sai su chocolates da sweets komai dai da ake bukata a birthday party Saida ya siya snn ya dauki hanyar gida…yana driving yana murmushi shi kadai..har ya isa gidan…yana gama parking bai tsaya daukan kayanda ya siyo ba ya nufi cikin gidan…a parlor ya samesu duka..Layla na kusa da ummi tana waya da abbansu…Taheer ko zama kasawa yayi..yai tsaye kawai yana jira ta gama wayan…tana gamawa kuwa ya kama hanunta da sauri ya dauki hanyan dakinta yana cewa”baby zo kiji wani mgn”…kmr sokuwa haka ta ringa binshi a baya tana mamakin sudden change dinshi…su ummi suka bisu da kallo baki bude…ummi tace”Anya Taheer qlou yake kuwa Aisha..ko kunya babu ya wani kama hanun yarinya ya shiga daki da ita”… murmushi kawai umma tayi tareda girgiza kai..har yanxu bata bar mamakin wnn soyayya da Taheer kema Layla ba..

Suna shiga dakin nata..ya saki hanun nata tareda hugging dinta gam gam…Saida ya sauke ajiyan zuciya me karfi yana cewa”baby am sorry..am so sorry ki yafemin plss..baby I slapped you..I shouted at you..i don’t know what has gotten into my head…kiyi hakuri kinji babyna…pardon my manners pls”…Layla da wani irin dadi ya mamayeta da jin abunda yake fada..tasa hannayenta itama tareda hugging dinshi..dukda hannayen nata basu ritsa bayanshi ba amma yanajin yanda tiny hands din nata suka zagayeshi…tana hawaye tace”daddy nima am sorry..Allah daddy ba kulashi nakeyi ba..shi yake kulani..shi yak”…bata karasa ba ya rufe Mata baki yana girgiza mata Kai…sai Kuma ya jata suka zauna gefen gado..yana murmushi ya goge Mata tears din dake fuskanta..snn ya juyo daidai saitin inda ya mareta ya tsurama wurin ido yana kallo…yana shafa wurin da hannu kmr zaisa kuka yace”baby am sorry plss..ban taba dukanki ba tun kina ‘yar karama..ban san meya kaini dora hanu a kan cute face din nn naki ba..am really sorry kinji”…Layla ta dora hanunta Kan nashi da har yanxu ke shafa wurin marin itama tana murmushi tace mai”stop apologizing daddy..it’s not your fault..kuma ni banji haushi dan ka mareni ba”…sai ta dan turo baki tana kallonshi tace”kasan me yafi bata mun rai daddy?..”ya girgiza mata kai da sauri alaman bai sani ba…a hankali tace”ni banaso inji ka kirani da Layla..Allah daddy duk kace Laylan nn ji nake kmr in hadiye zuciya in mutu…banaso”…Taheer ya sake hugging dinta yana fadin”na dena…bazan Kara ba baby tunda bakiso”…sai ya dan sassauta murya saitin kunnenta yace”Happy Belated Birthday babyna..bigger n older you i pray..I want you to always remember that I love you..I love you with all my heart…this whole world means nothing to me without you..I love you so much..am wishing you the very best life could offer..Allah ya rayamun ke..ya miki albarka”…sai ya sakeyin kasa da murya yace”and Allah ya bamu zuri’a mai albarka”…da sauri ta shiga boye fuskanta a kirjinshi tana smiling…shi Kuma yana shafa kanta yace”yeah baby…inaso ki haifamun cute baby girl..just like you..yanda zan ringa pampering dinta itama sai in dinga kiranta my baby”…har yanxu face dinta na jikinsh tana dariya…ya dagota yana cewa”yanxu fadamin me kikeso in siya maki as your birthday gift”…tana murmushi tace”I don’t want anything daddy..i just want you to stop being mad and stop torturing me”…saida yaja dogon hancinta snn yace”who’s torturing you..”tana turo baki tace”you”…dariya ya saki sosae kafin yace”come on baby how will I torture you…kema kinsan bazan taba iyawa ba..yanxu tashi muje kiga abubuwan da na siyo maki”…shi ya fara mikewa snn itama ya mikar da ita…hanunta cikin nashi suka fita daga dakin…su umma da har yanxu ke parlor suka sake binsu da kallo ganin sun fita waje…”iko sai Allah”..ummi ta fada yayinda ta bisu da kallo.

Suna fita ya bude mota ya shiga nuna Mata abubuwanda ya siyo Mata..she feels very excited..kawai sai ta rungumeshi tana fadin”thank you so much Daddy..I love you”…Saida yayi kissing both cheekss dinta snn yace”I love you more…yanxu mu koma ciki sai ki yanka cake dinki”…ba musu tayi gaba shi kuma ya kwashi uban kayan yayi ciki dasu.. Saida ya gama kwasa tsaf snn ya dauko Mata wani gown a cikin kayan da ya siyo yace tayi sauri taje ta sa…ba bata lokaci kuwa ta ziro rigan ta dawo parlon…rigan yayi mata kyau sosae..ta fito a birthday girl dinta…ta karaso parlon tana duban manyan Cakes din nata dake jere kan table..daya an rubuta Happy Birthday wife..daya kuma aka rubuta My baby @ 18…gaba daya ta sakejin wasu sabbin farin ciki na baibayeta…shi ya kamo hanunta zuwa inda cake din yake…su ummi dake zazzaune suka mike suma..suka tayata tayi cutting cake din..Taheer ta fara bama a baki shima ya bata..snn ta bama su ummi ma…Taheer sai daukanta pictures yake don ya kasa dauke idanunshi a kanta…wnn excitement da yake gani kan face dinta kadai ya isa ya sanyashi farin ciki na har abada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button