Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Bayan doc Afiya ta taimaka Mata tayi wanka ta gyara jikinta tsaf snn ta kaita zuwa post natal..nurse ta biyota da babynta…suna shiga ta hau gado ta kwanta ko babyn nata bata tambaya ba bacci me nauyi yayi gaba da ita…nurse na kokarin kwantar da babyn daketa tsala kuka a cradle dake cikin dakin suka shigo gaba dayansu kowa daukeda farij ciki…dama suna zuwa labour room da sukaga basu nn Taheer yace suzo post natal yasan dole can zaa kaita…tsakanin ummi da Umma har rige rigen daukan baby sukeyi…karshe dai ummi ta dauka tana fadin”ai nice babba sbd haka ni zan fara ganinta”…tana gama fadin haka tasa hannu tareda yin Bismillah ta amsa babyn da har yanxu bata bar kuka ba…ta kua mata ido tana kallo sai taga tamkar Taheer dinta lokacinda aka haifeshi…face dinta irin na Taheer ne sak sai fari Kuma data dauko na Layla…a hankali ummi tayi addu’a tareda tofa Mata a fuska…ta mikama umma tana fadin”Allah ya rayaki ya maki Albarka..Allah Kuma yasa ba halin kukan Layla Zaki dauko ba..don naga tunda Muka shigo dakin nn bakinki baiyi shiru ba”…umma na dariya itama ta karbi babyn…kallon nata itama takeyi tana kuma ganin kamrta da Taheer din kmr yanda ummi ma ta gani…tayi Mata addu’a itama ta shafa mata tana cewa”Allah ya maki Albarka..Allah ya raya mana”…da sauri Taheer dake kallonsu with so much love yace Ameen…doc Afiya tayi sallama dasu zata tafi Taheer yasa hannu cikin aljihunshi ya debo kudin da shi kanshi baisan adadinsu ba..ya Mika Mata su fuska daukeda murmushi yace”accept this little gift of mine plss..na gode sosae da taimako na da kikayi Allah ya saka da alkhairi”..doc Afiya na murmushi ta amsa kudin tareda yin godia snn suka fita daga dakin..ya rage daga ummi.. umma..sai Taheer da Kuma Layla dake bacci…Taheer ya matso jikin umma a hankali tareda rungumeta yana cewa”Umma am a father now..she’s my daughter umma I can’t believe this..Allah na gode maka ya Allah..Allah Alhamdulillah”…da sauri ummi tazo inda suke tareda amsan babyn dake hannun umma tace”kaidai zanga randa zaka nutsu wlh..dubi yanda kazo ka wani rungumeta ga yarinya Kuma a hanunta ko so kake ka yar daita Oho”…sudai basu tanka Mata ba..shikam Taheer cikin ranshi yace”ai yanda nakejin son yarinyar nn ummi ko kuda bazan iya bari ya sauka jikinta ba balle Kuma ni in yar daita kasa da kaina”…ita kuwa umma shafa bayanshi ta shigayi tana tayashi farin ciki…ita kuwa ummi kan daya daga cikin plastic chairs dake dakin ta zauna ta Dora yarinyan kan laps dinta snn ta dauko wayanta ta shiga neman layin Nafee.. ringing din farko Nafeesa ta daga kmr dama jiran Kiran take…hankali a tashe tace”Ummi haihuwan yazo koh”…Saida ummi ta saki dariya kafin tace”ai an rigama an sauka Nafee..kin ganni rikeda babyn a hannuna”…Nafeesa ta saki wani Hamdala..muryanta cikeda murna tace”dn Allah da gaske ummi..yaushe ta haihu..meta haifa…ya akai baku kirani ba ummi”…ummi na cigaba da dariya tace”duk wnn tambayoyin haka Nafee da wanne zan fara…tun daren jiya ake abu guda wlh amma sai asubahin nn ta haihu..an samu mace”…Nafee tace”MashaAllah ummi..Allah yaraya yayi Albarka..Ina Laylan take”…Saida ummi ta dubi inda Laylan ke bacci kasadan snn tace”she’s sleeping..tunda ta haihun ma inaga ko babyn bata ganiba.. amma dai lfynta Lou”… Nafee ta sake cewa”To Alhamdulillah tunda she’s fine..Allah ya Kara Mata lfy ya raya mana baby..Nima Ina nn zuwa ummi ko yau na samu available flight zan taho InshaAllah”…ummi tace”to shknn Allah ya kaimu”…daga nn sukayi sallama…ummi ta maida dubanta ga Umma da Taheer da har yanxu bai bar jikinta ba.. bai Kuma dena sambatun da yake ba..kawai he’s happy yau shine da ‘ya ta kanshi..jininshi…ba abinda zaiyima Allah daya wuce godia..he’s forever grateful…

3 Hours Later…

Saida Layla ta samu baccin good 3 hours snn ta tashi…a lokacin Ummi ce kadai a dakin..umma da Taheer sunje gida don su taho musu da abubuwan da suke bukata…Saida ummi tayi mai Jan ido ma snn ya tafi..don da farko cewa yayi bazai iya tafiya ya bar matarshi da ‘yarshi ba…

Da sauri ummi ta karasa kusa daita tareda taimaka Mata ta zauna sosae…tana kallonta tace”sannu kinji..bari a hada maki tea Kisha sai kiji da yarinyar nn..tun dazu take rabka mana uban kuka a dakin nn da kyar idan ba kukanki ta gada ba”…itadai Layla batace komai ba sai hawaye dake sintiri kan face dinta…ummi ta juya da sauri jin kmr tana shehshekar kuka tace”La’ilaha illallahu..ke meya faru kike kuka kuma…kodai wani waje na maki ciwo?..”a hankali Layla ta shiga girgiza Kai alaman ba inda ke mata ciwo…ummi ta danyi kasa da murya tace”to kiyi hakuri idan sbd nace tayi gadon kukanki ne..wasa nake maki wlh…in kukane ma ai Taheer yafiki..lokacinda yana karami yini yake yana kuka in fada maki ko gajiya ma bayayi..kuma gashi da murya don duk ya fara kukan nn ko Kiran sallah banaji”…itadai Layla batai mgn ba kuma hawaye bai dena zubiwa kan fuskanta ba…a rikice ummi tace”yau na shiga uku to meyake damunki Kuma..meya faru dn Allah ki sanar dani..keda kika haihu maimakon ki godema Allah sai ki farka da kuka Kuma..haba Layla idan kikayi haka kin godewa Allah knn”…har yanxu dai Layla shiru ba mgn…ummi tayi shiru kawai ta zuba mata ido don bata san me zatace ba Kuma..ita tsoronta kar wani abun ne ya faru ne da ita…daidai lokacin umma da Taheer suka shigo dakin a tare…da sauri Taheer ya karasa gareta ganin yanda hawaye ke ambaliya a face dinta…ya kamo ha nunta ya rike sosae idanunshi har sun canza launi yace mata”baby lfy..meya sameki..meyasa kike kuka..akwai inda ke maki ciwo ne”…shima batace mishi komai ba sai ma zame hannunta da tayi cikin nashi tareda juya mai baya ta kwanta…umma itama tayi tsaye tana kallon ikon Allah…sai Kuma taja tsaki tareda ficewa daga dakin…itama ummi mikewa tayi ta shiga bathroom don dama su take jira su taho Mata da kayanta sai tayi wanka…ummi na shiga bathroom din Taheer ya sake kamo hannunta ya rike cikin nashi..Yana murza hanun a hankali yace”baby am sorry plss..kiyi hakuri ki dena kukan nn dn Allah..idan ma wani abu nayi maki just tell me ni Kuma zan baki hakuri..I don’t want you to suffer by crying like this plss..am sorry”…a hankali ta mike zaune sai kawai ji yayi ta fada jikinshi gaba daya…ta rungumeshi gam tana girgiza kanta tace”daddy saura kadan in mutu wlh..ban taba tunanin zanci gaba da rayuwa ba..tun da nake ban tabajin ciwo irin Wanda naji jiyaba daddy nidai bazan kara haihuwa ba dn Allah”…a hankali Taheer yasa hannayenshi tareda sake rungumeta ga jikinshi…yana kokarin danne dariyan dake son kufce mai ya shiga bubbuga bayanta yana cewa”I agree with you my baby..nima bazan yadda ki kara haihuwaba sbd wahalan da kikasha..so ki dena wnn kukan kinji..ko babyn namu ma bakice a baki ki ganiba”…lokaci daya ta dago taga jikinshi tana goge hawayenta…sai Kuma idonta ya sauka kan cradle da babyn ke kwance a ciki…a hankali Taheer ya mike zuwa inda babyn take..ya daukota snn ya dawo inda take..Saida ya zauna ya dora babyn kan cinyanshi snn ya janyota ta dora kanta kan shoulder dinshi…ta kurama babyn ido tana kallo lokaci daya kuma tanajin wani irin feeling da bata tabajin irinshi ba na shiganta…bata san lokacinda ta Kai hannu tareda amsan yarinyan daga hanunshi ba…tacigaba da kallonta kmr ta samu mirror..sai Kuma ta lumshe ido tareda sunkuyawa tayi ma babyn kiss a goshinta..lokaci daya yarinyan tayi motsi hadda dan yatsine fuska..Layla ta saki dariyan da bata shiryaba ganin yanda tayi da face dinta..sai ta koma Mata kmr Taheer din itama..shima haka yakeyi da face dinshi…Taheer dake kallonsu full of love and happiness yace”baby ya kikaga babyn tamu”…a hankali ta kalleshi still tana murmushi tace”she’s cute”…shi Kuma ya matso tareda sa hannu ya zagayesu daga ita har babyn gaba daya…murya can kasa ya sake cewa”did you like her”…da sauri ta daga mishi kai snn tace”I love her”…Taheer ya manna Mata kiss a goshi snn yayima babyn ma haka yace”nima I love you both..you are my everything”..sai ya sakesu tareda amsan babyn ya maidata inda take..ya nufi inda kayan tea suke yana cewa”Bari in hada maki tea Kisha..idan kin gama itama sai ki bata nata tea din tasha tun dazu take nemanshi”…itadai Layla batayi mgn ba as har yanxu jikinta ba wani kwari sosae gareshi ba…nan da nan ya hado tea din mai kauri sosae ya kawo Mata..ba musu ta amsa ta fara sha don dama yunwa takeji…ya sake zaunawa kusa daita yana kallonta smilingly yace”baby thank you so much..na gode sosae da wnn cute baby da kika haifomin..I love you alot..ki fadi duk abinda kikeso ni Kuma I promise zan yi maki..zan iya maki komai baby don ban isa in biyaki wnn kyautan da kikaimin ba.. thank you so much..muaaahh”..ya karasa mgnr tareda kissing din hanunta…a hankali Layla tace”nidai kawai so nake ka yadda bazan kara haihuwa ba daddy..mutuwa zanyi Allah”…tana rufe baki yace”an gama baby..yanda kikeso haka zaayi”…daidai nn Kuma ummi ta fito daga bathroom…Kai tsaye Inda babyn ke kwance ta nufa tareda daukota..ta dorata cinyan Layla tana cewa”yi maza ki bata nono tasha dn Allah”…a hankali Layla tasa hannunta ta riko babyn…Saida ummi ta daidaita mata yanda zata rike babyn snn ta ciro nonon da kanta tasama babyn a baki aikam ta kamashi da kyau kmr abinda take jira knn…wani uban qara da Layla ta fasa Saida ummi ta toshe kunnenta da duk hannayenta…hawaye na sauka kan face dinta take cewa”wayyo Allah na ummi zafi wlh..cizona takeyi fa”…da sauri Taheer ya amsa babyn da saura kadan Layla ta yar da ita a kasa itama kuwa ta fashe da kuka…ya rungumeta a chest dinshi yana jijjigata amma kukan bai tsayaba…ummi tace”yanxu Layla wane irin iskanci ne wnn zaki kurma Mana ihu haka sai kace mahaukaciya…idan baki bata nonon ba ya kikeso muyi da ita”…Layla na girgiza kai tace”Allah ummi inaga cizona takeyi..bakiji zafin da najiba”…tsaki ummi taja tareda ficewa daga dakin…a hankali Taheer ya matso inda take…ya dora Mata babyn a cinyanta snn a nutse ya fara cewa”baby dn Allah kiyi hakuri ki bata ko kadan ne kinji…kinga yunwa takeji tunda aka haifeta bataci komai ba sai zamzam kadai…dn Allah ki daure ki bata idan kika saba Zaki denajin zafin”…wahaye na sake wanke Mata fuska tasa hannu ta dago babyn sosae…tana kallonshi tace”ni tsoro nakeji daddy”…da kanshi ya zaro nonon tareda daidatashi da bakin babyn…tana sake kamawa Layla ta Kara sakin ihu wnn karon dai bata cire bakinba…Taheer na zaune yana taimaka Mata don ko rike babyn bata iya sosae ba…Saida ya tabbatar ta Dan samu tasha dukda ruwan nonon baizo sosae ba snn ya kyaleta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button