Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Ehenn naga Baku following dina a Wattpad…why naa?aren’t you enjoying the story?
If NO then plss I need to see ur votes and comments on both WhatsApp and Wattpad..thanks n luv u all????

TeamTaheer…

TeamLaylah…

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

13

A hankali ya daga jajayen idanunshi ya sauke kan ummi…kmr zaice wani abu sai Kuma ya sake maida idon ya lumshe…umma ta Dan harari nafeesa tace”ke ba ruwanki dashi…kar Kuma ki sake irin wnn mgnr a gaban yara”…kema yaya kiyi hakuri a bar mgnr nn haka don Allah…Ni zanyi mgn dashi da kaina amma as for now ku kyaleshi yaje ya huta can’t you all see he’s exhausted?…ummi dai batace komai ba…umma ta mike zuwa inda yake ta kama hanunshi tana fadin”stand”…ba musu ya mike sai kawai yaga ta fara janshi har zuwa dakinta.
Ta maida kofa ta rufe bayan sun shiga dakin snn ta karasa gefen gado ta zauna tareda zaunar dashi a gefenta…idanunta a kanshi tace”fadamin Taheer…what exactly is wrong with you?..
Da mugun mamaki ya dago yana kallon umma…Allah dai yasa ba asirinshi ne zai tonu ba….yanzu idan umma ta gane ya zaiyi da ranshi…umma ta katseshi tana cewa”yane Ina mka mgn kayi shiru Taheer…kafiso in barka da Yaya koh…a hankali ya girgiza Mata Kai snn a hankali yace”umma ba abinda ke damuna fa…it’s only stress Kuma da zaran na samu hutu I’ll be alright”…umma na mai kallon tuhuma tace”karya kakeyi Taheer…abinda nakeso ka sani shine….the earlier you said abinda ke damunka the better for you…na tabbata idan nayi rantsuwa wani abu na damunka bazanyi kaffara ba…amma tunda you can’t share it with me shknn…a hankali ya matso jikinta tareda dora kanshi kan kafadanta kawai sai hawaye sharr ya shiga bin kuncinshi….umma ta dafa kanshi jikinta duk yayi sanyi…tausayinshi ya kamata don tasan duk abinda ke damunshi ba karami bane….cikin raunanniyar murya yace”kawai kici gaba dayimin addu’a ummata… InshaAllah I’ll be back to normal again”…umma naci gaba da shafa kanshi cikin sigan lallashi tace”InshaAllah son… amma ka dena wnn kukan Taheer sai kace namiji ba….kayi hakuri kaji…snn ka ragema kanka damuwa don zai iya ja maka matsala”…shi Kam Taheer ji yai kukan na sake tahowa…dama he’s longing for a shoulder to cry on sai gashi Allah ya kawo….Saida ya kwashi almost 30 minutes yana kuka a jikinta snn yai shiru…umma duk tausayinshi ya cikata hadda ‘dan kwallarta itama…she’s wondering wani irin Abu ne zaisa matured mutum kmr Taheer kuka mai tsayi haka…kuka na gasken gaske hadda su majina haka….anya yaron nn ba wani matsalan gareshi yake boyewa ba….Taheer ya katse Mata tunani ta hanyar daga kanshi daga shoulder dinta ya zaro hanky daga aljihunshi yai wiping tears din dake fuskarshi….yasa hanunshi ya kamo nata yana kokarin Dora murmushi a fuskarshi yace”ba komai fa umma…ba wani abu bane”…umma na kallonshi da kyau tace”shknn Taheer…yanxu ka kwanta Bari in kawo ma abinci….da sauri yace”No umma inaso in farayin wanka”…then use this bathroom tunda part dinka akwai baqo”umma ta fada tana pointing bathroom dake dakin…tana kokarin fita yace”umma kayan da zansa fa?…tace”zan aiko a kawo maka”…tana fadan haka ta fita a dakin…wayan Layla ta Kira ta sanr da ita data dakko light kaya ta kawoma Taheer Yana dakinta…ba bata lokaci ta shiga bedroom dinshi ta dakko mai wani well ironed jallabiya ta nufi part din ummi dashi….lokacin umma na kitchen tana kokarin hada mai abinci…su ummi Kuma har yanxu suna parlon…Layla na kallon Al’ameen dake game a gefe tace”Ina daddy na yake?…”dakin umma”… Al’ameen ya fada hankalinshi na kan wayanshi….ba bata lokaci Layla ta nufi dakin umma…shiganta yayi daidai da fitowanshi a wanka…Yana tsaye gaban mirror yana goge jikinshi…ta sunkyar da kanta da sauri tace”am sorry daddy…umma tace in kawo mka wnn”…ta nuna jallabiyan dake hanunta…bai ko kalli inda takeba yace”drop it”ta karasa ta ajiye gefen gado tana kallonshi zatayi mgn yace”get out”…Tai tsaye cak tana kallonshi kmr wata sokuwa…ganin taki tafiya ya juyo a fusace yana kallonta yace”ki 6acemin da gani nace”…kawai saiga hawaye…dama tasan hakan zai faru…ba yanda batayi da Usman kan bataso ya bata drink din a baki ba amma yaqi…yanxu gashi zai ja mata matsala wurin daddy….a hankali ta fara tafiya zata zauna gefenshi kawai ya mike ya kama hannunta tareda bude kofa ya turata waje cikin muryar gargadi yace”kar ki sake dawomin nan…I want to be alone”….yana gama fada ya koma dakin snn ya maida kofa ya rufe…Layla sandarewa tayi a wurin stabar mamaki…yanxu ita daddy ke treating haka sai kace stranger…wasu hawaye suka sake wanke mata fuska…tanajin footstep alaman ana tahowa ta nan wurin tayi saurin goge tears din nata…umma ta karaso tana kallonta tace”ke me kikeyi a nn wurin har yanxu?..”ba komai umma…dama yanxu zan tafi..tana gama fada ta bar wurin da sauri…umma tabita da kallo.

A gefen gado umma ta sameshi sanyeda jallabiyan da Layla ta kawo…yana ganinta ya saki murmushi snn ya tashi yana kokarin amsan tray din dake hanunta ta hanashi…Saida ta janyo table ta Dora tray din a Kai snn ta shiga zuba abincin a plate…yana kallonta har ta gama ta zuba drink a cup snn ta dago ta kalleshi tace”oya yi sauri kaci abinci son…nasan hadda yunwa ke damunka…ya karkatar da kai a shagwa6e yace”saidai kiyi feeding Dina umma…I don’t feel like eating”…murmushi kawai umma tai snn ta dauki spoon ta shiga bashi abincin a baki…ci kawai Taheer yake ba don yanajin dadin abincin ba…bai so ya bata mata rai ne kawai….ya danci kusan rabi yace mata ya koshi…ta dauko drink data zuba a cup ta nufi bakinshi dashi…ya lumshe ido zai sha kawai scene din dazu ya dawo mai… exactly yanda Usman ke Shirin bama Layla a baki…kawai sai ya dauke dai da sauri Yana salati…da mamaki umma ke kallonshi tace”Kai lfynka kuwa”…ya Dan shafa Kai yace sorry umma…kaina naji ya saramin…tace karbi kasha sai ka samu ka kwanta…baiyi musu ba ya amsa drink din…umma ta tattara kayan zata fita tace”ka kwanta ka samu hutu dn Allah…kar ka kuskura in ganka a parlor sai lokacin sallahn magrib…yana murmushi yace Mata”an gama ummata”tayi murmushi itama snn ta fita tareda rufe mai kofan…Taheer ya kwanta kan gadon tareda lumshe idanu…”I really am lucky to have u as my second mom..I love you ummata”ya fada a hankali.

Kmr yanda umman ta fada bai fito ba sai da aka Kira sallahn magrib…ya shiga bathroom ya dauro alwala snn ya fito…wnn karon ba kowa a parlon da alama duk sunje yin sallah ne…don haka direct ya wuce masjid.

Bai dawoba sai da akayi isha’a…ya samu gaba dayansu a dinning zasu fara dinner…umma ta karaso kusa dashi tareda kama hanunshi tace”dama yanxu nake Shirin kiranka…muje kaci abinci”baiyi Mata musu ba ya bita zuwa dinning din…da kanta tayi serving dinshi ta Mika mai snn ta zauna itama ta faracin nata…Layla duk hankalinta na kanshi…wani irin tsoronshi taji ya diran mata don bata taba ganin bacin ranshi a kanta irin Wanda ta gani dazu ba….ummi ce ta lurada Layla bacin abincin take ba tace”ke lafiyarki kuwa…ya kowa Yana cin abinci ke kin zauna kina tunani….a hankali Layla tayi qasa da kanta kawai sai ta fara hawaye…da mamaki ummi tace”lfy…meke damunki?…Saida ta saci kallon Taheer snn tace”ummi don Allah kice yayi hakuri…ni bazan Kara ba”…sakato ummi tayi tana kallonta kafin ta maida idonta kan Taheer din dake ta faman cusa abincin gabanshi irin bai da wani damuwan nn….”kai…meya hadaka da Layla?..tambayan da ummi tayi mai knn…ya dago Kai Yana kallon ummin a nutse yace”ba abunda ya hadamu mana ummi…laifin me zatayi min ni….da sauri Layla ta sake fashewa da kuka tace”don Allah ummi nidai kice yayi hakuri…wlh fushi zaitayi Dani na sani….ummi tace”to me kika masa da zaiyi fushi dake…kema ki kyaleshi mana yaje yayita fushin nasa…ya dade baiyi fushi dakeba mugu kawai”…gaba daya occupants din dinning din kallonsu kawai suke…Layla kuwa sai aikin kuka…umma na duban Layla itama tace”sai ki fadi laifin da kikai masa…don nasan haka nan Taheer bazai dauki fushi dakeba”…a fusace ummi tace”yo ai ba fada zatayi ba Aisha…wlh ko zaki shekara kina tambaya ba fada zatayi ba…shima Kuma ba fada zaiyi ba ko kin tambayeshi…haka suke wnn munafurcin…duk Taheer ya 6ata ‘yar nan da gulma da munafurci wlh….dariya kawai umma tayi snn taci gaba da cin abincinta…nafeesa na dariya itama tace”ummi baki saniba ko laifi tayi mai…nasan haka kawai bazai dauki fushi da Layla ba yanda akeji da ita din nan”…”may Allah bless you”…Taheer ya fada yana goge bakinshi da tissue…ummi Kuma ta tabe baki taci gaba dacin abincinta.
Taheer ne ya fara mikewa…umma na dubanshi tace”badai har ka koshi ba son?…ya langwabar da kai Yana shafa tummy dinshi yace”na koshi Mana umma…kinsan ban jima dacin abinci ba”…ta jinjina Kai snn tace”alright kaje…zanzo dakin naka muyi mgn”ya amsa da toh snn ya ma kowa good night ya bar wurin…Layla ta bishi da kallo don ita kadaine bai cema Saida safe ba ya wuce abinshi…ta sake rushewa da kuka kmr Wanda akama mutuwa snn ta mike a guje tayi dakinta(wnn yarinyan ta cika ta6ara da yawa wlh????haba komai kuka sai kace jaririya)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button