Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

37

Ta bude face din nata still smiling tace”to ka sakeni inje inci gaba da aikina”… maimakon ya saketan..sai ya dora left hand dinshi kan chest dinta..ya lumshe ido yana feeling tenderness din wurin a hanun nashi… right hand dinshi Kuma na rikeda ita har yanxu..idanuwanshi kyam a kanta yace”Allah yai min tsari da fadin wannan kalmar baby”…har ta fara turo baki tace”to ka kyaleni inje inyi aikina”…yana girgiza kai yace”no..mu cigaba da zama a haka”…tace”to abincin fa”…yace”a waje zamuyi dinner yau”…ta dago tana kallonshi da alaman tambaya…shi Kuma ya saketa yana cewa”kije ki shirya we are going out”..tace”ohk”snn ta haura sama don shiryawa..shima ya mike don yaje ya shirya.

A gurguje Layla ta dauko wani well ironed abaya dinta pusher pink..ta cire kayan jikinta snn tasa abayan..dama already tayi wanka..ta karasa gaban mirror tareda applying very simple mk up dinta as usual..ta gyra gashinta snn ta dauko veil din abayan tayi rolling dashi…ta feshe jikinta da perfumes..sai tai tsaye tana kallon kanta..tayi kyau ne ba kadan ba..cikin ranta tana addu’a Allah yasa bazaice sai ta dauko hijab ba..ta dauki phone dinta dake kan bedside drawer snn ta nufi dakinshi…daidai shiganta shi Kuma ya fito daga wanka..Yana daure da towle a kugunshi…ta juya a rikice zata bar dakin yai azaman kamota snn ya kulle kofan da key…ya juyota suna facing juna yace”Ina Kuma zakije”…idanunta rufe tace”inaso in baka space ne ka gama shiryawa”…yace”ai bance maki ina bukatar space dinba..so sit down and wait for me right here”…ta marairaice murya..Kuma har yanxu bata bude ido ba tace”daddy don girman Allah kayi hakuri..ni ban karasa shiryawa bafa”…Taheer bai ce daita komai ba ya isa gaban mirror…bayan ya gama tsane ruwan jikinshi ya shiga shafa mai..yanayi yana kallonta ta mirror..Yana gamawa ya nufi closet ya dauko kayan da zaisa..yau ko bathroom din bai shiga ba..a nn ya sa kayanshi.. ita kuma tana zaune har yanxu idanunta a rufe…Saida ys gama shirinshi tsaf snn ya kamata ya mikar da ita tsaye..a hankali ta shiga bude idanunta thinking har yanxu ba kaya a jikinshi sai Kuma taga yasa kayanshi complete…sai ta bude idanun nata tana mai murmushi…ya kama hanunta suka fita daga dakin bayan ya dau phone dinshi da Kuma car key… ya bude dakinta suka shiga ciki..ya zaunar da ita gefen gado snn ya nufi closet dinta ya bude..ya zaro wani gundumemen hijab light pink ya miko Mata..ta shiga bin hijabin da kallo idonta har ya ciko da hawaye tace”meye wnn”…yana murmushi ya kamata ya mikar tsaye..ya zare rolling din da tayi da veil dinta tareda zura Mata hijab din a jikinta…yana kallonta from head to toe yace”perfect..yanxu ma kinfi yin kyau”…kawai sai ta fashe da kuka tareda komawa ta zauna kan gadon…Taheer ya wara ido yana kallonta.. shima ya zauna kusa da ita da sauri yana cewa”menene Kuma baby..hijab din ne bakiso?..”yana rufe baki tace”Allah bazan fita da wnn zumbululun hijabin ba..kalleni fa kmr matar imam wlh saidai in fasa fitan amma bazanje ko Ina da wnn katoton abun ba”…dariya maganganun ta sukaso bashi amma ya gimtse…ya kamata suka isa gaban mirror yana kallonta yace”yanxu meye laifin hijabin nn baby..kinfi so kiyita fita anyhow..maza suyita kallonki suna cewa suna sonki koh”…gabanta taji ya bada sautin dammm..badai yasan mgnr AY Gambo ba…ta dan kalleshi tana goge hawayen idonta tace”to na fasa zuwa unguwan..kaje Kai kadai abunka nidai bazanje da wnn abun ba”…ta karasa mgnr tana nuna hijab din dake jikinta…yai shiru kawai yana kallonta..shi harga Allah baiso wani ya kalleta ba tareda hijab din bane…yasan maza nason mace mai kyau..Layla Kuma tanada kyau..kyau mai daukan hankalin maza ma kuwa..amma ita gani take kmr yana takurata ne…Saida ya sauke ajiyar zuciya snn ya sake komawa closet dinta..ya lalabo wani hijab din blue..Wanda bai Kai wancan girma ba snn ya dawo inda take…a hankali ya cire wancan daga jikin nata snn yasa Mata karamin daya dauko…sai ta juyo tana kallonshi tace”daddy wai meyasa dole sai hijab zansa..dagani sai kai fa zamu fita..ba Wanda zai kalleni yace zai kulani tunda am with you”…tana turo baki ta karasa mgnr…shi kuma ya kama hanunta ya rike..Yana kallon kyakyawar fuskanta yace”idan sbd kina tareda ni bazaa zo ayi maki mgn ba..amma kinsan bamu isa mu hana mutane kallonki ba koh..inda zamuje wurine da babu kalan mutanen sa basu zuwa..most of them maza ne..baby kinaso in barki ki tafi da mayafi yanda zasuji dadin kallan min ke knn”..itadai shiru tayi tana kallonshi..shi Kuma ya saki murmushi yana girgiza kai yace”Allah kadai yasan irin kishin da nake dashi a kanki baby..ni kadai nasan yanda nakeji duk lokacinda kika fita ba tareda kin suturce jikinki gaba daya ba..kiyi hakuri mu tafi a hakan kinji..kinga wnn ai baikai wancan girma ba”…ba yanda ta iya haka ta yadda suka tafi a hakan..cikin ranta ko sai ayyana yanda zaiyi duk ranan da ya san wani lecturer dinsu na sonta har yana kiranta office dinshi…”Allah ya kiyaye bacin rana”..tunaninta a zuci tayi mgnr batasan ya fito fili ba..Taheer dake driving yadan dubeta yace”Allah ya kiyaye bacin rana Kuma..what do you mean?..”da sauri tace”no it’s nothing daddy..zancen zuciya ne ya fito fili”…Taheer yai shiru bai sake tanka Mata ba..amma cikin ranshi yana tunanin wace rana ce wnn da take addu’an Allah ya kiyaye bacinta?

Washegari Layla ji tayi bata son zuwa makaranta don bata san kuma dame AY Gambo zaizo yau ba..so she decides tayi zamanta a gida kawai..in yaso duk abinda sukayi zata bama daddy in ya dawo ya koya Mata..

Bayan sun gama breakfast tace mai”daddy nifa yau bazanje school ba”..Yana dubanta da mamaki yace”why”..tana turo baki tace”Allah daddy na gaji da lectures din nn ne kullum ba hutu..shine nayi deciding yau in zauna a gida kawai in huta”…tana rufe baki yace”hakan bazai yiwu ba baby..ba haka akema karatu ba..idan kikace zaki fara fashi tun yanxu Kuma ai sai ki samu matsala”…ta sake rausaya Kai tace”daddy plss mana..ba wani abun fa akeyi ba mostly revision ne tunda mun kusa fara exams”…Yana girgiza kai yace”ban yadda ba baby..jeki dauko hijab dinki mu tafi don’t waste my time”…ta mike tareda haurawa don dauko hijab din ba don ta so ba..Allah ya sani ita haduwa da AY Gambo ne batasonyi…

Tana saukowa suka tafi..ko a hanya tayi shiru tana tunane tunane…Saida suka isa school din nasu kafin ta fita yace”ki fadamin idan wani abun ke damunki”…ta dubeshi da sauri..tana kakalo murmushi tace”Allah ba komai fa daddy..na fada maka gajiya nayi kawai”.. ya daga Kai kawai..Yana kallonta har ta fita daga motan ta tafi..cikin ranshi ko sam bai yadda da abunda ta fada ba..yasan dole akwai abunda take boye mai amma menene wnn abun?

Yau dai har suka gama lectures dinsu kaff bai kirata ba..hakan ba karamin faranta Mata rai yayi ba..a tunaninta ya hakura ne tunda yau bai nemeta ba…
Tana masallaci ta idar da sallhan asr dayake yau Hanna da wuri ta tafi gida batajin dadi.. wayanta ya shiga ringing..ta zaro wayan daga jaka tana kallon me Kiran..it’s unknown number..har ya gama ringing dinshi bata dauka ba..don tsoro takeji..ta mike zata fita daga masallacin wayan ya sake daukan ruri..Saida ta fita waje snn tayi picking..tayi shiru tana jiran ayi mgn amma sai taji tsitt..sun dauki kusan 5 mins a haka ba Wanda yai mgn..tana kokarin hanging call din taji ance”don’t hang the call pls”…ta zaro idanuwa tana jin abunda ya fada..ko baa fada mata ba tasan it’s him..ta gane voice dinshi…kmr zatasa kuka tace”na shiga uku..waya baka number na Kuma”…tana jin sautin murmushin daya saki…a nutse yace Mata”dama inada number dinki ai”..yana rufe baki tace”and why did you call me..meyasa zaka kirani fisabilillahi”…a hankali yace”sbd inaso inji muryanki..yau duk ban ganki ba Kuma nayi hakan ne sbd banson bacin ranki..na kira Kuma ko gaisawa baki bari munyi ba zaki fara complain”…har ta fara hawaye tace”ai dole inyi complain..don Allah ka rabu dani..ka fita rayuwata..kar ka sake kirana na rokeka”…tana gama fadan haka ta katse Kiran…ta samu wuri ta zauna tayi blocking number din nashi..yanda ko zai shekara yana Kira bazai shigo ba…ita tanata murna ya hakura ashe akwai abunda ya taka…tana gama abinda zatayi ta mike ta bar wurin…daidai lokacin Kuma Taheer yazo daukanta..so basu bata wani lokaci ba suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button