Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Karfe 3 yayi ma Taheer a airport…jirginsu umma na sauka ya dauketa suka tafi gida…tun a hanya umma ke tambayan meke damunshi amma amsa daya yake bata shine ba komai…gaba daya umma binshi da kallo takeyi don tasan karya yake yace mata ba abinda ke damunshi…har suka isa gida bata sake tambayanshi ba…ya bude mota ya fito bayan yayi parking itama ta fito…snn ya dauki kayanta suka shiga ciki…ummi da Layla na zaune a parlor…itama umma ta zauna suka shiga gaisawa da ummi…shi Kuma Taheer ya Kai Mata kayan daki Yana Shirin fita a parlon umma tace mai”zo nan Taheer…ai bamu gama mgnr da mukeyi ba”…ya dan rausaya Kai snn yace”umma to ki fara huta gajiya anjima sai muyi mgnr”…tun bai rufe bakiba umma ta mike tana fadin”nida ba mota na biyo ba ai bana tareda wani gajiya…sbd haka ka wuce muje kawai”..Taheer ba don yaso ba ya bita zuwa dakinta…ummi ta bisu da kallo cikin ranta tana addu’an Allah sa Taheer ya fadama umma damuwar shi…Sam batajin dadin ganinshi haka.

Suna shiga dakin umma dake nan fess kmr akwai mutum a ciki…umma ta zauna gefen gado snn tace mai ya zauna shima…ba musu ya zauna…idanunshi a kasa yaji umma tace”yau bazaka bar dakin nan ba saika fadamin mene damuwarka”…da sauri ya dago yana kallon umma snn yace”don Allah umma kiyi hakuri…wlh bazan iya fada ba”…”sbd bani na haifeka ba”.. umma ta fada idonta a kanshi…da sauri ya shiga girgiza kai sai Kuma ya fara hawaye a raunane yace”umma wlh auren nan ne banaso…don Allah kice ma ummi tayi hakuri ta karamin lokaci zanyi auren amma ba yanxu ba”…shiru kawai umma tayi tana kallonshi…yanxu Kam ta fara yadda da mgnr ummi da take cewa Taheer baida lfy…itama ta tabbatar baida lfy din…inba hakaba ya matured namiji kmr shi zaina kuka kawai sbd baison yin aure…Allah ya taimaka ta taho da magungunan da ummi tace a karbo mai…idan yayi amfani dasu da izinin Allah zai samu lfy…shiko Taheer jin umma tayi shiru ya share hawayen da yake snn yace”kinji umma ki taimakamin don Allah”…a hankali umma ta kalleshi snn tace”shknn Taheer zanyi mgn da ita…amma sai ka Dena wnn damuwan snn ka ringa cin abinci…banason ganin wnn ramar…da sauri ya shiga gyada Kai yace zanyi umma…zanyi…just talk to her pls”…umma tace to shknn yanxu kaje in anjima ka dawo akwai abunda zan baka…ya mike tsaye yana goge face dinshi yace”zanzo InshaAllah umma…I love you”.. umma tamai murmushi itama tace”I love u too my son”…tana kallonshi har ya fice daga dakin.

Kmr yanda yayi ma umma alkawari ya dawo bayan sallahn ishaa…suna dakin ummi zaune suna aikin lissafin kayan lefe da suka fara hadawa…ya Kai dubanshi ga Layla dake kwance can karshen gado waya kare a kunnenta tana mgn kasa kasa…ko baa fada ba yasan da Usman take waya…wani abu yaji ya taso ya tokare mai a wuya…sai Kuma ya dauke kanshi a kanta snn ya karasa ya zauna kusada umma yace”umma gani na dawo”…umma ta ajiye pen and paper dake hanunta tace”yawwa dan albarka…tasa hannu ta dakko wani leda a bayanta snn ta Mika mai tace ga wnn…bai musu ba ya amsa Yana kallonta don bai fahimci menene ba…umma ta dubi Layla tace”ke Layla tashi ki koma dakinki kiyi wayan nn…ko kunyarmu bakiji tun dazu kin zauna kina waya a gabanmu…a hankali Layla ta sauko daga gado zata fita…har taje bakin kofa ta fita bata lurada Taheer ba…wani malolo ya sakejin ya taso mai amma yai kokarin dannewa…umma na fuskantarshi bayan Layla ta fita tace”magunguna ne gasu nan na taho maka dasu…akwai bayanin yanda ake amfani dasu…kowanne an rubuta a jikinshi…sai ka fara sha daga yau snn kullum ka tabbata kasha don baa son tsallake kwanaki…cikeda mamaki Taheer ya bude ledan tareda dauko gora daya na maganin ya shiga karantawa…Saida ya gama ya dago Kai Yana kallon umma…ranshi ba karamin baci yayi ba…wato har yanxu kallon mara lfy suke mai knn… zaa wani kwaso magunguna a bashi yasha…duk kallon unable man sukeyi mai knn…kmr zaiyi mgn Kuma sai ya fasa…ya maida maganin ciki snn ya mike kawai ya fice daga dakin…cikin ranshi yake fadin”wai ni mutanen nn sukema kallon incomplete man…ni Taheer sukema kallon unable man…well ku bani auren ‘yarku mana ku gani…anan zaku tabbatar da cewa ni lafiyayye ne.????

A parlor ya tadda Layla…har yanxu Kuma bata gama wayan ba…tana ganinshi tai saurin ajiye wayan tace”laa daddy dama kana ciki wai?…wlh ban kula dakai ba lokacin da na fito”…Taheer bai tanka ta ba ya wuce fuskan nn a tamke…a ranshi yake cewa”Ina Zaki lura dani dama tunda kina soyayya.

Mum Ashraf ✨

????Dr.TAHEER????

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

This whole page is dedicated to my Wattpad people????you people are really amazing..thank u all for loving and reading Dr.TAHEER..ur comments are really encouraging me..so keep it up..Ummu Ashraf loves u sosae♥️????

16

Washegari umma ta tura Layla dakin Taheer..ganin har wajen 11 bai fito ba..tace aje a gano ko lfy..Layla na shiga Kai tsaye dama bedroom dinshi ta nufa…yana kwance kan bed…ya kudundune cikin bargo..sai rawan sanyi yake…da gudu Layla ta haura kan gadon ta yaye bargon tana kallonshi tace”innalillahi wainna ilaihi rajiun..daddy meke damunka”…a hankali Taheer ya shiga kokarin mikewa zaune amma ya kasa…sai kawai ya koma tareda sake kwanciya…Layla ta fashe da wani matsanancin kuka tace”na shiga uku…daddy wai meke damunka haka”sai Kuma ta shiga kokarin sauka daga kan gadon tace”Bari inje in Kira umma”…tun kafin ta sauka Taheer yai karfin halin mikewa ya dawo da ita kusa dashi…ya rike hanunta gam cikin nashi…yanason yin mgn Amma ya kasa…a hankali ya maida idonshi ya lumshe kawai sai ya fara hawaye…baison yin kuka gaban Layla..amma he couldn’t stop himself…hawaye yakeyi sosae kmr karamin yaro…Layla ba karamin tashin hankali ta shiga ba..ganin yanda yake hawaye…ta dora duka hannayenta a Kai ta sake rushewa da uban kuka tace”na shiga uku na lalace…kuka fa kakeyi daddy..don girman Allah ka fadamin mene matsalanka…meke damunka haka da har zai saka kuka daddy.. pls tell me”…a hankali Taheer ya bude idanunshi yana kallonta..kuka takeyi da gasken gaske…hakan Kuma ba karamin hurting dinshi keyi ba…ya gwammace yaita zama cikin yanayin da yake ciki yanxu..da dai tayita kuka haka…da kyar ya tattaro sauran energy dinshi ya janyota jikinshi..ta rungumeshi tsam tana ci gaba da kukanta…a hankali yasa hannayenshi ya rungumeta shima…sun dauki kusan 3 mins a haka kafin ta dago..idanunta a kanshi still bata dena hawayeba..kafin tayi mgn Taheer yai cupping fuskanta da hannunshi yace”banason kukan nn baby…I’ve told you babu abinda ke damuna…but definitely idan zaki cigaba da wnn kukan komai ma na iya faruwa Dani..you have no idea yanda zuciyata keyi idan kina kukan nan..sai ya saki face dinta ya kama hannayenta gam yace”ki taimaka min ki dena domin Allah baby…bazan iya daukaba wlh…abubuwan zasumin yawa plss”…da sauri Layla ta shiga goge tears dinta tana girgiza Kai tace”na dena kukan daddy…bazan karaba InshaAllah…but daddy don Allah mene ke damunka…ko ince umma ta kira doctor ya dubaka…or better still in Kira maka dr.salees yazo ya dubaka…inada number dinshi ay”…lokaci daya Taheer ya hade rai jin abinda tace…ya kalleta a kausashe yace”wane dr.salees?…Layla tadan buda ido snn tace”dr.salees na clinic dinka mana daddy… friend Dina ne a…bata karasaba yasa hannu ya buge Mata bakin…yana Mata mugun kallo yace”don’t you dare..kar ki kuskura ki sake cemin wani namiji is your friend…Layla na shafa bakin daya buga da hanunta kmr zatayi kuka tace”to kayi hakuri daddy”…Saida ya koma ya sake kwanciya snn Mata”you can leave”…ta kamo hanunshi tace”daddy nace kayi hakuri fa”…idonshi a kulle yace”naji…ki tashi ki tafi baby I want to sleep”…ganin yanda yai mgnr rai a bace ta sauka a gadon zata fita..ta sake juyowa tana kallonshi kafin tayi mgn yace”baby leave..don’t let me repeat my tself”…bata sake yunkurin mgn ba ta fice daga dakin… yanajin ta fita ya mike da kyar ya sama kofan key snn ya koma ya sake kwanciya…yasan for sure zata fada a halinda taganshi and ko ummi batazoba yasan umma sai tazo…shi Kuma bai shirya amsa tambayoyin da zasu fito a bakin umma ba so it’s better ya rufe kofanshi kawai…he needs to be alone and think of a way out of this mess.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button