Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Dr.TAHEER HAUSA NOVEL

Washegari karfe 8 suka dauki hanya…wnn karon a mota suka tafi…ko a hanya ba Wanda ke cewa wani abu a cikinsu…Taheer na driving yana duban Layla data kudundune kanta wuri daya…har yanxu bata bar hawaye ba…”so she loves him this much”…ya fada a zuciyarshi…a wani bangaren Kuma yanajin dadin daga biki da ummi tace zaayi.

Sai yamma suka isa Dutse…zuwa lokacin an rigada ankai Usman gidanshi na gaskiya (Allah ka kyautata mana makwancinmu na gsky????????)

Mutane nata zuwa gaisuwa…yayinda duk Wanda yaga Layla sai ta bashi tausayi sbd yanda ta koma…kallo daya zaka Mata kasan mutuwar ba karamin girgizata yai ba.

Kmr yanda ummi ta fada…sunyi mgn da uncle din Taheer ta Kuma sanar dashi tanaso a Dan daga biki…da farko bai amince ba…sai daya baya yace shknn zaiyi mgn da magabatan Sameera ko one week sai a Kara.

Ranan da akai sadakan uku suka koma kano…gidan umma suka sauka…Saida suka koma Dutse ranan bakwai snn suka koma Abuja.
Zuwa yanxu Layla ta Dan fara warewa amma har yanxu walwalarta bata dawo daidai ba kmr nada.

A bangaren Taheer kuwa ga koshi ga kwanan yunwa…ga dai Usman din dayake gani kmr shi zai rabashi da Layla ya rasu…ga kuma shi bazai iya bude baki ya furta Yana sonta ba…gaba daya he’s confused…ga aurenshi dake Kara matsowa…har yanxu Kuma baiji yanason Sameeran ba.

Yau Tuesday Taheer tunda yazo office bai aikata komai ba…kmr yanda biki ke Kara matsowa haka matsalolinshi ke karuwa…shi kadai yasan yanda yake jin jikinshi these days…kullum da fever yake kwana ga ciwon Kai mai zafi ko baccin kirki rabon da yayi har ya manta…ya tabbata yanzu idan aka gwada BPnshi zai iya haura 200…damuwa har yawa suke mai ya rasa da wanne ma ya kamata yaji…yana kwance bedroom din dake office dinshi yaji ana knocking ta waje…ya danja tsaki snn ya mike ya fito…ya riga ya sanar da nurses kan bazai iya duba kowa ba yau and Dr.Eze is around…so baisan wayake mai knocking ba kuma yanxu…yana bude kofan ya juya ya koma ciki ba tareda ya tsaya ya ga wanda yai knocking din ba…a hankali Layla ta karaso ciki tareda ajiye basket din dake hanunta…tai shiru kawai tana kallonshi…duk ya rame…haka nan takejin tausayinshi…”Daddy”..ta fada a hankali…da sauri ya bude idanunshi dake lumshe ya azasu a kanta…sai Kuma ya sake maida idon ya rufe ba tareda yace kala ba…Layla tayi dan yi murmushi snn ta karasa zuwa inda yake…kan table din gabanshi ta hau ta zauna tana facing dinshi tace”daddy”…shiru ya sakeyi ba amsa…ta kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”daddy plss…talk to me mana”…har yanxu idon nashi a rufe yace”who are you?…ta dan wara ido sai Kuma ta saki murmushi tace”it’s me…your baby”…ya dan tabe baki snn ya shiga girgiza Kai yace”No you are not…babyna dana sani ba haka take ba…my baby used to be happy and always smiling…so stop saying you are my baby cox you are not”…a hankali ta kamo hannayenshi ta rike snn tace”daddy mana…I’ve told you nice…ka bude idonka ka ganni”…ba musu ya bude idanun nashi ya dora a kanta.. yai cupping fuskanta yace”you’ve changed alot Layla…you are a Muslim so ya kamata kiyi accepting faith and move on… addu’anki kadai Usman ke bukata yanxu…not those tears”..ya karasa tareda pointing idanunta da har sun fara kwalla…ta dora hannayenta kan nashi tace”daddy kaima you’ve changed…Dan Allah daddy ka fadamin abunda ke damunka…nasan for sure akwai abunda kake boyewa”… murmushin takaici ya saki snn yace”somethings are better left unsaid baby…ba komai ya kamata ake fada ba”…shiru tai tana kallonshi sai Kuma ta fara hawaye tace”nidai dn Allah daddy ka fadamin…I promise bazan fadama kowaba…I don’t want to be seeing you like this plss”…ta sauri ya fara girgiza kai yace”baby kuka Kuma…stop crying plss…tashi muje ki zubamin abincin”ya fada don ta Dena kukan…Saida ta gama don kanta ta share hawayenta snn ta sauka ta karasa inda ta ajiye abincin…ta zuba a plate tareda Dora mai kan table…duk yana kallon yanda take turo baki yace”fushin na meye Kuma baby”…murguda baki tayi snn tace”nidai daddy kar ka sake cemin Layla plss…ko dadima baiyi ba”…ya Dan wara ido yana fara cin abincin yace”Laylan ne ba dadi Kuma”..da sauri tace”No a bakinka ba dadi…just call me baby kmr yanda kake fada…duk kace Maryam ko Layla Allah bana jin dadi”…dariya sosae Taheer ya saki kawai yana kallonta…wai ba dadi…Saida ya gama dariyan yace”to naji ban sake fada tunda bakiso kinji…now taso muci abincin”…ba musu ta mike zuwa inda yake suka shiga cin abincin tare…wani irin farin ciki Taheer ya samu kanshi ciki…ga dai damuwan nashi na nan cikin ranshi but he feel relieved just by talking to her…inama zasu cigaba da kasancewa a haka har abada amma inaa…

Basu suka bar clinic din ba sai after five…basu dade da komawa gidaba akai magrib…ya shigo da sallam parlon waya kare a kunnenshi…umma ce kadai zaune a parlon tana kallonshi…Saida ya gama wayan snn ya gaisa da umma…tana kallonshi da kyau tace”yau ka iya cin abincin knn”…ba tareda ya kawo komai a ranshi ba yace”yeah ai tareda baby mukaci”…umma tai shiru tana kallonshi…shi Kuma hankalinshi na kan wayanshi…Layla ta shigo parlon ta zauna kusa dashi tana nuna mai hanunta tace”daddy kaga wnn zoben daya Usman ya fara bani…ban San Ina son ring dinba sai yanxu da Ya Usman ya mutu… at least zan ringa tunawa dashi snn inyi mai addu’a…Allah ya Kai haske kabarinshi…duk wani walwala dayai saura a fuskan Taheer nan take ya 6ace 6att…bai San time din da ya daure fuska tamau kmr bai San me ake nufi da dariya ba…ya kama hanun nata ya rike…har ya kai hanu zai cire ring din sai Kuma ya tsaya cakk…kmr Wanda ya tuna da wani abun…a hankali ya kewayo da idonshi kan umma yaga idanunta kyam a kansu…da sauri ya saki hanun nata ya shiga ‘yan kame kame…umma kallonshi kawai take batace komai ba…daya ga kmr kallon tuhuma take mai sai ya mike da sauri ya fita daga dakin har Yana yin tuntube????

Part dinshi ya nufa Kai tsaye ya shiga tareda murzama kofan key ta ciki…nan bakin kofan ya durkushe yana salati… zuciyarshi sai bugawa take fat fat fat…yasa hannayenshi ya dafe Kai dasu…Allah dai yasa umma bata gano asirin zuciyarshi ba…bai San meya kaishi ga aikata hakan ba…bai San wane irin kishi yake dashi a kan yarinyar nn ba…”Allah ka rufamin asiri…Allah kar ka bari ta gane abinda na dade Ina boyewa…rabbi ka taimakamin plsss”…ya karasa mgnr hawaye na sauka kan kyakyawar fuskarshi…bai San lokacinda ya zama mai saurin kuka haka ba…da ba haka yake ba…it’s very hardly kaga hawayenshi amma yanxu a kan Layla abu karami sai yaji hawaye nabin fuskanshi…

Ita kuwa umma binshi tayi da kallo har ya fice snn ta mike a hankali zuwa dakinta…Layla na kokarin mikewa Nafisa ta shigo parlon tana dubanta tace”Ina daddyn naki ya tafi kuma”.. tace”yanxun nn ya fita Mami…Bari inje in kiras…bata karasa ba Nafisa tace”ba saikinje ba Bari in kirashi a waya”…Tai dialing number tasa a kunne…har ta gama ringing bai daukaba sai ta sake Kira…wayan na aljihunshi…da kyar ya zarota yana kallon me kiran…kmr bazai dauka ba sai Kuma yai picking tareda daidaita muryarshi yace”hello”…a daya bangaren Nafisa tace”bro kayi nisa ne?…yace”No Ina gida…what’s wrong”…tace”don Allah so nake if you are less busy ka kaimu shopping in anjima…akwai abubuwan da nace zan siya idan munzo nan Kuma ban samu na siyaba sbd rasuwar nn…gashi time ya fara kurewa…tun dazu naso fita ummi tace I should wait for you”…Taheer da ko kadan baiso hakan ba yace”ba damuwa…ana idar da sallah sai mu tafi”…”to shknn thank u so much bro…bari mu fara shiryawa”yace alright snn ya ajiye wayan.
Nafisa na gama wayan ta koma ciki ta sanar dasu ummi zasu fita yanzu…suma yaran duk tace su shirya snn ta tafi don shirywan itama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94Next page

Leave a Reply

Back to top button